{42..}
Tsallaka titin Nurain yayi ya isa wajen Motar Abba, driver ya buɗewa Abba motar ya fito, Abba ya ringa kallon Nurain da ya ƙurawa street din ido yace "wajen mahaifin Hajar na kawoka ka gaishesa, ya kamata ya sanka..", Nurain ya kare hasken rana da yake haske masa ido yana tunanin wace ce kuma Hajar, sunan ya ringa yawo a brain dinsa amma ya kasa gane wace, ganin bai fahimta ba Abba yace "your wife, ko baka san sunanta ba..?", Calmly Nurain yace "Ohk, amm nan ne unguwar...?", Abba yace "yess, ga layin gidan can" ya nuna kwarɓaɓɓen lungun gidansu Hajar, with disgusting look Nurain ya kalli layin, how mutane suka rayuwa a nan wajen, Abba ya ciro wayarsa daga pocket yayi making call na minti biyu, yana gama wayar yace "muje" da haka ya fara tafiya ya shiga layin, Nurain yabi bayansa, Nurain dai kawai bin Abba yake suna surƙumawa cikin lungun, wani irin nisa yaga tafiyar ta masa duk da cewa gidan bashi da nisa da titi, Abba ya tsaya a daidai ƙofar gidan, Baba da already yana soro ya fito waje sukay musabaha da Abba, Baba yace "Bismillah", Abba ya bisa suka shiga soron gidan ya zauna kan tabarma da ke shimfiɗe a soron, saida Nurain ya rage tsaho snn ya shiga, ya zauna daga gefe yana kallon Baba yace "barka da rana", da fara'a Baba ya amsa, Abba yayi murmushi yace "he is my second born Uthman, dashi aka ɗaura auren...", Baba yayi ajiyar zuciya yana kallon Nurain yace "masha Allah..", Nurain ya ɗaga kansa yana kallon roof din soron wanda spider web ta cikasa har tana zazzagowa, Abba da Baba sai taɗinsu suke, past dinsu suke tunawa suna mgana akai, after 5mins Nurain ya duba agogon wrist dinsa, Abba ya dubesa ta gefen ido kafin yace "Nurain you can go idan Kanada wani appointment din", cike da girmamawa Nurain ya yiwa Baba sallama kafin ya tashi ya bar soron, Nurain na fita daga lungun ya ciro handkerchief ya goge fuskarsa, titi ya tsallaka ya shiga motarsa, zaune yayi cikin motar bayan ya kunna ya ware Ac, So a nan Abba ya masa aure, Ghetto area, shi ba wnn ne damuwarsa ba ma, bayan ƴar Ghetto da aka aura masa kuma mara manners, da reverse ya fita daga street din, yana hawa main road ya take accelerator, hanyar gidansa ya ɗiba, few minutes ya isa unguwar duk da cewa akwai nisa cause ya take motar ba ƙarya, a ƙofar gida yayi parking ya fito, Garba dake tsaye bakin gate tare da wani mutumi ya taso yana yiwa Nurain barka da zuwa, Nurain ya amsa yana kallon mutumin dake tare da Garba, Garba ya dubi mutumin yace "ga uban gidan nawa fa..", da sauri mutumin ya russuna yace "barka da zuwa Alhj..", Nurain yace "an yini lfy...?", mutumin yace "lfy alhmdllh an gode Allah...", Nurain na kallon Garba yace "shine ko?", Garba ya shafa kai yana ɗan russunawa yace "Eh alhj ƙarami, shine wllh, ɗan uwa na ne na jini, da Babansa da mahaifina uwarsu ɗaya ubansu ɗaya..", Nurain ya jinjina kai yace "Ohk, hakan yayi" da haka ya ƙarasa bakin gate din ya buɗe, ya koma cikin motar Garba ya zuge masa gate ya shigar da ita huge parking space dake gidan nasa, saida Garba ya bari mutumin da suke tare ya shigo snn ya mayar da gate din ya rufe, Nurain ya fito daga mota bayan ya gama parking, ya ringa kallon compound din, kiran Garba yayi wanda ya taho da sauri, Nurain yace "ka gaya masa aikinsa ko?", Garba yace "Eh na gaya masa komai, gadi da bar ruwan shuka sai share tsakar gida", Nurain yace "Yawwa, kira min shi", Garba ya tafi ya kira mutumin suka taho tare, Nurain yace "Garba ya maka bayani ai", mutumin kansa a ƙasa yace "Eh alhj..", Nurain yace "yawwa, bar ruwan shuka da share tsakar gida na wani lokacin ne kafin a samu me yi naka dai shine gadi", mutumin yace "insha Allah komai bazai gagara ba..", Nurain ya gyaɗa kai yace "suna fa..?", mutumin yace "Inuwa..", Nurain ya jinjina kai kafin ya wuce ya bar wajen ya nufi main entrance din shiga gidan. Garba ya dashe haƙora yace "Allah kuwa Inuwa ka kwashi dami a akala don wllh tllh kirki dai a wajen bawan Allahn nan har ya masa yawa, ni dai na gaya maka ka zama mai gsky da amana, idan ka riƙesa da kyau tabbas zaka samu alkhairy bana wasa ba, wllh don ma dai kai ne amma in ba haka ba wani huhulahun zan nemawa wnn gangariyar aiki...", Inuwa yayi murmushi har cikin ransa yaji daɗi yace "ai Allah ne zai biyaka Garbati da wnn taimako da ka min", Garba yace "wnn fa aikin nawa ne na sadaukar maka..", Inuwa yace "ai shiyasa nake ta gode maka...", bayan minti sha biyu Nurain ya fito bayan ya rufe ko ina, keys guda biyu ya bawa Inuwa yace "key din ɗakinka ne da kuma gate, gobe da safe saika zo kayi abinda za kai ka buɗe ɗakinka, amma yau dai ka tsaya tare da Garba", hannu biyu Inuwa yasa ya amshi keys din, Garba ne ya masa nuni da ɗakin nasa wanda ke kusa da gate, Nurain ya ciro kuɗi daga pocket ya bawa Garba yace "saiku koma can gidan..", godiya Garba yayi masa sosai. sai bayan Sallahr la'asar wajen ƙarfe biyar snn Nurain ya koma gida, don sai yau ne ya samu yaje wuraren da yake son zuwa tin dawowarsa 9ja.
★Hajar ta saka Hijab dinta tabi bayan Noor data isar mata da saƙon kiran da Mami ke mata, Mami na zaune palourn ta tare da Tailor wacca ta saba musu ɗinki, Noor ta koma inda ta tashi ta cigaba da latsa wayarta, Hajar ta zauna kan carpet tace "gani", Mami ta dubi Tailorn tace "ga mai kayan nan", Tailorn tace "Okay tom bari na aunata..", bai ɗauketa wani lokaci ba ta gama auna Hajar tass, Mami tace "gobe fa nake son kayan nan Salmah", Salmah tayi murmushi tace "Mami kar kiji komai insha Allah gobe sha biyu na rana a gidan nan zata yiwa kayan nan..", Mami tace "toh Allah yasa", Salmah ta yafa mayafin Abayarta, ta ɗauki wata Babban leda dake kusa da ita tace "toh Mami na wuce, Noor sai anjima..", Noor ta ɗago kanta daga kallon waya tace "da wuri haka...", Salmah tace "gwara na tafi yanzu na fara aiki, bana so naƙi cikawa Mami alƙawari", Mami tace "dan kwa faɗa zanyi wllh idan kayan nan basu samu gobe da wuri ba", Salmah tace "insha Allah baza aji kanmu ba Mami.." da haka ta musu sallama ta tafi, Hajar bata koma ɗaki ba tayi zamanta anan, buɗe ƙofa akay Nurain ya shigo, hannunsa riƙe da handle ya ƙarewa ɗakin kallo, har yayi wanka ya canza kayan jikinsa daga manya zuwa ƙanana da yke zaman gida dasu, wani irin zaro ido Noor tayi ganinsa unexpected, da sauri ta kara wayarta a kunne ta fara wayar ƙarya, ta tashi zata shige bedroom din Mami, ƙarasa shigowa palourn yayi yace "idan kika shiga har nan zan biyoki na zaneki", Noor ta yarfe hannunta tace "yaya ka tsaya kaji don Allah...", yatsansa ya ɗora a lips yace "shhhh na tambayeki ne...?" ya samu Sofa ya zauna, yana zama Hajar ta miƙe ta nufi hayar ɗakin da take, Mami ta kirata tace "ina zaki...?", Hajar ta juyo a hankali tace "ciki zan koma..", Mami tace "dawo ki zauna nifa na kiraki kuma bance ki tafi ba..", ba yadda Hajar ta iya haka ta dawo ta zauna, koda wasa bata dubi position din da Nurain yake ba, shima tinda ya kalli inda tke sau ɗaya bai sake kallon wajen ba, Nurain ya dubi Noor da tay tsaye sai wurwurga idanu take, murya ƙasan maƙoshi yace "je ki kawomin abinci, surely we will meet later..", a ɗarare Noor tace "tom", har ta kai bakin ƙofa Mami ta kirata, ta dawo da baya tana kallon Mami, Mami tace "je ki kunna burners ki zuba turaren wuta..", Noor ta dubi Nurain kafin tace "tom" ta dawo ta shiga bedroom din Mami, Mami ta kalli Hajar da ta zubawa Tv ido, kawai Tv take kallo duk da ba wani abun arziƙi ake haskawa ba amma ta gwammace ta kalli Tv sbd kar idonta yaje inda zuciyarta zata sosu, Mami tace "Hajar..", Hajar ta kalli Mami tace "Na'am", Mami tace "tashi kije kitchen za kiga wasu silver warmers guda uku akan cabinet ki ɗakko min su, idan kin kawo sai ki koma ki ɗakko min ruwa da drink a fridge", Hajar tace "tom" ta tashi ta fita daga palourn, Nurain yayi kamar baiji me Mami ta faɗa ba ya fara duba Mac phone, Mami dake kallonsa tace "misplacing phone dinka kayi ne..?", yace "A'a, a ɗaki na barta", Mami tace "alright then", Hajar ta shigo da tray a hannunta mai ɗauke da warmers, ta ajiye nan kan carpet kafin ta juya ta sake fita, babu jiwa ta dawo da wani tray din na ruwa da lemo da Cup da kuma plate with spoon, ta ajiye kusa da warmers din, a hankali tace "zan koma ciki", ba ta bari ta kalli Mami ba ta faɗi hakan, Mami tace "toh", Hajar ta tafi a hankali tana zuwa ƙofar ɗakin ta buɗe ta shige da sauri har dasu tuntuɓe, jingina tay da jikin ƙofar ta lumshe idanunta. Ganin har wajen minti talatin da ajiye masa abincin amma bai taɓa ba yasa Mami tace "Nurain ba Abincin zaka ci ba kasa aka kawo maka..?", ya ajiye Mac phone din a gefensa yace "A'a ni ba ci zanyi ba, i thought ke zaki ci ma", da mamaki Mami ta ringa kallonsa, after looking at him for few seconds tace "zuba abinci kaci malam", ya shafa kansa yace "nifa am full bance zanci ba", Mami ta haɗe gira tace "nace ka zuba abinci", bai sake mata musu ba ya ɗebi abincin kaɗan wanda bai wuce loma biyar ba, duk da irin yunwar da yake ji amma samm yaji baya sha'awar abincin, gaba ɗaya ya fitar masa a raii, ya ringa juya spoon ɗin hannunsa, Mami dai ta ringa kallonsa ta gefen ido har ya gama caccakar abincin wanda ko kusa da baki be kai ba ya ajiye, ruwa da lemon ma bai sha ba haka ya tashi ya fita, Mami ta bisa da kallo, girgiza kai tayi a ranta tana addu'ar Allah yasa dai wnn abu mai ɗorewa ne kar ya zama fitina. washe gari wani irin odd Hajar ta ringa jin kanta, tinda aka kawota gidan yau ne ta wayi gari taji hakan, ita ba mai rashin lfy ba kuma bazata kira kanta da mai lfy kai tsaye ba, breakfast da aka kawo mata ma kaɗan taci, Noor ma saida ta tambayeta lafiyar ta kuwa sbd sauyin nata, Hajar tace "bacci ne bai isheni ba inajin", Noor tace "toh ki koma ki kwanta kawai..", Kwanciyar da Hajar tayi sam bata samu bacci ko na 1sec ba, kawai juye juye ta ringa yi sai kace ƙadondoniya, wajen ɗaya saura ta tashi ta shiga bathroom ta ɗora alwala ta fito, bayan ta idar da sallah ta sake kwanciya, kamar wasa sai bacci ya ɗauketa, ba ita ta farka ba sai daf da sallahr la'asar, Noor ce ta shigo ganin ta farka ta fita a ɗakin, babu jimawa sai gata ta dawo tare da Mami, Noor ta ajiye kayan da suke hannunta a gefen bed kafin ta juya ta fita, Mami tace "har kin tashi dear..?", Hajar ta gyaɗa, Mami tace "Sallah za kiyi ne..", Hajar tace "Eh", Mami tace "idan kinyi Sallahr sai kiyi wanka ki saka waɗan nan kayan kinji", Hajar tayi shiru tana kallon kayan dake gefen gado kafin ta gyaɗa kai tace "tom", saida tayi sallah taci Lunch da Noor ta kawo mata snn ta shiga wanka kamar yadda Mami tace tayi, ta fito ɗaure da towel ta zumbula hijab, mai ta shafa kafin ta dawo gefen gadon ta zauna ta fara warware gogaggun kayan, wani sassanyan ƙamshi ne yake tashi daga jikinsu, Atampa ce mai laushin gaske kai kana ganinta kasan mai tsada ce, Hajar ta ringa shafa kayan kafin dai ta warware ta saka a jikinta, sosai sukay mata kyau dass dass, riga da skirt sosai yake fito da ainahin shafe dinta, ɗan kwali da mayafi sai pendant necklace da ear rings ne kawai bata saka ba, da sauri ta fara ƙoƙarin rufe kanta ganin Mami ta shigo, ɗan kwalin ta yafa a kanta ta rufe gashinta, Mami ta zauna gefen gadon itama ta riƙo hannunta tace "Yau kuma sai gidanki insha Allah", wani darammm Hajar taji a ƙirjinta, Mami tace "Allah yayi miki albarka tare da zaman lafiya madauwami, maza ki ƙarasa shiriyawa...", hawayen da suka cika idanunta suka fara zarya bisa kuncinta wanda bata shiryawa hakan ba, Mami that was very surprised da ganin tears ɗinta tace "what happened Hajar...?, akwai abinda yake damunki..?", Hajar tasa bayan hannu ta goge hawayen ta girgiza kai a hankali tace "A'a, kawai dai ni bansan waye wanda aka aura min ba, ni dai nasan Baba na yace yamin aure amma ban san waye ya aura min ba..", ta fara kuka a hankali, Mami tayi ajiyar zuciya ta tausasa murya tace "dear he is my son wanda aka aura miki, yayan Noor ai kin ganesa ko", Hajar na kallon Mami da jajayen eyes ɗinta ta gyaɗa kai, knn dai shi ɗin ne ko, Mami tace "Stop crying kinji, he will not harm you i promise..", Hajar dai ta rasa a wani position zata ajiye zuciyarta don ji take tamkar an tsireta da tsinken tsire ana gasawa a tukuba, Noor ce ta shigo, ganin yadda idanun Hajar suka kumbura tace "subhanallah kuka kike..", Mami ta tashi tace "she is not, gyara mata fuskarta ina zuwa" da haka ta buɗe ƙofa ta fita, Noor ta saka mata ear rings da necklace snn ta mata ɗauri mai kyau, saida ta ɗauki kwalbar turare dake kan mirror ta sake baƙaƙa mata ajiki duk da irin ƙamshin da kayan suke, biyar da ƴan mintina Hajar na zaune main palourn tare da Noor, Mami ta fito daga part din Abba ta kama hannun Hajar suka shiga part din, 5minutes da shigarsu suka fito bayan Hajar ta gaida Abba, don daman bai taɓa ganinta ba sai yau. Mami na kallon Noor dake zaune main palour tace "Nurain din bai fito ba har yanzu..?", Noor tace "Eh bai sakko ba", Mami ta kalli stairs kafin ta wuce ta fara hawa, knocking door ɗin ɗakinsa tayi, ya buɗe ƙofar yana kallonta, tace "baka gama bane..?", yace "yanzu zan sauko" da haka ya mayar da ƙofarsa ya rufe, yayi ajiyar zuciya, ya ƙarasa buttoning rigarsa ya saka links, shi kaɗai yasan abinda yake ji a zuciyarsa kawai jurewa yake, down stairs ya sauka bayan ya kulle ɗakin nasa, part din Abba ya shiga ya masa sallama, ya yiwa Mami ma dake zaune main palour daga haka ya fita compound, packing space ya isa ga buɗe motarsa ya shiga, Noor riƙe da tagomishin kayan arziƙin da Mami ta haɗawa Hajar na turaruka ta fita compound, Noor ta saka turarukan a back seat, ta dawo ta riƙe hannun Hajar zuwa wajen motar, front seat ta buɗe mata, a hankali Hajar ta shiga motar, Noor tace "sai nazo sister" da haka ta rufe motar taja baya, Nurain ya ƙurawa steering ido bai bari ya kalli inda take ba, saida ya gama warming motar snn ya fara driving a hankali ya fita daga gidan, tinda suka hau babban titi Hajar ta juyar da kanta side glass din ƙofa kawai kallon waje take, sanyin Ac ya ringa shigarta ga kuma abinda yafi tsaya mata a maƙogoro scent dinsa, ita dai bata san ma ina suka bi ba kawai gani tai sun tsaya a bakin gate ɗin wani katafaren gida, Nurain ya danna horn, mai gadi ya buɗe gate da sauri, Nurain ya parker motar a parking space kafin ya kashe ya zare key daga Ignition, buɗe murfin motar yayi ya fita, a hankali Hajar ta buɗe motar ta fito, ya buɗe back seat ya ciro ledar da Noor ta ajiye ya rufe motarsa, dire ledar yayi nan bakin motar yayi wucewarsa ciki, a karo na farko data ɗaga kai ta kallesa, ta taɓe baki ta sunkuya ta ɗauki ledar tayi hanyar da ta ga yabi, tsaye tayi bayan ta shiga palour, ta ajiye ledar hannunta, ta ƙarewa palourn kallo tass, direct Nurain upstairs ya haura ya shiga ɗakinsa bayan ya kunna Solar, trolleyn kayansa tin wacca ya kawo last week ya buɗe, arranging kayan ciki ya fara yi awajen da yake so, duk yawanci ma kayan aikinsa ne aciki ba sutura ba don on Monday yake da shirin rusuming work, yana gama arranging kayan yaji ana kiran sallah, huge bathroom dinsa ya shiga yayo alwala, da sauri ya gama ya fito, fita yayi ya sauka down stairs, Hajar na rakuɓe daga bayan kujera har ta gaji da tsayuwa ta samu guri ta zauna, kallo ɗaya yayi mata ya fita zuwa masallaci wanda akwai tazara kaɗan tsakaninsa da gidan, Hajar ta miƙe tsaye tana tunanin ina ne alqibla don da alwalarta sallah kawai za tay, kallon stairs tai wani tunani yazo mata, bayan ta gane gabas tayi sallar ta, har sallar isha'i Nurain yayi kafin ya dawo gida wajen takwas da ƴan mintina, muƙullin motarsa ya ɗauka ya fita, eatery ya fita ya siyo abinci ya dawo, wai yau shine da siyar abinci a waje, abinda bai taɓa sha'awa ba knn, kan Centre table ya ajiye ledojin da ya shigo dasu kafin ya haura sama, Hajar da bacci ya fara kwasarta ba tama san ya shigo ba, Sha ɗaya da rabi ya sakko with Pajamas mai sweat pant, ledojin dake kan Centre table ya ɗauka ya bar guda ɗaya, har ya fara hawa stairs sai kuma ya dawo baya, tsayawa yayi yana kallonta, jingine take da kujera bacci yayi awan gaba da ita, maganar Abba ce tayi hitting brain dinsa, kallonta ma da yake wani maƙaƙi ya ringa ji a zuciyarsa, ya taka a hankali ya tsaya gaban kujerar da ta jingina da ita, kujerar ya bubbuga yace "hey"......✍️