WATA ALAƘA

BIYAR

by @zeeeyybawa

*WATA ALAƘA.....!*

*PAID BOOK* 

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* 


NA



STYLISH BTCH

Da

ZAYNAB BAWA


*SHAFI NA BIYAR*



  Ummie ce tsaye a kitchen wajan masu aiki tana duba yanda suke shiryawa Hydar breakfast da kuma abincin zuwa school ɗinsa saida ta tsaya ta tabbatar an gama haɗa komai yanda ya kamata sannan ta nufi ɗakin Hydar a hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga da niyyar kar sound na buɗe ƙofar ya tasheshi a bacci sai dai abin mamaki zaune taganshi a saman gado da alamu ya daɗe da tashi domin idonsa baiyi alamun tashin yanzu ba, mamakine ya kamata domin taga saɓanin halin Hydar data sani don ya kasance mai son bacci sosai daƙyar take iya tashinsa daga bacci, murmushi tayi ta ƙarasa ta zauna ta shafo kansa cikin harshen larabci tace.


"Habibi harka tashi? Fatan kayi bacci mai cike da nishaɗi?" Hydar bai amsa mata kamar yanda ya saiha sai canja zancen yayi da faɗin.


"Ummie ayi sauri a shiryani intafi school wajan Hidaya munata wasa da ita anan" ya nuna kan sopa dake gefen bed ɗinsa sannan kuma saiya ɓata rai sannan ya ƙarashe zancen da faɗin


"Yanzu kuma bata nan" Kallonsa kawai Umminsa keyi lamarin Hydar yafara bata tsoro tayi tunanin da zarar yayi bacci yatashi zai manta da Hidayar sai kuma yaje school ya sake ganinta amma yanzu yake bata labarin sunyi wasa a ɗakinsa tasan mafarkin Hidayar yayi suna wasa amma lamarin yafara bata tsoro, daurewa tayi ta miƙe haɗeda ɗaukan Hydar tashiga toilet dashi. Wanka tayi masa tafito ta shirya shi cikin Uniform sannan ta sake ɗaukansa tafito dashi zuwa palour. mai aikin shirya Hydar wacce firr yanzu yaƙi tana shiryasa sai Umminsa ta ƙaraso wajan ta miƙe hannu zata amsheshi domun cikin Ummi yanzu ya girma sosai ko Mai martaba yayi magana akan ta rage ɗaukan Hydar haka, Hydar yana ganin alamun ɗaukansa takeson yi ya maƙale kafaɗun Umminsa, murmushi Umminsa tayi cikin hausarta wacce har yanzu bata gama ƙwari ba tace.


"Barshi kawai zan karasa dashi" Jaa baya ma'aikaciyar tayi sukuma suka ƙarasa wajan dining, ɗaukin ganin Hidaya gabaki ɗaya ya hana Hydar cin abinci Umminsa gabaki ɗaya ranta cike yake da damuwa sai takeji kamar tabishi school ta duba Hidayar, bata ida tunaninta ba wayarta tafara ruri, ganin sunan mai martaba ya sanyata sauke ajiyar zuciya sannan ta amshi wayar, cikin girmamawa ta gaisheshi ya amsa sannan yafara tambayarta ko anshirya Hydar. Amsa masa tayi da cewar yana breakfast. Toh yace sannan yabada umarnin idan yaagama akaishi wajan Fulanin sarki (Hajiya zulaiha) kafin a wuce dashi wajansa, cike da ladabi Ummi ta amsa batareda taji komai aranta ba duk kuwa da tasan Hajiya zulaiha ba Masoyiyar Hydar bace. Cikin yanayinta mai cike da nutsuwa da kuma sanyi tace.


"Abien Hydar idan ka amince zanbi Hydar school" Cikin jin daɗin sunan data kirashi wanda kaff duniya babu mai masa wannan laƙanin sai ita yace.


"Ummin Abbana ko zan iya sanin dalilin da yasa kike son zuwa makarantarsu Hydar don nasan bakya taɓa yin wani abu batareda kwakkwaran dalili ba" Murmushi tayi sannan tace.


"Inaso inje inga wannan yarinyar Hidaya" Sannan tabashi labarin yanda sukayi da Hydar da safennan sannan ta shaida masa kafin tashiga wajan Hydar harya tashi daga bacci yana jira azo akaishi wajan Hidaya har tayi masa wanka tagama zancen Hidaya kawai yakeyi. Jijjiga Mai martaba yayi sannan yace.


"Nayi miki izini dama yanada kyau kasan dawa ɗanka yake tare, sannan kema zaki ɗan taka ƙafarki domin yanzu kin shiga lokacin daya kamata ace kin fara exercise, amma kafin ku wuce school ɗin ku taho tare da masu kawo Abbana mu gaisa kwana biyu kenan bansaka ki a idona ba sai dai inji muryarki awaya yakamata nasan halinda kike ciki" Murmushi Ummi tayi sannan tace.


"Abban Hydar abunda yau gabaki ɗaya ma zan koma sashinka har sai bayan kwana biyu menene na gaggawa" Murmushi mai martaba yayi ta cikin wayar sannan yace.


"Nidai tunda nasamu uzurin da zai bani damar ganinki zanyi amfani da ita basai dare yashiga ba a ƙa'ida bai kamata ace sai bayan 2days zanna sakaki a ido ba saboda ba cikekkiyar lafiya ce dake ba, ya kamata ace ko yaya ina ganinki don haka idan za'a kawo Hydar ki biyoshi ku taho tare kinga basai ansake komawa ciki ɗauko ki ba" 


"Toh shikenann in sha Allah" tafaɗa amma zuciyarta cike take fall da tsoro sam bata son wani abunda zai saka tashiga tarkon Hajiya zulaiha domin kaɗan take nema da ita sai takeji kamar tafasa bin Hydar school gabaki ɗaya gudun abunda zaije yazo sai dai jin muryar mai martaba yanda take nuni da yanason ganinta yasa taji bazata iya ƙin bin umarninsa ba, Miƙewa tayi ta nufi ɗakinta bayan ta bata saƙon a sanarwa sarkin mota ya shirya mota Hydar ya shirya fita, cikin 5minute ta fito sanye da Hijab a jikinta ta ɗauki Hydar ma'aikatansa kuma suka ɗauki schoool bag da lunchbag ɗinsa suka fita saida suka ajiye komai a mota sannan ita da Hydar Aliyu Turad suka shiga ciki. Bayan sarkin mota ya tada mota sannan tabashi Umarni akan sufara wucewa wajan Fulanin Sarki. Kafin su wuce wajn mai martaba, amsawa yayi sannan ya cilla motar izuwa layin da zai kaisu sashinta, a palour suka zauna bayan sun aika Jakadiyarta ta sanar mata da zuwansu. Daga Hydar da Umminsa a ƙasa suka zauna kamar yanda Fulanin sarki Hajiya zulaiha tabawa Ummi umarnin zama tun farkon kawota gidan, tsoro da gudun fitina yasa Koda yaushe Ummi a ƙasa take zama idan tana sashin Hajiya zulaiha. Tsawon 30minute suna zaune suna jiran fitowar Hajiya zulaiha amma shiru lokacin har 7:30am ta wuce jiya iwar haka Hydar ya daɗe a school. 


Mai martaba jin shiru basu ƙaraso wajansa ba yasanya yafara kiran Ummi, tsoron ta ɗaga Hajiya zulaiha tafito ta samesu suna waya yasa taƙi ɗagawa domin saiya zamo abun bala'i, mai martaba ganin ya kirata har 2missed calls bata ɗaga ba ya sanya ya kira sarkin mota nan sarkin mota ya shaida musa tun 7am suke isa wajan Fulanin sarki har yanzu kuma basu fitowa daga ciki ba, Dialing number Hajiya Zulaiha Mai martaba yayi saida gabanta yafaɗi ganin sunan mai martaba daurewa tayi ta ɗauki kiran kai tsaye mai martaba ya jeho mata tambayar.


"Mai Abbana yake a sashinki da tswon minti talatin har yanzu bai fito ba? Bayan kunsan zaije school a ranarsa ta biyu a zuwa makaranta kukeso ku sakashi latti?" Ran Hajiya zulaiha yaɓaci sosai amma ta shanye cikin kisisina irin nata tace.


"Hydar kuma yana sashina? Kaganni zaune a ɗaki babu wanda yazo ya sanar dani, kai amma basu kyauta ba suna so su saka afara tunanin iyayensa sunada careless daga zuwa ɗaya biyu har munfara barinsa yana late?" Ajiyar zuciya mai martaba ya sauƙe sannan yace.


"Yanzu ba wannan ba tashi kije ku gaisa lokaci yana tafiya" Tsaki taja bayan ta ajiye wayar saida taƙara samada 5minute kafin tafito, turus taja ganin Hydar da Umminsa ko kaɗan bata taɓa tunani Hydar tare suke da Umminsa ba don Jakadiya sanar da ita tayi kawai magajin gari yazo gaidata. Haɗiye wani baƙin cikinta tayi domin Allah yagani ta tsani koda ganin Ummi ne domin itace silar ƙwace mata duk wani farin cikin da take tunsnin tana dashi. Tamke fuska tayi ta ƙarasa cikin ladabi Ummi ta gaisheshi ko kallon yanda take batayi ba ahaka ta daure tasaka Hydar ya gaisheta. Juyowa tayi ta dubeshi sannan ta kauda kai. Tsawon 5minutes suna zaune ahaka saiga kiran mai martaba yashigo ƙara sunna kai ƙasa Ummi tayi tana jin tsoron idon Hajiya Zulaiha yakai kan wanda ke kiran nata, Kafin takaiga ɓoye wayar idon Hajiya zulaiha yakai kan wanda ke kira, wani murmushin takaici tayi sannan tajira kiran ya yanke har loacin idonta yana kan Ummi taɓe baki tayi tace.


"Au kece munafukar da kika sanarwa mai martaba Kunyi tsawon 30minute kuna jirana" Ummi wacce a halin yanzu tana fahimtar duk wata kalma ta zagi da take fitowa a bakin Hajiya Zulaiha saɓanin abaya da bata ganewa kawai dai tasan ba kalmomi masu kyau take faɗa mata ba, ta miƙe riƙe da hannun Hydar tayiwa Hajiya zulaiha sallama duk kuwa da tasan ba amsawa zatayi ba ta juya har suka fice tana jin tana binta da maganganu. Basu daɗe sashin mai martaba ba suka fito bayan yayita faɗa akan latti da suka sanya Hydar yayi. suka fito suka wuce school.




________



 Ummi suna tafiya Hajiya zulaiha taja tsaki tana jin ranta babu daɗi ganin yanda cikin Ummi yafito sai taji komai ya daina mata daɗi, Hajiya zulaiha macece mai masifar zafin rai da zafin kishi sam batada haƙuri kusan duk wanda zai zauna da ita toh haƙuri suke da wasu halayenta. Mai martaba kawai take iya ɗagawa ƙafa saboda irin soyayyar da take masa bata yarda taga kowa ya raɓeshi ba shiyasa takan iya ɓoye wasu ɓacin ranta amma banda akan Ummi, akoda yaushe batada wani buri daya wuce ta ƙuntata mata kamar yanda take ganin itama Ummin ta ƙuntata mata na aura mata miji da tayi. Gabanta ne ya faɗi rass tunawa da tayi daga waajanta sashin mai martaba Ummi zata nufa kuma ita keda mai martaba a wannan lokaci sannan taja layi akan hakan miƙewa tayi ta nufi sashin babu ɓata lokaci ta shirya shiga sashin mai martaba. ba kamar yanda Hajiya zulaiha taso ba domin bata isa ta samu Ummi a wajansa ba taso ace ta sameta yanda zatayi mata tijara son ranta. Palaour ta samu mai martaba lokacin yana ƙoƙarin fara breakfast domin bai samu damar yin breakfast ba har saida yaga tafiyarsu Hydar. Da sallama tashiga ta zauna gefensa bayan ta sallami wacce take shirya masa breakfast ɗin, ita da kanta tahau harhaɗa masa abincib mai martaba yana kishingiɗe yana dubanta tana haɗa masa breakfast, gyaran murya yayi wanda yasaka tabar abunda takeyi ta ɗago ta dubeshi.


"Hajiya Fulani wai yaya akayi Su Abbana sukayi zaman sama da 30minute a sashinki batare da kinsan sunzo ba? Sam banji daɗin yanda yaron nan yayi lattin makaranta ba, Saida ta kammala ta zubawa ta ajiye gabansa sannan tayi murmushi tace.


"Takawa ranka shi daɗe nima kasan bazanso ace yayi lattin makaranta ba sam bansan da zuwansu ba kamar yanda na sanar maka bayan sun fita nakira Jakadiya na hauta da faɗa sosai shine take shaida min akan tashiga ta samu ina wanka dake tasan yanayin daɗewar da nake a wanka kuma sai bata dawo ta sake sanar dani da wuri ba" jijjiga kai Mai martaba yayi sannan yace. 


"Akiyaye gaba dan Allah" 


"In sha Allah" tafaɗa sannan ta gyara zamanta a lokacin da mai martaba ya miƙe yafara cin abincin, sai da ta tabbatar ya kammala sannan ta gyara zaman mayafinta cikin tana murmushi batare da tayi maganaba. Mai martaba ya kalleta yasan da akwai abunda take buƙata don sani hali yafi sanin kamanni yace.


"Akwai wani abunne Hajiya Fulani?"


"Takawa dama idan kamiun izini gidan Ciroma nakeso na leƙa domin na kwana biyu ban leƙasu ba" Komawa mai martaba yayi ya kishingiɗe sannan yace.


"Bakuyi waya dashi ba koh?" kai ta jijjiga sannan ta ɗaura da faɗin.


"A'a bamuyi ba"


"Jiya na kirashi na turashi wani aiki kuma inada tabbacin yau yakama hanya ta'iya yiwuwa yaga lokaci baija da zai iya kirana ya sanar dani ya kama hanya bane yasa baiyiba" Cikin harshen fulatanci Hajiya Fualni tace.



"Toh Allah yakaishi lafiya ya dawo dasu lafiya ya kuma bada sa'a, zaiyi tafiyar da nisa kenan?" ta tambaya domin tana son jin abunda aka aikashi yayi.

Lumshe ido mai martaba yayi ya jin gina da royal tun-tun dake gefensa sannan yace.


"kwangilace wacce aka aikota nan fada saninki kuma babu wanda zaiyita yanda ya kamata sai shi shiyasa na turashi. nayi miki izini da zarar yadawo zaki iya zuwa gidansa" Cike da jin daɗi Hajiya zulaiha take yiwa Mai martaba godiya domin taji daɗin yanda mai martaba duk wani abu Babba daya taso baya ɗaura kowa sai ɗan uwanta a saninta baida wani amincecce bayanshi tun tasowarsu har izuwa yanzu. Hajiya zulaiha bata bar sashin mai martaba ba har saida ya shirya shiga Fada sannan tayi masa sallama tafito."





#*Ƴan tagwaye biyar*#

#*Wata alaƙa*#

#*zeeyy bawa#

#*stylish btch

#*Love & deatiny*