chapter 1
by @maikosai53
***
FATIMA ZAHRA
©Mai ƙosai
FCWA
Alhamdullilah Alakulli halin! Kamar kodayaushe yauma na dawo cikin wani sabon littafin nawa mai taken FATIMA ZAHRA, ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki da ya bani ikon kammala shi kamar yadda ya ba ni ikon fara rubuta labarin, ya sa na rubuta daidai wanda al'umma zasu amfana da shi, amin.
1.
Kano gari ne mai cike da tarin ɗumbin albarka, wacce ake yi wa kira da, 'Kano ta dabo tumbin giwa, ko da me kazo an fika' wacce ake yi wa kirari da, 'kano jalla babbar Hausa, garin da ba kano ba dajin Allah, mai mata mai mota, mai dala da goron dutse.'
Kano na ɗaya daga cikin manyan birane a ƙasar Hausa. Kano ita ce cibiyar kasuwanci ta Najeriya gaba ɗaya. jihar da take da ƙananan hukumomi guda arba'in da huɗu. Kano gari ne da yake da masarauta mai ɗunbun tarihi, mai kwarjini a cikin ƙasashen Hausa da kewaye. Haka kuma Kano gari ne babba wanda mazauna cikinsa ke magana da harshen Hausa. Kano ita ce gari mafi yawan jama'a a Nijeriya gaba ɗaya. Kamar yadda take jiha babba haka take da unguwanni da dama.
Mandawari.
Unguwace da ke cikin garin Kano, wacce take da sassa da dama, sai dai Zahra na zaune a cikin unguwar ba tare da an samu sauyin sunan gidansu ba wato dai lambar gidansu ta nuna ta Mandawari ce ba ɗaya daga cikin reshen Mandawarin ba. Zaune take ita da iyayenta guda biyu da kuma ƙannenta cikin farin ciki da kwanciyar hankali kafin ƙaddara ta juya akalar wannan farin cikin nasu, inda ta jefa iyayinta cikin ruɗu da tunanin shin anya Zahransu ce da suka sani tun farko? Ta yi silar cusa zukatansu cikin wasi-wasi, duk da ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin sun fahimci ita ɗin ce ba wata ba, ita ɗin ce dai da suka bawa cikakkiyar tarbiya kuma bata rushe wannan tarbiyar ba.
19-Agust, 2018.
Zaune take bakin gefen gado, ta sanya duka tafin hannayenta guda saman kuncinta, ba ta ji lokacin da ƙanwarta Husna ta shigo ɗakin ba, domin ta ri ga ta zurfafa cikin tunanin da ta faɗa.
Hawayen da suke sillowa daga cikin kurmin idanunta su suka tabbatarwa da Husna halin da yayarta ta ke ciki, ba tare da neman jin karin sharhin kukan ba ta soma magana,
"Wai don Allah yaya ba za ki daina wahalar da kanki ba, ba za ki cire shi daga zuciyarki ba ki bi umarnin su Abba?"
Sauke numfashi ta yi, ba tare da ta sa hannu ta goge hawayen da ke ta saraftu kan kuncinta ba ta ce,
"Hmm! Husna ke nan, ke yarinya ce baki san mene ne so ba, ba ki san me kalmar so take nufi ba. Wallahi har cikin zuciyata nake jinsa Husna bana jin zan iya rabuwa da shi, su Abba na neman sabauta rayuwata."
Da ido Husna ke bin ta, kafin ta ce,
"Idan har haka so yake yaya to bana fata na tsinci kaina cikinsa, kuma ina rokon Allah da ya shata min layi da shi. Don Allah karki watsar da tarbiyar da su Abba suka jima suna ginawa akanki yaya."
"Hmm! Husna ke nan, so ai ya zama dole tun da shi ne tsanin da zamu taka muje ga babban buri."
Husna ta mike tare da faɗin,
"Kizo umma na kiranki, ta ce tun da kika shigo daga makaranta ba ki leko ta ba."
Tana faɗin haka ta juya ta fice daga dakin, yayin da Zahra ta bita da kallo, tana sauke wata iriyar ajjiyar numfashi.
Husna ita ce 'ya ta uku cikin jerin yaran gidan Malam Ahmadu, mutum mai karamci da girmama jama'a, uwa uba ga kawaici da sanin dattako, wannan ya sa mutane da yawa ke girmama shi tare da ganin kima da darajar iyalansa. Anawar shi ne ɗa na farko, sai Mustafa ɗan auta wato na huɗunsu, yayin da Zahra ke a matsayin 'ya ta biyu. Daidai gwargwado iyayen sun tsaya kai da fata sun bawa yaran nasu tarbiya, duk da so da kaunar da suke yi musu bai sa hakan ya rufe musu ido sun gaza wajen inganta musu tarbiya.
ASABAR
Rana ce da Zahra ke hutu kasancewar ba ta da lecture, wannan ita ce ta sake bata damar nutsuwa da sake kutsawa cikin tunanin da kodayaushe ke mata zabari. Har a yau bata jin zata iya hakura da shi, tana sake jin soyayyarsa na sake komawa sabuwa dal cikin zuciyarta.
"Aunty ga shi in ji yaya Abdul" ta ji maganar Mustafa ta daki kunnenta hakan ne ya haddasa mata katsewar tunanin da take yi.
Cike da hanzari ta mika hannu ta karɓa, fuskarta washe tamkar wata gonar auduga, domin tana jin cewa wannan wasikar kaɗai za ta iya yaye mata duhun zucin da take ciki.
A hankali ta soma warware doguwar takardar da ke cike da rubutu, cike da zakuwa ta soma karantawa. Sai dai tuni annurin da ke wanze saman fuskarta ya ɗauke tamkar ɗaukewar wutar lantarki, ji take wani jiri na kwasarta yana neman son kadata da kasa, gaba ɗaya kafafuwanta sun gaza ɗaukar nauyinta, tuni ta koma ta zube gefen gado shakwab hawaye na samun damar zubowa daga cikin idanunta.
"Lafiya yaya? Me ya faru?" Mustafa ya jefa mata tambayar.
Da kyar ta iya yi masa nuni da ya fice daga dakin, babu musu ya fita yana tunani da sake-saken abin da ya sakata kuka, tun da ya san babu abin da tafi kauna irin Abdul.
12-June, 2012.
Soyayya wata aba ce da ke kafuwa tsakanin jinsi biyu wato mace da namiji, wacce ke samun gurbin zama a cikin zukatansu. Dace da juna ke sa a sake samun ingantacciyar soyayya, soyayyar da ta ginu tsakanin Zahra da Abdul tun tana karamar sakandire. Suna jin ba za su iya rabuwa da junansu ba, suna jin babu wani mahaluki da zai iya shiga tsakaninsu har ya yi musu farraku.
Farkon Haɗuwa.
A gajiye take likis ta dawo daga makaranta, burinta kawai ta isa gida ta yada jiki bayan ta sanyawa cikinta abin da yake biɗa.
Daidai bakin layinsu ta ji zazzakar sautin muryarsa, duk da cewa ba baƙuwar muryace a wajenta ba, domin mutumin da ta jima da sani ne, sai dai a yau ta ji salon muryar ta yi mata daban. Tamkar ba zata tsaya ba sai kuma ta juyo tana kallon fuskarsa da tuni ta ga ta yi mata kwarjini. Jin yadda zuciyarta ke harbawa ya hanata damar tsayawa ta saurari kalamansa, da sauri ta shige gida tana yada numfashi. Kai tsaye ɗakinsu ta wuce ta jefar da jakar hannunta, zubewa ta yi kan kujera tana sauke numfarfashi, tare da lumshe idanuwanta. Take fuskarsa ta soma yi mata gizo, murmushinsa na sake yi mata yawo kan majigin idanuwanta.
"Ke Zahra lafiyar kalau?" Kalaman umma suka doki dodon kunnenta, wanda suka sababa mata farfaɗowa daga suman wucin gadin da ta yi, tare da dawo da ita duniyarta ta zahiri.
"Uhm! Babu komai fa."
"Babu komai kika shigo ko sallama babu, ina magana kika wuce ɗaki kaitsaye?"
Sai a sannan ta tuna da ko sallama ba ta yi ba, shiru ta yi ba ta iya ce mata komai ba, tana ji umman na cewa,
"Ki fito ki watsa ruwa ki ɗau abincinki, idan kuma kin koshi shi ke nan."
Ita dai sauke ajjiyar zuciya take yi, tana faman murmusawa. Ta ɗan jima a ɗakin kafin ta fito don watsa ruwa.
Mai ƙosai
Inna fata za ku nuna min kauna kamar yadda kuka yi a baya kuka karɓi littafin HAFSATUL-KIRAM cikin aminci. Hallau dai kar a manta da COMMENT, VOTE and SHARE.