BABI NA SHA HUƊU
by @billysfari
GS. 14.
"Ina kika samu wannan kayan?" Jauhar tayi saurin kallon jikinta, bata kalli fuskar Alhaji Sha'aban ɗin ba dan sai take ganin kamar shima bai yadda cewa Uncle Irfaan ne ya bata ba tunda ai a gabansa Irfaan ɗin ya faɗi cewa shine ya kawo mata. Jin tayi shiru yasa yaji kamar tambayar ce bata fahimta ba, yadda jikinta yake rawa yasa tausayin ta ya kama shi, plate ɗin da ta ɗakko zata zuba masa ya janyo tare da cewa.
"Barshi Jauhar jeki kwanta." Ganin yana ƙoƙarin zubawa da kanshi yasa tayi saurin durƙushewa a gabansa tana sake waigawa ta kalli hanyar da Hajja Maimoon tabi, bakinta yana kyarma take masa magiya.
"Kayi haƙuri Alhaji wallahi Uncle Irfaan ya bani kayan ɗazu, sannan dan Allah ka kawo na zuba kar Hajiya taga bani na zuba ma ba." Karo na babu adadi da tausayin yadda yaga duk ta firgice ya dirar masa cikin zuciya. Cike da nutsuwa irin tasa da Allah ya wadata shi da ita yake girgiza kai yana faɗin.
"Irfaan ya kyauta sosai, sannan karki damu dan na zuba da kaina ai ni nace ki barshi. Oya koma ɗakin ki kiyi kwanciyarki dare ya yi, kinci abinci dai ko?" Ya tambayeta cike da son gyara kulawarsa da baya bata a da har sai da aka lurar dashi. Cike da mamakin yanayin da ya yi furucin Jauhar ta kalleshi. A cikin jikinsa yaji cewa kallansa ake domin da ya tambayeta sai kawai ya maida hankalinsa wajan zuba abinda yake da buƙata. Kallansa ya mayar saitin inda yake jin idon a jikinsa, yadda yaga Jauhar ɗin tana ware ido yasa shi saurin yin magana.
"Ya akai?" Ta sauke ido dan bata iya kallansa saboda yana da mugun kwarjini. Muryarta tana rawa tace.
"Alhaji naci."
"Masha Allah toh kije kiyi kwanciyarki Allah ya huta gajiya Allah yai miki albarka." Jauhar ta durkusa tana amsawa dan ba ƙaramin daɗi addu'ar tashi tayi mata ba, shine mutumin da yake yi mata wannan daddaɗar addu'a sai kuma idan Hajiya tazo wacce idan ba wani babban abu bane ya faru a gidan bata cika zuwa cikinsa ba. Ɗaki ta koma tana shiga kwanciya tayi akan carpet ɗin dake shimfiɗe a ciki wanda shine ya zamar mata kamar katifa da take kwanciya tayi bacci. Sai da ya kusan kammalawa Hajja Maimoon ta karaso inda yake tana jan kujera ta zauna. Dube-dube ta shiga yi ko zata hango Jauhar amma ba ita ba labarin ta. Kira ta shiga kwala mata Alhaji Sha'aban ya dakatar da ita.
"Me kuma zatayi?" Mamakin tambayar tashi tasa Hajja Maimoon kallon cikin idanunsa.
"Idan abinci za'a zuba miki madam kina dani a kusa meye na kiran yarinya?" Nan da nan farin ciki ya kamata tayi ƙasa da kanta cike da nuna kunya tana janyo boul, karɓa yayi da kansa ya zuba mata fresh milk ɗin a ciki sannan ya zuba mata cornflakes ɗin cikin extra boul dan ya lura shi tafi bukata a gurin. Suna ci suna hira har ta kammala suka mike zasu wuce ɗaki ta shiga kwalawa Jauhar kira dan tazo ta gyara wajan. Alhaji Sha'aban yana riƙe da hannunta yace,
"Me zatayi?"
"Ya Habiby tazo ta kwashe kayan ta gyara wajen ko?"
"Ki bari idan Allah ya tashe mu gobe sai tayi mana abinda tana nan ba wani guri zata je ba." Ɓata rai tayi tace,
"Yanzu Ya Habiby haka za'a bar gurin nan har sai da safe? Haba Ya Habiby sai kace gidan ƙazama? Tana nan fa meye amfaninta a gidan nan?" Ya ɗan sanyaya murya yana janyota cikin jikinsa dan harga Allah baya son a taso yarinyar nan yanzu tunda har shine yace taje ta kwanta. Hajja Maimoon kuwa ta sake haɗe rai dan tunda taga yana wani matseta cikin jikinsa tasan lallaɓata zaiyi ta haƙura tabar Jauhar zuwa safiya, ita kuma tana jin tamkar idan ta barta zuciyarta ƙonewa zatayi dan bata farin ciki idan taga Jauhar na hutawa ko tana samun walwala a gidan.
"Pls.. Nasan gobe tana idar da sallar asubahi zata fito ta gyara, yanzu dai kam kiyi hakuri ki kyaleta." Ganin da gaske hanawa zai yi sai kawai ta zare hannunta daga cikin nasa ta janye jikinta fuskar nan tata a matukar haɗe tace.
"Gaskiya Ya Habiby idan har na bar yarinyar nan bata gyara gurin nan ba shikenan haka zata dawo kazanta sai wacce batayi niyar yi ba. Kabar ni da ita kawai Allah sai tayi aikin nan." Kallon yadda ta kafe tana yi masa gaddama yake ya ji abun yai matukar ɓata masa rai, a tunaninsa duk abinda yace mata ya kamata ta dinga yi babu jayayya koda ranta baya so kamar yadda shima yake hakura da wasu abubuwan koda ba dai-dai bane dan gujewa ɓaci ransa, amma ya lura sam bata tunanin hakan, takan yi masa kafiya musamman idan abun ya shafi Jauhar takan nuna masa bai isa ba itace wacce take da iko da ita. Ransa a ɗan ɓace da yake ba saba bari ya yi ɓacin rai ya yi tasiri a zuciyarsa ba ya sauke nauyayyen numfashi yana ambaton Allah abakinsa. kallanta da idanunsa yai cike da san nuna matsayinsa na mijinta agareta yake cewa.
"Me kike nufi kenan? ban isa nace ga abinda za'a yi ba kiyi ne ko?" Cikin rashin nuna damuwa da sauyawar da fuskarsa tayi Hajja Maimoon ta kawar da fuska tana sake haɗe rai.
"Kizo ki wuce muje bana san kuma yin magana akan wannan." Zuciyar Hajja Maimoon ta shiga yin zafi tana wani irin tururi ji takeyi tamkar ana ƙara garwashi. Idan har Jauhar tayi kwanan farin ciki a gidan nan tabbas ba sunanta Maimuna ba dan kuwa abu ne da bazai yiwu ba indai har tana cikin gidan. Yayi taku biyu yaji alamar bata biyo shi ba, hakan yasa shi juyowa ya ganta tsaye ta kafe idanunta akan ɗakin da Jauhar ke ciki hannayenta naɗe a ƙirji. Ransa ya sake ɓaci ya hango tsantsar raina shi da Maimoon tayi wanda besan ya kai har haka ba.
"Ya yi kyau." Haka kawai Alhaji Sha'aban Sada ya faɗa kawai ya wuce bai bi ta kanta ba.
Ganin ya wuce ita kuma ta nufi ɗakin Jauhar ba tare data fasa yin abinda zuciyarta take umartar ta ba. Tana shiga ta tarar da Jauhar ɗin kwance ta saki baki tana ta sharara bacci dan tun lokacin da Alhaji Sha'aban ya umarce ta da taje ta kwanta tana shiga ɗakin kwanciya tayi dan ba ƙaramin bacci ne ke damunta ba, dalilin da yasa ko kiran Hajja Maimoon bata jiyo ba duk kuwa da cewa ko bacci takeyi sai ta dinga jin kiran matar nan. Kallanta kawai Hajja Maimoon keyi cike da tsabar mamaki, abubuwa da yawa suka sanyata ta yi cak wajan kasa tashin Jauhar ɗin. Kayan jikinta, da kuma yadda take ta sauke minshari da alama baccin ya yi masifar yi mata daɗi. Toilet ɗin cikin ɗakin ta shiga da niyar ɗebe ruwa ta watsa mata wani irin hamami ya doki hancin Hajja Maimoon tayo baya tana jin tamkar zatayi amai. Cikin sauri ta fito daga ɗakin, kai tsaye ta nufi kitchen ta buɗe fridge. Ruwa ta ciro gora guda a freezer ta juye shi cikin wata roba ta sake ɗakko wani ta juyo sannan ta nufi ɗakin Jauhar kamar zata tashi sama dan sauri. Tana zuwa ta saita robar a saitin fuskar Jauhar kawai ta sheƙa mata ruwan sanyin nan duka.
"Wayyo Allah na na shiga uku na lalace." Jauhar ta faɗa a gigice tana mikewa tare da kai hannu tana neman abinda zai ceceta. Kafin ta gama dawowa daga cikin tashin hankalin data shiga ciki ne taji an shaƙota ana jijjigawa, Jauhar ta dinga ihu tana neman taimako can taji Hajja Maimoon ɗin na cewa.
"Ai dama nace ke kika ɗauke zinariya ta munafuka kika siyar, idan ba haka ba a gidan uban waye kika samu kudin siyar rigar nan?" Jin tambayar da takeyi mata ne yasa Jauhar da kyar ta iya janyo kalamai dan har lokacin Hajja Maimoon bata sakar mata wuyan ba tace.
"Uncle Ir.. Ir.. Faan.. ne.. Ya bani."
"Ohhhh! Irfaan ne ya sake siya miki ko? Dama kayan da ya siya a shago na munafikin ke ya siyawa da kuɗin zinariyata da kika bashi ya sayar?" Kai Jauhar ta shiga girgizawa alamun a'a dan har lokacin Hajja Maimoon bata iya sakinta ba. " Idan basu bane Jauhar to ki gaya min uban me kike yiwa yaron can yake yi miki wannan hidimar ko kuma nayi takakkiya muje wajan su Baffa wallahi ayi min iyaka dake dan ba zakisa bakin tarihin abun kunyar da ubanki ya yi ba ya maimatu acikin gidana ba. Dole ki gaya min uban me yake miki har yake jin daɗi yana siyo miki kayan da ni zan iya sakawa ko kuma su Jannat?" Tana kaiwa nan ta saketa tana jiran jin abinda Jauhar ɗin zata faɗa. Ita kuma banda tari babu abinda takeyi saboda wuyan ta da take jin kamar numfashinta zai tsaya. Gefe guda kuma kalaman Hajja Maimoon ne yake mata yawo na cewa zata kaita wajan su Baffa, toh kodai tace itace ta ɗauka? Tayi amfani da damar a kaita wajan su tace ba zata biyo ta ba shikenan ta kubuta daga hannun jarababbiyar matar nan.
"Zaki gaya min ko sai na kasheki a cikin ɗakin nan?" Hajja Maimoon ta faɗa cikin tsawa.
"Hajiya wallahi... Wallahi shine... Shine.. Ya..." Cikin zaro ido tun kafin Jauhar ɗin ta ƙarasa yin magana tace.
"Ya yi me?" A gigice Jauhar tace,
"Ya bani."
"Ohhh! kina nufin dai ba kudin zinari na ne da kika bashi ba?"
"Eh wallahi Hajiya ban ɗauka miki ba na rantse da Allah." Hannu takai ta fizgo Jauhar da karfi ta haɗe da jikin ginin dakin tana cewa.
"Toh taɓa miki jiki yakeyi ko?" Jauhar taji maganar a wani iri, cikin sauri tace.
"A'a Hajiya."
"Zaki gaya min ko sai na yankaki dan ubanki?"
"Wallahi Hajiya kinji na rantse miki Alkur'an baya taɓa ni, kawai yana bani kayan yake tafiya wallahi gaskiya nake gaya miki." Jin hakan yasa Hajja Maimoon ta taso ƙeyarta suka fito daga ɗakin tana cewa.
"Toh idan ma kin bari yana miki wani abun ke kika sani ba damuwata bace wallahi, sannan kina gama gyara wajan nan kije ki cire kayan nan ki ajiye min su zanzo na ɗauka ai ba kalarki bace ba dan sunfi karfin ubanki ma bare kuma ke banza a banza."
Ta ƙarasa maganar tana tura ta wajan dining area ɗin da karfi sannan ta wuce ɗakinta tana sakin tsaki da ƙarfi. Jauhar kuwa tana hawaye dafe da ƙasa dan turewar da aka yi mata sai da ya kaita ƙasan taels sauran kaɗan ta fasa goshi. Tana kuka tana kwashe kayan takai kitchen, ta rasa me yasa Hajja Maimoon ta zaɓi yin rayuwa da ita tun ƙanƙanuwa dan ta bautar da ita bisa wasu dalilai nata da batasan koma meye ba.
Tsab ta gyara gurin tayi wanke-wanke ta ajiye komai inda ya dace sannan ta koma ɗakin ta. Jikinta ta kalla yadda rigar ta amsheta duk da cewar ta ɗan yi mata yawa amma ba wani sosai ba. Kuka taji yazo mata ganin an rabata dasu akaro na biyu. kenan ba damar ta saka ɗayar rigar wacce ke cikin ledar duk da yadda ta burgeta! kenan har handbag ɗin da takalman duka Shikenan an rabata dasu? Bata san lokacin da ta durƙushe a kan carpet ɗin baccinta tare da fashewa da wani kukan mai bala'in taɓa zuciya.
________
Hajja Maimoon kuwa tana komawa ɗaki wardrobe ta nufa ta shiga nemo kayan da zata saka. Wata orange ɗin sleeping dress ta janyo sabuwa dal bata daɗe da siyan su ba, ta feshe su da turaruka masu masifar ƙamshi sannan ta zare kayan jikinta tasa na baccin. Wajan mirror ta nufa tana kallan fuskarta ta saki murmushi tuna shirin da tayiwa Habibyn nata na nuna godiya abisa farin cikin da ya sanyata. Idan ta tuna cinikin da tayi a yau kaɗai sai taji wani irin farin ciki yana mamaye ta. Jan baki ta goga tabi jikin mata da khumras masu daɗi sannan ta fito ta nufi ɗakin Alhaji Sha'aban Sada. Cike da nutsuwa tasa hannu akan handle ɗin ta murɗa ta shiga. Kwance ta hango shi sai dai tasha mamaki ganin ko kallan ƙofar baiyi ba bare tasa ran zai miƙo mata hannunsa kamar yadda yake yi mata idan tazo.
Kan bed ɗin ta nufa ta hau still bai ko kalleta ba bare ya nuna yasan tazo ba. Mamaki ya kamata ta kwanta sai taga ya juya mata baya. Shi kuwa ransa ne ya ɓaci ganin yace tayi abu taki duk da cewa ba wai yau ne na farko ba, sai dai yau abin yafi bashi haushi saboda yana ganin kamar so takeyi ta nuna masa tafi karfinsa bai isa da gidansa ba. Kasa yi masa magana tayi dan tana jin wata irin izzah gani take idan har itama ta kulashi to ta ɓarar da ajinta matsayin ta na ƴa mace. Shi kuma kamar jira yake dama ta shigo kawai bacci ya ɗauke shi ya barta cike da masifaffan mamaki. Ƙeyarsa kawai ta zubawa ido tama rasa uban me takeyi a wajan, ga wata irin kulawa da take buƙatar ya bata bawai na kwanciyar aure ba, a'a tana buƙatar ya rungumeta yana bata labari ko kuma nuna mata yadda take da muhimmanci a rayuwarsa kamar yadda ya saba akoda yaushe, hakan zai bata damar sake yimasa godiya da nuna masa jin dadin abinda ya yi mata yau na sake ɗaga darajarta acikin yan uwanta mata.
"Kenan hakan bazai faru ba?" Ta tambayi kanta.
"To me nayi masa?" Ta sake jefa ma kanta tambaya a karo na biyu tana jin zuciyarta tamkar ta fashe Dan tsabar takaici.
"Akan maganar ɗazu ta Jauhar shine yayi fushi dake." Taji zuciyarta tana sanar da ita. Cije lips tayi tana sake jin wani irin zafin Jauhar, lallai ma akanta ne mijinta yau ya juya mata baya? Allah ya kaimu gobe mai raba ni da ita sai Allah, Hajja Maimoon tafaɗa cikin zuciya tana juya kwanciyarta tare da kashe fitilar dakin ta kunna masu bed lamp...
#A heart touching story
#Gonar Sharri
#Billy s Fari
#Hajja ce
#Ƴan Tagwaye