BABI NA SHA UKU
by @billysfari
GS 13.
Yana ƙoƙarin tura kan motarsa cikin gidan, yayin da Alhaji Sha'aban Sada na kawowa zai fita campany dan yana ajiye su Suhaila aka kirasa aka ce yayi baƙi masu matukar muhimmanci. Reverse Irfaan ɗin yai har sai da Yayan nashi ya fito zai wuce sukayi clashing Alhaji Sha'aban Sada ya tsaya ya sauke glass ɗin gefensa yana cewa.
"Yauwa Irfaan ka zauna da yaran nan haka baƙi zasu zo yiwa Hajiya Maimoon murna kafin nadawo ba jimawa zanyi ba, bana son barinsu gidan su kaɗai kasan yanayin rayuwar yanzu sai a hankali sam bani da wata natsuwa akan barinsu cikin gidan ba wani babba. Kaga Baba Bello shekaru sun miƙa balle nasa ran babu wata matsala idan na barsu tare." Irfaan dake riƙe da steering motarsa yana sauraren Yayan nasa yace.
"Shikenan Yaya babu damuwa sai ka dawo." Horn Alhaji Sha'aban Sada yai masa alamar amsawa yana maida glass ɗin motarsa ya wuce shi kuma Irfaan ya tura hancin tasa motar ya shiga ciki ya samu waje yayi parking. Tsaye ya yi yana kallon yadda Baba Bello mai gadi keta ƙoƙarin rufe gate ɗin har Allah ya taimake sa ya rufe yana faman sauke numfashi ɗaya bayan ɗaya sai kace wanda yayi wani aikin wahala, dan gate ɗin turoshi kawai za'a yi ya rufe kansa ba tare da ansha wahala ba. Kai Irfaan ya girgiza cike da tausayinshi yana sake fahimtar maganar da Yayan nasa ya gama yimasa yanzu akan tsufan Baba Bellon da yake tunanin sam bazai iya bawa yaransa kulawar data dace ba idan buƙatar hakan ta taso. Har ya nufi cikin gidan sai ya tuna da saƙon daya kawo shi gidan, dan haka ya koma ya buɗe motar ya ɗakko sannan ya wuce ciki.
Sallama yai abakin ƙofar shiga palourn haɗe dayin tsaye yana kallon Jauhar dake goge-goge, kammala girkinta kenan na dare tafito tana sake gyara gidan dan hakan al'adarta ce kullum safe da maraice sai ta share ko'ina kuma ta goge duk wani abu dake cikin parlorn. Kallo yabi palourn dashi yaga ba kowa sai ita kaɗai dake faman aiki. Wata sallamar ya sakeyi dan da alama bata ji ta farkon ba da yayi tare da ƙarasa shiga cikin palourn ya faɗa kan ɗayar kujerar yana cewa.
"Sannu da aiki Jauhar duk ina yaran gidan ne?" Jauhar da jin muryar sallamarsa tasa ta juyowa riƙe da ƙyallen da take goge-gogen tace,
"Sunu da zuwa Uncle, Ina wuni?" Tayi maganar tana sinne kanta ƙasa cike da jin kunyarsa tunowa da kayan da ya siyo mata kwanaki.
"Lafiya ƙalau Jauhar, kin dai warke ko?" Ta sunkuyar da kai tana faɗin,
"Eh." Tafaɗa tana ajiye ƙyallen da take goge-gogen dashi ta nufi kitchen dan takawo masa ruwa. Dakatar da ita yai yana tashi zaune daga ɗan kishingiɗa da yai a jikin kujerar yace.
"Zo Jauhar ina zaki je?"
"Ruwa zan kawo maka." Ta bashi amsa ba tare data bari sun haɗa idanuwa ba duk da yadda yake kallonta, shi har ga Allah mamakin yadda suke iya cin abincin da Jauhar ke girka masu yakeyi saboda yanayin kayan jikinta da zai iya rantsewa tana kwana bakwai bata wankesu ba balle kuma ayi batun sauyawa. Ya sauke wani nauyayyar numfashi tare da ɗaukar ledar dake gefen ƙafafuwansa yana cewa.
"Zoki karɓa." Ta ɗago kai ta kalli ledar da yake miƙo mata. Ƙofar shigowa palourn ta ƙalla sannan ta girgiza masa kai tana cewa.
"A'a Uncle Mommy kasheni zatayi idan na karɓa, wancan ma.." Sai kuma tayi shiru haɗe da rufe bakinta tana kallon stairs cike da tsoro dan kada ɗaya daga cikin su Suhaila sufito su jita. Haɗe rai Irfaan yai yana kallonta yace.
"Ta karɓe ko?" Bata iya bashi amsa ba ta sake kallon stairs ɗin, ya taso ya iso gabanta yana cewa.
"Karɓi wannan bazata karɓar ba in sha Allah saboda a wajenta na siya miki. Ko da bazaki saka ba kifito kiyi ƙoƙarin sauyawa idan kikayi wanka da kuma idan zakiyi sallah, dan bana tunanin ubangiji na karɓar sallarki acikin wannan shigar Jauhar."
"Ai bana yin sallar ma." Jauhar ta tsinci kanta da faɗar hakan ba tare data sani ba, zaro idanuwa Irfaan yai yana haɗe gira jin abinda ta faɗa.
"Me kikace Jauhar?" Ya faɗa cike da mamaki yana kallonta, sadda kanta tayi ƙasa tana ɗan ja da baya ganin yadda fuskarsa ta sauya dan a tsammaninta zai iya kai mata duka. Jin ya sake jeho mata tambayar rai a ɗan ɓaci yasa tace,
"Bana yin sallah Uncle ban iya ba!."
"Ban gane baki iya ba Jauhar, bakyayi ne saboda wani dalilin ko kowa bakyayi gaba ɗaya." Irfaan yai maganar cikin ɗan sassauta murya ganin yadda take ja da baya saboda ta tsorata da yanayin yadda yakeyi mata magana.
"Ban iya ba Uncle Mommy bata koya mun ba."
"A islamiya fa?" Ya tambayeta with so much shock,
"Ban taɓa zuwa ba." Itama ta bashi amsa cikin sanyin jiki.
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, Jauhar bakiga ƙawayenki nayi bane? Ko bakya ganin Mommyn nayi da sauran mutanen da kike rayuwa zagaye dasu? sallah fa Jauhar? Baki san sallah itace cikon musulunci gaba ɗaya ba?." Irfaan yai maganar cike da tashin hankali da tausayin Jauhar idanuwansa cike da ƙwalla." Ganin haka yasa jikin Jauhar ɗin ya mutu ta duƙa agabansa tana cewa,
"Uncle kayi hakuri Mommy bata bari na, ina kwantata yadda sukeyi, amma dana fara ma zakaji ta kwala min kira, ko ta shigo taga ina yi sai tace, kinibibin banza me na iya banda na dinga daukarwa kaina zunubi. Uncle zan fara yin sallah daga yau, kuma idan an kirani bazan amsa ba sai na gama. Banda ƙawaye shiyasa ban koya daga wajensu ba, Mommy dasu Aunty Suhaila kuma bana fahimtar abinda sukeyi ko sunayi ina gani, na dai san sallah sukeyi kamar yadda naji sunanta abakin mutane." Jiki a sanyaye Irfaan ya kalleta yana cewa.
"Tashi kije idan kin gama aikin kin zan nemeki." Yafaɗa yana sake miƙa mata ledar dan gaba ɗaya kansa ya kulle da jin wannan sabon al-amari acikin rayuwar Jauhar da bai taɓa zato ko tsammani ba, yana bukatar tunani mai zurfi domin nema mata mafita acikin rayuwarta kafin ta lalace. Karɓar ledar Jauhar tayi haɗe dayi masa godiya sannan ta ɗauke ƙyallen da ta gama goge-goge ta wuce ɗakinta saboda ta kammala aikinta gaba ɗaya.
Irfaan kuwa kallo yabi upstairs ɗin da ɗakunan su Suhaila suke dashi yana jin wata irin damuwa a ransa, ya buɗe baki kenan da niyar kiran Suhana ya ji ankira sallar magariba sai kawai yasa kai yafice daga cikin parlorn. Anan bakin fanfon dake laƙe a jikin katangar dake jikin ɗakin Baba Bello mai gadi ya tsaya yai alwala ya shiga Masallacin dake cikin gidan Baba Bello ya jasu jam'i sukayi sallah.
__________
Gidan Kawu Ibrahim yana zaune sun idar da sallah yana ta kwararawa Alhaji Sha'aban Sada addu'a domin ya kasa mantawa da tarin alkairansa. Ayusher ƴah ce tilo a wajan Kawu Ibrahim ɗin, ita kaɗai Allah ya bashi aduniya, suna matuƙar sonta shi da Ummanta irin son da baki bazai iya faɗa ba. Hakan ne kuma yasa ta taso cikin kulawa da gatantawa dai-dai karfinsu, sai dai duk da haka basu bari son da sukeyi mata ya rufe masu idanuwa ba sun kasa bata tarbiyya, kama daga ilimin boko har na Arabia dan tsaye suke akanta tun tana ƙaramar har zuwa yanzu data kammala secondry ta shiga jami'a kuma take kan yin haddarta ta alƙur'ani da yanzu ta haddace hizif arba'in, Ayusher yarinya ce mai natsuwa sosai da kuma alkunya da rashin son hayani, hakan yasa tunda ta taso ba tada wasu ƙawaye in ba ƙawarta Khadija ba da kusan halayensu suka zo ɗaya. Kyakkyawace sosai mai matsakaicin tsawo kuma tana da hasken fata data gado wajen mahaifinta. Sun yi matuƙar shakuwa da Irfaan tun suna ƙanana kafin daga bisani shakuwarsu ta juye takoma soyayya tare da yiwa juna alkawarin aure bayan ta kammala karatunta, wanda sai alokacin suka ɗauki alwashin zasu bayyanawa iyayensu soyayyar dake tsakaninsu dan har yanzu kowa ɗauka yakeyi shakuwa ce kawai. Wannan dalilin yasa kuma Ayusher bata saurarar kowa duk da irin tarin samarin dake kawo mata hari, wasu ma sai dai su biyo ta hanyar mahaifinta idan yayi mata magana sai tace ita karatune gabanta sai ta kammala, da yake mahaifin nata shima yafi bukatar hakan sai kawai ya ƙyaleta ya basu haƙuri. Wannan shine.
___________
Bayan su Irfaan sun kammala sallah awaje ya tsaya wajen Baba Bello ya ciro wayar ya kira Ayusher suka sha firarsu da ita har aka kira sallar isha'i sannan ya yi mata sallama ya shiga masallaci sukayi sallah. Yana fitowa ya koma cikin gidan ya tadda yaran gaba ɗaya sun sauko palour sun zauna suna kallo, Jannat kuma na haɗa homework ɗinta da batayi ba.
"Uncle Irfaan Ina wuni." Duk suka faɗa ya amsa masu fuskarsa a sake yana cewa.
"Ɗazu na shigo ban taddaku ba sai Jauhar na samu tana aiki, in ce dai ba baccin yamma kukayi ba." Yafaɗa yana zaunawa kusa da Jannat haɗe da gyara mata wasu errors da har ya hango tayi wajen calculation saboda hankalinta data raba biyu rabi wajen kallo rabi kuma wajen homework ɗin. Suhana ce ta amsa masa da, "Wallahi Uncle wani irin bacci ne ya ɗauke mu da muka dawo mu duka saboda gidan ya zama empty."
"Saboda Momynku bata nan ko?" Irfaan ya faɗa yana kallon suhana
"Exactly Uncle Irfaan wallahi gidan duk ba daɗi." Suhaila dake kwance tafaɗa tana miƙewa zaune da ɗan damuwa ɗauke a fuskarta. Murmushi ya saki haɗe da cewa,
"Ai kuwa sai ku fara sabawa tun yanzu tunda Momynku kuɗi take so."
Muryar Dady ce ta katse firar daya shigo hannunsa riƙe da ledoji. Suhaila ce ta miƙe ta karɓi ledojin hannunsa haɗe da yi masa sannu da zuwa tana ƙwalawa Jauhar kira suma su Suhana da Jannat suka miƙe suna yi masa sannu da dawowa.
"Sannu da dawowa Yaya." Irfaan ya faɗa yana miƙewa saboda dama ɗaya daga cikin shi da Mommyn yake jira su dawo ya wuce gida.
Daidai lokacin Jauhar data fito wanka tana gwada ɗaya daga cikin rigunan da Irfaan ɗin ya saya mata ta saka har da handbag ɗin da takalmin tana jujjuyawa cike da farin ciki, tana san gayu, tana san abu mai kyau sai dai anyi mata shamaki da samun duk abinda zai sakata farin ciki. Can kuma sai ta jiyo muryar Suhaila na ƙwala mata kira, bata tsaya wata-wata ba ta fito da sauri cikin ruɗewa ba tare data tsaya cire komai ba ta nufo cikin palourn saboda sanin halin Suhaila da tayi har tana gurɗewa tana faɗuwa saboda rashin iya tafiya da takalman da batayi ba. Zaro idanuwa duk sukayi suna kallonta mayafin abayar ya rufe mata fuska sai kiciniyar yadda zata buɗe fuskar tata takeyi gata sagale da jaka. Da kyar ta iya fito da fuskar daga cikin vail ɗin, yadda ta zaro idanuwa tana fiƙifiki dasu haɗe da kallon mutanan wajan tamkar mara gaskiya yasa Suhana ta kwashe da dariya, Irfaan ma murmushi yai yana kallon yadda ta saƙala jakar da takalman kaɗai da ya isa yasa ƙasan bata saba saka irin kayan ba. Jannat data buɗe baki tace.
"Sata kika yiwa Mommy? ba tace bazata baki ba?" Rai aɗan ɓace Irfan yace,
"Wane irin shirme ne haka kike yi Jannat? Ba sata Jauhar tayi ba ni ne na saya mata na kawo mata." Yai maganar saunding so very angry.
"Uncle ka siya mata? Wannan yarinyar zaka siyowa kayan nan? Hmmm!" Suhaila tafaɗa tana taɓe baki cike da takaicin Uncle Irfaan ɗin ta ajiye mata ledojin agabanta ta haye sama abunta. Daddy kam da kallo yabi Jauhar data kwashi ledojin ta wuce kitchen dasu kafin ya maido hankalinsa ga Irfaan yace,
"Har zaka tafi kenan bazaka tsaya kaci abinci ba?" Girgiza kai kawai yai tare da sake kallon gefen kitchen ɗin sannan ya yiwa Yayan nasa sai da safe ya wuce. Ajiyar zuciya Daddy ya sauke ya wuce part ɗinsa, da kansa ya haɗa ruwan wankansa bayan ya rage kayan jikinsa. Sai a lokacin yaji ƙarar shigowar motar Mommy ta dawo. Kai tsaye ɗakinta ta wuce dan agajiye take tafara shiga ta watso ruwa tayi sallar isha'i da batayi ba sannan ta wuce ɗakin su Su haila. Da gudu Jannat ta taso tana yi mata oyoyo tayi hugging ɗinta tana cewa.
"Daughter bakiyi bacci ba? Kinci abinci kuwa?"
"Eh Mommy yau gidan so boring da bakya nan." Jannat tayi maganar tana sake shigewa jikinta tamkar wadda ta daɗe bata ganta ba. Ta bayanta taji Suhaila da Suhana sun rungumota suma suna cewa,
"Welcome home Mommy we missed you." Ta shafo fuskokinsu da hannuwanta atare tana murmushi tace.
"I missed you too yarana, Ina fatan ba wata matsala kunci abinci ko?"
"Eh Mommy." Suka faɗa atare suna breaking hug ɗin tare da komawa kan gadajensu. kayansu da suka zubar a tsakiyar palourn ta shiga tattarawa tana kwashe su takai washing mashin sannan ta dawo tana cewa.
"Oya akwai school gobe kun sani ya kamata ku kwanta da wuri, bari naje gun Dadynku." Taƙarasa zancen tana ficewa tare da ja masu ƙofar. Hajja Maimoon na sakkowa Dady nafitowa dan yunwa yake ji,
"Sorry Ya Habibi wallahi customers suka riƙeni. I can't believe yadda aka samu kasuwa yau daga buɗe shagon nan." Taƙarsa maganar tana janyo masa kujerar dining da suka nufa, murmushi ya saki yana cewa.
"Masha Allah abu yayi kyau Allah yaƙaro kasuwa, ina fatan ba wani abu wurin yayi miki sosai ko?"
"Ai ina faɗa maka wajen nan is extremely good, yau ɗinnan da aka buɗesa har anyi cinaki over 1.5million, gaskiya alhamdulillah mun shiga kasuwar nan da hannun dama." Tayi maganar tare da jawo kujera ta zauna itama, tana kai hannu zata fara saving ɗinsu wayarta tayi ƙara, duba kiran tayi taga wata customer ce da tazo ɗazu sukayi maganar tana son turarukkan ƙamari zata siya, ba shiri ta miƙe tana ƙwalawa Jauhar data soma bacci kira sannan ta ɗaga wayar takai a kunne, da gudu Jauhar da bata san da dawowarta ba ta iso wajen ta zube ƙasa tana cewa.
"Sannu da dawowa Hajiya gani." Ɗan janye wayar tayi daga kunnenta tana cewa.
"Ki zubawa Daddy abinci, Ya Habiby ina zuwa customer ce." Ta wuce abunta zuwa ɗakinta tana ci gaba da wayar ba tare data tsaya saurar abinda zai ce ba. Da kallon mamaki Alhaji Sha'aban Sada ya bita har ta haye sama kafin ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Jauhar data ɗauki plate da serving spoon tana cewa.
"Alhaji me zan zuba maka?" Mamaki ne shima a saman fuskarsa, kayan ɗazu ne a jikinta, kalmar Jannat ta dawo masa cikin kwakwalwarsa dan haka yace,
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye