SHEIKH HEESHAM

PAGE TWO

by @nanameera08

*🌹SHEIKH HEESHAM🌹*


     *MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*.



   Nanameera.


02.

Farka warta kenan ta tashi zaune tana kallon cikin bukkar da take, tashi tayi ta fito tsakar gidan nasu ta tararda mai gari zaune sai Arɗo sai kuma wani abokinsu, ƙarasowa ta yi ta tsuguna tana kallonsu dan gani take kamar zataga Baffanta a cikinsu, ganin yanda take binsu da kallo yasa Arɗo ya ce" Jiddoh tashi ki tafi wajen Adda zata baki abinci" tashi tayi jiki a sanyaye tayi waje.....


   Kusan sati É—aya da mutuwar Baffa kenan kuma sai a yanzu takejin mutuwar sabuwa mussamman yanda batada kowa da zata ce wannan natane ko zaiji tausayinta babu dangin Uwa dan bata taÉ“a ganinsu ba dangin uban kuma su ArÉ—o ne dan shi kaÉ—ai ya rage masa É—an uwa, babu wata wacce zata bata shawara ko kuwa ta rarrasheta kullum sai dai ka ganta cikin shanu tana zaune dan sunfi É—ebe mata kewa. Haule ce ta fito tana shan fura ta kalleta dan rabonta da abinci tun shekaranjiya kallonta ta yi ta ce

"Jiddoh zaki sha?"

Gyaɗa mata kai tayi ta harareta ta ce "mayya to ko zaki mutu bazaki sha ba" tana gama faɗin haka ta juya ta koma ciki. Shuru Jiddah tayi tana tunani haka zata ƙare rayuwarta har ta mutu babu wani abun arziƙi?, haka zata zauna har yunwa tayi ajalinta?, zama ya yi gefenta ta ɗago a ɗan firgice tana kallonsa. Murmushi ya sakar mata ya ce

"Gani nayi kin zauna kinyi shuru shine na ce bari nazo na tayaki zama" shuru tayi dan ita yanzu magana sai ta kama take yinta ya ce" Jiddoh zaki aureni?" da sauri ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta ya ce "idan har kin amince zanwa Baffana magana Jiddoh kuma nasan bazai ƙiba" share hawayen fuskarta tayi a hankali ta miƙe batace komai ba tabar wajen, kallon kawai ya yi dan shi harga Allah tausayin Jiddoh yake kuma zai cigaba da faɗa mata har ta amince ya aureta......


Wata irin azababbiyar yunwa ce ta tasheta daga baccin buÉ—e idanuwanta tayi wadanda ko buÉ—uwa sosai ba su yi saboda tsananin yunwa, fitowa tayi daga cikin bukkar batareda taji tsoron komai ba har ta fito daga cikin gidan nasu, garin ya yi tsit babu abinda kake iyaji sai kukan karnuka amma kwata-kwata Jiddah bataji tsoron wannan dare ba ta fara tafiya batareda tasan inda ta nufa ba.....

  Tafiya kawai take cikin garin jimeta sai kace aljana ce, jitayi kamar ta taka wani abu hakan yasa ta tsuguna tana kallon Æ™afarta, Æ™aya ce ta soketa ta zauna tana cirewa sam bata lurada wadanda suka zo suka mata Æ™awanyaba. ÆŠago kanta tayi taganta tsakiyar maza sunkai su biyar, ji tayi gabanta ya waÉ—i abinda kawai yazo ranta shine ranar mutuwarta ce tazo, kasa kwakkwaran motsi tayi har sannan su kuma kallonta suke. Wani daga cikinsu ne ya ce

"Me muke jira kawai mu aikatata mana lokacifa na ƙurewa kuma munada yawa"

Batayi zaton yanda zuciyarta ta buga ba mutuwa zatayi ba amma sai taga ta samu kanta da kallonsu dukkan ninsu Æ´an fulani ne kamar ta kuma duk basuda wani jiki, batayi aune ba taji sun fara janta har cikin wata bukka Æ´ar madaidaiciya......


   Banda tsuma babu abinda jikinta keyi amma kwata-kwata ta kasa kuka sai kallonsu take dan ta tabbatar da yau zatabi Baffa da Amminta......

  Fuskokinsu É—auke da annuri suke kallonta dan gani suke sun samu nama a banza, É—aya daga cikinsu ne ya fara cire rigarsa É—ayan ya kalleshi ya ce

"Kai bangane me kake nufi ba"

Harararsa ya yi ya ce" nufi nake ni zan fara" wani mugun kallo na ukun ya yayi masa ya ce"_ kama isa ai aradu nine nan zanfara" wanda ya tsaya daga bakin bukkar ne yazo duka ya hankaÉ—esu ya ce

"Tunda nine nake muku gadi ni ne wanda zai fara saina koma wajen zamana, cecekuce suka fara akan wanda zai zama na farko hakan yasa suka fara faÉ—a i junansu, fita sukayi daga cikin bukkar sunata faÉ—ace-faÉ—ace......

 Zama tayi da farko sai kuma wata zuciya ta raya mata "ga dama kinsamu kawai kiyi guduwarki bai kamata ace a cikin nan kika mutu ba" da wannan tunanin ta fara kalle-kalle ai kuwa tayi sa'a daga can Æ™arshen bukkar ta É—an yage, da sauri ta Æ™arasa wajen dukda batada wani kwari amma haka tayi jarumta tana zuwa ta saka kanta ciki amma inaaa bazata iya fita ta ciki ba. Fashewa tayi da kukan baÆ™in ciki ta haÉ—e hannanyenta biyu waje guda tana kuka ta ce

"Allah na roƙeka ka taimakeni nabar nan wajen da mutuncina dan darajar Annabi" ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka, har sannan kuma tana jiyo hayaniyarsu suna faɗa kamar ba dare ba.....

  Sake gwada fita tayi amma still taji ta kasa, can wata dabara tazo mata ta zauna ta fara kakkarya karan jiki da hannunta kasancewar tsohuwar bukkah ce yasa duk inda ta karya yake karyuwa saida tayi hanya data tabbatar zata isheta ta fita sannan ta saurara. Tana Æ™oÆ™orin zura kanta ciki suka shigo, da sauri ta Æ™arasa fita suka biyota da gudu......



Gudu kawai take babu ƙaƙƙautawa kuma har sannan suma binta suke har ta fara galabaita, batasan sanda ta waɗi ƙasa sumammiya ba.........


  Tsayawa Driven ya yi da tuÆ™un, ahankali ya É—ago idanunsa daga kan computern hannunsa juya idanunsa ya yi kamar zai yi magana sai kuma ya yi shuru da bakinsa kusan 2mins amma bai ce komai ba cikeda ladabi driven ya ce

"Sheikh motar ta samu matsala kuma gashi dare ya rigada ya yi saidai mu samu wani wajen mu zauna zuwa safiya"

Sai a sannan ya kalleshi da fararen idanunsa kuma manya, sunkuyar da kansa drivern ya yi domin duk rashin kunyarka baka isa ka haÉ—a idanu da Shaikh Heesham ba. A hankali ya buÉ—e bakinsa yana tasbihi ga ubangiji kusan mintuna biyar sannan ya ce cikin tsantar nutsuwar data gama ratsashi

"Allah ya kaimu"

Abinda kawai ya furta kenan bai kuma sake wata maganar ba ya lumshe idanunsa masu kyau. Sheikh Heesham Muhammad kenan babban malami a ƙasar saudia yankin larabawa, ya kasance kyakykyawa dan asalin balarabe ne mahaifinsa Alhaji Muhammd ɗan asalin ƙasar saudia ne amma bai rayu acan ba kasancewar duka danginsa mutanen Nigeria mahaifiyarsa ta haifeshine a ƙasar dalilin zuwa omrah. Sanda aka samu cikin Sheikh Heesham sai mahaifiyarsa Hajiya Amina ta tafi saudia dan rainon cikin jikimta har kuma ta haihu ƙasar hakan yasa shima ya kasance indigin na ƙasar saudia saboda haka sanda ya fara tasawa sai mahaifinsa ya kaishi karatu ƙasar, ya kasance ya rayu a ƙasar tun yana ɗan karamin yaro har girma shiɗin likitane gefe guda kuma babban malami a ƙasar. Wannan shine ƙadan daga tarihin rayuwarsa..

Ganin dare na ƙara yi yasa drivern ya ce

"Sheikh ko zamu samu wani gurin mu zauna?"

Ba zaka taɓa cewa da Sheikh Heesham ake magana ba dan ko kallonsa bai yiba bare ya saka ran zai bashi amsa saima cigaba da danna cazbahar hannusa da yayi..

Hadarine ya haɗo ganga-ganga kuma kana gani kasan ba ƙaramin ruwane zai sauka ba, ɗaya daga cikin securities ɗinsa dake ɗaya motar ne ya fito yana tafiya kamar wani zaki yazo gaban motar ya sunkuyar da kansa ya ce

"Sir wannan hadarin zai iya sakawa ayi ruwa mun samu wani waje zaka je ka zauna saboda lafiyarka"

Sai a sannan Sheikh ya kalleshi amma bai ce komai ba, buɗe masa motar ya yi yana kallonsa. A hankali kuma cikin nutsuwa ya zuro ƙafarsa waje sannan ya fito daga motar yana gyara zaman al-kyabbar jikinsa ya ce

"Ya Allahu"

Shine abinda ya furta yana sake kallon yanda garin ke yin duhu na haÉ—owar hadari sannan ya fara tafiya yana goya hannunsa a bayansa....

Wata bukkah ce suka nuna masa ya sunkuya domin kwata-kwata bukkar batayi rabinsa ba, zama ya yi kan carpet ɗin da suka shimfiɗa masa kamar kuwa jira ake ruwan ya fara sauka da ƙarfinsa...

Ba ƙaramin ruwa akayi a jimeta ba ko'ina ya yi daɗin gwanin ban sha'awa ganyayyaki da shuke-shuke duk sunyi kyau, yanayi ne wanda zai sanyaka cikin nishaɗi da annashuwa haka kuma har Allah ya wayi garinsa.....

Zaune yake inda ya yi sallar domin bai iya bacci ba yana azkar É—insa wani guard ya shigo ya sunkuya cikin girmamawa ya ce

"Barka da safiya Shaikh!"

Ba tareda ya kalleshi ba ya ce

"Barka"

Abinda kawai ya iya furtawa kenan, guard É—in ya ce

"Sir ya kamata mu tafi dan jirgin ya kusa tashi"

Batareda ya yi magana ba ya miƙe yana ambaton sunayen Allah a ransa kamar koda yaushe ya yi waje.....



   Sosai take mamakin inda taganta kwance, ahankali ta miÆ™e zaune tana kallon kusan duk mutanen rugar da suka zagayeta ana Æ´an Æ™ananun maganganu, mai garin ne ya fito yana kallon kowa ya ce

"Ina fatan kowa ya shaida abinda wannan yarinya ta aikata?, saboda haka za'ayi mata hukunci daidai da laifinta saboda kada Æ´an baya suce zasu kwaikwaya " gyaÉ—a kai duk suke alamar gamsuwa da abinda ake faÉ—a d'in ita kuwa sai idanuwa take binsu dashi dan bata gane inda zance ya dosa ba....


Wata zabgegiyar bulala aka É—auko irin wacce suke amfani da'ita idan za'ayi shaÉ—i tasha manshanu sai kyalli take, kallon bulalar kawai take dan batasan me zasuyi da itaba, mai gari ne ya kalli mutumin ya ce

"Zaka yi mata bulala 80 shine hukuncinta da kuma kora daga cikin garin nan".

Karɓar bulalar ya yi yana sake gyara zamanta a hannunsa ya ce"za'a riƙetane saboda kar ta wahalar dani?"

Girgiza kai ya yi ya ce

" Ai bata isaba dole ta tsaya ayi mata hukunci tunda shi ya zama É—an iska"

Allah sarki Jiddah banda kallo babu abinda take amma zuwa lokacin ta gane inda maganar tasu ta dosa, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata ta saka hannunta tana sharewa Allah ya sani bata aikata komai ba kuma batasan ya akayi ta zo wajen nan ba amma wa zata faÉ—awa ya yarda da ita?!, babu..........



Tafiya kawai suke acikin motar, idanunsa a lumshe suke dan wani azabbaben ciwon kai yake ji, ji yayi zuciyarsa tayi wani kyakyawan bugu ya buÉ—e idanuwansa yana kallon garin daidai nan kuma ya hango wasu cuncurundon mutane kuma fulani ya yinda har sannan yake jin bugun zuciyar na sake tsananta.

"Stop the car"

Ya faɗa ba tareda ya kalli drivern ba cak kuwa ya tsaya yana juyowa dan yasan ba ƙaramin abune zai sa Sheikh ya magantuba. Kamar wanda akama tilas haka ya kama murfin motar ya fito, nan take duk guards ɗinsa suka fito kowanne ya yi cirko-cirko dashi...


Tafiya ya fara yi torward direction ɗin da yake hango mutanen, yana kusantar wajen yanajin bugun zuciyar na ƙaruwa fiyeda na baya a haka har ya ƙaraso.....



Ganin balaraben mutum yasa duka suka dare masa hanya, a hankali ya matsa har inda yarinyar ke kwance sai zabga mata bulalar ake, duk jikinta jini ne kana gani kasan ba ƙaramin duka suka mata ba..

Ba tareda ya yi magana ba ya ƙarasa wajenta yana kkallon mutumin, ahankali kuma ya zare bulalar daga hannunsa cikin yanayinsa nason kamewa ya ce

"Ka bari babu kyau zalunci"

Sakar baki sukai dan basu ɗauka ya iya hausaba, mai garin ne ya ƙaraso gabansa wani guard ya daka masa tsawa

"leave that place"

Zabura ya yi Sheikh Heesham ya riƙoshi yana kallonsa ya ce

"Mene?"

Cikin inda-inda ya fara faÉ—in

"Daman..Dama..Daman wannan yaron ya mana laifi ne an kamashi da maza da daddare kuma hukuncinsa shine bulala 80 sannan a koreshi daga garin"

Kamar bazai magana ba sai kuma ya ce

"Ku rabu da'ita"

Girgiza kai ya yi ya ce "ai saidai ka tafi da'ita dan indai tana garin nan to sai angama mata bulalar nan kuma bulala 20 aka mata"

Shuru Sheikh Heesham ya yi sai kuma ya sakeshi ya juya dan komawa mota....


Da gudu arÉ—o ya bishi kafin ya isa motar ya cimma sa cikin magiya ya ce

"Dan Allah dan Annabi yaro ki taimaka ki tafi da Jiddoh ko zata samu rayuwa me kyau zata mutu anan aradu indai suka gama yi mata wannan bulalar to bazata tashi ba, ki taimaka yaro"

Ya ƙarashe maganar yana kuka...

A nutse ya saka tattausan hannunsa ya É—ago arÉ—o yana kallonsa sai kuma ya yi murmushi ya ce

"Shikenan zan kula da'ita"

Ajiyar zuciya arÉ—o ya sauke sannan ya ce

"Amma baza su barka ka tafi da'ita ba har sai ka aureta"

Da sauri ya kalleshi sai kuma ya girgiza kai alamar bai yarda ba.

Tsugunawa arÉ—o ya sakeyi ya ce

"taimakawa zakayi idan kuka bar garin nan sai ka saketa kaji yaro" shuru Heesham ya yi arÉ—o ya ce

"Naga kayi kalar taimako yaro ka taimakawa marainiyar nan batada kowa sai Allah sai kuma kai yanzu"

Bazai iya cewa A'a ba dukda yasan bazai zauna da ita matsayin mata ba amma zai taimaketa yayi jahadi.......

Murmushi ya yi yana kallon ArÉ—o ganin yanda yake kuka da idanunsa ya ce

"Shikenan na amince".......

Kama hannunsa arÉ—o ya yi jikinsa har rawa yake suka koma wajen....



Yana kallon mai gari ya ce

"Zai tafi da'ita"

"Amma yasan saidai ya aureta?"

GyaÉ—a masa kai ya yi ya ce" shikenan"

Anan aka ɗaura auren Sheikh Heesham Muhd da Hauwa'u Ahmad sadakinma zoben hannunsa suka karɓa.......


Kallonsa Ardo ya yi ya ce

"Na yarda dakai yaro nasan zaka kula da rayuwar Hauwa'u kada ka barta ta yi kuka kaji"

Riƙe hannunsa Sheikh ya yi ya ce

"Har ƙarshen rayuwa"

Kwance take dan har sannan bata farfaɗoba ya saka tattausan hannunsa ya ɗauketa yana tafiya har suka isa cikin motar, tsayawa arɗo ya yi yana musu addu'a har suka ɓacewa ganinsa.........



 Share it plx.

*Paid book #500.*

*SHEIYK HEESHAM*