KI NA ZUCIYATA

ONE

by @nanameera08

*KI NA ZUCIYATA 01*


Mikiya writer's association.


*Bismillahi-Rahmani Raheem, Ina godiya ga Ubangiji maɗaukakin sarki wanda ya sake bani damar zuwar muku da wani sabon littafin nawa mai taken KI NA ZUCIYATA idan har kinsan kina wani aikine tofah sister ki bari ki ƙarasa dan gudun Book ɗin ya ɗauke miki hankali 😍Ba kullum zan dinga posting ba coz ina typing book biyu ne nd paid saboda haka idan na samu dama zaku jini idan kuma kunji shuru tofah saidai wata ranar😂 Amma zan dage da typing in Sha Allah ku kasance tare da mu cikin tafiyar SQUAD na tabbata bazakuyi nadama ba🔥 Queen of the Squad ce 👸✍️*


*Nanameera*





Da sauri ta juyo jin muryar da ko amafarki bazata taɓa mantawa ba cikin babban stadium ɗin wanda yake ɗaukeda manyan mutane daga nahiya-nahiya na faɗin duniya, idanunsa a lumshe cikin cool voice ɗinsa mai ɗauke da nutsuwa ya fara waƙar tasa kamar haka



"Kina zuciyata ban manta da keba masoyiya"....


"Kina zuciyata ban manta dake ba sahiba"...



"_Ehee cikin Zuciyata ban manta dake ba_"



"_Cikin rayuwata banga kamar yake ba_"



"_Har ina manta kai na idan ban ganki kussa dani ba_"



"_Kina zuciyata sonki yay minni gata_"



"_Ina da burin dake zan ƙare rayuwata_"



"_Banga kowa ba sai ke domin kina zuciyata aminiya_".........





Hawayene tab idanunta tana kallon wanda yake rera waƙar cikeda kwarewa lumshe idanunta ta yi wasu zafafan hawaye suka sakko mata kan kuncinta ita kaɗai tasan abunda take ji cikin zuciyarta, tana tsaye daga gefe har ya kai ƙarshen waƙar yana ajiye mic ɗin, tashi mutane sukai ana masa tafi cikeda nuna soyayya domin ba ƙaramin so sukewa mawaƙin ba. Cikin tafiyarsa ta cikakkun maza ya sakko daga kan stage ɗin ya fara tafiya toward direction ɗin fita daga stadium ɗin da sauri securities suka rufa masa baya, a hankali ta goge idanunta tana sauke ajiyar zuciya




"Nazeefa zo mu tafi"



Kallon me mata maganar tayi sai kuma ta ce"okay" sannan suka fito daga cikin wajen. Tsaye suka tadda shi suna magana da wani bature kallonsa kawai ta yi suka ƙarasa gaban motarta, da sauri ya ƙaraso wajenta lokacin har ta buɗe murfin mota, kallon-kallo kawai suka tsaya yi kowa ya gagara furta komai kowanne akwai abinda zuciyarsa ke raya masa babu abinda take tunawa sai lokaci mai tsawo da suka kasance a tare soyayyar da suka gunadar mai cike da tsafta da kuma begen juna rayuwa mai daɗin gaske kullum cikin farin ciki, ahankali ta sauke idanunta ƙasa tana goge hawayen da yake ƙoƙarin zubo mata kallonsu kawai Fateeha take cikeda tausayawa domin duk wanda yaji labarin soyayyar su dole ya tausaya musu, zafaffan numfashi ya fitar daga bakinsa yana sake ƙare mata kallo akaro na babu adadi a kasalance ya furta


"Slimzy why?"


Ɗago kanta ta yi ta kallesa sai kuma ta ɗauke kai bata furta komai ba, wata kyakkyawar budurwa ce wacce aƙalla bazata shige 19-20yrs ba ta ƙaraso wajen, sanye take da wasu riga da wando ta ɗora jacket fara ce tas dan kana ganinta kasan ba bahaushiya bace tana zuwa ta kamo hannunsa cikin shagwaɓa ta ce


"Ayyah my singer mu tafi"


Hannunta ya riƙe amma bai ce komai ba, juyowa ya yi da niyyar yiwa Nazeefa magana amma wayam babu ko inuwarta kallon Fateeha ya yi wacce har sannan take tsaye ya ce


"Please kiban address naku"


Gyaɗa masa kai ta yi sannan ta miƙa masa complement card nasu ta ce"duk sanda zaka zo ka sanar dani first" ok ya ce mata sannan ya juya ya kalli Raihana ya ce" let go" murmushi ta yi sannan suka tafi suna riƙe da hannun juna.


Da gudu ta shige bedroom ɗin bin bayanta Fateeha ta yi tana kiran


"Nazeefa!! Nazeefa!!


Ko sauraronta Nazeefa bata yiba tana zuwa ta faɗa kan royal bed ɗin lokaci ɗaya ta fashe da wani raunataccen kuka, tsayawa ta yi jikin ƙofar ta naɗe hannayenta tana kallonta girgiza kanta tayi jin yardar Nazeefa ke kuka kamar ranta zai fita tabbas tana matuƙar tausayin Nazeefa domin labarinta abin dubawa ne, tabbas ƙaddara ce mai ƙarfi cikin labarin rayuwarta. Tana nan tsaye kusan 5mins har sannan kuma Nazeefa bata yi shuru ba, jiki asanyaye ta ƙarasa gefen gadon a hankali ta sunkuya daidai fuskarta ta taɓa ta



"Kiyi haƙuri Nazeefa ki ɗauki ƙaddara kamar yanda kikayi abaya dan Allah dan Annabi karki saka abin nan aranki ki jawowa kan ki wani sabon ciwon bayan wanda kike fama dashi ki taimaka kiyi haƙuri"



Kasa shuru Nazeefa tayi dan ji take kamar yanzu ne komai ya faru ji take zuciyarta na yimata wani irin zafi tabbas tasan ciwonta na gab da tashi matuƙar ta cigaba da jin irin haka, da kyar Fateeha ta samu ta rarrasheta tayi shuru gudun kada wani sabon ciwon ya sameta bayan wanda take ciki, tana fitowa daga toilet ɗin ta tsaya jikin dreesing mirror ɗin dake maƙale a ɗakin, duk ta rame dukda daman bawai mai ƙiba bace amma yanzu ramar ta koma ta cuta, fara ce tas kuma kyakyawa tanada doguwar fuska da kuma siririn hanci wanda yake har baka idanunta manya ne irin sosai ɗin nan kuma kwayar idonta irin blue colour ɗin nan ce tanada zara-zaran gashin ido wanda har inuwa suke idan ta rufe idanunta, bakinta ɗan ƙarami ne kuma jajur dashi saboda yawan tauneshi da take yi, Nazeefa asalin kyakkyawa ce dan tabbas ubangiji ya yi halitta a fuskarta harma jikinta, amma dukda wannan hakan bai sa ta samu farin ciki ba cikin rayuwata, kwata-kwata bata mori lokacinta ba sakamakon ƙaddara wacce ake cewa ta riga fata. Saida ta ƙarema kanta kallo sai kuma ta sunkuyar da kanta a hankali wasu hawaye suke rige-rigen zubowa kan kuncinta drawer jikin mudubin ta buɗe a hankali ta zaro wani ƙaramin hoto komawa gefen gadon tayi ta zauna tana ƙarewa hoton kallo, hotonsu ne lokacin da aka yi musu orientation farkon fara zuwansu makaranta hoton ya yi kyau sosai musamman daya kasance wanda ya wanke hoton ya iya sosai fuskarsu ɗauke take da annashuwa da farin ciki aƙalla hoton zai kai 8yrs da ɗauka lokacin bata fi shekara 18 ba a duniya, hannunta ta sanya ta shafi hoton hawaye na biyo kuncinta Fateeha ce ta shigo tana kallonta, karɓe hoton tayi ta mayar dashi sannan ta ce



"Wai dan Allah Nazeefa mene haka?, kinfi so ki koma ƴar gidan jiya ne?, idan Allah ya baka sauƙi nunawa ake dan girman Allah ki bar wannan tunanin mana just move on Hameed ya rigada ya yi aurensa kema kuma kinga matarsa da idanunki kuma kema kinyi naki auren saboda haka wannan labarin soyayyar ku barshi haka ok?"



Kallonta kawai Nazeefa tayi amma batace komai ba, ta kwanta kan gadon tana jin duk yanayinta na sauyawa abubuwan data manta na dawo mata sababbi fil shekarun da suka shuɗe suna sake dawo mata cikin kwakwalwarta wanda hakanne yake haifar da duk wata matsala dangane da lafiyarta. Tana nan zaune har saida taga bacci ya ɗauketa sannan ta miƙe ta rufeta da blanket saboda sanyin da ake ta fita a ɗakin, zaunawa tayi gefen Mom wacce take shan yoghurt ganin yanayinta yasa ta ce" lafiya dai?" ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Mom daman Nazeefa ce..." da sauri Mom ta ce" meya sameta?, ko jikin nata ne?, daman batada lafiya kuka fita?" ta jera mata tambayoyin hankali tashe, numfasawa Fateeha ta yi ta ce


"Daman munje kallon show ne saboda wai hankalinta ya ɗan nutsu tofa shine muka tararda wannan boyfriend ɗin nata Hameed shine yake show ɗin domin kuwa shine mawaƙin, Mom Allah ya cika burin Hameed ya zama mawaƙi ashe daman duk waƙoƙin da ake cewa H.slimzy nayi daman Hameed ne Allah ubangiji ya ɗaukaka Hameed fiyeda zatonki Mom tabbas arayuwa kaji tsoron Allah ka kuma yarda shine wanda ke azurtawa" ajiye cup ɗin yoghurt ɗin Mom ta yi tana gyara zama ta ce" wai bangane wane Hameed kike nufi ba kiyimin bayani yanda zan fahimta anutse kinji" ta ce "Mom Hameed dai wanda Dad ɗinsu Nazeefa yace bazai aurawa ba wanda kullum suke cikin zagi da cin mutunci wanda suka wulaƙanta akan Nazeef asaboda bashida arziƙi yanzu shine wanda ya zama abun kwatance gurin duk wani mai taƙama da arziƙi domin kuwa Hameed ya zama billoniere na masu kuɗi" cikeda mamaki da kuma al'ajabi Mom ta ce



"Tabbas wannna lamarin na Allah ne shine wanda yake azurta wanda yaso kuma ubangiji na kishin bawansa babu yanda banyi da yaya ba akan ya daina zurfafawa akan irin wannan abin amma yaƙi ji har ya fara ganin tamkar nice banason ƴarsa ta auri mai kuɗi, sai gashi ya aurar da'ita inda ba'aga girmanta ba inda basu ɗauketa mutum ba inda suka nakasa rayuwarta nakasa irinta har abada, tabbas koda Nazeefa ta rayu tofa zata kasancene cikin baƙin ciki da ƙuncin zuciya dan mahaifinta ya cuci rayuwarta batareda shima yasan ya aikata hakan ba" goge hawayen idonta ta yi cikin shashsheƙar kuka ta ce



"Wlh Mom kullum cikin tausayin Nazeefa nake duk ta fita hayyacinta musamman yau da muka haɗu da Hameed sai naji na sake tsinkewa da lamarin ubangiji, Nazeefa bata cancanci irin wannan cikin rayuwarta ba domin bata kasance mai yiwa wani mugunta ba kullum burinta ta zama silar farin cikin wani sai gashi ita bata samu irin haka ba cikin rayuwarta, tsawon waɗannan shekaru batayi farin ciki ba kwata-kwata Daddy bai kyauta ba" girgiza mata kai Mom ta yi ta ce" ba'a cewa haka duk lalacewar iyayenka dole suna nan a matsayinsu baka isa ka sauya musu ba saboda haka karki sake faɗar haka shi yayi haka ne wai dan ƴarsa ta samu kyakkyawar rayuwa karta sha wahala cikin rayuwarta sai gashi ya kaita inda babu Allah cikin ransu"



Taɓe baki tayi ta ce" Allah ya kyauta ya kuma saka mata dan an cuceta" girgiza kai Mom tayi dan tasan halin Fateeha indai ta riƙe abu tofa har abada yana cikin ranta. Ilahirin jikinta rawa yake yi ga wani azababban zazzaɓi daya rufeta, ƙoƙarin miƙewa take daga kwancen da take amma ta kasa dan ko motsa hannunta ta gagara yi runtse idonta tayi wasu hawaye na sakko mata tabbas da irin wannan yanayin da take ciki gwara ta mutu tasan bata raye dan daman rayuwartata batada wani amfani. Hucin da take fitarwa shine ya farkar da Fateeha, dakyar ta buɗe idonta saboda wani bacci datake ji, murje idanunta tayi ta miƙe da sauri tana taɓata ta ce



"Nazeefa!!! Nazeefa!!! Nazeefa!"_


Shuru kake ji wai malam yaci shirwa dan Nazeefa ta daɗe da sumewa anan kwance cikin tashin hankali ta sauka daga kan gadon ta fita a ɗakin da sauri.