GONAR SHARRI...

BABI NA SHA BIYU

by @billysfari

GS 12.


Ɗaya daga cikin ƙananun shagon Alhaji Sha'aban Irfaan ɗin yaje ya kwaso duk wani abu da ya sani na daga kayan abinci kafin ya nufi gidan kawun nasu. Sai da Irfaan ɗin yasa almajirai suka sauke masa kayan abincin dake makare a boot ɗin motar suka shiga dashi ciki sannan yabi bayansu. Anan cikin zauren gidan ya iskosa zaune tare da almajiransa yana biya masu karatu. Gefe ya samu ya tsaya haɗe da fiddo wayarsa yana latsawa har sai da su kawun suka kammala almajiran suka tashi suka tafi, jefa wayarsa Irfaan ya yi cikin aljihu ya ƙarasa bisa tabarmar ya zauna cike da girmamawa yana gaida kawu Ibrahim ɗin dake tattare littafan gaban nasa waje ɗaya yana mayarwa gefe. Fuskar kawu Ibrahim a sake ya ɗago kai tare da miƙa masa hannu sukayi musabiha yana amsa gaisuwar da ya yi masa yana ɗorawa da cewa. 


"Sannu da ƙoƙari malam Irfaan ya mahaifiyar taku da ƴan uwan naka?"


"Duk suna lafiya Kawu sunce na gaisheka sosai, ga saƙonan inji Yaya yace akawo maka."


"Masha Allah, agaida Alhaji Sha'aban, ubangiji Allah yai masa albarka ya jiƙan mahaifinku. Yadda kuke kula dani tamkar ni na haifeku Allah ya kula da zuri'arku gabaki ɗaya. Nagode nagode sosai Allah ya saka da alkhairi kaima Allah ya yi maka albarka."


"Amin ya rabbi kawu."


"Taso mushiga ciki kasha ruwa kafin kawuce." Kawu Ibrahim ya faɗa yana miƙewa haɗe da gyara babbar rigarsa sannan ya yi gaba zuwa ciki. Ba yadda Irfaan ya iya dole ya miƙe yabi bayanshi suka shiga ciki.


Zaune take tana wanke kwanuka Umma na jiranta zata kwashe abinci saboda bata jima da dawowa wajen haddar Alqur'ani da suke tasowa ba bayan sallar magriba. Sallamar mahaifin nata daya shigo yana ƙwalawa Umma kira yasa ta ɗago kai, karaf sukayi ido biyu da masoyin nata da ya kafeta da idanuwa, dan tunda Irfaan yake da ita bai taɓa zuwa gidan ya iskota cikin irin wannan shigar ba ta riga da skert, da yake wuyan rigar na da ɗan faɗi zaka iya hango tudun albarkatun ƙirjinta da take dasu masha Allah. Da su Irfaan yai tozali lokacin dayake shigowa, hakan yasa yakasa ɗauke idanuwansa akanta har sai data lura da hakan ta shiga ƴan kame-kame. Murmushi Irfaan ya sakar mata ta sadda kanta ƙasa cike da jin kunya shi kuma yaƙarasa ciki ya zauna saman tabarmar da Umma ta shimfiɗa masa suka shiga gaisawa da ita tana tambayarsa ya Hajiya take.


Ganin haka yasa Ayusher ta miƙe ta kwashe kwanonin ta nufi kitchen kirjinta na bugawa ta shiga kwashe abincin kafin Umma tazo. 


"Tashi kije ku gaisa da Yayanki sai ki kai masa ruwa na ƙarasa kwashe abincin sai kizo ki ɗaukar masa nashi ki kai masa." Ayusher taji mahaifiyarta ta data shigo kitchen ɗin yanzu tafaɗa tana ƙoƙarin karɓar abun kwashe abincin a hannunta. Ɗaki Ayusher tafara shiga ta sanyo hijab ɗinta haɗe da dakko ruwan leda guda biyu masu sanyi ta ɗoro akan plate ta nufo wajensu. gabansa ta ajiye plate ɗin ruwan ta zauna, ceke da natsuwa take cewa.


"Ya Irfaan sannu da zuwa, ina wuni?"


Daidai nan aka aiko yaro ana yiwa kawu Ibrahim sallama awaje dan haka ya miƙe yafice daga gidan ya basu waje. Da idanuwa Irfaan ya bita yana ƙara jin ƙaunarta na ratsa masa zuciya, kunya da natsuwa na ɗaya daga cikin abubuwan dake sashi yake ƙara jin sonta akoda yaushe. Ɗan lumfasawa yai sannan ya amsa mata da cewa.


"Lafiya kalau Ayusher har an taso daga wajen haddar?"


"Eh, ya Hajiya da Ya Maryam da wajensu Suhana?" 


"Kowa lafiya kalau." Daga haka shiru ya ratsa tsakaninsu na mintuna sakamakon ruwan da Irfaan ya ɗauka yana sha, 


"Alhamdulillah." Yafaɗa yana ajiye sauran ruwan a plate, miƙewa tayi da zimmar zuwa ta karɓo masa abincin kamar yadda Ummanta ta buƙata yai saurin dakatar da ita.


"Ina zuwa kuma bayan ko lafiyata baki tambaya ba?" Murmushi ta saki kafin tace, 


"Ai naga lafiyarki ƙalau shiyasa ban tambayeka ba, bari nazo Umma tace na karɓo maka abinci."


"A'a dawo ki zauna alhamdulillah a ƙoshe nake."


"Wane irin ƙoshe kuma Irfaan ga abinci angama, ke Ayusher je ki dauko masa kinji ko?" Suka ji muryar Umma tafaɗa daga tsakar gidan. Kallonsa tayi ta sakar mashi murmushi tana ɗage kafaɗa alamun ba ruwanta, 'yar hararar wasa Irfaan ɗin ya aika mata da ita tabar wajen tana dariya. 


Tuwon shinkafa ne da miyar agushi wacce tasha tantakwashin naman rago da man shanu, Ayusher takawo masa agabansa tayi masa saving da kanta yaci suna ɗan taɓa fira, dan suna ɗaukar gidan su Ayusher ɗin tamkar gidansu kasancewar da mahaifinta da mahaifinsa uwa ɗaya uba ɗaya suke, kuma duk da rashin wadatarsu sosai basu taɓa nuna ƙyanƙyami ko kuma ƙyamarsu ba idan sun zo gidan. Hakan yasa Irfaan ya saki jiki ya ɗan ci abincin kaɗan yace ya koshi saboda da gaske yakeyi akoshe yake, kawai baya son yiwa Umma gardama ne yaki ci taji ba daɗi.


Kwashe kayan Ayusher ta sake yi sannan ta dawo ta tadda shi har ya miƙe yana yiwa Umma sallama tana yimasa godiya haɗe da sanya masa albarka shi da Yayan nasa, ta kuma ce idan yaje yayi masu godiya sosai wajen Alhaji Sha'aban da Hajiya. Har zaure Ayusher ta rakashi kafin tace, 


"Toh Ya Irfaan Allah ya kiyaye ya tsare hanya, ina gaida su Hajiya."


"Amin 'yan matana, amma sakonki kije da kanki." Ya faɗa cike da son sanya ta magana, 


"Kai Ya Irfaan! Nice fa?" Ta faɗa tana langaɓe kai. 


"Eh ai nasan ke ɗin ce, kin girma tubarkallah kamar ba ƴar yarinyar da nake goyawa ba, ina zuwa zan sanar da Yaya yazo ayi magana da Kawu abani aurenki in huta da hadiyar yawu." Irfaan ya faɗa cike da tsokana yana murmushi. Ayusher tasa tafin hannayenta ta rufe fuskarta haɗe da barin wajen aguje dan ba ƙaramar kunya kalaman nasa suka sakar mata ba. Irfaan yasa dariya yana kallonta har ta shige ciki sannan ya juya yafice daga cikin gidan. A bakin ƙofar gidan sukayi karo da Kawu Ibrahim wanda har bakon nasa ya tafi zai shigo gidan. Irfaan ya ɗan rissina yana cemasa zai wuce. 


"Toh ka gaida mahaifiyar taku sosai Nagode Allah yai maku albarka." Kawu Ibrahim yafaɗa yana miƙa masa hannu suka sake yin musabiha sannan Irfaan ya shiga motarsa ya tayar ya wuce.

__________

Cikin sati ɗaya duka kayan da Hajja Maimoon tayi odar suka iso tasa aka kawo mata su har gida aka baje su a nan tsakiyar palourn ƙasa ta watsesu ɗaya bayan ɗaya tana lissafa komai ta gani idan ya iso dai-dai kafin akai su shago. Suhaila ke taimaka mata wajen haɗa lissafin yayin da Suhana da Jannat ke gyara mata kayan suna haɗa su waje ɗaya. Bayan tagama haɗa komai tace kowacensu ta zaɓi abinda takeso kafin akwashi kayan anjima akai shago. Jauhar dake rakuɓe gefe taji kamar itama abata damar ɗaukar abunda take so da ta ɗauki wata ƴar ƙaramar jaka data hango mai kyau data burgeta, fannin dogayen riguna da ƙananan kaya ne kawai bata damu dasu ba balle har taga abinda ya burgeta, haka ma takalma da mayafan kala-kala da turarukkan ƙamshi irin masu tsadar nan na waje duk hankalinta bai kai wajen ba, kyan jakar ne ya sake janta bayansu Suhaila sun zazzaɓi abubuwan da suke so tace.


"Mommy dan Allah na ɗauki waccan jakar..?"


Kafin taƙarasa rufe baki Hajja Maimoon ta jefeta da wani kwali da aka cire cikin wata jakar cikin ɓacin rai a tsawace tace, 


"Me na gaya maki akan ganin yaran nan da abu kisa ran kema zaki mallaki irinsa, su sa'aninki ne ko an faɗa maki matsayinku ɗaya dasu? Tukuna ma bance kidena kirana Mommyn nan ba amma kika sake? rainani kikayi ko Jauhar?" Yadda ta dire maganar cikin wani karaji tana yowa kanta yasa Jauhar ɗin miƙewa da gudu tabar palourn ta zagaya ta can bayan kitchen.


"Ƙaramar mara kunyar yarinya da ki tsaya na nuna maki banbancin dake tsakanin waɗanda keda gatan mahaifi dake da baki da wata daraja ko gata awajen ubanki tunda har yakasa zuwa ya ɗaukeki agabana, shashasha kawai. Wannan da kike ganinsu, su ɗin ƴaƴan so ne kuma ƴan gatan iyayensu gaba da baya masu mutunci da daraja, kefa? Wane so iyayen naki keyi maki balle kisa ran zaki samu gatantawa irin tasu?" Hajja Maimoon ta ƙare maganar tana haɗa zufa saboda tsabar masifa duk da sanyin A.c dake tashi acikin palourn. Kallo Suhana da jikinta duk ya mutu ta bi Hajja Maimoon dashi ganin irin masifar da data balbali Jauhar da ita da irin maganganun da take faffaɗa mata tamkar mai yi da sa'arta, shin ina iyayen Jauhar ne? Me suka yiwa Mommy haka data tsani ƴarsu bata sonta? Shin basu san halin da take ciki bane ko a'a da baza su zo su ɗauketa ba takoma hannunsu?. Tambayar data jefawa kanta kenan da a ƴan kwanakin nan take yawan yiwa kanta amma tarasa wanda zai amsa mata su, cikin sanyin murya tace,


"Mommy dan Allah kibata tunda tana.." Kasa ƙarasa maganar tayi ganin yadda Hajja Maimoon ta fizgo kai tana kallonta sai dai ta sadda kanta ƙasa tana cewa.


"Sorry Mommy." Sannan tabar wajen. Suhaila da Jannat ko ɗauke kai sukayi suka kwashi kayan su suka haye sama dan ko ajininsu.


Daɓas Hajja Maimoon tafaɗa kan kujerar tana ɗage kanta da taji ya soma yi mata wani irin ciwo, wai yaushe tayi sanyin da har Jauhar tafara tunanin amfani da kayan kyale-kyali a rayuwarta? Yaushe mafarkanta suka nuna mata irin wannan rana zata taɓa zo mata bayan ita ɗin ba kowa bace acikin gidan? Lallai dole ta sake tashi tsaye ta nuna mata wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa. Da wannan tunanin ta jingina ajikin kujera haɗe da lumshe idanuwanta suka rufe tana laluben ko meye mafita.


Jauhar na zuwa bayan kitchen ta zube ƙasa ta haɗe kai da giwowinta waje ɗaya ta saka wani irin kuka jin kalaman da Hajja Maimoon ke jifanta dasu tana mai dana sanin tambayarta abinda take da yakinin cewa koda zata mutu bazata taɓa samu ba a wajenta. Gashi ta tada mata da fami a zuciyarta na son sanin inda iyayenta suka shiga suka barta a hannun matar da tafi ƙaunar mutuwa da ita. Shin kodai da gaske mahaifinta baya sonta shiyasa yabarta babu wata kulawa balle gata kamar yadda kowane ɗa ke samu agun iyayensa? Da haka bacci mai nauyi ya ɗauke ta awajen har akayi sallar la'asar ba tare data sani ba.


_Bayan kwana biyu_


Hajja Maimoon ce da tuni ta manta da abunda yafaru dan har an kwashe mata kayanta an kai mata shago angyara komai kamar yadda taba yaran da zasu riƙa tayata kula da shagon umurni, tana sakkowa daga upstairs cikin wata irin shiga ta alfarma su Suhaila na biye da ita sai ƙamshi suke zubawa kai da ka gansu kasan mutane ne masu alfarma. Fitowar Daddy kawai suke jira su wuce wajen gagarumin bikin data gayyaci kawayenta da mutanen arziki na buɗe katafaren shagon nata data sawa suna 'SUJASU COLLECTION' wanda tuni mutane sun hallara su kaɗai ake jira.


Da ɗan hanzari Dady yafito daga part ɗin nasa yana saƙala agogon hannunsa taƙarasa wajensa ta karɓa ta sanya masa. Zaman hular kansa ta gyara masa ya fito cas abunsa tamkar bai isa aje su Suhaila ba sai wani sheki yakeyi yana zuba nashi ƙamshin. Murmushi ta saki tana cewa.


"Ya Habiby anya zan yarda kaje wajen nan kuwa? Kaga kyan da kayi kuwa?" Side ɗinta ya kalla inda yaransa ke tsaye ta bayanta sun sha kyau suma kafin ya maido kallonsa gareta yace.


"Asalin kyan ai kece kikayi sai wani sheƙi kikeyi Mommyn Jannat." Ya yi maganar yana ɗaga mata gira, hakan yasa ta saki dariya tana gyara sarkarta ta gwal dake wuyanta da mayafinta tace, 


"Allah Ya Habiby?" Yace, 


"Eh mana muje kinsan mu ake jira." Yayi gaba Jannat ta ruga ta riƙe masa hannu, Hajja Maimoon kuwa ɗakin Jauhar ta leƙa ta ganta kwance, wani mugun takaici ya taso mata tasa ƙafa ta kai mata shuri tana cewa.


"Waya baki izinin zuwa ki kwanta? Tukunna ma wa kike so ya kula da gidan kafin mudawo?" Jauhar da zafin shurin da Hajja Maimoon tayi mata ya shiga jikinta ta tashi zaune tana shafa wajen tace.


"Kiyi haƙuri naga na kammala komai shine na ɗan kwanta." Da wani irin fushi tace da ita, 


"Dallah rufamun baki kifice ki zauna daga bakin ƙofa kafin mudawo, kuma karki sake mudawo mu tadda wani abu ya ɓata a gidan nan, idan har haka ta faru sai na lahira ya fiki jin daɗi." Tana kaiwa nan ta juya tafice daga ɗakin. Jauhar tamiƙe a kasalance ta biyo bayanta ta zauna daga bakin ƙofar shiga cikin gidan dan tuni motarsu tafice daga gidan. Baba Bello maigadi ta hango yana kicaniyar rufe gate da a yanzu keyi masa nauyi musamman wajen rufewa duk da kasancewar gate ɗin mai tayu ne da turashi kawai akeyi saboda manyan ta data cin masa. Da gudu ta taso ta dafa masa suka ƙarara rufe gate ɗin tana cewa.


"Sannu Baba Bello." Ya amsa mata da cewa.


"Yawwa Jauhar ba dake aka tafi ba?" Zaro idanuwa tayi tana rufe bakinta haɗe da cewa.


"Baba Bello karufa mani asiri kar Hajiya taji ta datse maka harshe! Ina ni ina zuwa irin wannan taron manya na masu kuɗi?." Murmushi Baba Bello yai haɗe da cewa.


"Jauhar kenan! Ai wannan ba halin Hajiya bane balle ta aikata akaina, kece dai nake mamakin irin takurawa da tsangwamar da takeyi maki, na kuma rasa dalilin da yasa bazata sallameki ba ta sauya wata mai aikin, ko kina yimata wani laifi da bata so ne?" Cikin sauri Jauhar tace, 


"A'a Baba Bello ni ko dana tashi wajenta cikin wannan hantarar da takura na ganni, bansan laifin dana yimata ba take tsangwama min haka tun ina ƙanƙanuwata." Ya tausaya mata musamman yadda yaga tana shirin yin kuka yace. 


"Kiyita hakuri komai zai wuce in sha Allahu." Ya faɗa cike da tausayinta dan ba wanda bai san kalar ukubar da take fuskanta wajen Hajja Maimoon ɗin ba.


SUJASU COLLECTION


 Tunda sukaje wajan ya sake ɗinkewa, manyan mata ne da ƴan gayu masu ji da kansu ta tara. Ganin yadda aka cika dan batayi zaton za'a zo har haka ba, ya sanya taji wani irin girman kai ya sake shigarta. Suka gaggaisa da kaɗan daga cikin bakin kafin cikin isa da tinƙaho Hajja Maimoon ɗin tayi nasarar buɗe katafaren shagon nata da taimakon Alhaji Sha'aban dake gefenta tare da ƴaƴansa, sai kuma Hajiya da Irfaan da Maryam da suma sun samu hallarta wajen taron duk da Hajja Maimoon ɗin bata so hakan ba. Murna aka shiga tayata ana tafi da hannuwa kafin mutane su shiga cikin shagon su zazzagaya suna yaba kyan kayan da aka zuba a ciki da tsadar su, ba abunda ya tafi da zuciyar Alhaji Sha'aban Sada sai yadda ta tsara shagon da kuma sunan data saka mashi wato (SUJASU COLLECTION) dake ɗauke da farkon sunayen 'ƴaƴan nasa wato Suhaila, Jannat da kuma Suhana. Daga ciki kuma kowane ɓangare tayi amfani da sunayen yaran inda ɓangaren takalma da handbags aka rubuta 'Suhana shoe's and bags fashion design'. A ɓangaren jallabiyoyi da mayafai kuma aka rubuta, 'Jannat Italy and Arabian gowns.' Ɓangaren turarukka kuma nan aka sa 'Suhaila perfumes'. Hatta Hajiya wannan abun da Hajja Maimoon tayi ya matuƙar burgeta sosai dan tsakaninta da jikokin nata tasan soyayya takeyi masu ta gaskiya ba cuta ba cutarwa. Hakan yasa nan take tafitar da kuɗi ta sayi wani turare mai kyau da tsada tana cewa. 


"Nice zan fara saka albarka a wannan shagon naki Maimunatu Allah ya sanya alkhairi ya buɗa maki kasuwa kuma yasa albarka aciki." Hajja Maimoon tayi dariya cike da makirci ganin Alhaji Sha'aban Sada na tsaye wajen tace, 


"A'a Hajiya ai bama karɓi kuɗinki ba duk wannan addu'a da kikayi mana da sanya albarka ai ta ishe mu." Ta ɗauki turaren hadda wani takara ta miƙawa Maryam tace ta riƙewa Hajiyan. A kasan zuciyarta kuwa tsine mata takeyi yafi dubu tana hango asarar da taja mata ta makudan kudaɗen da zata karɓar a turarukkan dan Exclusive turarene na manyan mata da Hajiyoyi. Kamar Alhaji Sha'aban yasan meke ranta yace,


"Nima dai bazan fita ba ban sanya na saka albarka ta ba, saboda haka Maryam keda su Suhana ku shiga ku zaɓo duk abinda kuke so." Duk irin yadda taji yace zai siya, sai da taji har lokacin ranta bai sakko ba na daga kyautar da ta yiwa Hajiya. Kaya suka ɗakko masu kyau da tsada musamman Maryam dan su Suhaila turarukka kawai suka ɗauka, da yake akwai kuɗin komai a rubuce Alhaji Sha'aban baice uffan ba yaje yai making payments duka har na turarukkan da aka sanyawa Hajiyarsa. Haka kuwa akayi Irfaan yaje yayi payment sannan ya cire kudinsa ya zagaya ya ɗakko dogayen riguna guda biyu da hand bag da takalmi ɗaya da turare yaje wajen Hajja Maimoon ya ajiye yana cewa, 


"Tunda babu irin namu kayan na maza bari muma musa albarka musayawa kannenmu." Ba kunya Hajja Maimoon tayi dariya ta karɓi kuɗin tana mikawa cikin yaranta ayi payment tare da cewa, 


"Thanks Irfaan, haka muke so na gida su riƙa supporting kasuwancin mu." Dan a tsammaninta Maryam ya siyawa kayan. Baice komai ba ya koma gefe har sai da Hajiya tace a maida ita gida saboda lokacin ɗora abincin sadaka ya yi, duk da akwai masu yi takan bada umarnin yin wasu abubuwan. 


Sai da kowa ya watse a shagon sai ɗaiɗaiku masu zuwa sayayya sannan Alhaji Sha'aban Sada ya kwashi yaransa suka wuce gida, haka ma Hajiya dasu Maryam Irfaan ya kasu suka wuce gida. Yana ajiyesu ya juyo ya nufi gidan Yayan nasa da ledar kayan daya siya...




#A heart touching story

#Gonar Sharri..

#Hajja ce

#Billy s Fari

#Ƴan Tagwaye