GONAR SHARRI...

BABI NA GOMA

by @billysfari

GS 10.


"Mommyn Jannat babu abinda nake buƙata a gareki sama da kulawar da kike bani, wannan kaɗai ya wadatar dani domin duk abinda zanyi miki wajibina ne nayi miki, but akwai alfarma ɗaya da nake son roƙonki sai dai bana so kiyi tunanin ko don zan yimiki waɗannan abubuwan ne zan roƙeki ita...." Ɗan yatsa Hajja Maimoon ta ɗora a saman labɓansa tun kafin yaƙarasa rufe bakinsa, cike da kulawa ta riƙo hannunsa tana matsawa a hankali tare da kallonsa tana narkewa haɗe da cewa. 


"Ka faɗi abinda kake so kai tsaye ina tabbatar maka da zanyi maka ba tare da ɓacin rai ba ko musanta maka ba, faɗamun meye Ya Habiby?" Taƙare zancen tana kallon cikin idanuwansa. Murmushi yai haɗe da ɗago hannunta dake riƙe da nasa ya sumbata sannan ya kalleta yace, 


"Ina so kada kisake ɗakko zancen gold ɗinki daya ɓata, Please kibar zancen nan ya wuce kada ya zama wata damuwa tunda Allah zai baki wanda yafishi kin ji ko?" Ya faɗa yana nuna mata son abar zancen akan fuskarsa. Sai da tayi murmushi tare da shigewa jikinsa tace, 


"Shikenan Ya Habiby bazan sake ɗakko zancen ba in sha Allahu." Hajja Maimoon tafaɗa ba don ranta ya so hakan ba tana ƙara jin tsanar Jauhar acikin zuciyarta. A cewar ta ba dan ta ɗauke gold ɗin ba idan ta haɗasa da wanda Dady zai saya mata yanzu ba ƙaramar kaddara zata tara ba, gashi ta janyo mata asarar da batasan ranar maidata ba koda kuwa kullum zata samu ƙarin gold don ta riga ta rasa wancan ɗin da ba ƙananan kuɗi ne dashi ba. Tana wannan tunanin taji yai hugging ɗinta duka yana cewa. 


"Thank you so much Madam. Ya jikin ƴar taki?" Sai da Hajja Maimoon ta sake shigewa cikin jikinsa sannan tace, 


"Taji sauƙi." Har zai tambayi jikin Jauhar ɗin sai ya tuna ba lallai hakan yayi mata daɗi ba, dan haka ya kama bakinsa yayi shiru ya shiga ƙoƙarin rage kayan jikinsa Hajja Maimoon na taimaka masa.


Alhaji Sha'aban Sada na kammala shiryawa cikin kaya marasa nauyi da suka karɓi jikinsa sosai suka nufo palour shida ita, duka yaran na kwance saman kujerun palourn suna kallo Jannat ce kaɗai ke zaune riƙe da wayar Mommy tana buga game, tana ganin Daddyn nasu ta taso tayo wajensa yasa hannu ya rungumeta yana kallonta cike da kulawa. Cike da sakalci take rungume hannunsa tana kwantar da kanta. 


"Dady sannu da dawowa." Suhana da Suhaila suka faɗa atare, cike da jin daɗin ganin su ya amsa hankalinsa nakan Jannat ɗin yana tambayarta ya jikin nata ita kuma tana sake shigewa jikinsa cike da shagwaɓa take amsa masa da taji sauki. Da haka suka ƙarasa wajen dinning da Jauhar ke sake gyarawa saboda basu jima da kammala lunch ba. Cikin girmamawa kan Jauhar a ƙasa ta gaishesa tana ƙoƙarin barin wajen saboda mugun kallon da Mommy ke wurga mata, sai taji Daddyn ya dakatar da ita yana tambayarta. 


"Ya jikin naki?"


"Naji sauki Dady."


"ALLAH yaƙara sauƙi." Yafaɗa yana basar da zancen ba tare daya bi takan Mommy data juyo tana kallonsa ba na jin tambayar da yai wa Jauhar. Ita fa sam bata son duk wani abu mai kama da tausayi ko kuma kulawa ya dinga ta'allaƙa da Jauhar bare har ta sameshi acikin gidan, so takeyi ko yaushe Jauhar ta kasance cikin kunci da baƙin ciki kamar yadda ta zamo silar shigarta cikinsu a lokutan baya. Da wannan tunanin ta shiga zuba masa abinci yaci, yana kammalawa yace ta shiga ta dakko mayafinta suje yana jiranta a waje.


"Dady zan je nima." Jannat tafaɗa har lokacin hankalinta na akan game ɗin da take bugawa. Hannun da Hajja Maimoon ta miƙawa Jannat ɗin ne yasa Jannat ta miƙe mata nata Hajja Maimoon ɗin tana cewa, 


"Oya taso muje ki sauya kayan jikinki." Jannat tamiƙa mata hannun suka wuce Dady ya bisu da kallo cike da so dan idan ka gansu tamkar Hajja Maimoon ɗin ce ta haifeta, wannan na daga cikin dalilan dake sa a kullum yake ƙara jin kaunar Hajja Maimoon tare da hauhawar matsayinta a cikin zuciyarsa yanda ta ɗauki ƴaƴasa tamkar ita ta haifesu.

__________


"Wai lafiya ka samu waje ka zauna kana faman cika ina yi maka magana ka ƙyaleni? Meke faruwa ne Irfaan?" Hajiya ta faɗa tana tsaresa da idanuwa, jin yai shiru bai amsa mata ba yasa takira Inna Deeje mai aikinta tace takawo masa ruwa, ba'a jima ba sai gata ta dawo ɗauke da ɗan ƙaramin tray ta ɗoro gorar ruwa mai sanyi da cup data wanko ta ajiye masa agabansa, 


"Ɗauki ruwa kasha." Hajiya ta faɗa tana ba Irfaan ɗin umurni. Sai da yai kamar bai jita ba kafin ya ɗauki ruwan ya tsiyaya yasha, ya dire cup ɗin lokaci ɗaya tare da nauyayyen numfashin dake nuni da zuciyarsa daskare take da ɓacin rai. A karo na biyu Hajiya ta sake jeho masa tambayar da tayi masa a farko da take cike da son jin amsar ta, dan yanda tasan halayyar ɗan nata da dabi'unsa ba ƙaramin abu bane ke jefasa a irin wannan yanayin damuwa da kuma ɓacin ran ba.


"Hajiya wai meyasa sam babu ɗigon tausayin yarinyar can a zuciyar Hajja Maimoon, me yasa take wulakantata da ƙasƙantar da ita haka? bayan Allah ya ɗaukaka ɗan Adam ya kuma darajasa? Shin ita ba mutum bace ko kuma ita ta zaɓawa kanta rayuwa a yadda take? Duk da itace ta zo da ita gidan a ganina be daje ana treeting yarinyar nan haka ba." Nauyayyar ajiyar zuciya Hajiya ta sauke dan bata ɗauka damuwar ɗan nata akan wannan matsalar bace da ita kanta ta jima tana cimata tuwo a ƙwarya, kawai ba yadda zatayi ne tunda tare ta gansu da yarinyar. Amma sam bata jin daɗin yadda ake kawo mata labarin irin wahalhalun da yarinyar ke sha da tsangwamar da akeyi mata a gidan ɗan nata. Kallonsa tayi tace, 


"Bansan dalili ko hujjar da tasa Hajiya Maimuna take yin hakan ba bayan ita tazo da yarinyar nan gidan, meke faruwa ne halan?" Nan fa Irfaan ya kwashe komai ya sanar da Hajiya har yana ƙarawa da cewa.


"Hajiya nafahimci so takeyi kowa ya guji yarinyar nan ya cutar da ita kamar yadda takeyi, sai dai ni bazan taɓa yin hakan ba saboda har cikin zuciyata nake jin tausayin yarinyar nan. Kuma wallahil azhim Hajiya tayi duk abinda ta yi bazan fasa taimakon Jauhar ba da dukkanin karfina da kuma dukiyata ba sai dai tayi min duk sharrin dataga zata iya ni kuma zan ɗauka kuma zan jure har lokacin da Allah zai kawowa Jauhar mafitar tafiya daga wannan kangin bautar da takeyi. Ni wallahi Yaya ne ma har mamaki yake bani akan abubuwan da akewa yarinyar nan agaban idanuwansa amma baya cewa komai. Bansan yaushe zuciyarsa takoma haka ba!" Hajiya ta sauke numfashi, tabbas abun babu daɗi, gashi ita kam duk abinda zai taɓa mutuncin Alhaji Sha'aban bata son shi, dalilin da yasa kullum gidan ta sai an sauke tukunyar abincin sadaka da niyar Allah ubangiji ya ƙare mata shi ya kuma ci gaba da rufa masa asiri duniya da lahira. Bata taɓa sanar da kowa dalilin yin girke-girken da take sawa ayi ba daga ita sai Allah. Ajiyar zuciya ta sauke tare da faɗin. 


"Allah ya kyauta, ita kuma Jauhar ɗin Allah yai mata mafita ta alkairi, ni wannan abun duk laifin iyayenta nake gani aciki, bazan hanaka taimakonta ba amma kariƙa yin taka tsantsan tunda bata so, kuma ta fika kusanci da iyayan yarinyar." Jin Hajiya ta karfafa masa guiwa yasa yaji nutsuwa ta fara saukar masa yace, 


"To Hajiya amma fa indai ta sake yimin sharri wallahi ajiye girman Yaya zanyi nafaɗa mata ba daɗi tunda zuciyarta ba imani da tausayi, yarinya ƙarama ki zauna kina azabtar da ita ko da me hakan zai rageta..?" Duk suka yi shiru Hajiya ta kasa cewa komai. Haka Irfaan yai ta magana Hajiya na kallonsa tana son gano wani abu tattare dashi akan yarinyar har ya gama faɗan ya tashi ya fita.

__________


Kasuwar Rimi Alhaji Sha'aban Sada ya nufa yai parking a bakin wani katafaren store na Muhammad gold accessories. Tare suka buɗe murfin motar suka fito yana gaba Hajja Maimoon na biye dashi a baya riƙe da hannun Jannat, juyowa yai bayan sun shiga ciki yace ta duba ta zaɓi duk sarkar data yi mata ta dai-dai adadin kuɗin waccan da aka ɗauke mata. Nan take Hajja Maimoon ta saki murmushi ta shiga duba sarkokin gwalagwalan dake wajen. Sai da ta kusan zagaye ko'ina can ta hango wacce tayi dai-dai da zabinta sannan ta nuna tace ita take so Alhaji Sha'aban yace a ɗakko mata ba tare daya damu da sanin ko nawa take ba har sai da aka ɗakko. Sosai Hajja Maimoon ta girgiza da jin adadin kudin sarkar dan sun kusa ninka na sarkar ta da aka sace sau uku, amma ga mamakinta ko tsayawa tayawa baiyi ba ya fitar da kuɗin duka ya biya aka miƙo masa sarkar tare da reciept ɗin ya miƙa mata. Tsabar farin ciki ruɗewa Hajja Maimoon tayi ta rungumeshi a wajen tana zuba masa godiya dan ko a mafarki bata sa ran zata mallaki sarka mai tsada irinta ba, hannun Jannat ta kama suka fice shi kuma ya tsaya wajen ya duba wata sarkar gold ɗin da zata dace da mahaifiyarsa ya siya ya jefa cikin aljihunsa.


A can waje kuwa Hajja Maimoon ƙawarta takira tana sanar mata haɗe da shaida mata sarkartata da aka dauke har tana faɗa mata tsadar wacce Alhaji Sha'aban ya siya mata ɗin yanzu. Kasancewar tana cikin farin ciki har sanar da ita irin ribar da taci da wannan sabuwar. Sosai aminiyarta ta tayata murna tare da sake ɗora ta akan hanyar da zata ribatu da kuɗin Alhaji Sha'aban Sada ɗin tunda baya iya bayarwa sai da dalili. Tana hango shi yafito tayi saurin yin sallama da ita tana cewa sai takirata zasu ƙarasa magana idan takoma gida. Daga nan kuma wajen shakatawa suka nufa suka ɗan zazzagayo dan Alhaji Sha'aban mutum ne mai son wayewa da kuma burge iyali. Bayan sun kammala suka nufi hanyar komawa gida, nan yake yimata zancen a ina take son yin business ɗinta? A online ko kuma a gida? Murmushi ta saki haɗe da cewa,


"Gaskiya bana son business a gida, online kuma ai kaga kamar kafa ne da zan tallata kayan, in son samu ne kawai shago zan kama a zuba kayan aciki ina sayarwa ko ya ka gani?" Shiru yai dan har ga Allah duk abinda zai janyo tawayar samun kulawarta gareshi baya so, kuma gashi yana son ya kyautata mata kamar yadda take kyautata masa shi da yaransa.


"Ya Habiby ya naji kayi shiru? I think is better da azo ana cika maka gida, kare da doki wasu ma su cuce mu ta hanyar zuwa gidan da zasu yi." Juyowa yai ya kalleta kafin yaci gaba da tukin yake cewa. 


"Wannan ni ba matsalata bace indai zanci gaba da samun kulawarki, kin sani bana son kinayin nisa dani inba dole ba shiyasa zancen shagon nan bai kwanta mani ba."


"Oh God! Ya Habiby hakan fa bazai canza komai ba a kulawar da nake baka, I promise you that." Tayi maganar cikin kashe murya tana wani mammatsa hannunsa cike da salon son shawo kansa. Sake juyowa yai yana kallonta yace,


"Are you sure?." Bata iya amsa masa ba saboda ta shagaltu wajen yimasa wani irin fitinannen kallo daya kusa dakatar da bugawar zuciyarsa sai dai ta ɗaga masa kai alamun


"Eh".


Take Alhaji Sha'aban Sada yaji jikinsa ya mutu ya samu daƙyar suka ƙaraso gida suka nufi sashensa kai tsaye. Jannat kuma ta kwashi kayan kwalam ɗin daya siya musu ita da ƴan uwanta ta wuce musu dashi. 


A takaice duk da yadda lokacin magriba ya soma karatowa sai da Hajja Maimoon ta jefasa duniyar da suka farantawa junansu haɗe da samawa kansu natsuwa. Bayan yafito wanka yace tayi magana da ƙawarta da zata turo mata kayan ta turo mata account zai tura mata adadin kuɗin da zata zabi duk abinda take so, ya kuma ce akwai shaguna acan farkon titi kafin a shigo unguwarsu da ake talla zai kama mata guda biyu sai a haɗe a sake gyara mata su kafin kayan su iso. Hajja Maimoon taji daɗi sai taji darajarta ta sake girmama, addu'a sosai tayita masa har da kwallarta ta farin cikin ganin mafarkanta sun fara tabbata, sannan atake takira ƙawar tata tace ta turo mata account ɗinta, ba'a jima ba ta turo mata taba Alhaji Sha'aban ɗin shi kuma atake awajen ya tura mata kuɗin yace tafara gwadawa dasu, idan yaga kasuwar ta karɓeta to zai ƙara mata wasu sannan ya mike ya nufi masallaci yana cemata daga can zai biya gidan Hajiya ya gaisheta. Har mota ta rakosa tana yi masa adawo lafiya sannan takoma ciki zuciyarta cike fal da farin ciki tana ganin auran ta da Alhaji Sha'aban nasararta ne kuma matakin daukakarta ne.

__________


Tunda ya doso ƙofar gidan annurin dake kan fuskarsa ya soma gushewa har ya ƙaraso wajen ganin ƙanwar tasa Husnah tsaye da wani agefen gidansu. Tsaye yai yana ƙarewa yaron kallo tun daga sama har ƙasa, sanye yake da gajeren wando iya guiwa, sai riga armless mara hannuwa wuyansa sanye da wata kafceciyar sarƙa ƴar Chaina. idanuwansa ne suka sauka akan kunnen Guy ɗin daya sanye da ɗan kunne tamkar mace sai kansa daya sha wani irin aski na Bobby, acikin mintuna biyu kacal yaƙare masa kallon da ya gama tabbatar masa da cewa gaba ɗaya yaron ba musulmi bane, ransa ne ya sake ɓaci lokacin da idanuwansa suka sauka akan takalman dake ƙafafuwansa wasu irin kafta-kafta farare irin canvas ɗin nan na gayu dake ji da kansu. Rai aɓace Zain yai parking mashin ɗinsa a ƙofar gida ya sauko ya nufo wajen da suke tsaye sun shagalta da aikawa juna wani irin kallon soyayya. Wata uwar tsawa ya dakawa Husnah da tasa tayi wata irin zabura yace ta wuce cikin gida. Baki sake Zain yake bin yaron da kallo lokacin daya miƙo masa hannu cikin girmamawa yana cewa, 


"Assalamu alaikum, Yaya barka da dawowa." Me hakan ke nufi? Kenan wannan yaron yana nufin shi musulmi ne yake cikin irin wannan shigar da ba ta da banbanci data ƙabilu? Daƙyar ya iya buɗe baki ya amsa masa sallamar da yai masa yana cewa, 


"Ko menene tsakanika da ƙanwata ka rabu da ita saboda karatu zatayi, a mutunce nake faɗa maka hakan kafin akai ga ɓacin rai tsakanina dakai idan nakuma ganinka a ƙofar gidan nan, babu kai babu ita kana jina ko?" Zain yaƙare maganar haɗe da kama kunnensa ɗaya alamun jan kunne sannan ya juya rai aɓace ya wuce cikin gidansu. Saurayin kuma mai suna Iliya ya bishi da kallo cike da mamaki kafin yaja tsaki yace, 


"Wannan kwafsa min zai dinga yi kenan? Ahhh lallai za'a kwashi uwar watsi indai akan Huscy ne. Kai..! Lallai ma gayen nan, wato duk wannan gayun nawa dana kwaso dan na burge yarinyar nan sai da ya yimun bakin cikin yin hira da ita. Mtssss! wallahi ni da Huscybaby mutu karaba dan bakin ciki kawai. Zaka gane waye ILLiyasmarter na rantse da Allah kuwa." Daga haka yaja kafafuwansa da daƙyar yake ɗaga su yana jefawa irin tafiyar ƴan iskan nan saboda nauyin takalmin. ILIYA ɗan nan cikin garin su ne acan kauyen dake gabansu, ya jima yana son Husnah tun tana jss 3 amma yadda yake ganin takunta irin na yaran masu kuɗi ƴan gayu yasa ya ɗauki alwashin zama gaye kafin ya tunkareta dan yasan hakan kaɗai zai sa ta saurararsa. Yayi nasara kuwa domin tun a ganin farko da Husnah taji yes zai yi daidai da wanda zata iya tsayawa. 


Zain kuwa yana shiga gida Husnah na tsaye a ƙofar ɗaki ta cukuikuye hijabin ta na makarantar boko data dawo dan ta maraice takeyi tana faman haɗe rai, bai tsaya wata-wata ba yana shiga yayo kanta. Husnah kuwa da gudu ta ɓuya bayan mahaifiyarta dake kukkulle kayan yaji. 


"Kai..kai wai lafiya Zain? Meye haka daga dawowarka zaka rufar min yarinya? Me kika yimasa ne?" Taƙare zancen tana juyowa wajen Husnah dake faman tura baki, 


"Ba dake nake ba ko sai nabarshi yayi miki shegen duka?" Cike da son a kareta tace, 


"Mama ni banyi mashi komai ba.." Kanta da ya yo ne yasa ta kasa karasa maganar, Mama tayi saurin tareshi. Cikin ɓacin rai yace, 


"Mama da wani ɗan iskan saurayi na ganta fa a waje sunq tsaye kana ganinsa kaga Christian." Cike da jin haushi Husnah ta ɗago kai tana cewa.


"Ya Zain bafa Christian bane, sunansa Iliya kuma so na yakeyi." Da sauri Mama tace, 


"To kaji amma zaka zo ka saukewa yarinya ɓacin rai, ai sai ka mayar da wukar tunda kaji masoyinta ne, ko kuma kana nufin bata kai munzalin tsayawa da saurayi ba?" Baki Zain ya saki jin abinda mahaifiyar tasa ke cewa kafin yace, 


"Mama Husnah guda nawa ce da zata fara kule-kulen samar? kinga yaron kuwa? Na rantse kada kibari na sake ganinki dashi idan ba haka ba na lahira sai ya fiki jin daɗi." Cikin sauri Mama tace dashi. 


"Toh sannu ubanta, nace sannu isasshe gawurtacce, idan bata kula samari ba taya kake so ta zabo mijin aurenta? Ko kai zata aura? Nifa bana son haka tunda ba kamata kayi tana yin dabi'u marasa kyau ba ka ƙyaleta ta kula duk wanda yazo wajenta, ta haka zata tantance mijin aure tunda ba zama zatayi muna kallonta ba..." Wani irin haushi ya sake kama Zain yana kallan Mama yama rasa ta yadda zai suffanta mata yadda Iliyan yake. Rai a ɓace ya nufi ɗakinsa yana jin zuciyarsa na masa zafi, wai ace wannan guy ɗin ne zai nemi ƙanwarsa saboda ance ciwon makanta ya kama su. Idan har yana numfashi bazai bar ILIYA tare da jininsa ba..... 

KU AJE MANA COMMENT IDAN HAR KUNA JIN DAƊIN LABARIN, HAKA ZAI SA MU ƘARA MAKU YAWAN FREE PAGES KAFIN SAUKAR PAID. MUN GODE.


INA TEAM HAJJA MAIMOON? INA MIKO GAISUWA🤣🏃



#A heart touching story

#Gonar Sharri..

#Hajja ce

#Billy s Fari

#Ƴan Tagwaye