RAMIN KARYA

Chapter 11

by @kyautadagaallah10

๐Ÿ‚๐Ÿ‚_*RAMIN K'ARYA*_ ๐Ÿ‚๐Ÿ‚




 NA 



IKILIMA ADAM 


 *( Kyauta daga Allah)*


Marubuciyar da ta nishandantar daku a littafanta kamar haka:


Kai ka jawa kanka



Kanwata



Rai daya ( Jan zaki)



Rudani



Makauniyar shari'a


And now


Ramin karya yan karin magana suka ce kurarre ne , mu je zuwa.



Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai .




 SHAFI NA GOMA SHA DAYA ( 11)




Bata gama mamaki ba , sai da ta ga prince yana kokarin daukar su selfi. Kanta a kasa , shi kuwa hotuna yayi ta dauka ba tare da damuwa da rashin dago kanta ba.


" Na dauki hoton nan ne , da nuna wa duniya ina son auren" ya fadi haka yana mai sakin hannunta.


Kamar jira take a hanzarce ta shige cikin Gidan , tareda isa wajen Ummi ..


A cikin gidan Matar Alhaji Halliru sosai ta shiga yiwa Jidda da Ummi nasiha. Babbar diyarsu mai suna Hajara , wacce suke da kawance da su Jidda ce , ta zauna tana mamakin wai Jidda ce ce matar prince Adamsy, ita kuwa Ummi matar prince Abdullahi . Sosai take nazartan yanda akayi suka yi babban kamu gasu talakawa , arzikin ma sun fi su , abu daya ne gare su shine kyaun halitta .



Prince da abokansa shiga motocinsu , suka yi domin komawa Masarautar. Zahradeen ke kallon Prince yana danna wayarsa alamun yana amsa sakon masu masa murna na nesa ne.


" Kai prince kai da baka auren so, zaka yi da yarinyar nan , dan wata manufa ce , meye na rike hannunta " Zahradeen ya furta yana mai sakin dariya.


 Dago kai yayi daga kallon wayar yana kallon sa .


" Idan tuki zakayi, kayi abunda zaka yi , hoto na dauka ni da ita , dan kauda zargin Masarautar akan manufarsu, kuma in zaka duba shafina na Whsap na daura a status dina" ya fada yana mai dawo da kallonsa akan wayarsa.


Abokansa biyu dake kujerar baya , cikin mai suna Umar ya ce .


" Ai shi Zahradeen baya gane karatun kurma, shi komi ya fi son dallah_dallah ". Ya fada yana murmushi.


Na kusa da shi ne ya amshi zancen da fadin.


" Ai nima irin Zahradeen din ne , ai yanzu da ya bayyana mana dalili ai mun gane ko , kuma takunsa yayi wallahi" Cewar Abdul Rahman.


" Ka san dai ni bana gani nayi shiru" Zahradeen ya fada yana mai karya kwanar Masarautar.

Prince Adamsy kuwa Banda girgiza kai ba abunda yake dan ya lura , abokansa manyan yan hau ne .


Wayarsa ce ta fara ring , ganin sunan My sister ya bayyana ya sanya cikin hanzari ya daga .


" Ina jin ki ya taro" ya fada yana mai jin daga gareta.


Dayan bangaren Sumayya ta ce" Yaya ina fa lafiya ga hassana ta fadi ta ji rauni goshinta ya fashe , sai da aka kira family docto" ta fada cikin damuwa.


Cikin tsananin tashin hankali ya furta " Sumayya gani nan mun karaso" daga haka ya katse wayar. Cikin tsananin damuwa kamar me shirin kuka yake bawa su Zahradeen labarin abunda ya faru. Dukasnu rudewa suka yi suna mai fadin Allah yasa raunin ba babba bane .


A ujajajan suka shiga Masarautar , duk gaisuwar da ake masa , sam ko kallon idan suke baya yi , yana isa cikin Masarautar ya hadu da Lailat zaune gefe daya kan kujera 1st alamun waya take .


Kadan daga cikin wayar da take .


" Ai wallahi tunda yayi aure ya ringa ganin tashin hankali kenan , mutumin da sam be sauke hakkin iyalinsa ba , har yana iya karo wata dan zalunci , kuma wallahi bakin cikin da ze gani akan Hassana na yau ya isa ya hanashi kwana dakin Amarya ". Caraf kalamanta sai kunnen prince da abokansa. Har yayi gaba sai ya dawo da baya baya , tare da kusanto inda take. Fisgar wayar da ta ji anyi yasa ta juyo a fusace domin tayi fada.


Caraf idanunsu suka tsarke cikin na juna ita da Prince .


" Dawa kike waya ".? Ya tambaya cikin daga murya.


Murya na rawa cike da tsoro da fargaba tace , 

" Maimuna ce ".


" Okay". Ya furta kana ya kama hanya domin beda bukata da ita wuce yaga Hassana.


" Baka bani wayata ba " ta furta cikin damuwa , kana idanunta na kan su abokansa da suke aika mata da kallon banza.


Be tanka ba , illah cigaba da tafiyarsa yayi yana jin zuciyarsa kamar zata fado kasa , dan bakin ciki.


Ganin ya fice ne ya sanyata fara sakin kuka , kada ya bincike mata waya. Rasa mafita ya sanyata hanzarta zuwa sashin Gimbiya Humaira , Koda isarta bayi suka fice domin basu wuri.


" Na shiga uku , ya karbe min waya" cewar Lailat cikin kuka.


A rikice Gimbiya Humaira ta furta " a garin ya hakan ta faru?".


Nan ta zayyana mata komi ,Gimbiya Humaira kuwa , sosai ta nuna damuwa akan hakan.


Hakan ya sanyata zaunar da Lailat suna face din juna.


" Kwantar da hankalinki babu abunda zeyi da wayar ki , nan da mintin arbain wayar ze dawo hannunki". Ta fada cikin tsigar rarrashi.


" Amma..." . Shiru tayi sakamakon katse ta da Gimbiya tayi ta hanyar fadin. " Nace kada ki damu waye Adamu be isa ya duba wayarki ba , yana hauka ne ". Ta fada cikin takaici.


" Kuma zan kira Nura, duk da anje dauko amaryansa , ba ze hana ayi aiki akai ba , yaran nan yana ji yana gani zasu barshi , in banda kaddara tun farko ai ke ya kamata ya aura , sai ya dauko yayarki " ta fada tana nuna takaici akan hakan.


Ajiyar zuciya ta sauke , cikin jin sanyi a ranta.


" Lokacin da ya auri Anty Maryam ban kai aure ba , amma kuma ai aka min aure zan zauna ,kuma ni ba zan rike dan kowa ba wallahi sai nawa". Ta fada cikin takaicin Prince.


" Wallahi ina bayanki , kuma in Sha Allah Nura ne ze gaji sarauta Lafiya".

Nan da suka ci gaba da hirarsu.


Bangaren Prince Adamsy


Hassana rike hannunsa alamun kuka take , wanda fuskar ya bayyana hakan. Cikin idanunta babu wacce take gani sai fuskar Jidda . Tana son tayi magana babu dama, hakan ya sanya kukan nata kara tsananta hawaye na bin kuncinta.


" Wallahi ko arziki na ze kare in har zan samu yaran nan farinciki, zanyi wallahi , in har zan samu magani zan musu ina son su " ya fada hankali tashe.


"Ku Kalli Hassana tana kuka bama iya tambayarta inda yake mata ciwo , bata jin mu bata ganin mu "ya fada jijiyoyin hannunsa na tashi.


" Don Allah kadaina kashe mana jiki , duk abunda kake fadi , wallahi yana sanya mu kuka " cewar Zahradeen yana mai shafa bayan Prince Adamsy.


Shigowarsa Hajiya babba da Sarki da kansa ne , da waziri ne ya sanya , Prince tashi zuwa rumgumar Hajiya babba yana kuka yana kallon Hassana.


" Prince Adamsy" Sarki ya kira sunansa cikin dattako.


Sakin Hajiya Babba yayi ya karasa gaban Sarki cikin sanyin jiki , runguma ya kai masa . Yana jin son Mahaifinsa har kasan ransa.


" Adamu in sha Allah zasu warke , ina ji a jikina , kuma zaka yi mulkin Lafiya cikin kwanciyar hankali da nitsuwa ya kai dana" . Cewar Sarki yana mai Karasawa wajen Hassana, daukarta yayi akan kafafunsa yana mai mata adu'oi yana tofe ta.


Prince kalmar zeyi Mulki ya mugun daga masa hankali ,sam baya son mulkin nan da ake son kakaba mishi.


Cikin ban girma , su Zahradeen suka gaishe da Sarki da Hajiya babba har da Waziri.


Magunguna Sarki ya baiwa Hassana da kansa , kana ya furta.


" Tunda ka Kara aure , kaga an kara samun wacce zata taya Lailatu rikon yaran nan " ya furta yana mai janyo Hussaini a jikinsa.


Prince Adamsy shida su Zahradeen kallon juna suka yi , kusan a tare suka fesar da numfashi.


Maganganun Lailat ne ke yawo saman kansa , kana yana mai kallon wayarta dake hannunsa.


" Dare nayi a hanzarta zuwa dauko amaren nan , yanzu za'a kawo ta Nura " cewar Sarki .


Zahradeen kam , cikin hanzari suka furta , a basu mata da zasu raka su. Sarki ya bada Umarnin a je da jakadiya da Gimbiya Humaira.


Sallamar Maman Lailat ne ya sanya su kai dubansu akanta , da kukanta ta shigo . Murya na rawa ta gaishe da Sarki da Hajiya babba , su Prince kuwa cike da ladabi suke gaisheta.


Kai tsaye wajen Hassana ta nufa cikin damuwa tana kallon yanda aka nade goshin da bandeji.


" Ya jikin nata "? Ta tambaya tana kallon Hajiya babba.


" Da sauki" ta bada amsa.


" Allah ya kara sauki" .


" Ameen ya Allah" dukan dakin suka amsa.


Su Prince ganin Maman Lailat ta iso ya sanya suka bar dakin , domin masu shirin dauko amarya su shirya.


Hajjya Babba bayan sun taba hira ,ita ma barin dakin tayi, domin shiryawa, kafin a kawo amaren.


Sarki ma shima sahunsu ya bi , don tarban amare.

Dakin daga Sumayya sai Maman Lailat ne .


Nan ta kamasu tayi masu wanka da kanta , sam bata bari ruwa ya taba ciwon Hassana ba .


Sumayya na ganin Maman Lailat, fita daga dakin tayi , ta je ta shirya domin tarban amare.


Maman Lailat kuwa sosai ta basu kulawa, ta sanya su a gaba tana rera kuka , Babu abunda take tunawa irin ranar da Maryam zata bar duniya .


Kadan daga cikin abunda take tunowa.


" Mama ina ji a jikina ba zan tashi ba , don Allah ki yafe min duk abunda na miki a rayuwa , kuma Allah be sanya zan kara ganin yar uwata ba , gashi zan bar duniya".


Cikin kuka Mama ta ce , " a'a Maryam na ce miki bana son jin haka daga bakin ki ". Ta bata amsa cikin kuka.


" Nayi shiru Mama tunda baki so , ga jikoki nan duk sanda kika gansu kina min adua". ta furta hawaye na bin kuncinta.


" A'a Maryam karki sa na zauce , nace ki daina bana so , zaki haihu bakiga har yan biyu kin haifa ba , yanzu ma wannan dayan ba ze gagara ba in sha Allah , ki daina saka ni kuka ".


Shiru Maryam tayi tana mai kallon Mahaifyarta , kana idanunta be daina zubar da kwallah ba .


Firgit ta dawo hayyacinta jin karar faduwar kofi daga center table.


Lumshe idanunta tayi tana mai kallon Hussain dake kokarin dauke kofin.

Goge kwallah dake zubo mata , tayi tare da zuwa wajen sa .


_______________



Sai bayan Isha'i aka je dauko amare.



Jakadiya da Gimbiya Humaira da Gimbiya Zainab ne suka jagoranci tafiyar.


Cikin tsantsani suka shiga Gidan ,banda Jakadiya dake tausaya musu.


" Don Allah ku fito da amaren nan " Gimbiya Humaira ta furta tana mai toshe hanci.


Caraf sai kan idanun Alhaji Halliru dake ma su Jidda nasiha yana nuna musu yarda da kaddara.


Cikin rashin tsoro ya fito daga dakin.


" Hajiya ai kamata yayi ku tsaya waje in mun gama musu nasiha sai a akawo su ". Ya furta cikin takaici.


" Kai ka san wa kake fadawa hakan matsiyaci"?.


" Matar Sarki ta uku ce , bana son kiyi amai ne , dan toshe hanci dake sai ki gaza numfashi mai kyau". Ya fada yana mai kama hannun Jidda da Ummi domin kai su bakin motar.


Matar Alhaji Halliru ta so ta bisu ya hana domin gudun wulakanci.


Jakadiya da kanta ta rike su , ta nemi wani daya daga cikin manya ya bi su , hakan ya sanya Matar Halirru ta biyo su.


Motar amaren a tsakiya suke .


Da kuka da rarrashi suka shiga motar.


Gimbiya Humaira da Gimbiya Zainab banda takaici ba abunda ke kamasu a wurin.


Karfe tara saura kwata suka Isa Masarautar Lafiya.


Inda aka zaga da amaren kowani sashi , har wajen Sarki ankai su , nan ma Sarki ya zaunar dasu da Abdullahi da Nura da Adamsy ya masu nasiha akan zaman aure .


Ankai amaren sun gaishe da Maman Lailat , kana aka kai Ummi dakinta , sosai take kuka ganin an ajiye wani babban katafaren daki ita kadai.


Ita kuwa Jidda sai aka nufi sashin Lailat da ita domin al'adar Masarauta sai ka gaishe da kowa ranar zuwanka na farko amatsayin mata.


Lailat kuwa jin guda na tashi ya santa saka cimgam a bakinta tana taunawa karas karas.


Ana shigo da Lailat ta fara karkada kafafuwa daya kan daya.


Cikin ladabi Jakadiya ke sanar mata an kawo amarya domin ta gaishe ta .


Kallon Jidda take da take a durkushe , kana ta kalli Matar Halliru da kallon banza.


" Allah ya baku zaman lafiya ya baku ikon kwantar wa mijinku hankali" cewar Matar Halliru.


" Ba Ameen ba " suka ji ta furta, tana mai ci gaba da taunan cimgam.


Firgit Matar Halirru da Jakadiya ke kallonta , Jakadiya sauke kanta kasa tayi cikin ban girma ta ce " mun tafi".


Kallon banza ne ta aika musu, tana mai bin su da.

Suna ficewa daga dakin , ta saka ihuuu na bakin ciki.


" Wai ni ce prince Adamsy ya turo Amarya ta gaishe ni , tabbas mugun mai dani shara a Gidan nan " ta fada tana buga gini da dukan hannayenta.


Kai tsaye dakin dake Mazaunin na Jidda nan aka nufa da ita.


Sosai suka mata nasiha da nuna kada ta damu da abun da Lailat tayi.


Bayan sun fita ne , abokan prince suka rakaso da abokansa , hade da naman kaji.


Suma sun zauna suyi adua sosai kana suka fice .


Prince yana dawowa dakin da Jidda take , kalomta yake yanda take kuka bilhakki da gaskiya.


Jin ya yaye mayafin kanta ne , ya sanyata dago jajayen idanunta ta sauke akansa.


" Kina kuka ne dan ankawo Gidan makiyin ki ko?". ya furta yana kallon yanda hawaye ya bata simple make-up da suka mata.


" Ka mayar dani Gidan mu" ta fada cikin kuka.


Lumshe idanunsa ya yi , tare da bude su a hankali , kana ya tashi domin fita daga dakin.


Ganin yana shirin fita daga dakin ne , ya sanya cikin hanzari ta ........



***


Taku har kullum kyauta daga Allah