WATA ALAƘA

SHIDA

by @zeeeyybawa

*WATA ALAƘA.....!*

*PAID BOOK* 

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* 


NA


STYLISH BTCH

Da

ZAYNAB BAWA


*SHAFI NA SHIDA*


  8am saura kaɗan tacika Hydar suka isa school lokacin har ana shirin kulle gate ɗib da ake shiga dashi sun dakata ne kawai domin ba'a sanar dasu bazai samu zuwwa. A harabar makarantar dake baya akayi parking motocin da suka kawo Hydar, tare Ummi suka fito a cikin motar da Hydar bayan tagoya masa school bag ɗinsa a baya ta amshi ta lunchbox ɗinsa ta riƙe, ma'aikackyar da akayi assigning domin shigar da Hydar Aliyu Turad da kuma fito dashi bayan antashi tayi masa jagora har izuwa wajan motacin da zasu ɗaukeshi itace wacce tayi musu jagora har izuwa class ɗinsu Hydar, A lokacin da 8:00am tacika dott yayi dai-dai da lokacin da classroom teacher ɗinsu itama ta shigo nannys kam dama already suna a cikin class ɗin domin kula da student da ake shigo dasu kusan kaff student ɗin sun hallara saura Hydar Aliyu Turad kaɗai, Hidaya gabaki aya idonta ya cicciko da hawaye tunda taga Abbanta ya ajiye kuma babu Hydar a cikin class ɗin tafara hawaye tana shirin fara kuka. Hydar da Umminsa suna shigowa Hidaya ta ƙwala ihu irin nasu na yara a lokacin da idonta ya sauka akan Hydar.


"Yeahh Aydar, Aydar" shine abunda take faɗa taba tsalle. Hydar ma sake hannun Umminsa yayi ya nufo Hidaya sai da yazo dai-dai seat ɗinta ya tsaya fuskarshi cike da fara'a. fitowa Hidaya tayi daga cikin seat ɗin ta saƙalo hannuwanta a wuyan Hydar sai tsalle takeyi tana murna shikuma yana Dariya, Ummin sa wacce ke tsaye tana kallonsu sai abun ya burgeta, murmushi ta saki tana ganin yanda yarinyar data tabbatar itace Hidaya take tsakke da murnar ganin Hydar hakan ya tabbatar da Hydar kaɗai ya ƙwallafa yarinyar a ransa ba harda ita yarinyar, bayan Hidaya tagama tsalle-tsallenta Hydar ya kamo hannunta zuwa gaban Ummiensa cikin harshen larabci da yafi iyawa akan kowane irin yare kasancewar yafi zama da umminsa akan kowa yace.


"أمي انها هدايا "

(Ummi itace Hidaya) Rage tsayi Ummi tayi a hankali ta shafo fuskar Hidaya wacce har a lokacin fara'arta bata ɓace ba, kamar yanda Ummi ta saka hannu ta shafo Hidaya haka itama Hidaya tasa hannu ta shafi fuskar Ummi saida tasaka Ummi dariya, cike da jin daɗi Hydar ya dubi Hidaya batareda sani bata jin harshen larabci ba yace.


"هدايا هيً أمي"

(Hidaya wannan ce Ummina) Hidaya bata fahimci abunda yane Faɗa ba Ummin cikin kawai ta tsinta don haka tace Ummie? Gyada mata kai Hydar yayi cike da jin daɗi. Miƙewa Ummi tayi dake cikin jikinta bazai barta ta daɗe a tsugunne ba. ta kamo Hannun Hydat dana Hidaya har izuwa seat ɗin kowanne daga cikinsu idonta yakai kan sunan dake rubuce a jikin seat na Hidaya "SADIYA MUHAMMAD ARABI" Maimaita sunan tayi cikin ranta bayan ta zaunar da kowannesu a seat ɗinsu batayu spending yafi 5minute atare dasu ba saboda class zai fara ta juya tare da yiwa classroom teacher sallama tafice. Tana fita classroom teacher tafara kiran sunan kowannesu ɗaya bayan ɗaya domin tabbatar da kowa ya iso duk da kowanne seat is occupied tabbacin kowanne student yana zaune a mazauninsa. 


"Sadiya Muhammad Arabi" 

"Sadiya Muhammad arabi" Classroom teachern take kira amma Hidaya bata amsa ba bata san ana kiranta ba hankalinta gabaki ɗaya yana wajan Hydar tana bashi labarin maminta tayi musu meatpie. Hydar ne ya taɓata ya nuna mata ana kiran sunanta domin tun jiya da yaji sunan yafara kiranta dashi ta ɓata rai akan ita sunanta Hidaya shine ya canja zuwa Hidaya batareda ya manta ɗaya sunan nata ba. Juyawa Hidaya tayi ta amsa sannan tacigaba da bashi labari shikuma yana sauraronta yana murmushi har izuwa lokacin da clasaroom teachern ta kammala kiran sunan kaff student ɗin sannan tayi amfani da dabarunta ta sakasu yin shiru.

_____


 Ummi na fita daga class ɗin kai tsaye hanyar da suka biyo tabi don komawa ranta yayi sanyi yanzu taga Hidaya kuma taga itama yanda take ɗaukin ganin Hydar ɗin alamu ya nuna kamar tafishi ɗaukinma kodan shi namiji ne kuma bamai hayaniya ba yasa nasan bai fito kamar nata ba. A yanda taga Hidaya ta tabbata iyayenta suma zasu sha surutu akan Hydar har ta isa mota tunanin Hydar da Hidaya takeyi yanda sabo yashiga tsakaninsu lokaci guda batare lamarin har abun mamaki. Dake Drivern Hydar da masu tsaronsa sai antashi zasu koma dashi yasa tun daga gida Ummi tazo da Driver da zai maidata, Sallama tayiwa masu tsaron Hydar ta shiga mota aka fice da ita sannan aka kulke gate na school ɗin.

_____


Tunda motarsu Ummi ta shige cikin masarautar taji wani yanayi yana riskarta wanda ba zata iya cewa ga kalarsa ba bare tasan musabbabin abinda ya janyo mata shiga yanayin. Addu'a ta farayi har driver ya gama yin parking a bakin apartment dinta. Ji tayi ta kasa fitowa daga cikin motar tana jin kafafuwanta sunyi mata nauyi ko motsa su bata iya yi. A fili take fadin. 


"La'ilaha illah anta subahanaka inni kuntu Minal zali min, ya haihu ya kayyum ya giyasil mustaqim." Tana idarwa taji kafafuwanta suna motsawa dan haka ta daure ta fito daga motar cikin dauriya ta nufi ciki, domi ko kadan bata son yin abinda za'a je a gayawa Hajja Fulani bare ta samu damar yi mata abinda zai saka zuciyarta kunci da damuwa. 


"Takawarki lafiya farin cikin mai martaba, an gaisheki Maman magajin sarki Aliyu dan Aliyu sukari bakiyi farin banza ba. Sannu da dawowa fitilar mai martaba." Ummi batace komai ba dan ta riga da ta sabajin irin wadannan kodawar daga bakin mutane tun bata fahimtatarsu har ta dawo tasan ma'anonin wasu daga cikinsu, Idan anayi bata kulawa take barin wajan domin duk lokacin da aka yi mata su a gaban Hajja Fulani sai ranta da na wadanda sukai yi kirarin ya baci. Ummi bata da hayaniya hasalima bata yi tun yarintarta har girma gashi kuma tayi aure, hakurin ta da rashin son fitina shine yake kara mata girma da matsayi a wajan mijin su dama mutanen da suka rabeta. Ko gani tayi Hajja Fulani tana masifa da tada jijiyar wuya tausayinta takeyi takan ji ina ma ace zata iya bata shawara da ta bata. Tana cire hijab din jikinta ta saki murmushi tuna yanayin da ta baro yaronta. Bathroom ta wuce tayo wanka da alwala ta zura doguwar riga marar nauyi ta fara sallar walha kamar yadda ta saba. 



_______



 Atine wacce daya ce daga cikin hadiman Ummi kuma gulmammiyar da take zukar duk wani abu da aka yi a gabanta taje ta sanarwa Hajja Fulani, itace ta zame ta nufi apartment din Fulani zuciyarta cike da munafunci dan ta ƙagu taje ta sanar da abinda yake ranta. Iso aka yi mata dan ana cewa Fulanin Sarki Atine ce tazo babu wani jan aji ko izzah kawai tace a shigo da ita ciki. Atine na shiga jikinta yana rawa ta durkushe a gaban Hajja Fulani duk da cewa bata da yakinin abinda zata fada zai yi tasiri a zuciyar Fulanin dan ba komai take bawa muhimmanci ba idan ta sanar da ita. 


"Ya aike Atine?" 


"Allah ya kara miki lafiya, yanzu waccan sadakar yallar ta dawo. A yadda naji yau itace takai yaronta makaranta." Hajja Fulani dake kishingide tayi saurin mikewa zaune tana waro idanuwa. Kafin tace wani abun Atine taci gaba da cewa. 


"Duk yadda kike jan kunnan Tani akan kirarin da take yiwa matar can wanda bai cancanci ayi mata ba, Tani ta kasa denawa, harda cewa farin cikin mai martaba a rai na nace to ke kuma wane matsayi take baki?" 


"Tani? Wato Tani bata jin maganata ko?" Fulani ta fada ranta yana zafi. 


"Ai ranki ya dade wasu abubuwan ma bazan iya faɗa bane dan Tani tana wuce iyakarta a gaban sadakar yalla." Da yake duk wasu masu goyan bayan Fulani sadakar yalla suke cewa Ummin Hydar idan har suna gaban Fulanin. Idan kuma a gaban Ummi ne masifar biyayya sukeyi mata fiye da yadda suke yiwa Hajja Fulani. 


"Zanyi maganin Tani, bana san gulma sannan bana san yaudara. Tani bata Kai matsayin da zan ce ayi abu ta dinga kin yi ba. Kamar kullum zansa a kirata, karki mata magana dan kar ma ta gane cewa kece kike gaya min komai." 


"To ranki ya dade maji dadin mai martaba, tauraruwar da babu matsayin ta, matar sarki, jikar sarki kun gaji sarauta dan ba haye bace gado ce, kinfi su kinfi sauran mata." Atine ta fada tare da mikewa tana yin baya kanta a kasa harta bar parlorn. Fulani ta sauke numfashi tana haskilo fuskar Ummi da tutsetsen cikin dake jikinta. Me hakan yake nufi? Me suke nufi da kai Hydar school ba tare da an bari driver da masu kula dashi sun kaisu ba? Haka kawai taji ranta na zafi tana ganin kamar saboda ita ne suka tsiri wannan abun idan banda haka wace gulma ce zata sa Ummi kai Hydar school da kanta. Juyawa tayi ta dubi kanwar mahaifiyarta wacce take zaune a kujerar kusa da ita, zuwanta kenan altine tashigo da muryar da take nuni da ranta yana matukar ɓace tace.


"Aunty kinji wani rainin hankali? Wai da kanta taje ta kaishi can you Imagine tana fama da tirtsetsan ciki tana fito da salon munafunci?" kyaɓe baki ƙanwar mahaifiyar Fulanin Sarki tayi sannan tace.


"Abunne najishi jima yamin wani iri shiyasa nakasa cewa komai har Altine tafita"


"Ai dole kikasa magana Anty koda yaushe da wani sabon salon munafurcin da take fitowa dashi shikuma Takawa a koda yaushe biye mata yakeyi sam baya fahintar makircu irin nata" Nisawa Antyn Fulani tayi ga dukkan alamu akwai magana sosai a cikinta miƙewa tayi haɗeda faɗin.


"Tashi mushiga ciki" Bbu musu Fulani ta miƙe don ta lura akwai magana a bakin ƙanwar mahaifiyartata. Saida suka ƙule can cikin ɗakin Hajiya zulaiha sannan ta dubeta da damuwa cike a fuska tace.


"Fulanin sarki kinsan fa dole hankalin mai martaba ya karkata zuwa kan wannan yarinyar basai na faɗa miki ba kinfini sanin dalili, bayan haka yakamata kiyi tunani ace kinyi shekara dashi amma lokaci guda tazo tanaso ta amshe komai da komai, ke kyace lafiya? Na tausaya miki matuƙa a lokacin da naji mai martaba ua auro ƴar ƙasar Egypt wanda ake faɗin sune suke da the most beautiful arab women, ba wannan ba yawnacinsu fa matsafa ne, sufa tsafi ma sukeyi. A kowace ƙasa tsoran auro matansu sukeyi sbaoda duk yanda suka zauna sai sun mallake wajan sun kanainaye komai, a auran da bai ida cika shekara huɗu ba Hydar ko shekara uku ina tunanin bai ida cikawa ba gashi nan yau ko gobe wata haihuwar zata sake kinga ta ɗaura niyyar kanainaye komai kuma kinsan yanda mai martaba yake akan yara ke zaki bada labarin hakan" tsoro da firgici suka cika Fulani idanuwan ta suka cicciko da hawaye ta dubi Ƙanwar mahaifiyarta"Anty yanzu yaya za'ayi?"


"Yanzu kam fulani ai sai mun zauna akan wannan lamarin tun wuri saken da kikayi shine da kika barta harta fara haihuwa da ta haifi ɗaya nayi tunanin kinada wayon da zaki ɗauki measures yanda bazata sake ba kwatsam ranar saiga labarin wani cikin lokacinma harya girma.


"Anty ciroma ke hanani aikata komai koda nace zanyi wani abun sai yace A'a nabi komai a sannu" 


"Eh toh ba'aƙin ta mutum amma kema ai bakya zauna haka kara zube don yace karkiyi komai ba" Cikkn ƙosawa Fulani tace.


"Yaya za'ayi yanzu"


"Yanzu dai mugama abunda ya kawoni Zanje nasan ta hanyar da zamu biyo" Kai Fulani ta jijjiga gabaki ɗaya hankalinta atashe yake batason wani abun da za'ace zai iya nisantata da Mai martaba taƙi jinin duk wani abin da zai iya giftawa ta tsakaninsu ya raunata alaƙar da takeji kamar kaff duniya babu wanda yakaita kusanci dashi. Kasancewar sun ɗauki tsawon shekaru atare ta sanshi ciki da bai fiye da sanin da kowace ƴa mace tayi masa bata so ace yau wata mace tazo ta goge mata wannan tarihin data shimfiɗa, canja akalar maganarsu sukayi izuwa abunda ya kawo Antyn Fulani amma Fulani hankalinta gabaki ɗaya baya wajan. 




#Zee Bawa 

#Stylish bch 

#Yan Tagwaye 

#Love and destiny