BABI NA SHA ƊAYA
by @billysfari
GS 11.
Da yake yau tana cikin farin ciki gabaki ɗaya ta manta da wata Jauhar a cikin gidan, su Suhaila ta tarar a parlour suna ta cin kayan kwalam ɗin da Jannat tazo musu dashi wanda ko tunanin ajiyewa Jauhar basu yi ba, dama ita tsakanin ta da irin abubuwan sai idan sun rage taje gyara gurin idan taji abu ya bata sha'awa koya burgeta sai ta ɗauka taci idan na ci ne, idan kuma na sha ne shima ta tsotse ta maida mugun yawu. Dukkansu kallonta sukeyi ganin farin ciki yaki gushewa akan fuskarta yasa Suhaila gyara zama tana murmushi take cewa.
"Mommy sai farin ciki kike yi ko ƙanwa za'a yiwa Baby Jay?" Duk da kasancewar kalmar tayi matukar nauyi da ya kamata ace Hajja Maimoon ta yiwa Suhaila magana akai, sai kawai Hajja Maimoon ɗin tayi dariya kasancewar farin cikin da take ciki bata kawo wani abu na ɓacin rai a lokacin bare har ta tsawatar tana cewa.
"No... No.. No Suhaila! Ni ai kun isheni hakan nan ba sai an sake kawo wani babyn ba. Ku tayani murna zan fara business kamar yadda kuka san cewa dama tun da nazo ina yinsa. Kunsan ƴar matsala na samu wacce tasa dole na ajiye komai. Kuma wannan karon ba a gida kawai zanyi ba Daddyn ku zai kama min shago a can bakin titi." Gabaki ɗayansu suka tayata murna wanda hakan ya sake farantawa Hajja Maimoon zuciya tana sake jin yaran a cikin zuciyarta.
_____
Tunda ya nufi layin gidan mutane suke ɗaga masa hannu yana yi musu horn alamar amsawa fuskarsa kunshe da murmushi. Yana isa wajan gate ya yi parking bai shiga da motar ba kasancewar ba daɗewa zai yi a ciki ba. Har Alhaji Sha'aban ya shiga parlorn Hajiyarsu mutanan dake shawagi a gidan basu dena gaishe shi ba. Zaune ya tarar dasu tana inda take zama tayi sallah yayin da Irfaan ke kwance cikin 3seater ya ɗora laptop a saman cikin sa yana aiki a ciki. Maryam ƙanwarsu wacce ta kasance auta a wajan Hajiya tana zaune wajan center table ta ɗora handouts da alama assignment takeyi, shigowarsa yasa har Hajiya dake dama fura cikin ƙoƙo sai da ta dawo da hankalinta wajansa, sosai take jinsa a ranta haka kuma bata haɗashi da kowa a kaf cikin yaranta, kauna take masa wacce ita kanta idan aka ce ta faɗi irinta ba zata iya bayyanawa ba saboda mutum ne shi da yake bata matsayinta na uwa a gareshi fiye da tunani.
"Hajiya sannu da aiki." Ta amsa masa,
"Yauwa sannu da shigowa. Maimakon kayi kwanciyarka ka huta shine sai da ka taso kazo har nan?" Murmushi yayi yace,
"Hajiya ai nazo naga lafiyarki, idan na kwanta banzo ba tunani zantayi ina jin babu daɗi."
"Yaya sannu da zuwa." Maryam ta faɗa tana karkaɗa biron hannunta.
"Yauwa Auta kina ganin Hajiya na aiki baki tayata ba ko?" Cikin sauri Maryam tace.
"Yaya wallahi cewa tayi in bar mata zatayi wai ban iya dama furar yadda takeso ba." Ta faɗa tana maida idanunta kan takardun ta.
"Eh naji, amma da ta faɗi hakan maimakon kizo kiga yadda takeso ɗin ki koya shine kika barta tana yi." Irfaan dake kwance ne ya tashi zaune yana cewa.
"Yaya barka da zuwa." Yana magana yana haɗe rai tamkar wanda basa zaman lafiya.
"Yauwa Irfaan." Alhaji Sha'aban ya furta yana kallon yanayinsa, duk da cewar yawan tambaya akan abinda ba'a nemi ya sani ba baya daga cikin al'amuransa. Sai dai a yanayin ɗaya ga ƙanin nasa yasa shi son jin ko meye damuwarsa.
"Naga kamar kana cikin ɓacin rai, lafiya dai ko?" Irfaan ya sake tsuke fuska yana janyo wayarsa dake gefensa yace.
"Ba komai." Hajiya najin su tayi murmushi jin abinda Irfaan yace. Dama zaiyi wahala ya iya gayawa Yayan nasu abinda yake damunsa domin suna masa kallon uba ne dan shine tsaye akan su. Hajiya tasan duk masifar da Irfaan yayi akan matsalar Jauhar da yake cewa harda laifin Alhaji Sha'aban tasan ko da wasa ba zai iya rufe ido ya yi a gabansa ba. Kallon Maryam Hajiya tayi tace.
"Zoki ɗakko kofi na zubawa Yayanku fura da nono yasha." Da sauri Alhaji Sha'aban yace.
"A'a Hajiya kisha abarki." Maryam jin yace abarshi yasa ta koma ta zauna, Hajiya ta kalleta.
"Ke kuma daga yace insha abuna shine kika fasa ɗakkowa? Yanzu fa naji ya yi miki faɗa akan kulawa da abubuwa. Tashi ki ɗakko ai ba mai yawa zan zuba maka ba."
"Nima fa nace zan sha." Cewar Irfaan jin ba'a ce a taho da nashi kofin ba.
"Kai da kace sai mai ayaba da kwakwa a ciki? Meye kuma na canza shawara?" Alhaji Sha'aban yace,
"Kishi ne da alama." Gabaki ɗaya sukayi dariya. Kofuna uku Maryam ta dire tana durƙushewa a gaban Hajiya tare da cewa.
"Kawo na zuba mana." Da sauri Alhaji Sha'aban ya nufi wajan, karɓar ƙoƙon ya yi tare da cewa,
"Kawo nasan wayo kika shirya yiwa Hajiya ta." Duk suka sake yin dariya ya zubawa kowa a cikin kofi shima ya zuba ƴar kaɗan dan ma kartaga bai shaba taji babu daɗi shi yasa ya zuba. Sai da ya fara miƙa mata wacce zata sha sannan ya miƙe ya koma kan kujera. Irfaan ya karɓi tashi a hannun Maryam ya nufi wajan fridge, ƙanƙara da madarar freshyo ya zuba a ciki sannan ya koma inda ya taso ya zauna.
"Wai meke faruwa tsakanin Maimuna da yarinyar nan da take mata aiki?" Hajiya ta jefo maganar wacce sai da Alhaji Sha'aban yaji ta har cikin zuciyarsa dan bai taɓa tunanin zatayi masa ita ba. Irfaan yai saurin tashi zai bar gurin dan bai shirya yin wannan maganar da Yayansa ba.
"Dawo ka zauna Irfaan ai da kai za'a yi maganar." Cike da wata irin kunya ya koma duk da yana jin zuciyarsa tana karfafa shi akan karya ƙi yin abinda yake ganin mafuta ce a wajan Jauhar. Kamar marar gaskiya haka ya koma ya zauna yana jujjuya spoon ɗin hannunsa yama kasa shan furar yadda ya kamata.
"Hajiya wani abun ne ya faru? Daga gidan nake amma banji ance da matsala ba." Hajiya bata ce komai ba sai kallon inda Irfaan yake da tayi tana jiran ya yi bayani. Dariya ce ta kwace mata ganin ko inda suke zaune Irfaan ɗin be kalla ba dan haka Hajiya ta daure tare da cewa.
"Sanar masa abinda ya faru Irfaan." Cike da jin nauyi dan baisan a yadda Alhaji Sha'aban ɗin zai ɗauki maganar da zai yi ba. Da kyar Irfaan ya daure jin da yayi shi ake jira ya yi bayani, ya daure yace.
"Yaya kamar dai yadda kasani ne, ni wallahi kawai bana son ana cin zalin yarinyar nan saboda duk abinda ya sameta a gidan Yayana ne. Bana son naga ana musguna mata kuma wai a gidanka Yaya kai da kake mutum mai tausayi akan komai..."
"Please kayi min bayani sosai meke faruwa a gidan nawa?" Alhaji Sha'aban ya katse shi dan ya matsu yaji. Murya Irfaan ya sanyaya tare da sake yin ƙasa da kanshi yace.
"Jauhar koda ta kasance ƴar aiki a gidanka, sam bai dace ana yi mata wasu abubuwan ba. Yaya kaga kai ne kace mu tafi da yarinyar nan asibiti amma wallahi karkaga da yadda suka yadda ta shiga motar nan, munje asibitin ma aka rubuta magunguna amma haka Aunty Maimoon tace ba zata siya dana Jauhar ɗin ba tasa aka bada na Jannat kaɗai. Duk da haka Yaya na fito na siyawa Jauhar ɗin magani da kuɗi na sai na haɗa da wata ƴar riga nace tayi amfani dasu dan naga a yadda take rayuwa kuma wai a gidan ka Yaya. Shine Auntyn ta kwace kayan harda cewa wai...." Da sauri Alhaji Sha'aban ya katse shi dan yanaji a ransa maganar karshen babu alkairi a cikinta kuma yasan itace mafi munin ji a duk maganganun da yake ji daga bakin ƙanin nasa. Shi kansa yafi su jin rashin daɗin yadda ake yiwa yarinyar, ya yi kuma iya yinsa wajan nunar da Maimoon hakan ba daidai bane amma ta nuna masa cewa tun daga wajan iyayenta komai yake faruwa, ta kuma tabbatar masa da cewa idan har ta bari Jauhar ta samu kwanciyar hankali toh tabbas ita kuma zata kasance cikin damuwa. A lokacin ya hango tsantsar haushi, bakin ciki da kuma damuwa akan fuskarta wanda ya tabbatar da har ranta take jin haushin cewa da ya yi ta kula da yarinyar.
"Wai kana sane ake yiwa yarinyar nan haka? Kulawarta yana kanka fa yanzu ba wai dan tana mai aiki ba kayi shiru ana mata ba daidai ba. Kuma ita kaɗai ce ake samun matsalar nan ko masu gadi sun fita jin daɗi da kwanciyar hankali ita da take mace mai ƙananun shekaru. Idan ba zaku kula da ita ba ya kamata ku maidawa iyayenta abarsu suyi yadda zasuyi da ita, bana son zalunci ban kuma koya muku shi ba, haka zalika bance ku bari ayi ba." Shiru Alhaji Sha'aban ya yi yana jin damuwa a cikin zuciyarsa, shi kam besan yadda zai yi da matsalar nan ba harga Allah, amma saboda ya kwantar musu da hankali tunda dai sun shiga damuwar ne saboda shi dan haka cikin taushin murya yake cewa.
"Insha Allahu za'a gyara Hajiya, ni nafi ganin laifin iyayen Jauhar saboda tun lokacin da nake neman auran Maimoon tare suke kuma babu abinda ya canza na game da yadda suke rayuwa da ita. Naso yiwa mahaifin Maimoon magana amma ya nuna min cewa gwara abarta a wajanta yafi mutunci akansu su riƙe ta."
"Kasan ɗan kauye kuma da muguwar kafiya, ana nuna masa gabas yana cewa yamma yafi. Duk da haka kayi ƙoƙarin ganin an sassautawa yarinyar, haka duk sanda Maryam taje gidanka sai tayi min ƙorafin yadda take ganin yarinyar, kuma wai da kazantar nan take yi muku girki ku cinye." Alhaji Sha'aban dai ya yi shiru baice komai ba dan shi kansa abun nan yana bashi haushi yadda Jauhar take rayuwa dasu cikin rashin daraja. Ganin Hajiya tasa baki yasa Irfaan yaji hankalinsa ya ɗan kwanta, sannan yaji karfin guiwar samun damar taimakawa Jauhar ɗin. Sun taɓa hira sosai kafin yasa hannu cikin aljihu ya zaro sarƙa da ɗankunnen da ya siyawa Hajiyan, ya miƙe tare da isa wajanta ya durƙusa har ƙasa ya saka mata a cikin tafin hannunta. Kallon hannun Hajiya tayi kafin ta kalleshi da sauri tana cewa.
"Na menene wannan?" Cike da soyayya yace.
"Naki ne Hajiya." Kallon hannun ta sake yi tana jin zuciyarta na karyewa, ta kalleshi kamar zatayi kuka dan muryarta har rawa takeyi kafin tace.
"Me yasa kake san wahalar da kanka? Haka kawai kaje ka kashe kuɗinka maimakon kasasu cikin kasuwancin ka shine zaka siyo min zinari? Ina dasu fa wajan guda nawa ma amma kaje ka sake siyo min." Murmushi ya yi tare da miƙewa tsaye yana cewa.
"Haba Hajiya, duk wani abu da zan miki koma bayan abinda kika yi min ne, ko shagon zinari na kawo miki Hajiya ban isa na biyaki ba bare dan ma siyo miki wannan. Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana domin ke ɗin garkuwa ne a garemu." Maryam ce ta taho da gudu, karɓar ƴankunnayen tayi tana jujjuyawa kafin ta narke fuska tana turo baki take faɗin.
"Toh Yaya nifa?" Ya kalleta tare da faɗin.
"Ohhh haɗa kanki kike yi da Hajiyata?" Sai da ta sake shagwaɓewa tana noƙe kafaɗa tace.
"Ni da nake ƴan mata ai ni zaka dinga kashewa kuɗi Yaya, Hajiya fa tana dasu da yawa."
"Ki bari idan kasuwa ta sake yin kyau sai na bawa Irfaan kuje a siya miki." Alhaji Sha'aban ya faɗa yana kallonta.
"Yaya kasuwa fa tana kyau, ko addu'ar da Hajiya keyi maka kaɗai ta isa tasa kasuwancinka habɓaka bare mutane da bakinsu baya gajiya wajan yi maka addu'o'i. Kawai nidai Yaya ka ce zaka tura masa kuɗin." Maryam ta faɗa tare da langaɓe kai. Sai da ya saki murmushi yace.
"Shikenan Irfaan zan tura maka sai kuje tare ta siyo." Farin ciki ya kama Maryam ta shiga murna tana yi masa addu'a Hajiya kuma na sake sanya masa albarka. Sallama ya yi musu inda Irfaan ya tashi yabi bayansa sukaje har bakin motarsa.
"Kayi amfani da Atm ɗina na wajanka Sai kuje a siyawa Maryam ɗin, ina so a siya kayan abinci a kaiwa Kawu Ibrahim karka manta dan Allah Irfaan." Cike da girmamawa Irfaan ɗin ya amsa daga nan Alhaji Sha'aban ya shiga motarsa yaja yabar unguwar.
______
Tsaki ya dinga saki ba ƙaƙƙautawa, banda zafi babu abinda zuciyarsa keyi, yaso Mama ta barshi ya faffallawa Husnah mari ko zata farka daga nannauyan baccin da takeyi na ganinta da Ilyasmater dan shi a ganinsa mafarki kawai takeyi shi yasa har ta tsaya tana sauraransa harda cewa wai saurayinta ne. A hankali ya zare rigar jikinsa yaje ya sagaleta yana sake jin wani ɓacin rai a ransa. Jikinsa babu kwari ya shiga ɓalle belt ɗin dake ɗaure a ƙugunsa ya kasa cire hotan guy ɗin nan a cikin idanunsa dama zuciyarsa. Ba irin mazan da yake son ƙannansa su dinga kulawa bane, yana da wani irin buri akan ƙannansa dan haka ne ma yake da mugun taka tsantsan akan tsare mutunci da kuma ƙimarsa dan kar yaje shima a yiwa wata a cikin ƙannansa. Jeans ɗin jikinsa ya cire ya rage daga shi sai gajeran wanda da black singlet, Wanka yake son ya yi sai dai baya son sake komawa cikin gidan. Ɗakinsa yabi da kallo yana jin takaicin rashin bathroom da babu a ciki. Da kyar ya iya karfafa zuciyarsa ya janyo jallabiyarsa da yake shiga wanka da ita ya sanya bayan ya cire singlet ɗin jikin nashi. Kwandan wankansa ya ɗauka sannan ya fito tare da janyo ƙofar ya shiga cikin gidan. Cikin sa'a ya tarar da Husnah tana tarar ruwa a fanfo bataji motsinsa ba sai ji tayi kawai an sakar mata rankwashi a tsakiyar kanta, kafin ta ɗago taji yana cewa.
"Sakarai kawai, wannan gayen meye abun burgewa tare dashi? Idan na sake ganinki dashi sai na miki shegen duka a gidan nan, bazan bari ki janyo mana surutun mutane ba." Yana kaiwa nan ya ɗauke bokitin ruwan da ta tara ya shige toilet ya barta. Husnah ta saki kuka tana rugawa cikin parlorn Mama da gudu kamar wacce aka biyo.
"Mama kinga Yaya Zain ko?" Cewar Husnah tana dafe da tsakiyar kanta.
"Kai innalillahi Wainna ilaihir raji'un wai dama bekyale ki ba da nace babu ruwansa?"
"Kuma har cewa ya yi idan na sake kula saurayi sai ya min shegen duka." Husnah ta faɗa tana sake rushewa da kuka.
"Ina jin dai auran ku zai yi, banda haka banga dalilin da zai sa yaron nan ya dinga takura muku ba dan kun kula samari, bari ya fito zai sameni gwara ya yi min bayani naji idan ya yi shirin auran ku ne sai naji dalili." Ta ƙarasa maganar tana ɗaga murya yadda Zain ɗin zai jiyo.
Rufe bakinta keda wuya sai ga Abba ya shigo. "Haba! Dawa kike wannan faɗa ake jin muryarki har ƙofar gida?" Yafaɗa yana miƙawa Husnah dake yimasa sannu da zuwa ledar dake hannunsa.
"Sannu da dawo." Itama Mama tafaɗa cikin ɗan ɓacin rai tana miƙewa daga kwance da take Husnah kuma ta karbi ledar da yake miƙo mata ta nufi kitchen da ita. "Ni da waye banda Zain kuwa yabi duk ya takurawa yarinyar nan sai kace ba ƙanwarsa ba." Sai da Abba ya zauna saman kujera sannan ya amsa sannu da Mama tayi masa yana cewa.
"In banda abunki meye laifi idan ya tsawatar mata tunda yayanta ne? Ai hakan shine dai-dai tashi ki je ki kawo mani ruwa." Yaƙare zancen haɗe da cire hular kansa ya ɗora saman hannun kujera.
Mama bata ce komai ba taje ta kawo masa abincinsa da ruwa ta ajiye masa agabansa sannan ta zuba masa ya soma ci. Bayan ya kammala ta tattare wajen ta kwashe kayan takai kitchen ta dawo. Nan ta shiga labarta masa abinda ke faruwa ba tare data tuna da halin mijin nata ba da ba goyon bayanta zaiyi ba akan wannan, dan in dai akan tarbiyar yaransa ce a tsaye yake sosai. Sauke lumfashi yai cike da mamaki yana kallonta kafin yace.
"Ina tunanin Alhamdulillah girma yazo kin sauya daga Halimar dana sani ada kin koma wata kamilalliyar Halima uwa da zata cigaba da tayani ba 'ya'yana tarbiyya idan bana kusa ashe har yau akwai sauran rina a kaba? Yanzu fisabilillahi wannan dan iskan yaro Iliya da naji ya ma sauya sunansa ya koma Iliyasmaster tsabar rashin ji ko ke kika ganta tsaye dashi baza ki koreta ki hanata sake tsayawa dashi ba? To bari kiji in faɗa maki ba Zain ba wlh koni na sake samun labarin angata tsaye da wannan ɗan iskan yaro lalatacce sai na ɓaɓɓallata kuma kema saina saɓa maki dan bazan lamunci wannan shashancin ba acikin gidana." Ya ƙare maganar cikin faɗa haɗe da ɗaukar hularsa ya maida akai ya fice daga gidan dan an kira sallar magrib, da kallo tabishi bata iya cewa komai ba saboda ranta aɓace yake itama akan ƙa'idojin nan nashi da yake kira tarbiyya dake hanata rawar gaban hantsi ita da yaranta...
#A heart touching story
#Gonar Sharri
#Billy s Fari
#Hajja ce 👈
#Ƴan Tagwaye