BABI NA TAKWAS
by @billysfari
GS 8.
Da kyar Irfaan ya iya buɗe idanunsa yana kallan gefe, shi kam shaf ya manta da zasu taho bai yi tunanin ɗauro mata hijab ba akai kawai suka taho, asali ma shi bai wani kula da yanayin da take ba sai yanzu, kuma yanzun ma da ace babu wani a kusa da ita ya tabbatar ba wani lura zai yi ba. Ya saba ganinta cikin riga da zani na atamfa rigar kuma burmemiya ce yanzu kuma wata yaloluwar t-shirts ce hakan yasa abubuwan nata suka kusa tsone musu idanuwa lokaci ɗaya duk kuwa da cewa ba wani girma ne dasu ba kasancewar babu kwanciyar hankalin da zata samu natsuwar da har zasu iya taso sosai, ɗan tsaki ya ja tare da sake ɗauke kansa gefe. Shi kuwa Zain saboda yanayin aikinsu sun saba ganin ire-iren haka ga patient sai kawai ya maze tare da buɗe idanunsa yana kallan fuskar Jauhar tare da don kaucewa kallonsa ga kirjin nata, amma duk da haka da yake ido gulmammi ne sai da yaji sun sake sauka wajen, cikin sauri ya sake kawar da idanuwan nasa daga wajan yana cewa.
"Zo muje naji meke damunki ko akwai taimakon da za'a iya yimaki kafin Dr ya ƙaraso." Ya faɗa yana juyawa tare da shiga wani office dake nan kusa dasu. Ɗan ƙaramin tsaki Irfaan yaja ganin Jauhar ɗin ta mike tabi bayansa sai faman durƙushewa take alamar tana jin jiki sosai. Kallon inda su Hajja Maimoon suke tsaye ya yi cikin sa'a suka haɗa ido da Suhana ya kirata da hannunsa. Kamar ba zataje ba sai ta daure taje lokacin har Jauhar ta shiga cikin office ɗin. Hannun Suhana yaja suka zauna akan bencin da Jauhar ta tashi ya kalleta sosai sai kawai tasha jinin jikinta cewa akwai abinda tayi, mamakin irin kallan da yake binta dashi takeyi kafin tace.
"Uncle menene?" Irfaan ya sauke numfashi tare da lasar lips ɗinsa da suka soma bushewa yace.
"Yanzu abinda kukayi ɗazun kun kyauta? A ina ko koyo zuciyar rashin son taimako? Allah yaji ƙan Aunty yai mata rahama sam halinta ba haka yake ba" Jikin Suhana ne yai sanyi jin abinda ya faɗa kafin ta amsa masa da.
"Amin Uncle." Tana sinne kai ƙasa, sake kallonta yai akaro na biyu tare da sauke numfashi yace.
"Amin ɗinki ba zatayi mata amfani ba Suhana, kawai ki amsa Mani tambayar da nayi maki." Duk da tasan akan Jauhar yake zance da suka nuna ko oho da rashin son taimaka mata da zasu zo asibiti, hakan bi hanata yin tunanin me yasa zai kawo zancen mahaifiyarsu acikin zancen ba? hawaye taji ya tarar mata acikin idanuwa ta ɗago kai ta kalleshi tana cewa,
"Innalillahi saboda me zaka ce Amin ɗina ga mahaifiyata ba yada amfani Uncle? Wane laifi nayi ne?" Cike da damuwa dake kwance akan fuskarsa ya riƙo hannunta haɗe da cewa.
"Saboda baku da hali mai kyau dukkan ku Suhana. Gabaki ɗayan ku babu wanda yake faranta mata a nan duniya. Tana kwance a kabari abinda zai sanya ta farin ciki baifi a tashe ta ace tashi kiga abinda ƴaƴanki keyi aduniya mai kyau, amma na tabbata da wannan halin naku da kukeyi Suhana da akwai hanyar da Aunty zata fito ta gaya muku ku gyara da tayi, amma babu hanya sai dai kawai ta ganku ta kyale har zuwa lokacin da kukaje inda take." Hankalin Suhana ya fara tashi dan gabaki ɗaya taji cewa suna yin abinda bai kamata ba duk kuwa da cewar har yanzu bata tunanin abinda sukayi ɗazu ɗin laifine. A gigice take kallansa tana jin tamkar ta fashe da kuka take cewa.
"Dan Allah Uncle ka sanar dani me mukayi da har mahaifiyar mu baza tayi farin ciki damu ba?" Ganin anzo gabar da yake jira yasan ya shi cewa.
"Wulakanta ɗan Adam da nuna baya da daraja ta kowace fuska, wato Suhana Allah shi yasan dalilin da ya yo ɗan adam a mafifita darajar duka al'umma. Me yasa kuke yiwa Jauhar haka? Kuna tunanin da tazo aiki gidan ku hakan yana nufin Allah baya sonta ne? Please Suhana kuyi abinda Allah zai baku lada, kinga kece mai sauki a cikinsu, kece muke ganin kamar zaki ɗakko dabi'un mahaifiyarki amma wani lokacin sai ki karkace ki koma irin su, dan Allah ki riƙa tausayin Jauhar, yarinya ce kamarku dake bukatar kulawa irinta uwa da uba kamar yadda kuke samu amma tarasa saboda haka Allah ya tsaro rayuwarta zata kasance mata." Take hawaye suka fara zubowa daga fuskarta tasa hannu tana sharewa, dama duk cikin su itace mai sauki kuma batada weak point aduniya kamar na zancen mahaifiyarsu, dan haka maganar Irfaan ba ƙaramin tasiri tayi a zuciyarta ba. Murya a sanyaye take kallonsa haɗe da cewa.
"Insha Allah Uncle na bari kuma daga yau na dena takurawa Jauhar saboda bana so Mami taji haushinmu idan taga abinda mukeyi marasa kyau". Cikin ƙarfafa guiwa ya sakar mata murmushi yana cewa.
"Insha Allah zatayi farin ciki dake Suhana duniya da lahira idan kikayi kokarin gyarawa. Kinga yanzu tana ciki ita kaɗai sai nurse ga jiki tana ji, ki shiga ko zata bukaci taimakonki kin ji ko?." Ɗaya masa kai tayi haɗe da miƙewa a hankali ta nufi cikin office ɗin jiki duk babu daɗi. Zaune ta tarar da Jauhar ɗin akan kujera ta ɗora kanta saman table ɗin da Zain ke rubutu bayan ya gama gwada BP ɗinta da kuma yi mata tambayoyi akan abubuwan da takeji. Shigowar ta Suhana yasa shi ɗan sakin murmushi, duk da shi ɗin ba mai yawan hayaniya bane, zamowarsa nurse kuma sai ya sake sashi kamewa musamman idan yana kan aiki kasancewar dole sai da natsuwa a aikin nasu, duk da wani lokacin yakan zama mutum mai sakin fuska da kuma barkwanci saboda ya ƙarfafawa marasa lafiyan da yake kulawa dasu guiwa.
"Ya akai? Ko so kike kiji abinda yake damun ƙawata?" Mamaki ya kama Suhana ta ɗan zaro idanuwa tana kallonsa tace,
"Ƙawarka?" Yace,
"Eh mana muna sirri da ita kika shigo ko tare kuke?" Ya tambaya yana tsare Suhana da ido. Lanƙwasa idanuwan nata tayi kafin tace
"Dama kasanta ne?" Yace,
"Eh yau muka ƙulla ƙawancen da ita gashi har allura ma zan yi mata." Jauhar dake jin abinda suke cewa ta ɗago da kyar tare da zuba masa ido jin yace wai ita ƙawarsa ce. Gira ɗaya ya ɗage mata hakan yasa tayi saurin juyawa ta kalli Suhana taga ko ta ganshi. Suhana ce tayi magana cikin kulawar da ta bawa Jauhar ɗin mamaki take cewa.
"Sannu Jauhar kin ji abokin naki wai allura zai yimaki, meke damunki ne halan?" Mamaki yai bala'in ɗaure ta dan haka da kyar ta iya girgiza mata kai tana cewa.
"Ba komai." Zain dake jinsu yana miƙewa tsaye yake cewa.
"A'a fa ƙawata jininki ya hau sosai kuma kin ƙi sanar dani meke cikin ranki taya zaki ce babu komai? Please ko zaki fadawa Yayar mu sai ta faɗa mani". Ya faɗa yana maida kallonsa ga Suhana, kafin ta bashi amsa ya nuna Jauhar da hannu yana cewa Suhana.
"Ki ɗan taimaka ki yafa mata ɗan kwalinki tunda bata sako hijab ba tana ƴan mata da ita." Murmushi Suhana tayi tare da zaro ɗankwalin material ɗin jikin nata ta ɗorawa Jauhar akan kafaɗunta. Kallansu ya yi tare da faɗin.
"Bari naje sai kun jira likita yazo muji wane irin taimako zai bata." Yaƙare zancen tare da ficewa tun kafin su bashi amsa. Kai tsaye Zain ya dinga duba mararsa lafiyan da aka kawo har yazo kan Jannat wacce ya tarar da ita kwance a kan gado Hajja Maimoon tana faman shafa bayanta sai wani sake narkewa takeyi. Inda take ya ƙarasa yana sargafe hannayensa a kirjinsa. Jannat ta ɗago kyawawan idanunta ta zuba akan na Zain, ganin yadda yake kare mata kallo ne yasa ta turo baki tana cewa.
"Mommy kin ganshi ko?" Da sauri Zain ya ware ido yana cewa.
"Good girl, dama so nake naji kina magana ne ko bebiya ce sai na san ta inda zan fara dubaki. Da alama ma lafiyarki ƙalau kawai raki ne irin naki dan ki tayarwa dasu Momynki hankali ko?" Zabga masa harara Jannat tayi bata wani damu da girmansa ba tana sake shagwaɓewa cikin jikin Mommy take cewa,
"Mommy ki masa magana wai cewa yai ƙarya nakeyi." Hajja Maimoon ta kamo hannayenta cike da kulawa tace,
"Rabu dashi tsokanarki yake yi shima kansa in yasan aikinsa to tabbas yasan bakida lafiya" Hajja Maimoon tayi maganar tana wani mammatsa hannun Jannat ɗin a cikin nata. Cikin rashin nuna damuwa da kalaman na Mommy Zain ya shiga duddubata ya yana sake cigaba da tsokanarta ita kuma tana yiwa Mommy ƙorafi da taɓara, a haka likita yazo Zain ya gaggabatar masa da abubuwan da ya yi wanda aka sakawa kowa cikin files ɗinsa dan shine on duty yau a emergency ɗin.
Yaso a fara duba Jauhar saboda tafi Jannat buƙatar kulawa amma yadda su Mommy suka tsare komai ya sanya sai da aka kira su Jannat likitan ya yi mata duk abinda ya kamata kafin aka kirawo Jauhar, tana isowa likitan dake rubuce-rubuce akan folder din tata ya ɗago kai don ganin kowaye saboda yadda yaji tsamin kayan dake jikinta ya cika musu hanci. Irfaan kuwa gabaki ɗaya ya fara jin haushin Zain ganin yadda yake ta yi musu wani irin faran-faran duk da ya lura da cewa hakan yake yiwa mararsa lafiyan dake wajen gabaɗaya, wanda cikin ƙanƙanin lokaci yaga sunyi wani irin sabo shida Jannat ta yadda komai zai ce sai yaji yace mata 'Mommy's daughter' Ita kuma yaji tace 'likita'. basu wani jima ba aka gama duba Jauhar da Jannat, inda Doctor Habu ya sanar dasu cewa a kula da Jauhar sosai dan a wannan stage ɗin tafi Jannat buƙatar taimako da kuma kulawarsu, ganinta a yanayi irin na ƴan aiki yasa shi sake cewa idan baza'a iya kula da ita ba to a kaita wajan iyayenta zama tafi samun kulawa a wajan su sosai. Da Jauhar taji abinda Doctor Habu yace ba ƙaramin daɗi taji ba dan ko babu komai tasan zata huta da wannan masifar ta cikin gidan Alhaji Sha'aban Sada. Nan likitan ya miƙo takardun magungunan da za'a siya masu daya rubuta Uncle Irfaan ya karɓa suka fice, Har sun kusa shiga mota Jannat ta kasa yin haƙuri tasan idan har suka bar asibitin nan zai yi wahala ta sake ganin Zain gashi sosai ya burgeta lokaci ɗaya saboda yadda yayita kanta da wasa tana dariya. Hannunta ta zare daga cikin na Mommy tace.
"Mommy please aron wayarki." Hajja Maimoon ta miƙa mata, cikin sauri Jannat ta juya tare da shigewa reciption tana wurga ido dan gano inda zata ganshi. Tsaye ta hangoshi gaban wata mata yana taɓa goshin yarinyar dake kan cinyar matar da alamar dubata yakeyi. Waya kawai yaga ana miƙo masa, kallan wayar ya yi kafin a hankali ya ɗora idanunsa akan wacce take miƙa masa ɗin. Murmushi yayi tare da miƙewa sosai yana kallon wayar yake faɗin.
"Mommy's daughter yae za'a yi? Duba maki wayr zanyi itama bata lafiya?" Dariya Jannat tayi kafin ta turo baki cike da salon rigima tace,
"Dama banda mutane har wayoyi kana iya dubasu in basa da lafiya?"
"Ban taɓa ba amma da alama rigimar Mommy's doughter zatasa nafara yau."
"Ni dai a'a i just need Your phone number please." Zaro idanuwa yai cike da mamakin rigimar Jannat yana naɗe hannayensa a kirji haɗe da lasar lips ɗinsa na ƙasa ba tare daya karbi wayar ba. Jannat ta sake shagwaɓewa kamar zatai kuka tace.
"Please take it mana kasa mani kada uncle yai mun fada." Jin abinda tafaɗa shima ga patient na jiransa ya sashi dan duƙowa saiti ita yana cewa,
"Wayar kice?".
"No ta Mommyna ce." Zain ya sake ware ido akaro na biyu yana miƙewa tsaye da ƙafafuwansa yake cewa.
"Toh ba ruwa na haka kawai Daddyn ki yaga sunan namiji a ciki, da alama so kike nayi kwanan police station Ko?" Sai da ta kuma turo baki wanda yasa Zain kai hannunsa kamar zai janyo mata shi sai kuma ya karkaɗa mata yatsunsa guda biyu yana cewa.
"Ba ruwa na." Haɗe da ƙoƙarin juyawa.
"Please dan Allah dan annabi kasaka min, kaga idan bani da lafiya kawai kiranka za'a yi aji ko kana asibitin." Lumshe ido ya yi yana jin girman Allah da ta roƙeshi ya tsaya masa a wuya, ya karɓi wayar tare da saka mata dama already taji yadda abokan aikinsa suke ta kiransa dan haka bata tambayi sunan ba ta juya tana saving fuskarta kunshe da farin ciki ba zaka taɓa cewa ita aka kawo ranga-ranga ba. Babu wanda ta kula kawai ta shiga motar ta zauna, wannan karon a can wajan glass suka bar Jauhar a cewar Suhalai iska zata fi ɗaukar warin da Jauhar ɗin keyi tana fitarwa waje ba sai sun shaƙeta ba.
"Ke kuma me kika koma yi ciki?" Irfaan ya jehowa Jannat tambayar ba tare da ya juya ya kalleta ba hankalinsa yana wajan tuƙi. Jannat dake karewa sunan Zain da ta gama saving kallo tayi murmushi kawai ba tare da ta bawa Irfaan amsa ba dan ita kanta ba ta san me zatace ba, kuma bata san dalilin da yasa taji nurse ɗin ya shiga ranta da wuri haka ba. Jauhar kuwa duk ta matsu suje gida zama tare da su a wannan yanayin yana sake ɗaga mata hankali saboda fargabar maganganun da suke jefa mata ƙasa-ƙasa dan ma Suhana bata cewa komai amma yadda take kauda kai zaka san cewa tsamin jikin Jauhar ɗin yana damunta. Suna zuwa kuwa ta ɓalle ƙofar ta fito tare da rakuɓewa tana jiran su wuce ciki sannan tabi bayan su.
Hannun Jannat Hajja Maimoon ta kama ba tare data kalli gefen da Jauhar take ba tana jin wani irin jiri na addabarta. Kallon su ta shiga yi tana jin kuka na shirin zuwa mata, ina ma ace itama za'a kaita inda za'a ji ƙanta a kula da ita a kuma yi jinyarta cikin kulawa. Sanin bata da wannan gatan ne yasa ta fara ɗaga ƙafa jin Suhana tana cewa tazo su shiga ciki. Har ta juya taji Irfaan ya kirata, ta juyo a hankali ba tare da ta kalleshi ba dan ba kaɗan ba takejin kunyarsa.
"Zanje na kawo miki magunguna sai ki samu kisha kinji ko?" Jauhar ta ɗaga kai alamar to sannan ta buɗe baki da kyar tace.
"Nagode Uncle." Tausayinta ya sake shigarsa yace.
"Ki samu ki kwanta saboda jininki ya dawo dai-dai. Please ki cire komai a ranki kiyi addu'a kinji ko?." Kanta kawai ta ɗaga amma ita bata ma san wace irin addu'a zatayi ba saboda ba wani koyar da ita aka yi ba ballantana ta dinga yiwa kanta. So yake ya tambayeta shin bata da bireziya ne da bata sakawa? Amma sai ya kasa saboda girman maganar gashi kuma baya son girmansa ya ɓare a wajan ta. Ko a hospital yaso yiwa Suhana maganar amma ya kasa. Har ta shiga ciki bai ɗauke ido akanta ba, yana son ya taimakawa Jauhar kota wani irin yanayi ne koda kuwa Hajja Maimoon zatayi masa sharrin da har ya koma ga Allah ba zai yi mutunci a idanun duniya ba. Yana fita daga gidan kai tsaye gidan su ya nufa ya ɗakko atm card ɗinsa ya fito, pharmacy ya wuce already Jannat tun a hospital aka siya mata nata magungunan, Jauhar ce Hajja Maimoon taki siyawa shi kuma bai fito da kuɗi ba. Yana siyo magungunan ya biya ta wani boutique ya siyo mata bra wacce bashi da masaniyar zatayi mata dai-dai ko zatayi mata yawa, kawai ya siyo mata ne gwara tasa akan ta dinga yawo a haka tana saka mutane cikin yanayin da sai sunyi shahada zasu iya rike kansu. Ya siya mata harda su pant da skirt underwear sai wasu riga da skirt kala ɗaya dan bai san awonta ba karya jidar mata kaya a samu matsala.
******
Jauhar na shiga cikin parlorn ta tarar Hajja Maimoon tana tsaye tana jiran shigowarta, tunda ta hangota taji kirjinta yana bugawa tasan kawai wani bala'in kecin matar tunda a iya saninta babu abinda tayi wanda zai sa ayi mata irin wannan jiran. Suhaila da Jannat suna kwance akan soofa Suhana ta shiga cikin ɗaki da alama ko tsayawa batayi a parlorn ba. Kanta ta sake sunkuyarwa tana jiran taji da wane bala'in za'a tare ita, cikin zuciyarta tace mutum bashi da lafiya amma matar nan ba zata ɗaga mata ƙafa ba taji da abinda yake damunta. Abinda yake bata haushi kuwa tamkar bata santa ba batasan wacece ita ba da ta wofintar da al'amarinta ta fifita wasu akanta wanda duk matsayin su a wajanta ai basu kaita ba, kuma tare aka gansu bare ace a gidan ta tarar da ita a matsayin mai aiki.
"Wato saboda nayi maganar ki fito min da gold ɗina shine dan bakin munafunci kika fara rashin lafiyar karya ko Jauhar? Toh bari kiji na gaya miki ko asibiti ne gabaki ɗaya a jikinki sai kin amayo min da abubuwana dan ba zakici banza ba. A iya zamana dake tun lokacin da aka liƙa min ke kika zame min jaraba na taɓa nuna miki yadda ake sata?" Jauhar ta shiga girgiza kai alamar a'a, hakan ya sake tunzura Hajja Maimoon ta ƙarasa inda take tsaye tare da shaƙo mata wuya tana cewa.
"Dan ubanki da ka nake miki magana da zaki dinga amsa min da kanki?" Jauhar da taji matsar tana shirin kaita ga mutuwa yasa ta fara ƙoƙarin kwacewa, jikinta babu karfi hakan yasa ta kasa har sai da Suhana ta taho da gudu wacce fitowarta kenan daga cikin ɗaki ta hango su. Da kyar ta iya kwace Jauhar daga hannun Mommyn tasu wacce takejin ko mutuwa Jauhar tayi ba zatayi nadama ko da na sani ba koda kuwa ace zata mutu a gidan gyaran hali ne.
"Na kusa sallamaki wallahi Jauhar, da kaina zanje wajan waɗanda suka liƙa minke su san yadda zasu yi dake ko kuwa aure ne suyi miki da ko uban waye nima na huta da kallonki da nakeyi kina manne dani ko na dena sakaki a cikin idanuwa na." Jauhar dake rakube a bayan Suhana tana jin duk kalaman da Hajja Maimoon ke gaya mata, ita da za'a kaita ɗin da taji daɗi koda auran ne ayi mata ko zata samu ƴancin kanta, amma zama tare da matar nan ba alkairi bane a tare da ita.
"Mommy dan Allah ki barta bata da lafiya fa." Suhana ta faɗa kamar zata yi kuka. Duk suka kalleta baki buɗe, bata damu da irin kallonta da sukeyi ba burinta kawai ta aikata abinda zai sa mahaifiyarsu ta samu sassauci a makwancin ta kamar yadda Uncle Irfaan ya tunatar da ita.
"Zoki wuce ki shirya mana breakfast." Cewar Hajja Maimoon tana dakawa Jauhar ɗin wata gigitacciyar tsawa. Jiki na rawa hankali a tashi zuciya a cunkushe Jauhar ta nufi kitchen tana share hawayen da yake yawo a kan fuskarta...
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye