RAMIN KARYA

Chapter 13

by @kyautadagaallah10

๐Ÿ‚๐Ÿ‚_*RAMIN K'ARYA*_ ๐Ÿ‚๐Ÿ‚




 NA 



IKILIMA ADAM 


 *( Kyauta daga Allah)*


Marubuciyar da ta nishandantar daku a littafanta kamar haka:


Kai ka jawa kanka



Kanwata



Rai daya ( Jan zaki)



Rudani



Makauniyar shari'a


And now


Ramin karya yan karin magana suka ce kurarre ne , mu je zuwa.



Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai .




 SHAFI NA SHA UKU



Dafe da kirjinta ta furta " Maryama" kana tayi shiru tana mai fesar da numfashi.


Kallonta Jidda take ita da Jakadiya.


" Wannan ba Margayya Maryam bace , Amaryan Adamsy ce , mai suna Hauwa'u" cewar Jakadiya cikin sanyin murya.


Ajiyar zuciya Jidda ta sauke tana mai juya kalaman Jakadiya , kana ta dan dago kai tana kallon Maman Lailat haka nan ta ji zuciyarta ta harba , gwuiwowinta sun sare .


" Ina kwana Mama" ta tsinci kanta da fadi.


Maman Lailat da bata gama kare mata kallo ba , bata ma san tanayi ba ,sake maimaita gaisuwar ne ya dawo da ita hayyacinta.


" Am sorry diyata , kina kama da diyata , kuma sannunmu dana rashin iyayenki da kuka yi , hakika ba dan na san komi ba , sai nace ke ce Maryam , ina miki fatan alkhairi ku zauna lafiya ke da yar uwarki Lailat , ga yayan ki nan ". Ta fada tana mai nuna mata Hassana da hussaina.


Jidda sanya idanu tayi akan yaran tana mai kallon farin idanun Hassana yanda suka juye kasa , " ya salam " ta furta kasan zuciyarta. Kallon Hussain take , dake zaune yana kallon tv kai kace me magana.


" Ita Hassana bata magana ,sannan bata gani , shi Hussaini ji ne baya yi kadai amma idanunsa rass suke " cewar Maman Lailat tana mata magana cikin kulawa.


Jidda nan da nan idanunta suka cika da hawaye , tabbas duk duniya tana tausayawa makaho ko makauniya , bare kuma ace kurma , kuma yara dasu. Kwallan da Maman Lailat ta gani idanun Jidda ya sanyata jin nutsuwa a cikin ranta a game da ita .


" Haka Allah ya tsara, kuma in sha Allah ze bada mafita , tunda ba haka aka haife su ba". Cewar Maman Lailat.


Jidda ba karamin shock ta shiga ba , jin wannan kalaman.

Jakadiya cike da kulawa take kamawa Jidda yaran domin basu abinci.

Maman Lailat na ganin haka, cike da farin ciki suka yi sallama.


Ko da ta fito daga dakin yaran , daga hannunta sama tayi tana ma Allah godiya dan tana jin Jidda kamar wata tsoka na jikinta. Cikin kwarin gwiwa ta kama hanyar fita daga Masarautar bayan tayi wa Hajiya babba sallama. Karo tayi da Lailat dake saukowa daga matakalan step.


Lailat na karasowa cike da mamaki ta furta.


" Mama yaushe kika zo Gidan nan , naga kamar ma tafiya zaki yi"?.


" Eh tafiya zanyi mana , tun jiya na zo" ta bata amsa a gatsai...


" Subuhannallah Mama daman kina Gidan nan, shine baki leko ni ba " . 


" Kece baki lekoni ba , dan ina uwar banza sai na biki har dakinki".


" Bansan kin zo ba ".


" Taya zaki sani tunda baki san halin da yaranki suke ciki".


" Ya salam, daman dakin yaran kika kwana , ai kin san hidimar biki shiyasa".


" Nima gajiyar biki ya sa ban sanar miki na zo ba " ta bata amsa tana mai kokarin barin falon.


Lailat dake sanye cikin doguwar riga fara , cikin damuwa take juya kalaman mama. Ganin zata fice ne ya sanya cikin hanzari ta bita tare da shan gabanta ta hau bata hakuri tana kukan karya. Nan da nan Mama ta ji tausayin yarta.


" Allah ya shirya min ke " Lailat ta fada tana mai sha fa kanta.


" Ameen , ai na shiryu" Cewar Lailat.


Kokarin shiga motar ta , take , ta hango Prince Adamsy tahowa yana zufa, alamun yasha traini.


" Mama har zaki tafi " ya furta tun daga nesa , yana mai kallonta .


Murmushi ta sakar masa , " Eh zan tafi, amma na bar Amaryarka a dakin tana cen tare dasu " .


Sosa kai yayi cikin jin kunyar kalamanta .


" Da ai na so ki mana kwana biyu " .


" Aa gwamma na je gida , nima ina dan kintsa gidana " ta fada cikin kulawa.


" Allah ya tsare ya kai ki Gida lafiya, in sha Allah zan shigo anjima " ya fada yana mai kauda kallonsa akan cikin Lailat da ya dan turo. Suna yin sallama ya fice daga ciki ya bar Mama da Lailat.


Ita kuwa Lailat hankalinta yayi mummunar tashi, jin wai Jidda tana dakin yaran, kuma ta san Adamsy cen ya nufa .


" Sai anjima Mama" ta fada tana kallon mamarta na tayar da mota.


A ujajajan take bin sahunsa , kallonsa take ya bi sashin dakin yara cikin sauri_sauri , bayi na ta zuba masa gaisuwa , shi kam hannu yake daga musu. Kai tsaye dakin ya cusa kai.


Ita kuwa Lailat tana ganin ya shiga , nan da nan idanunta suka kawo hawaye , kokarin bin sa take ta san sarai ze iya ci mata mutunci gaban Jidda hakan ya sanyata dawowa falon Masarautar tana mai jiran fitowarsa.


Jidda da sam bata ga shigowarsa ba ,Hassan da Hussain suna rungume a jikinta , kuka take a hankali , dan yanda ta ji mutuwar Umma haka ta ji mugun tausayin yaran nan .


Tsaye yake na wasu mintuna, nade da hannayensa ,kana yayi gyaran murya tare da doka sallama.


" Waalaikum salam" ta amsa tana mak fitar da yaran daga jikinta .


Kallon kallo suke wa juna ita da shi , kwayar idanunta yake kallo yanda suka yi ja har fuskarta ya kumbura.


" Ke bakya gajiya da kuka ne ?". ya fada kamar bashi ne yayi maganar ba , yana mai isa kusa da yaran, ganin kamar duk a koshe suke , suna baza kamshi ,sun sha wanka ya sashi fadi a kasar zuciyarsa. " Wannan ta san yanda ake kula da yara , har ta fi Sumayya iyawa". Ya fada yana mai yiwa yaron adua ya sha musu jiki dashi.


" Zan kira Sumayya , dan ita ke kwana dasu , sai ki tafi dakin ki" ya fada.


" Anan zan kwana " ta bashi amsa, sam daman bata son kwanan kadaici.


" Okay sai ku kwana da Sumayya , na tafi sai anjima ko kuma da safe in ban shigo " ya fada yana mai fita daga dakin.


Yana mai kokarin yin sashinsa ya ci karo da Lailat.


" Yaya Adamsy , cikina ke min ciwo tun safe ". ta fada tana marairaice fuska.


" Ki sha flagyl " ya bata amsa.


" Babu kyau shan flagyl,ga mai ciki ".


" A wace aya kenan ?". ya bata amsa yana kokarin bude kofar dakinsa.


" Likitoci ne suka fadi hakan , please ka kaini asibiti a duba danka".


" Ba sai na je ba , kema ai danki ne "?. ya bata amsa yana mai kokarin shigewa dakinsa.


Karo na farko data rike hannunsa gam , cikin karfin hali.taushin hannunsa ba karamin rikita mata tunani yayi ba. Kallon yanda ta kama masa hannu yake.


Cikin bacin rai ya wabce hannunsa daga nata.

" Baki da hankali ne "?.


" Haba masoyina , wallahi ina sha'awarka , kuma na soma gajiya tunda na samu ciki baka Kara kusantata ba , ciki ya shiga wata na shida yanzu" ta fada cikin rashin tsoro.


Kallonta yake da idanunsa masu eye lashe, kana ya lumshe idanu ya bude su ahankali.


" Da cen wa yake kusantar ki" ?.


" Wannan maganar da kake haramun ne a musulunci , kuma zan nemi a min izini ga Sarki dan na fada masa baka bani hakkina" ta fada dan ta san baya son bacin ran Mahaifinsa.


" Babu laifi dan kinyi hakan" ya fada cikin yakini tare da rufe kofar ya barta nan tsaye.


Ganin ya shige ya sanyata cizar yatsa , cikin hanzari tayi sashin dakin yaranta domin zuwa ganin fuskar amarya.


Babu sallama ta fada dakin . Iske Jidda tayi kusa da ita Ummi ce zaune suna cin abincin da aka kawo musu.


" Ya salam " suka furta a tare, ganin Lailat kamar an jefota daga sama 


" Wace ce Jidda a cikin ku" cewar Lailat fuska babu annuri.


Ummi da Jidda kallon junansu suke , suna kallon ikon Allah. Basu bata amsa. Hakan yasa ta daka musu tsawar daya firgitasu har suka zabure, cokula na faduwa daga hannusu...


" Ni ce nan Jidda " ta fada amsa cikin tafasar zuciya.


Wani irin mahaukacin dariya Lailat tayi tana tafa hannu 


"Watau wuyarki ya iya yanka ,ni kike baiwa amsa babu laushi.


" Eh !!an baki amsar" ..cewar Ummi cikin tsiwa.


" In kika ce zaki takura muna , sai muyi miki dukan kawo wuka " cewar Jidda cikin fada.


" Zan ga yaya Adamsy in fada masa jakunan da ya kawo Gidan nan , ba masu hankali bane ".


Ji kake tass , Jidda ta dauke ta da mari , zata kara mata Ummi ta rike mata hannu cike da magiya. " Don Allah ki kyaleta kada ace daga zuwan mu har mun mata duka" Cewar Ummi cikin ban hakuri.


Huci Jidda take kamar zakanya , saisaita nutsuwarta tayi tare da samun wuri ta zauna. Lailat rike da kuncinta ta bar dakin.


Kai tsaye wayar Nura ta fara kira , tana ta safa da marwa ganin be daga ba , cen sai aka daga . Muryan matar Nura ce ta ji tana fadin" Hello".


" Ina me wayar" ?. ta fada murya na rawa.


Nura dake kwance gefen amaryansa , amsar wayar yayi , yana mai kokarin fita daga dakin.


" Ina zaka je ?". cewar amaryarsa, " kuma dawa kake waya" . Ta kara masa wata tambayar, tana masa kallon tsanake .


Hannun ya daga mata me nuni ina zuwa ,ba tare da ya amsa tambayarta ya bar dakin.


Ita kuwa , matar Nura , kishi ne ya fara kamata , duk a tunaninta budurwa ce ke kiransa.


Bangaren Nura bayan ya fita.


" Garin ya ta mareki ". ya fada cikin fusata.


Daga cen bangaren cikin muryan kuka ta fara bashi labari daki daki.

Fesar da numfashi yayi yana mai nazartan wannan Jiddan .


" Amma anyi yar iskar yarinya , ta daga hannu akan ki , kina uwar Gidan ta ".


 " Don Allah ka daukar min fansa, dan wallahi ba zan kyaleta ba".


" Tana ina yanzu hakan ".?.


" Dakin yara mana ".


" Bara na je Gidan tsafi , bani mintuna talatin, sai na dagula mata lissafi " ya fada yana mai katse wayar.


Koda ya koma dakin iske amaryarsa yayi tana ta safa da marwa , ganinsa ya sanya ta tararshi.


" Duka yaushe muka yi aure , har yan mata ke kiranka?". ta fada cikin zafin kishi.


Murmushi ya sakar masa yana lakacar hancinta cikin so da kauna ya ce .


" Matar Yaya Adamsy ce , ta kirani wani aikin zan mata, kin ga ai be kamata nayi magana a gabanki ba".


" Yo meye a ciki in har kayi a gabana, tunda antyn mu ce ".


" Okay nan gaba , a gabanki za'ai, zan je na dawo, bani awa daya" ya fada yana mai kiss din goshinta kana ya bar dakin.


__________________



Nura zaune gaban dodon tsafi. " Amaryar adamsy gaskiya ba zamu iya taba lafiyarta har sai tana cikin jinin al'ada" cewar dodon tsafi.


Cikin damuwa Nura ya ce " taya zan san tana al'ada har na fada muku".


" Cikin kannenka Rayyah ko Surayya kasa wata ta shige jikinta sosai, zasu sani, dan da zarar mun samu tana cikin jinin zamu sakar mata yoyon fitsari " cewar dodon tsafi.. suna mai bushewa da dariya shida Nura.


" Ai wallahi yanda Prince ke da mugun tsafta na rantse da Allah , fitar da ita ze yi daga Masarautar, in ta auna arziki ya barta dakuna compound din Gidan , in har beta auna ba , wallahi ticket ze yanka mata " cewar Nura yana mai bushewa da dariyar mugunta.


_______________


Bayan kwana biyu



Alhaji Faruk ne zaune shida abby suna magana akan yanda za'a tunkari Masarautar Lafiya da zance basu matar da suka aura.


Zaune cikin ahlinsa , Mahaifiyarsa na zaune hade da ya'yanta.


" Nuna min hoton yarinyar nan " ta fada tana mai jin zafin lamarin.


Nuna mata hoton yayi wanda ya dauka ba tare da Jidda ta san yayi ba.


" Wow Allah mai halitta , lallai Umaru dole ka rikice akanta , amma fa wannan ba bahaushiya bace " ta fada cikin jinjina zallar kyawun da Allah ya baiwa Jidda.


Kalamanta ne ya sanya abby dake kokarin shan ruwan lipton fadin.


" Mu Gani " sai ya kurbi ruwan Lipton , kana ya amshi wayar daga hannun Mamar Faruk.


Yana sanya idanunsa akan hoton, mikewa yayi tsaye yana mai kwarewa.


Da mamaki suke binsa da kallo dukansu .


"Lafiya daga kallon hoto sai ka tada hankali" cewar ummu Faruk.


" Kai ni inuwa " ya fada zufa na keto masa , jikinsa ya dau rawa kamar mazari.


Abby lafiya kuwa ?".

 

Ganin yanda yake salati ne ya sanya su fadin " Abby lafiya kuwa ? ". Be samu damar basu amsa ba , illah kokarin faduwa da ya fari, wanda ya sanya , cikin hanzari suka tare shi.


______________________


Khadija Kanwar Nura , diyar Sarkin Lafiya , zaune a falonsu ita da mijinta Abdul kadri , wayarta ce ya fara vibration. Da idanu yake kallonta , yana kallon wayar. " Ki daga mana " ya fada yana kallon fuskarta.  

Daga wayar tayi ganin ansa A yasa ta kallon abdul , ganin ita yake kallon ya sanyata fadin.


" Haba Surayya na ce miki zan zo , ki daina damuna da kira " ta fada kirjinta na dukan uku_uku.


Jin ta ambaci Kadija ya sanya shi , tashi domin shiga daki. Ita kuwa tana ganin ya shige ciki. Tayi murya kasa_ kasa.


" Haba ya zaka min haka ? na ce ka daina kirana ni zan kiraka, gabanshi ka kirani fa , gaskiya bana son haka " ta fada cikin kasa da murya.


Dagacen bangaren ya ce " Haba Dijat , ki min uzuri wallahi ke din ce , kina da dadi na musamnan" ya fada yana lasar baki kamar wani maye.


" Sai anjima ga shi nan ya fito" ta katse wayar, tana mai kashe wayar gabakidaya , sai ajiyar zuciya take saukewa akai akai . ganin uwargidanta ta iso falon ne ya sanyata fadada murmushinta , tana mai fadin " zan je na shirya, domin duba ameren mu" ta fada tana mai barin falon.


" Sai kin fito" ta bata amsa tana mai zama saman kujerar.


__________________



Bayan Isha'i , prince na kokarin shiga cikin Gida ya ci karo da Kadija ta shigo cikin hanzarinta , a ujajajan ta gaishe shi , tana gudu_gudu , sauri sauri ta shige cikin Gidan.


Kokarin bin sahunta yake , ya ji horn din mota.

Kokan ya karasa shiga ya juya , ganin Abdul kadri Mijin Kadija ne ya sanya shi tsayuwa domin gaisawa da masa godiya akan gajiyar biki.


Abdul kadri na karasowa suka yi musabaha , kana ya masa godiya da kokarin su .


" Daman na zo daukan Kadija ne , tunda ta wuni yanzu Kuma , sai mu je Gida" ya fada yana murmushi.


" Ta wuni" ?.


" Eh mana " cewar Abdul kadri.


" Okay , tana ciki " prince ya bashi amsa yana mai shiga gaba. Abdul kadri na bayansa.


_______________



Jidda zaune dakinta aka sanar mata da sarki na son ganinsu ita da Prince Adamsy.


Bayan sun zauna gaban Sarki , Jidda cikin faduwar gaba take tunanin ko me ze fada.


" Daman na tara ku ne ,anan na samu labari tunda aka kawo amarya dakin yara take kwana , Haba adamu" Sarki ya fada cikin bacin rai.


Duk inda tashin hankali yake ya gama bayyana a fuskar Jidda.


" Don haka ina me tabbatar maka kowacce daga cikin su , zata ringa kwana dakinka ranar kwananta.".


Zumbur prince ya mike tsaye. Murya na rawa ya ce......



Taku har kullum kyauta daga Allah