BABI NA TARA
by @ummasghar
*BISHIYAR TSIYA*
*DAGA ALKALAMIN YAN TAGWAYE*
*Umm Asghar*
*Sadiya Nasir Dan*
Arewa book
@ummasghar
Page 9
Ƙarfe biyu daidai Suleiman yayi parking motarshi a ƙofar gidanshi, sai faman cika yake yi yana batsewa shi kaɗai, fatan shi kawai ya isa cikin gidan idan har Batulu bata dawo mishi da wayar nan ba yayi mata dukan mutuwa. Fahad da tun da uban ya ɗauko shi daga makaranta yayi laƙwas a jikin kujera ganin yau Dadyn nashi yaƙi sakar mishi fuska, yana tsayawa a ƙofar gidan ya fice da gudu ya shiga ciki yana ƙwala kiran "Ammie, na dawo." Yunƙurawa Batulu tayi ta miƙe zaune daga kwanciyar da tayi akan doguwar kujera, babu laifi tunda ta samu ta sha paracetamol ɗin jikin nata yayi sauƙi. A kasalance ta sakar mishi murmushi tace "An dawo yaron kirki?" Ɗaga mata kai yayi alamun amsawa. "To yi maza ka kai lunch box ɗin kitchen kazo ka cire uniform sai aci abinci ayi sallah kafin lokacin islamiyya yayi." Daidai lokacin Suleiman ya shigo fuskar nan a murtuke tamkar wanda bai taɓa yin dariya ba. Yau ko sallamar ma bai yi ba saboda yana ji da zafin kai. Cikin sanyin murya tace "Abban Fahad sannu da dawowa." Wani matsiyacin tsaki ya saki yasa kai yayi shigewarshi ɗaki, sanin yadda yanayin zaman nasu ya koma yanzu yasa ko bin shi bata yi ba sai hannun Fahad data kama suka tafi ɗaki ta canja mishi kaya zuwa ƙananun kaya na shan iska, sai data bashi abinci yaci tasa shi yayi sallah sannan ta koma kitchen ta shirya abincin Suleiman akan tray ta ɗora kwalin wayar data bawa Mus'ab ya sayo mata akai ta ɗauka ta nufi ɗakin nashi.
Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga ɗakin, ta tarar dashi ya kishingiɗa akan gado yana waya da sahibar tashi Fadila, shigowarta bai sa ya katse wayar da yake yi ba sai ma wasu kalaman soyayya da ya hau furta mata duk don ya ƙara ƙular da ita. Ai kuwa wata irin mummunan faduwa gabanta yayi, "Wato kenan saboda Mace ƴar uwarta Suleiman yake yi mata duk waɗannan wulaƙancin?" Tayi wa kanta tambayar, akan reading table ɗin shi dake gefe ɗaya na ɗakin ta ajiye tray ɗin tasa kai ta fice tana sharar ƙwallar baƙin ciki. Bata taɓa tunanin akan wata Suleiman zai iya cin mutuncin ta ba sai yanzu da kunnuwanta suka jiye mata wayar da yake yi a gabanta babu wani shayi ko kunyar idonta bai ji ba ya zauna yana faɗawa wata mace kalaman da ita ya dace ya gayawa amma yaushe rabon da su zauna suyi hirar arziƙi ma balle har yayi mata kalamin da zai sanya taji daɗi.
Ya daɗe yana waya da Fadila suna musayar kalaman soyayya kafin suka yi sallama ya ajiye wayar yana jin matsuwar son kasancewa da ita, dole ne ma yaje ya samu Hajiya da batun ta don baya jin zai iya jure rashinta a kusa dashi har na wani lokaci. Idon shi ne ya kai kan tray ɗin kayan abincin da Batulu ta ajiye sai kuma yaga kwalin wayar data ɗora akai. Tashi yayi ya ɗauki kwalin yana jujjuyawa, tabbas irin wayar ce dai sai dai wannan sabuwa ce kar a kwalinta ga alama ko buɗewa bata yi ba. Tsaki yaja cikin ranshi yana jin takaicin dawo da wayar da tayi don shi sam ba hakan yaso ba, yaso ne ya dawo ya iske babu wayar yadda zai ci ubanta la'ada waje gobe ma idan aka ce ta taɓa kayanshi ta yiwa faƙirin ubanta da baya iya tsinanar mutane da komai hidima baza ta ƙara ba.
Bedside drawer ya buɗe ya ajiye kwalin wayar daga nan ya shiga banɗaki ya watsa ruwa, yunwa yake ji amma ba zai iya cin abincin Batulu ba gara yaje gidan Hajiya yaci acan. Shiryawa yayi cikin dark brown ɗin yadin filtex ɗinkin half jumpa, light brown ɗin hula ya saka a kanshi sai kayan suka haskaka shi kasancewar shi farin mutum mai cikar zati. Makullin motar shi ya ɗauka ya fita. Batulu na zaune a parlourn tana koyawa Fahad homework, ƙamshin turaren shi ne ya fara iskota kafin ya fito, ɗaga kai tayi ta kalleshi sosai yayi mata kyau a take kuma taji wani irin kishi ya kamata, tasan zai yi wuya idan ba wajen budurwar data ji suna waya zai je ba. Tabbas da ace lokacin da suke ƴar daɗi ne sai ta tuhume shi akan wayar data ji yana yi har ma tayi ƙoƙarin hana shi fitar da yake da niyyar yi amma a yanzu da tasan ƙiris yake jira ya hau jibgarta kamar ya samu jaka sai taja bakinta tayi shiru. Fahad ne yace "Dady baza ka kai ni islamiyya ba?" Ganin da yayi bai ce ya tashi su tafi ba, sai cewa yayi "Amminka ta kai ka sauri nake yi." Ya fice babu ko waiwaye. Da kallo Batulu tabi ƙofar daya fita tana jin zuciyarta nayi mata zafi, kenan har fitar da zai yi tafi kai Fahad makaranta muhimmanci a wurin shi? Babu komai ai akwai Allah, yana ji kuma yana gani In Sha Allahu shi zai yi mata magani.
Suna gama homework ɗin ta shirya Fahad cikin kayan islamiyya suka fita, kasancewar makarantar islamiyyar tasu da ɗan nisa yasa ta fita da wuri ta kai shi don kada yayi latti.
*****
Suleiman kuwa yana fita daga gidan shi gidan Hajiya ya nufa, acan cikin ɗakinta ya sameta ta kishingiɗa kan sallaya tana jan carbi. Tana ganin shi ta tashi zaune tace "yanzu nake zancen ka cikin raina nace yau Suleiman bai leƙo mu ba ashe kana tafe." Zama yayi akan kujerar zama ƙwaya ɗaya dake cikin ɗakin yace "eh wallahi Hajiya gida na wuce na ajiye Fahad tukunna, an yini lafiya?"
"Lafiya lau Alhamdulillah, ya gidan? Yasu Fahad ɗin da Batulu?"
Sai da ya ɗan yatsina fuska jin Hajiya ta ambaci sunan Batulu kafin yace "suna nan lafiya lau."
"To ayi ta haƙuri dai kaji Suleiman, ayu ta haƙuri shi babba da haƙuri aka san shi."
Ɗan siririn tsaki yayi yace "shikenan Hajiya duk rashin mutuncin da Batulu take yi mini sai dai ace nayi ta haƙuri bayan yarinyar nan sam bata da mutunci ban isa nasa ko na hanata ba sai abinda taga dama take yi gashi kin hanani ɗaukar mataki."
Ɗan murmushi Hajiya tayi tace "Fahad nake tausayi Suleiman shi yasa nake cewa kayi haƙuri ka ƙyaketa ta kula da ɗanta don yanzu idan ka rabu da ita ma wata zaka auro ba kuma kasan irin wacce zaka auro ba, gara dai da daɗi babu daɗi ita Batulun an san halinta sai aci maganin zama da ita."
Kawar da maganar yayi ta hanyar tambayar Abdulhamid don baya son wancan zancen da Hajiyar ke yi, shi fa ko bai rabu da Batulu ba babu abinda zai hana mishi auren Fadila don ita ce ta dace dashi ita ce kalar matar da yake so, kyakkyawa mai aji kuma ƴar babban gida wacce ba dai iyayen shi su nema a wurin shi ba sai dai shi suyi mishi don sun fi ƙarfin duk wani abu da zai ɗauka ya basu.
"Abdulhamid ya shiga gari tun ɗazu, watakila kuma yana wajen Saudat don yace idan ya samu lokaci zai ƙarasa can ɗin su gana su fahimci juna, don so yake yi kafin ya koma ayi auren ya tafi da matar shi can." Fuska ƙunshe da mamaki yace "Yaya Abdulhamid ne zai yi aure Hajiya? Wacce Saudat ɗin? Kada dai Yar Hajiya Rabi?"
Tana murmushi tace "ita fa, kasan ta daɗe tana son shi yana basar da ita to kamar da wasa dai ɗazu yake ce mini ya amince zai aure ta, wallahi baka ji yadda nake ji ba. Abdulhamid ya faranta mini sosai don dama ina jin kunyar Hajiya Rabi ganin yadda na kasa tanƙwara shi ya auri ƴarta." Sosai yaji farin ciki ya kama shi, tabbas ya taya yayanshi murna domin kuwa yayi dace da samun macen ƙwarai ƴar babban gida ba irin shi da yaje ya auro ƴar ƙananan mutane ba faƙirai masu jiran ayi musu.
"Hajiya a bani abinci yunwa nake ji."
Kallon shi Hajiyar tayi tace "kai da ka fito daga gidanka shine zaka zo nan kana neman abinci, ko dai har yanzu faɗan kuke yi da Batular?"
"Abincin da tayin ne bai gamshe ni ba shi yasa ban zauna naci ba."
"Allah ya kyauta," kawai Hajiya tace ta ƙwalawa Hafsa kira. Tana shigowa Hajiya tace "ki kawowa yayanki abinci," juyawa tayi taje ta haɗo mishi abincin ta kawo mishi. Karɓa yayi yana ci a hankali suna hirarsu da Hajiya har ya gama sannan ya tashi yace "Hajiya bari na tafi naji ana kiran la'asar daga masallacin zan wuce akwai wanda yake jirana zamu haɗu."
"To Suleiman, Allah yayi albarka kaji. Ka gaishe mini da Fahad tunda yau bai zo ya gaishe ni ba."
"To," yace yasa kai ya fita yana turawa Fadila saƙon text ɗin gashi nan zuwa tayi mishi tanadi mai kyau.
*****
Ƙayataccen murmushi ta sakar mishi ta rausayar da kai gefe ɗaya tace "sannu da zuwa Yaya Abdulhamid." Murmushin ya mayar mata shima yace "yauwa Saudat, kina lafiya?"
"Lafiya ƙalau, yasu Hajiya?"
"Duk suna nan lafiya Alhamdulillah, tace ma a gaishe ki."
"Ina amsawa," tace tana sakin murmushi zuciyarta cike da farin ciki, ta kasa yardarwa kanta wai yau Abdulhamid ne tsaye a gabanta yazo neman aurenta, abinda ta daɗe tana fatan faruwarshi har ma ta soma cire rai da zai sota kamar yadda take masifar son shi ai gashi Allah cikin hukuncin shi ya karkato mata da hankalin shi a lokacin da bata yi zato ko tsammani ba. Shiru ya ratsa tsakaninsu na ƴan mintuna na rashin sabo da kasancewa da junansu, sai kuma tace "Mu shiga daga ciki Yaya Abdulhamid." Ɗaga mata kai yayi alamun amsawa ya fito daga motar bayan ya rufe yabi bayanta tayi mishi jagora har cikin gidansu ɓangaren mahaifinta inda ta sauke shi a parlourn saukar baƙin mahaifin nata. Wuri ta nuna mishi ya zauna ita kuma ta shiga cikin gida ta haɗo mishi drinks da ruwa akan tray ta ɗauko ta kawo, a gabanshi ta ajiye ta buɗe robar ruwa dana lemon duka ta tsiyaya a tumblers ta ajiye. Komawa tayi ta zauna akan kujerar dake facing wacce yake kai. Kallon ruwan data ajiye mishi yayi ya ɗan yi murmushi yace "Ruwa da lemo duk ni kaɗai, to wanne zan sha a ciki?"
A kunyace tace "Duka," tana ƴar dariya. Dariyar yayi shima yace "Tunda haka kika buƙata hakan za'a yi ranki ya daɗe." Ɗan ɗagowa tayi ta kalle shi jin ranki ya dade daya ambace ta dashi sai suka haɗa ido, da sauri ta sauke kanta ƙasa tana sakin wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Dama ashe Yaya Abdulhamid yana barkwanci haka ita ce bata sani ba. Ji tayi yana tambayarta "Ya karatu?"
Tace "Ai na gana, fitowar result muke jira mu tafi NYSC."
"Masha Allah, hakan nada kyau. Shi kenan sai kiyi NYSC ɗin ki a Abuja ko?" Sunkuyar da kai tayi tana murmushin farin cikin jin abinda yace. Jefi-jefi suke hira kasancewar babu wani sabo a tsakanin su, yawanci dai shi yake yi mata ƴan tambayoyi akan al'amuran da suka shafi rayuwarta tana bashi amsa. Ya daɗe sosai a wurinta kafin yayi mata sallama yace zai koma gida sai ya ƙara dawowa amma kafin ta saka mishi number wayarta don a riƙa gaisawa ta waya, ya miƙa mata wayar ta karɓa ta shigar da numberta sannan ta mayar mishi yayi saving da 'WIFE'. Har waje inda yayi parking motar tayi mishi rakiya, sai da ya shiga ciki ya zauna sannan tace "Kayi haƙuri ban san zaka zo ba ban shirya maka abinci ba."
Kallonta yayi yace "Kada ki damu wanda kika kai mini da safe ya cika mini ciki har yanzu bana tare da yunwa." Rufe idonta tayi tana dariyar jin daɗin jin cewa yaci abincinta. Sallama suka yi yaja motarshi ya tafi sai da taga ƙulewar motar shi sannan ta koma cikin gida tana sauke ajiyar zuciya, tabbas mahaƙurci mawadaci yau gashi cikin hukuncin Allah Abdulhamid yazo gidan su da nufin aurenta abinda ta daɗe tana fatan ganin kasancewar shi......
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce
*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jidda Aliyu
*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch
*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.
*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso
*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000
*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya ***
*KATIN MTN*
***
Shaidar biya ta lambar.
_*ƳAN TAGWAYE BIYAR*_
#SADIYANASIRDAN
#UMMASGHAR
#ƳANTAGWAYEBIYAR