BABI NA TARA
by @billysfari
GS. 9
Koda ta shiga kitchen ɗin rasa abinyi tayi dan gabaki ɗaya komai na cikin kwakwalwarta tsayawa ya yi cak na wucin gadi. Suhana ce ta shigo kitchen ɗin ita sai yanzu take lura da irin matsin da ake yiwa Jauhar a cikin gidan wanda tasan da mahaifiyarsu tana raye tabbas ba zata bari su dinga yin abunda suke yiwa yarinyar ba. A bayanta ta tsaya tare da yi mata magana cewa.
"Jauhar kije ɗaki kiyi wanka mana, bari na fara tayaki kafin ki dawo." Jauhar ta girgiza kai dan ba zata iya fita ba Mommy ta ganta tasan sai ta kusan kashe ta musamman idan tace mata wanka zatayi.
"Idan na gama sai naje nayi." Cewar Jauhar ɗin tana sake share hawayen fuskarta.
"A'a kije kiyi saboda kayan jikin ki ma suna buƙatar ki sauya su." Ganin yadda Suhanar ke yi mata magana cike da jin ƙai ita duk tsoro ma sai ya kamata, tun a asibiti ta lura da sauyi a wajanta sosai. Tsoro take karta saki jiki da ita daga baya tayi mata sharrin da zata kasa fitar da kanta tunda ba haka ta saba ganin tana yi mata ba tunda tazo gidan nan. Amma ganin ta dage akan sai taje tayi wankan yasa taje wajan sink tasa hannunta ta tsiyayo liquid soap ta juya zata fita Suhana da ke kallanta da mamaki tace,
"Meza kiyi da shi?" Kanta a ƙasa tace,
"Zanje ne na ɗan goga a jikina ne."
"You mean dashi zaki wankan?" Suhana tafaɗa cikin tashin hankali tunda yasan ba na wanka bane har tana turo idanuwa waje, Jauhar ta ɗan dago ta kalli yanayin fuska da Suhana ta koma jiki ba kwari take faɗin.
"Dan Allah kiyi haƙuri shi nake ɗan ɗiba na goga a jikina idan zanyi wanka, kingani ba da yawa na tsiyaya ba." Tayi maganar tana buɗewa Suhana hannun alamar ta duba ta gani dan a tunaninta ran Suhana ɗin ya ɓaci zata ce tayi masu sata. Karo na farko da Suhana taji mugun tausayinta ganin da abinda zatayi wanka, su suna can sabulu sai sun zaɓa kuma duk masu tsada amma ita Jauhar tana nan ta rasa yadda zatayi tana ta raɓe-raɓe da abinda zata tsabtace jikinta ko tsoron yayi mata illa bata yi
"Ina zuwa." Cewar Suhana tana ficewa daga kitchen ɗin. Jauhar tabi ta da kallo, bata san me yasa tace tana zuwa ba dan haka da sauri taje ta ɗauki sosan wanke-wanke ta juye soap ɗin a jiki tare da zuwa tayi saurin ɗakko kettle taje ta tara ruwa a sink ta ɗora akan gas. Tea spieces ta zuba sannan tayi saurin ɗakko roba mai ɗan faɗi ta ɗebo Irish a ciki tana ferewa, zuciyarta bugawa kawai takeyi duk a zaton ta Suhana taje ne ta sanar da Hajja Maimoon cewa da abun wanke-wanken su take wanka bayan kuma Hajja Maimoon ɗin taja mata kunne akan cewa karta sake ta ɗauki abun su idan har ba bata aka yi ba. Suhana ta dawo tare da miƙa mata sabulu sabo dal a cikin kwalinsa tace taje tayi wankan bari ta ƙarasa mata aikin. Baki a wangale Jauhar ke kallonta ta kasa karɓar sabulun saboda tsabar mamaki har sai da Suhana ta riko hannunta ta saka mata sabulun aciki.
"Angode." Jauhar ta faɗa hawaye yana zuba a cikin idanunta haɗe dasa hannu tana shafewa.
"Ba komai jeki yo wankan ki dawo."
Fitowa Jauhar tayi ta shige ɗakinta, jiki babu karfi ta cire kayan ta nufi banɗakin dake cikin ɗakin nata. Ba ƙaramin daɗi taji ba yau tana wankan ƙamshin sabulun yana sa taji kamar ta lashe jikinta. Tana fitowa ta ɗauki yagalgalallan pant ɗinta wanda ita kanta ba zata ce ga tsawon shekarunsa ba duk ya buɗe ya tale ya yi baki ya dafe robar ta buɗe sai dai ta ƙulleshi ta gefen kugunta ta sanya shi yadda zai zauna mata.
Irfaan ne ya shigo parlorn da sallamarsa babu kowa duk sun koma ɗakunan su tun ɗazu. Kai tsaye ya nufi ɗakinta dan yasan yadda bata da lafiyar nan zai iya kasancewa tana ciki a kwance. Sai da ya yi knocking sannan ya murɗa handle ɗin ya shiga a nan ya tarar da ita tana saka kaya.
"Sorry Jauhar." Ya faɗa yana juya bayansa tare da miƙa mata ledar hannunsa yana cewa.
"Ga kaya nan ki saka karki maida na jikin ki, sannan da magani a ciki idan kinci abinci sai kisha." Jauhar mamaki ya kamata ta isa inda yake da kyar tasa hannu ta karɓi ledar, bai jira me zata ce ba yabar ɗakin daidai lokacin da Mommy ta fito ganinsa yana fitowa daga ɗakin Jauhar yasa ta ware idanunta tare da kafeshi da idanun tambaya mai cike da zargi, hakan da Irfaan ya gani ne yasa zuciyarsa ta ɗan yi rawa sai dai ya karfafa kansa tunda yasan babu abinda ya yi a cikin ɗakin saboda yana ganin kamar akwai wata manufa a kallon da Hajja Maimoon keyi masa ya tsuke fuska yana ƙoƙarin raba ta gefenta ya wuce.
"Lafiya naga ka fito daga ɗakin Jauhar?" Tayi maganar tana haɗe fuska.
"Na kai mata maganin da likita ya rubuta shine na siyo."
"Ohh good! Toh Irfaan daga yau daga yanzun ina so ka fita daga rayuwar Jauhar babu ruwanka da ita bana so." Duk da Irfaan besan me yasa Hajja Maimoon ɗin tafaɗi haka ba sai da maganar ta dakar masa zuciya dan baisan ya take son rayuwar Jauhar ɗin tazama ba, Jauhar kuwa yana bata ledar bayan ya fita tazaro duka abubuwan dake ciki, ganin irin kayan yasa ta rintsa ido sunyi matukar kyau sai dai tasan bai zama lallai abar mata ba dan ansha bata kaya amma Hajja Maimoon sai ta kwace. Murmushi tayi lokacin da ta zaro bra ɗin ga wata kunya da ta lulluɓeta. Cike da jin nauyi tamkar ance mata Irfaan ɗin yana wajan. Da sauri ta rintsa ido lokacin da ta gama sakawa taga fitulun nata sun yi kyau a ciki duk kuwa da cewa ba wai manya bane suna kan fitowa. Duk kunya ce ta kamata a haka ta kammala saka komai sai ta dinga jin tamkar ba ita ba, zata so ganin yadda tayi a cikin kayan dan kuwa babu madubi a cikin ɗakin. Tunawa tayi da glass ɗin window tayi saurin juyawa ta fito daga ɗakin nata dan zuwa taga yadda tayi.
Karaf sukayi ido huɗu da Hajja Maimoon, baki buɗe take kallonta cikin kayan da daga gani masu tsada ne. Jauhar tayi cak ta kasa barin wajan da take tsaye sai hankalinta da ya tashi dan bata son ganin matar nan a cikin idanunta. Kallonta kawai Irfaan keyi daya fara kokarin barin wajen yana ji zuciyarsa tana biya masa wani irin karatu akan Jauhar ɗin. Muryar Hajja Maimoon kawai sukaji tana tafa hannuwa tana kallon Jauhar da tayi ƙasa da kanta tana jiran jin yadda za'a yi da ita. Suhaila da Jannat suka fito da sauri yayin da Suhana ma ta baro kitchen ɗin duk suka zubawa Jauhar idanuwa bakin su a buɗe tamkar sunga abin tsoro.
"Wannan yana nuna cewar da ta sace min gold ɗina bayar dashi tayi sai ake siyo mata kaya ko?" Maido idanuwansa Irfaan yai jin kalaman dake fitowa bakinta masu kama da gugar zana yace
"Wait Aunty please dan Allah haba mana, wane irin gold ɗinki aka siyar? Me kika ɗauke ni ne? Kinsan ni ba matsiyaci bane, sannan bandogara da kowa ba ballantana kice sai an sammin wani abun nake iya gudanar da rayuwa ta ba. Enough is enough na kawowa Jauhar kaya ne saboda bai kamata dan tana matsayin mai'aki amma ace a yadda take jage-jage a gidan nan haka take rayuwa tare da ku ba. Bansan wane gold kike magana ba dan haka maganarsa ta tsaya iya nan." Ya faɗa yana juyawa zai bar wajan, cikin gadara da nuna isa Hajja Maimoon ta ƙarasa wajan Jauhar tana cewa.
"Iskancin banza zanyi lokacinka ne, ke kuma muje ki ciro su bazaki saka su ba dan baki cancanci irin waɗannan kayan ba, saboda rainin hankali za'a baki wannan kayan salon a kasa ware ki da yaran gidan? Ina son kowa ya tsaya a matsayinsa, Jauhar kayan nan ba kalar darajarki bane ba dan baki cancanci saka irin su a jikinki ba. Oya muje ki ciro su kafin ma ku saba dasu, ina nan ina jiran ki fito min da gold ɗina shine ke kina gefe guda kina zaɓar abubuwan da suka fiki mutunci da daraja." Kallanta kawai Jauhar keyi tana jin wani baƙin ciki yana mamaye mata zuciya. Kallan da takeyiwa Hajja Maimoon ne yasa ta buga mata wata uwar tsawa wacce tasa Jauhar ɗin shigewa cikin ɗaki da gudu. Wani irin gigitaccen kuka ta saki mai taɓa zuciya tana yi tana cire kayan daga jikinta, ita kam ta rasa irin ƙiyayar da Hajja Maimoon keyi mata. Idan ta gaji da ganinta ta kaita inda ba zata sake ganinta ba mana, ta kaita ayi mata auran da take ta faɗa koda zata samu sassauci daga zaman ƙuncin nan da takeyi yanzu. Ta gaji bazata iya jurewa ba dan kuwa babu alamar Hajja Maimoon zata ji ƙanta bare ta bata farin ciki dai-dai dana rana ɗaya.
"Ki gaya min gaskiya Jauhar me kike bawa Irfaan da har yake miki irin waɗannan abubuwan?." Abinda Jauhar ta jiyo Hajja Maimoon na faɗa daga bakin ƙofar zuwa shigowa cikin ɗakinta. Kafin tace wani abun ta ƙaraso ciki tasa hannu duk ta kwashe kayan, ta kalli Jauhar ɗin ta hango bra ɗin jikinta, da sauri ta ɗaga zanin da Jauhar ɗin tayi ɗaurin kirji dashi, nan ta hango sabon pant mai kyau. Gabanta ne ya faɗi ta zaro ido tana damƙo wuyan Jauhar ɗin cikin tashin hankali take magana.
"Harda waɗannan abubuwan ya siya miki?" Jauhar cike da tsoro tace,
"Dan Allah Mommy..." Kau...! Hajja Maimoon ta kwashe mata kumatu da mari mai zafin gaske.
"Kiyi hakuri Hajiya." Kallan juna suka yi Hajja Maimoon da ranta yake sake ɓaci tace.
"Ki gaya min ya akai yasan baki da kayan ciki? Naji wannan ya siya miki ne saboda baya ganin kina saka masu kyau, amma pant da bireziyar nan na jikin ki ko ki sanar dani yadda akai yasan size ɗinki ko kuma yanzun nan nayi gunduwa-gunduwa dake dan na kashe ki dan ubanki." Wani irin kuka ya kwacewa Jauhar take cewa.
"Allah kuwa babu abinda na bashi." Hajja Maimoon ta sake shaƙo mata wuya Suhana tayi saurin zuwa tana son kwatar Jauhar cike da tashin hankali.
"Mommy ki rabu da ita please." Cikin sauri Hajja Maimoon ta kalli Suhana tana cewa,
"Doughter kinsan abinda tayi ne? Ko kin gane abinda nake tunanin ta aikata Suhana?" Girgiza kai Suhana tayi alamar bata gane ba, Jannat dake bayan su ce tace,
"Ta fara canza ɗabi'a daga sata tana son fin karfinki Mommy." Hajja Maimoon taja tsaki jin babu wanda yake tunanin abinda take zargin Jauhar ɗin ta farayi. Cikin fushi ta ture ta tana faɗin.
"Wallahi baki isa ki janyo min wata masifa ba Jauhar, bazan ɗauki ɓacin rai da tashin hankali ba kamar yadda ubanki bai ɗauka ba son zuciya yasa da shaiɗanci baki rayu a hannunsa ba sannan ni kuma ki jefani a damuwa. Aure ɗaya tak nayi a rayuwata kuma bana son ganin wani abun yazo ya min shamaki a cikin sa. Ki kiyayeni Jauhar bake ba Irfaan da duk wani namiji ma. Babu ke babu soyayya dan kuwa baki da rabon yin ta a cikin duniyar nan." Kuka Jauhar ɗin keyi amma babu mai lallashinta, Suhana ma da taje zata tayar da ita hanawa Mommyn tayi. Tassss ta kwashe duk wasu abubuwan da Irfaan ya kawo har maganin bata bar mata ba. Jiki a sanyaye Jauhar ta maida kayanta masu dauɗa sannan ta dawo kitchen lokacin sauran kaɗan Suhana ta kammala soya dankalin. Kallonta Suhana tayi ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita tace,
"Kiyi hakuri Jauhar ban san me yasa Mommy bata tausaya miki ta kowane yanayi ba. Shin wai ina ne garin ku Jauhar?" Jauhar ta share hawayen fuskarta tana cewa.
"Mommy ce komai nawa tun bansan wacece ni ba, ban san kowa ba sai ita. Kuma idan zataje can garin na mu bata tafiya dani sai dai muyi waya da Kakanni nawa idan taje. Lokacin da zasu yi aure da Daddyn ku a gidan da take zaune a nan ƴan uwan namu suka zo aka ɗaura a kuma ranar ne na gansu inda suka yi ta bani haƙuri suna cewa Allah zai saka min. Ban san me yasa basu jani wajan su ba suka barni a wajan ta kuma bata sona." Yadda tayi maganar ya matukar sanyaya jikin Suhana, cike da tausayinta take ce mata.
"Kiyi haƙuri dama haka Allah yake abubuwan sa akan bawa, mu ma kinga bamu rasa komai ba gashi nan amma mahaifiyar mu bata tare da mu." Cikin sauri Jauhar tace,
"Ni da ku ba ɗaya bane Suhana, ku ga mahaifin ku nan kuma kunsan inda mahaifiyarku take. Ni kuma ban rayu dasu ba, tun sanda naji Kaka na yana cewa. Allah bazai kyale iyaye na ba akan zarafi na da sukaci na kan so naji me yasa suka barni? Idan nazo tambayarsu ina iyayen nawa? Sai Hajiya ta make min baki tace na fiye shegiyar tambaya sai kace in naji inda suke wani abun zasu tsinana min." Jauhar ta ƙarasa muryarta na daɗa karyewa.
"Kiyi hakuri." Suhana ta faɗa dan bata da wani abun sake faɗa. Suna kammalawa suka jera komai a dining table, su Suhaila kamar zasu mutu dan ganin yadda Suhana ke yiwa Jauhar ɗin. Jannat ta dinga yin kwafa tana ji a ranta bazai yiwu su bar Suhana ta dinga biyewa Jauhar ba, yau kawai sunga ta canza tamkar ba Suhana da suka sani a baya ba. Kujera Suhana ta janyo ta zauna duk da tana kallon yadda ƴan uwan nata suke harararta bata kulasu ba. Jauhar na gefe tun lokacin da suke aikin taji wata irin yunwa tana taso mata, nata yana kitchen wanda Suhana ta ɗibar mata tace idan ta kammala komai ta zauna taci. Tana son komawa kitchen ɗin amma tana tsoran juyawa ta bar gurin wata ta buƙaci abu aga bata nan. Fitowar Hajja Maimoon yasa Jauhar sake kama nutsuwarta kanta a ƙasa tana tsoran kallonta. Da hannu Hajja Maimoon ta nunawa Jauhar ɗin hanya alamar tabar wajan bama ta san ganinta bare har wani abun ya haɗa su. Hakan ba ƙaramin daɗi yaiwa Jauhar ba dan sai takejin tamkar an yaye mata wani nauyi da ya tsaya a kirjinta. Kitchen ta zauna ta janyo abincin da Suhana ta rage mata, zama tayi ta fara ci tana tunanin yaushe daɗi zai zo mata kamar yadda take ganin mutane cike da walwala Ali yaushe.
******
Kunnensa sakale da wayarsa yana magana a haka ya shiga bedroom ɗinsa, Hajja Maimoon ya tarar ta fito daga bathroom fuskarta duk ruwa da alama wanketa tayi. Murmushi ta sakar masa tare da ƙarasawa wajansa tayi hugging ɗinsa rightside dai-dai lokacin da ya sauke wayar bayan sunyi sallama da wanda yake wayar. Sosai ya janyota cikin jikinsa tare da janta suka isa wajan madubi yana cewa.
"Madam ki shirya zamuje wajan siyan zinarinki, sonake daga can ɗin a yau ɗin nan kiyi magana da mai kayan da kika ce zaki fara business ɗinsu. Kuɗi ne suka zo min so bana son kuma su tafi cikin harkokina ba tare da na cika miki alƙawuran dana ɗauka ba." Hajja Maimoon ta ware ido duk irin ajinta da kwalisarta sai da ta bayyana farin ciki tana yi masa godiya tare da addu'o'i na karin buɗi da kuma gamawa da duniya lafiya. Sake riƙo hannunsa tayi tana kallon fuskarsa take cewa.
"Ya Habiby me zanyi dan na biyaka kwatankwacin irin wannan farin cikin daka sani?" Kafin ya yi magana tace.
"Ka sanar da ni komenene I will definitely do it yadda ka sani farin cikin nan." Murmushi ya yi kawai shi a ganinsa wannan abun da zai yi mata ba komai bane ba, hasalima yana ganin tamkar hakkinsa ne ya yi mata shi musamman ma jarin da yake son ya bata. Kallonta ya yi yana matse kafaɗunta yake cewa...
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye