WATA ALAƘA

TARA

by @zeeeyybawa

*WATA ALAƘA.....!*

*PAID BOOK* 

*ƳAN TAGWAYE BIYAR* 


NA


STYLISH BTCH

Da

ZAYNAB BAWA


*SHAFI NA TARA*



 "Takawa ina zakaje haka da wannan suturar?" Ajiyar zuciya ya sauke bayan yakai kallonsa ga suturar dake jikinsa yace.


"Zaynab ke naƙuda ga dukkan alamu haihuwar tazo gaff." Duk da fulani tayi zaton hakan saida gabanta ya faɗi amma ta daure tace.


"Allah ya sauƙeta lafiya amma fita a wannan yanayin cikin wannan suturar bata kamace kaba, yafi ka kira ka sanar akaita asibiti, daga nan idan kayi sallah bayan ka kammala shigar da ta kamata kamar yanda ya kamace ka saika isa ka dubata yanzu ko kaje ma ba komai zaka iya yi mata ba dole asibitin nan dai shi za'a kaita." Cike da jin shawaar Fulanin sarki Mai martaba ya koma ya ɗauki wayarsa yafara kiran layin da yasan agaji zai jewa Ummin Hydar da gaggawa. 


____


  Saƙon mai martaba yana gama isa gareshi ya ajiye wayar ya fito izuwa sashin ɗaya matar tasa, hankali kwance take baccinta domin tunda cikin Ummin Hydar ya isa Haihuwa mai martaba ya tsaida fitarta dutyn dare domin zuwan rana makamanciyar wannan, itama saƙon yana isarta ta shirya a gaggauce ta fito ta baya da babu yalwar mutane wanda zai miƙata izuwa shashin Ummmin Hydar dake duk cikin fada suke. Dr Jamila itace wacce take duba Iyalan mai martaba, Babbar likitace dake aiki a Babban asibitin dake garin, sannan tana ɗaya daga cikin likitocin da suke jagorantar TURAD INTERNATIONAL HOSPITAL. Tana zuwa ta auna Ummin Hydar ta tabbatar da haihuwace a lokacin takai 5cm ta shiryata tareda taimakon hadimanta suka haɗa duk wani abu da za'a buƙata suka wuce TURAD INTERNATIONAL HOSPITAL. Ɗakin haihuwa na musamman aka shiryawa Ummin Hydar bayan Dr Jamila ta shirya midwives da kuma nurse da zasuyi assiting ɗinta ita kuma ta jagorance su.


 Har akayi Sallar asubahi shiru babu wani labari duk sunyi zugum, mai martaba kuwa izuwa wannan lokaci ya ƙagu sosai da son ganin Ummi yaji halin da take ciki. Yana zaune a gidane kawai saboda kar Fulanin sarki taga kamar bai mutumta shawararta ba amma a haƙiƙanin gaskiya gabaki ɗaya hankali da kuma nutsuwarsa yana can asibiti. Sai 7:am kafin Allah ya sauki Ummin Hydar cikin koshin lafiya ta haifo ɗiyarta kyakkyawa mai kama da ita sakk da kuma Hydar, duk da akance kamannin jariri yana iya sauyawa a kowane irin lokaci. Bayan albishir na haihuwar ya isa zuwa wajan Mai maitaba yayi farin ciki sosai sannan yayita addu'a akan Allah ya raya masa ita kamar yanda ya raya Hydar. 


  Hydar yaƙi yarda hadimarsa mai masa hidima ta shiryashi zuwa school babu irin rarrashin da bata yi masa ba amma yaƙi firr yace sai Umminsa ce zata shirya shi. Jin shiru har kusan 7:20am ba'a fito kaishi makaranta ba yasa mai martaba ya nemi ma'aikatan sashin don jin ba'asi. Kai tsaye mai tsaron lafiyarsa yashiga domin dubashi don su already sun shirya fitowarsa kawai suke jira. Ganin yadda ake fama da shi yasa shi kiran mai martaba ya shaida masa halin da ake ciki, saida mai martaba ya nemi abashi wayar ya lallasheshi kafin nan ya yarda aka shiryashi..

___


 Hutun 4hours tayi a asibiti kafin aka dawo da ita gida tunda tana da mai kula da ita akusa, alokacin mai martaba yashiga dubata, ɗaukan yarinyar yayi yamata addu'a ya ajiye ta sannan ya duba lafiyar Ummi ya tabbatar babu wata matsala kafin ya koma sashinsa ya shirya zuwa cikin fada. Kafin wannan lokaci gabaki ɗaya labarin haihuwar ya karaɗe ko'ina kaff illahirin ahlin SARKI ALIYU TURAD ɗaɗaikune wanda labarin haihuwa bai je musu ba. Masu murna sunayi masu baƙin ciki ma suna yi. Ko Kafin ƙarfe sha biyu sashin Ummi yafara amsar ƴan dubiya, duk yanda tagaji kuma takeson hutu dole tasa tafito palour ta zauna saboda akwai manyan mutane masu zuwa wanda yazama kamar dole ne sai sun ganta koda bacci takeyi a wannan lokaci za'a iya tasota. Akai-akai martaba yake kira yaji jikinta kusan kowane lokaci yakira sai yaji alamun akwai mutane a sashinta, yana zaune a cikin Fada amma gabaki ɗaya tausayinta ya cika shi domin yasan a wannan lokaci hutu kawai take buƙata. Ƙarfe sha ɗaya da rabi Kilishi da Ayna'u suka iso cikin fadar. Sashin Fulanin sarki suka wuce saida sukayi kimanin 30minute Fulani tana sake haɗa musu ƙarya akan wacce tayi kwanakin baya, basu bar sashinta ba saida tacika musu ciki famm da haushin Ummi harda shi kansa mai martaba din, ransu yakai ƙololuwa wajan ɓaci a lokacin da tace musu yau Takawa yaso ɓarar musu da mutumci akan Hadiman gida saboda ƴar gwal zata haihu, tana sanar dasu Jallabiya kawai ya ɗaura akan ƙananin kayan dake jikinsa yayi niyyar fita wanda gabaki ɗayansu sun san hakan ace sarki wanda yake wakiltar alƙarya guda sarauta da mulkinsa wanda a wannan lokaci gabaki ɗaya babu wanda yakaita ƙarfi da iko ace yafita babu kamilalliyar shiga ba. 


A palour suka samu Ummi tana zaune gabaki ɗayansu fuska babu yabo ba fallasa suka gaisa, basu tada halinsu na rikici ba domin a wannan hali da Ummi take ciki idan ba rashin tunanin mutum yakai maƙura ba bazai tare ta da wani ɓacin rai ba. Suna zaune gabaki ɗaya zaman ya gunduri Ummi domin zama waje guda dasu baya jawo mata komai sai zallan ɓacin rai, yanzu haka tasan albarkacin haihuwa da tayi ayau ya sanya bata samu wasu kausasan kalamai da zasu iya raunata farin cikinta ba. Suna zaune ahaka aka shigo da Hydar daga makaranta gabaki ɗaya dama hankalinta yana wajansa, ana ajiyeshi ya ƙaraso da gudu ya hau cinyarta cikin harshen larabci yake faɗin.


"أمي لقد عدت"

(Ummi na dawo). Faɗaɗa murmushin fuskarta tayi sannan itama cikin harshen larabcin ta maida masa da faɗin.


"الحمد لله مرحباً حبيبي"

(Alhamdulillhi Welcome Habibi). Surutun Hidaya zai fara yi mata wanda tasan baida lokacin ƙarewa tayi saurin tsayar dashi da faɗin.


"Je Tani ta canja maka kaya kaji?" Jijjiga kai yayi cikin shagwaɓa yace.


"A'a Ummi ni kece zaki canja min." Langaɓar dakai tayi tayi alamun maras lafiya sannan tace.


"Kaga banda lafiya maza je ta canja maka saika fito nan ka sameni acigaba da labarin Hidayan" Hydar yarone ƙarami amma zuciyarsa tana cike sosai da tausayin mahaifiyarsa, ƙarancin shekarunsa bai hanashi shiga wwni yanayi ba, tallafo fuskarta yayi da hannu yana faɗin.


"آسف أمي الله يشفيك "

(Sorry Ummi Allah yabaki lafiya.


"أمين حبيبي شكرا "

(Amin yarona nagode). Yanda suke gudanar da mu'amalarsu abun gwanin ban sha'awa hakan, amma sam bai burge su Kilishi da suke zaune ba sai suke ganin kamar yadda takeyi din da gayya takeyi. Tani tana tsaye tana jiran Hydar Ummi tabata Umarni ta karaso ta ɗaukeshi tayi masa wanka sannan ta shiryashi. Kilishi wacce tun ɗazu dama neman abunda zatayi magana akansa take tayi zaraff tace.


"Yanzu wannan ƙaton yaron sai an ɗaukeshi? Zaynab kuna sakalta yaron nan da yawa fa." Ƙasa Ummin Hydar tayi da kanta Ayna'u ta amshe da faɗin.


"Bayan sakalci ma ai Yaa kilishi basu koya masa tarbiya ba, yanzu ki duba yashigo aiko yake ƙaramin yaro yakamata ace yasan gaishe da manya amma ko uwar bataci arzikin gaisheta ba bare mu." Kilishi ta kalli Hydar sannan tace.


"Tayaya kike tunanin gaisuwa a wajan wannan yaron sister Ayna'u? Tunda mukazo kinji ya furta wata kalmar da Hausa?" Murmushin yaƙe Ummi tayi sannan tace.


"Ya iya fa Ya Kilishi kawai batayi ƙarfi a bakinsa bane Hydar sauko ka gaida su."


"Ba shakka amma ai gashi nan larabci yakama bakkinsa sosai kina haɗawa yaro yare uku tayaya kike tunanin zai iya hausa? Bare ainihin yaransa fillanci? Shikam bana tunanin ko kalma ɗaya zai iya tsinta aciki." Ƙasa Ummi ta sakeyi da kanta Tani kuma ta sauƙar da Hydar daga hannunta, babu yanda basuyi Hydar yayi gaisuwa ba haka firr yaƙi ƙarshe dai haka Tani ta ɗaukeshi ta shige dashi cikin ɗaki.


 Suna fitowa Hydar bai yarda ya sake zama a wajan ba yace wajan Abiensa zaije, ita kanta Ummi zata fi son hakan domin jikinta ba wani ƙarfi ne dashi ba Hydar kuma ba yarda yake wasu suna masa abubuwa ba, ga kuma su Kilishi a gafe da kalma mai kyau bata fitowa a bakinsu, bataso yaron ya tashi da sanin cewa dangin mahaifinsa basa ƙaunarsa wanda koda yaso ko yaƙi sune danginsa, sannan tana mamaki sau dayawa idan taga yanda suke yiwa Hydar kamar ba yaron ɗan uwansu ba. A ganinta koda ita zasu tsaneta bai kamata ace ya shafi Hydar ba, Hajiya kawai ke sonsa sosai ita da autarta wacce bazata wuce 23years ba, ita kuma Hajiya ba zaman nan take sosai ba, dake batada cikekkiyar lafiya kusan koda yaushe tana Egypt. Tani Ummi tasaka ta fita da Hydar takaishi wajan masu tsaronsa da sarkin mota bisa umarnin a miƙashi wajan mai martaba.


 Tunda aka kai Hydar fada mai martaba yana idar da sallah ya wuce ciki domin samun lokaci tare da ɗansa. Hira suke sha sosai kamar wani abokinsa shi kansa Hydar yau ya fahimci Abiensa yana cikin farin ciki, sannan shima ya shiga farin ciki sosai a lokacin da Abien yake shaida masa Umminsa ta haifo masa ƙanwa kyakkyawa kamarsa. Ahaka su Kilishi suka shigo suka samesu. Bayan sun gaggaisa haɗe da yi masa barka da azikin da aka samu sannann kai tsaye Kilishi taje ga abunda ya kawosu, duk da mai martaba ƙaninta ne saida ta sassauta murya kafin tafara magana kasancewar Allah ya ɗaukaka matsayinsa daya wuci raini a wajan kowaye, 


"Takawa wata shawara mukazo da ita." Hankalinsa yana kan Hydar yace.


"Ina jinku." 


"Nace mai zai hana abawa Fulanin sarki Hydar? Ko hakan zai share mata damuwar da take ciki tunda Allah yasa ita Zaynab tana da rabo a duniya." Sai a lokacin Takawa ya ɗaga ido ya kalleta sannan yace.


"Ita Fulanin tace miki tana cikin damuwa ne?" Ayna'u ce ta amshe zancen da faɗin.


"Toh ai damuwa kam bamu isa muce bata ciki ba Takawa tunda dai duk wani mahaluki yanada burin ganin jininsa ya rayu a doran ƙasa, karka manta halin da kashiga a shekarun baya pain guda kuke sharing yanzu dan Allah ya azurtaka kada kace zaka manta da irin wannan raɗaɗin" Kai mai martaba ya jijjiga sannan yace.


"Toh shikenan zamu duba tunda kunsan dama wannan bawai shawara bace wacce za'a yanketa kai tsaye ba inada buƙatar jin ta bakin Umminsa tunda tana da hakki akai." 


"Aikuwa itama bai kamata taƙi ba domin ciwon ƴa mace na ƴa mace ne (Kuji fa? amma sufa basu san da hakan ba) Kuma ita kanta a wannan hali da ake ciki taimakonta za'ayi tunda yaron naga alamun fitina ne dashi." Mai martaba baiji daɗin yanda Ayna'u ta kira Hydar da fitinanne ba ko akan fuskarsa saida ya nuna. Fuska babu wata walwala yace.


"Duk da haka yazama dole muji ta bakinta." canja zancen yayi da faɗin. 


"Kunyi waya da Hajiya?"


"Eh munyi waya itace ma ta azalzalemu muka taso muka taho bansan wanda ya shaida mata cewa tana asibiti ba, kuma ita kaɗai ba." Jijjiga kai mai martaba yayi sannan yace.


"Ni na shaida mata tana asibiti zata haihu kuma tunda ta kiraku taji kuna gida ai tasan bakuje ba kenan, kuma baku kyauta ba Yaa Kilishi kece Babba yarinyar nan amana aka bayar a hannunki batada kowa a nan yanzu zaki iya barin Ayna'u ita kaɗai a asibiti a lokacin da take gaɓar rayuwa ko mutuwa?"


"Toh yanzu Takawa wani abun tace anyi mata ba dai-dai ba?"


"Ko ɗaya batace ba amma aini ba makaho bane." Duk cikinsu babu wacce zataso saɓawa dashi don haka Kilishi tace.


"Takawa adai bar wannan zancen amma sam baka fahimta ba ita amanace a wajanmu amma Fulani ƴar uwar muce har yanzu bata gama hucewa da Kishiyar daka mata babu zato babu tsammani ba tayaya kake tunanin zamu sake da ita mu ƙara mata wani zafin akan wani?" 


"Yaa Kilishi nifa ban aikata rashin dai-dai ba don ƙarin aure ba haramun bane ina tunanin idan baku fini sanin hakan ba toh sanin mu zaizo dai-dai. Don dukanku biyun nan babu wacce ta auri mijinta a matsayin matarsa ta farko ko kuma ta karshe." Numfashi Kilishi taja ta sauƙe sannan tace.


"Yanzu ba wannan ba ya ya ake ciki?" 


"Yanda ake ciki shine izuwa yanzu kulawarta tana hannunki har zuwa lokacin da ƴan uwanta zasu iso su amshi ragamar kula da ita." Badan Kilishi taso ba ta amsa masa basu bar wajansa ba saida suka ƙara masa tuni akan komawar Hydar wajan Fulani.

_____


 Misalin ƙarfe tara na dare bayan jama'ar da suke ziyartar sashin Ummi sun ɗauke sannan Mai martaba ya nufi sashinta. Shigowar mai martaba yasa gabaki ɗaya hadimanta suka fice zuwa ɓarin da suke rayuwa domin basu sarari.


  Kallon yarinyar mai martaba yakeyi yana murmushi bayan yagama tofa mata addu'oi cikin ransa kuma yana mai addu'ar Allah ya raya masa ita kamar yanda ya raya Hydar. Saida ya gama sannan ya ɗago ya dubi Ummi wacce take kallonsu tana murmushi. Bayan sun ɗan taɓa hira sannan mai martaba ya ɗauko mata da zancen da ƴan uwansa sukazo dashi duk da shima a ransa yanaji kamar bai kyauta mata ba idan ya ɗauke mata yaro sai dai wani ɓari na zuciyarsa yana mai tausayin Fulani sosai. Hawaye ne yacika idonta taf tayi saurin kawarda kanta saboda bata son su zubo akan idonsa, mai martaba kuwa ya rigada ya ankare dasu cikin karyewar zuciya yace.



#ZEEYY BAWA

#STYLISHBCH

#ƳAN TAGWAYE

#WATA ALAƘA