BISHIYAR TSIYA....

BABI NA GOMA

by @ummasghar

*BISHIYAR TSIYA*


*DAGA ALKALAMIN YAN TAGWAYE*


*Umm Asghar*

*Sadiya Nasir Dan*


Arewa book

@ummasghar


Page 10


Fadila tunda Sulaiman ya kirata yace gashi a hanya ta miƙe daga zaunen da take tana kallon series tayi ɗakinta, shiri tayi na riga da wando daya kama jikinta sosai ya fito da sura ta baiwar da Allah yayi mata, ƙarewa kanta kallo tayi sosai a mirror ta tabbatar komai yayi kafin ta feshe jikinta da designer perfumes ta fito, umurni tayi wa mai aiki tare da shaida mata abinda take so ta kai guest sitting room ɗin Daddy. Pictures da videos ta cigaba dayi har ta fito harbar gidan.

   Gate man yana jin horn ya fito daga ɗaki da sauri, ganin motar Sulaiman yasa babu ɓata lokaci ya wangale gate ɗin. A nutse ya shigo gidan yayi parking motar Idon shi akanta yana mai ƙare mata kallo da ƙara godiya wa Allah daya kawo Fadila cikin rayuwarshi a lokacin da yake buƙatar ɗauki, yana da tabbas idan ya Aure Fadila zai samu nutsuwa. Ɗaukewar numfashi ya samu na wasu sakanni daya dawo dashi daga duniyar tunanin daya faɗa, sakamakon jin abinda bai yi zato ba ko tsammani, kyakyyawar rungumar da tayi mishi wanda yasa dukkan wata jijiya dake jikinshi amsawa, ƙara shigewa jikinshi tayi sosai hannunta cikin gashin kanshi tana wasa dashi, jin yadda dukiyar fulaninta suka samu mazauni a ƙirjinshi ga yatsunta dake yawo cikin gashin kanshi yaji hankalinshi na neman gushewa, ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi ya ɗan tureta gefe, murmushi tayi mishi cike da kissa tace "My love nayi missing ɗinka so much, shi yasa na kasa ɓoye maitata." Tayi maganar a shagwaɓance tare da kashe mishi idanu, kasa cewa komai yayi sai murmushi daya mayar mata. Hannunshi ta riƙe cikin nata suka nufi guest sitting room ɗin Daddyn ta.


****

Batula ƙarasa wunin ranar tayi zuciyarta sam babu daɗi, tsananin kishi ke damunta a ƙasan zuciya tare da son sanin wacece wannan yarinya da tayi nasarar ture soyayarta a zuciyar mijinta, kenan idan Suleiman yayi Aure abinda zata gani na wulaƙanci sai yafi wannan? "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un", ta furta a hankali saboda tsananin zafin da zuciyarta keyi mata, ganin lokacin tashin Fahad yayi yasa ta miƙe jiki duk babu kuzari tasa mayafi ta rufe gidan ta nufi Islamiyar. Tun kafin ta ƙarasa ƙofar makarantar aka tashesu, shi yasa bata saki mai Napep ɗin daya ɗaukota ba ta shiga ta ɗauko Fahad suka tafi.


*****

Suleiman ƙaɗan yaci abinda Fadila ta tanadar mishi saboda yaci abinci sosai a wurin Hajiya cikin shi ya cika, hira sosai suka yi, mafi yawan zancen nasu tsarin yadda auren su zai kasance ne. Da ƙyar ya iya yakice Fadila a jikinshi ganin shida saura, ya sanar da ita zai je ya ɗauki Fahad time ɗin tashi a islamiyya yayi. Ba don ranta yaso ba ta amince da tafiyarshi, haka suka sauko hannunsu maƙale dana juna zuwa parking space, anan ɗin ma sai da yayi da gaske kafin Fadila ta ƙyale shi ya tafi, a motar tunaninta ya cigaba dayi, ya rasa ya aka yi Fadila tayi tasiri a rayuwarshi sosai, ji yake yi kamar ya matso da nesa kusa, da isar shi makarantar parking yayi ya cigaba da danna wayarshi, ganin duk yara sun watse sai tsirarru babu Fahad hankalinshi ya soma tashi, fitowa yayi ya shige cikin makarantar, sam hankalinshi bai kawo masa Batulu zata zo ɗaukar Fahad ba, kai tsaye office ɗin shugaban makarantar ya nufa, nan suke sanar dashi Batulu tazo ta daukesahi. Sosai ranshi ya ɓaci na abinda Batulu tayi, amma sai ya wayance wajen ce musu daga tafiya ya dawo bai ƙarasa gida ba, haka yayi musu sallama ya fito zuciyarshi na zafi. Zaman su da Batulu ya kai yanzu baya da mutuncin da zata kirashi a waya tace mishi za tazo ɗaukar Fahad? Tun a cikin makarantar ya soma kiran number Batulu, amma sai tayi ringing ta yanke ba'a ɗauka, hakan ba ƙaramin ƙara tunzura shu yayi ba, ya shiga mota sai huci yake ya kama hanyar gida. 

  Batulu sam ba taji ringin na wayarta ba, tun dawowarsu da Fahad ba tabi ta kan wayar ba, ta kunna ma Fahad cartoon ta shiga kitchen ƙoƙarin haɗa musu dinner. "Batula! Batula!" "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un," ta furta a hankali sakamakon yankewar da zuciyarta tayi jin irin kiran da Suleiman yake yi mata, ƙoƙarin amsa kiran take yi ya faɗo kitchen ɗin a fusace, kafin ta kai ga ɗagowa yasa ƙafa ya shureta. "Wayyo Allah na," ta ambata da ƙarfi jin tsananin azabar daya ziyarci ƙwaƙwalwarta, da sauri ta durƙushe a wajen hawaye masu zafi na sauka akan fuskarta. "Don Uwar ubanki waye ya baki izinin zuwa ɗaukar Fahad? Sau nawa nake yi miki magana akan fita babu izini? Wato kin mayar dani wawa ko? Saboda kina samun ɗaurin ƙarƙashi daga wajen Hajiya idan kin yi laifi tana bani hakuri? To yau me rabani dake a gidan nan, sai kin fada mun dalilin da yasa kika raina ni." Yayi maganar cikin ƙaraji da yasa jikinta soma rawa babu shiri, "Don girman Allah kayi hakuri Abban Fahad." "Hakuri nace ki bani ko amsar tambayar da nayi miki?" Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin sake kai mata naushi. Ganin haka yasa Batulu ƙoƙarin mikewa domin tsira daga bugun da Suleiman yake ƙoƙarin yi mata, amma ina kafin ta miƙe har ya cafko gashin kanta ya damƙe da ƙarfi tamkar zai fisge, "ba magana nake yi miki ba?" Murya a wahalce tace "Abban Fahad kayi hakuri, tunani na cewa da kayi na kai shi makarantar uzurin ba zai bari kaje ka ɗauke shi na, wallahi Allah shi yasa na fita naje na ɗauko shi, amma ka...." kafin ta ƙarasa yasa hannu ya buge bakinta, wani irin ƙara ta saki take jini ya soma zuba. 


"Da nace ki ɗauke shi ki kai shi makarantar me yasa daza kije ɗaukar shi baki faɗa mun ba? Da anyi magana kin iya marairaice fuska kice ayi haƙuri, ni dake ne a gidan, matuƙar baza ki dawo hayyacinki ba Ubanki za kici a hannuna wallahi." Yaja tsaki tare da wurgata gefe. Fahad dake rakuɓe a jikin ƙofa sai rawa jikin shi yake yi na tsoron ganin yadda Abban nashi ke cin zarafin Amminshi kamar ya samu jaka, da gudun gaske yayi kanta tare da cewa "Ammie, Ammie," da ƙarfi ya rungumeta ya fashe da kuka mai sauti, hakan yasa Sulaiman yin ƙwafa ya fice daga kitchen ɗin ranshi a matuƙar ɓace.


****

Saudat da tsananin murna ta shigo gida, Hajiya Rabi na zaune sai ji tayi an rungumeta ta baya, "Wayyo Mummy daɗi zai kasheni, ashe da gaske Abdul-Hameed zai soni? Wayyo Mummy kar kiga yadda ya sake dani abu kamar shirin film, ashe dama yana hira yana sakewa da mutane? Allah Mummy ko mun haɗu a gidan Hajiya baya ko murmushi bare nayi tunanin zai amsani cikin daɗin rai." Murmushi irin nasu na manya Hajiya Rabi tayi, "Me yasa kullum idan kina damuwa nake ce miki ki kwantar da hankalin ki, in har kinga baki auri Abdul-Hameed ba to bana numfashi ne, na riga na jima da sanin cewar za kuyi Aure Saudat." Shiru Saudat tayi tana kare wa mahaifiyarta kallo. "Kina mamaki ko? Me yasa ki kaga bana damuwa da yawan nuna kulawarki gareshi? Sai don nasan wata rana Abdul-Hameed a tafin hannunki zai kasance sai yadda kika yi dashi." Ajiyar zuciya Saudat ta sauƙe ta zauna ta fuskaci mahaifiyarta sosai tace "Mummy nasan yanzu idan na tambayeki ya aka yi kika san Abdul-Hameed zai soni har muyi aure cewa za kiyi bincike ki kasa malaminki yayi miki, don Allah Mummy ki daina yarda da maganganun malamai, Allah ƙarya suke yi."

"Kaji ja'ira? Ke wai a tunaninki haka kawai Abdul-Hameed ɗin yazo yace zai aureki? Kin san yawan kuɗaɗen dana kashe akan wannan hidimar?" "Please Mummy ni dai na roƙeki, bana so, gara ki koma ga Allah akan yadda kika kasance mai amincewa da maganar bokaye da malaman tsubbu." Ta ƙarasa maganar fuskarta da alamar damuwa. "Humm yaro kenan, tashi kije kiyi sallah ki samu ki dafa mana ko taliya ce, tunda yau miji yazo babu zancen tuwo." Dan rufe fuska tayi ta miƙe alamar kunya, "Ja'ira". Hajiya Rabi ta ambata tana murmushin farin cikin ganin burin ƴarta ya cika.


****

Abdul-Hameed yana rabuwa da Saudat shagon aminin shi ya nufa wato Kashim da suke tare tun yarinta. Duk da ɗaukakar da Allah yayi mishi bai sa ya mance Kashim ba, duk zuwan da zai yi garin Jigawa baya tafiya ba tare daya ziyarce shi ba, shi yasa alaƙarsu take nan kullum zumuncinsu na ƙaruwa, wannan kenan.

 Kashim na hango Abdul ya buɗe baki cike da mamaki na shigowar ba zata da yayi mishi. "Me idona yake gane mun? Ko dai gizo ne?" Ya ƙarasa maganar da alamar zolaya. Murmushi Abdul yayi ya ƙarasa shigowa cikin shagon ya zauna, "Jiya na shigo, naso na kiraka na sha'afa ne, toya garin ina Madam da yaran?"

"Lafiya ƙalau suke, muna nan muna basu haƙuri rayuwar sai hamdala." "Allah ya kawo mana ɗauki amma al'amuran ƙasar nan sai dai godiya." "Ameen ya rabbi, da ganin yanayinka akwai magana a bakinka, ko dai?" Dariya Abdul yayi, "Shi yasa ma nazo, ka samu ka had'ani da mutanenka wajen hadmɗa lefen Amarya."

"Kaii haba? Mutumina zancen gaskiya fa?" 

"Allah Kashim Aure zan yi nanda wata daya zuwa biyu, Hajiya hankalinta yana kaina akan maganar aure, a waya tayi mun, idan nazo nan ɗin ma maganar kenan, shi yasa zan yi nima ina da buƙatar Iyalin."

 "Masha Allah, gaskiya naji daɗin wannan zancen naka, ni kaina na damu naga ka ajiye iyali Abdul, kana da rufin asiri bakin gwargwado, kana rayuwa a bariki dole hankalin Hajiya ya karkata kawai kayi aure, a ina matar take? Abuja ko Jigawa?" "Waneni da auren yaran Abuja? Ƴar uwata zan Aura, da Hajiya da Mamanta aminai ne kamar ni da kai." "Aaa abu yayi kyau,

kace mu shirya akwai gwangwajewa?"

"Kwarai kuwa Gwabro zai angwance." "Sai dai Tuzuru". Kashim ya ambata gami da fashewa da dariya, shima Abdulhameed dariyar yayi don ya saba jin irin wannan zolayar a bakin aminin nashi. 


Abdul anan yayi sallar magrib da isha'i suna hira, sai kusan ƙarfe takwas da rabi kafin yayi wa Kashim sallama ya kama hanyar gida


*****

Suleiman ɗakinshi ya nufa ya cire kaya saboda jinin bakin Batulu daya taɓa, in banda huci da tsaki babu abinda yake yi, toilet ya shiga yayi wankan tsarki da alwala ya fito. Matuƙar zai je hira wajen Fadila to tabbas sai ya dawo da janaba, shi yasa ba zai taɓa samun kwanciyar hankali ba in har ba aurenta yayi ba, a yadda yake jin tsanar Batulu baya tunanin zai iya sake hada shimfiɗa da ita. Masallaci ya nufa yana Isa ana idarwa, ya gabatar da nashi ya dawo gida.




*ƳAN TAGWAYE BIYAR*


*GONAR SHARRI*

Billy S Fari & Hajja ce


*IDANIYAR RUWA*

(Mai wuyar toshewa)

Ayusher Muhd & Jidda Aliyu 


*WATA ALAƘA*

Zee Bawa & Stylish bch


*BISHIYAR TSIYA*

(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)

Umm Ashgar & Sadiya Dan.


*TSARIN ALLAH*

(Ba mai iya canzawa)

Asmy b Aliyu & Nana Diso


*ZAI IYA BIYAN*

GUDA 1 akan 500

GUDA 2 akan 800

GUDA 3 akan 1200

GUDA 4 akan 1600

GUDA 5 akan 2000


*BANK ACCOUNT*

8098456130

Opay digital services

Shaidar biya ***


*KATIN MTN*

***

Shaidar biya ta lambar.


_*ƳAN TAGWAYE BIYAR*_


#SADIYANASIRDAN

#UMMASGHAR

#ƳANTAGWAYEBIYAR