Chapter 1
by @mlumu
***
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
👑 *JININ SARAUTA* 👑
*PAID BOOK*
*N=200*
*Only* 👌👌👌
*Acc No* . *7040902537*
*Acc Name.Maryam Bello*
*Bank.Opay*
*Domin ƙarin bayani za'a iya tuntuɓata ta wannan* *number *** ko **** .
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*STORY &WRITING*✨
*BY*
*MARYAM BELLO LUMU*❤️
*(M.Lumu)*✨
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪
(J.W.A)
*{Rubutu baiwa ce daga Allah,jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi.✏️}*
Email: ***
Facebook: Maryerm Lumu
Telegram: Maryam Lumu
TikTok: Maryam_Lumu4090
*Dedicated To....*✨❤️
*Hajiya Suwaiba Muhammad Barmo*❤️🔐
*FREE PAGE*
*Page 1*
*Da Sunan Allah mai Rahama Mai jin ƙai, Ina godiya ga Allah da yasake nunamin wannan lokaci da nasake dawowa da wannan littafi nawa mai cike da abubuwa da dama, Ina roƙon Allah yadda nafara lafiya Allah kasa na ƙare lafiya.*
*Wannan labarin ƙagaggen labarine banyi shi dan cin zarafin wani ko wata ba, dan haka idan kinga labarin yayi daidai danaki to a bisa kuskure ne.*
*ADAMAWA STATE* !
______Babbar masarauta ce,wadda tana ɗaya daga cikin masarautun da ake magana a kansu ga kuɗi ga kuma mulki mai ƙarfin gaske.
"Haba Aunty taya zan yarda da wannan magana da kike faɗa min?
wadda aka kira da Aunty ce tayi wani shu'umin murmushi ta ce,
"Ai dama ba so nakeyi ki yarda ba"
tayi maganar cike da izza,
"Hmmmmm Aunty kinsan yadda wannan masarautar ta ke ba wanda yake yadda da wata magana indai ba ganin akayi ta tabbata ba, amma dai Allah yasa wannan maganar taki gaskiya ce da saina fi kowa jin daɗi"
ta ida maganar tana barin gurin, murmushi Aunty tayi ta ce,
"Zainab kenan har yanzu bakisan wacece Ni ba amma garki damu na miki uzuri"
ta ida maganar tana daidaita kwanciyarta.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un Mama mutuwa zanyi"
cikin tashin hankali ta ke maganar numfashinta na haɗewa guri ɗaya sai nishi takeyi,
"Kiyi haƙuri Gimbiya ki ƙara jurewa ki ɗaga numfashinki.."
Kamin Mama ta ida maganar ji kake inyar inyar da murmushi Mama ta kalli Gimbiya ta ce,
"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah"
daganan Mama tafara gyara Gimbiya sai kuma tabawa Jakadiya yaron tare da cewa,
"Kije ki gyara yaron"
da sauri Jakadiya ta bar gurin tana mmurmushi.
Bayan wasu mintuna an gyara Gimbiya tare da gyra yaron, cikin farin ciki Mama ta je fada domin bawa Sarki babban albishir.
"Ranka yadaɗe Gimbiya Allah yayi ta sauka lafiya kuma da yardar Allah ansamu yarima"
Wani murmushi Sarki yayi ya sakko saman kujerar da yake zaune, ya kalli gabas yayi sujjada saida yayi kusan Mintuna goma sannan ya taso ya kalli Mama ya ce,
"Mama ya jikin ita Balkisu?
"Alhamdulillah jikin Gimbiya da sauƙi kuma duk suna cikin ƙoshin lafiya ita da yaronta"
cikin farin ciki Sarki ya kalli Mama ya ce,
"Mama kinada babban tukwuicin wannan albishir da kika kawomin"
wangale baki Mama tayi da ganan tayi gaba Sarki ya bita daga baya.
"Alhamdulillah Balkisu kinga abun Allah ko? gashi yau Allah yabamu ɗan da muka shafe shekaru muna nema"
ya ida maganar yana shafe guntayen hawayen da suka fara zubo mishi,
"Dama haka Allah yake al-amarinshi kuma wannan ba komai bane daga hukuncin Allah"
"Hakane Allah ya rayamuna wannan yaron akan Sunnah"
da "Amin" suka amsa suna cigaba da kallon ni'imar da Allah yayi musu tare da jaddada hukuncin Allah.
Cikin wasu ƴan awanni gaba ɗaya masarautar ta kaɗe da zancen sabon yarima da aka samu, wasu na farin ciki wasu kuma na nuna baƙin cikinsu ƙarara.
Sosai Sarki ke nunama yaronshi soyayya,bayan sati ɗaya akayi walima sosai wadda duk garin saida suka san ansamu yarima a masarautar, manyan mutane sosai sun halarci bikin da ikon Allah yaro yaci suna Muhammad (Jawad).
Sosai Gimbiya ke nuna ma yaron ta soyayya tare da kulawa.
After 20 years ago!
"Uhum Uhumm Momyyy"
"To ƴar Momy miyafaru ne kuma waya taɓa min ke?
"Ba Dady bane"
"Mi kuma Dady yayi?
"Wai bazai kaini School ba"
Ta ida maganar cike da shagwaɓa da yarinta, dariya Momy tayi ta ce,
"Ga Habu driver kice ya kaiki"
"Uhum Ni Allah idan bazai kaini ba bazanje ba"
ta ida maganar tana zaunawa saman kujera tana bubbuga ƙafa ga ƙasa,
"Mamana kiyi haƙuri mana yau zanyi meeting kije Habu ya kaiki"
"To amma da sharaɗi"
"To miye sharaɗin?
"Idan ka gama meeting ɗin zakaje ka ɗakkoni kayi alƙawari?
"Eh to nayi"
Da murmushi ta tashi ta rungume shi taje gurin Momy ta manna mata Kiss a goshi ta fita parlourn da gudu tana murmushi.
"Haba mana Beenah kiyi a hankali mana garki zame ƙafa"
Batama bi ta kan Momy ba ta faɗa mota Habu yajata sai makaranta.
Shima Dady shiryawa yayi yayima Momy sallama ya nufi gurin meeting ɗin shi.
"Wai ina Beenah ko ta manta da yau munada text"
"Hmmmm kinfa san halinta ba wani son lecture ɗin malamin nan ta ke ba may be shiyasa batazo dawwuri ba"
Basu ida maganar ba sai ganin fakawar mota sukayi a gabansu kamin kace mi sai ga wadda suke nema tafito cike da murmushi a kan fuskarta.
"Hey Guys Haw far?
"Haba Beenah tunɗazu fa muke jiranki kindai san halin mutumin nan ba wani mutunci ya cika ba yanzu sai ya hana mu shiga"
"To yanzu dai muje"
daganan suka cigaba da hirar text ɗin da zasuyi suka kama hanyar class ɗin su.
Bayan sungama text ɗin su suka suna fira kamar daga sama sukaji ana cewa,
"Wallahi Beenah idan har baki ƙarɓi soyayya ta ba saina ɗauki mummunan mataki akanki"
da mamaki suke kallon wanda yayi maganar fuskar shi ba alamun wasa ko kaɗan,
"Haba mana Munir tace bata sonka soyayya ai ba doli bace"
👑👑👑👑👑 *JININ SARAUTA 👑* 👑
*M.Lumu* ✍️
*Page 2*
"Dakata Ilham.."
bai ida maganar ba sai ji kake Tassssss an ɗauke shi da wani mahaukacin mari da saida kanshi ya juya,
"Munir ana soyayya doli ne nace bana sonka bana sonka kaje kayi duk abunda kake ganin zaka iya"
Beenah na gama faɗin haka tayi gaba fuskarta ɗaure ba alamun murmushi ko kaɗan,daganan Munir ya bar gurin a kunyace.
Misalin ƙarfe 4:30pm aka fara sanarwar saukar jirgi sosai gurin ya cika da mutane da kuma bushe bushe da kuma kaɗe kaɗe dan gurin ko ba'a faɗama ba zakasan wanda aka zo tarbo ɗan gidan sarauta ne.
Kamar daga sama suka hango wanda suka zo danshi nan take guri ya sake ɗauke wa a hankali yake tafiya cike da ƙasaita da kuma izza ta Jinin sarauta.
Daga gefe mutane sai gulma suke,
"Ma sha Allah amma dai Allah yayi halitta nan gurin amma waye wannan naga yanada mutane sosai?
wadda tayi maganar tana ƙara jaddada kyau irin na wannan mutum,
"Yarima Jawad ne"
"Yarima Jawad?
ta sake tambayawa da mamaki take ƙara kallonshi.
"Eh Yarima Jawad bayan wasu shekaru da yaje karatu sai yau yadawo"
"Ma sha Allah amma dai Allah yayi mishi halitta ba kaɗan ba"
tana ida maganar sukayi sauri suka bar gurin.
"Takawarka lafiya ɗan Sarki jikan Sarki wanda ya gaji sarauta gaba da baya"
Haka kawai Fadawan dake gurin ke maimaitawa cike da girmamawa,
shikuma Yarima ko a jikinshi dan ya lura da tunda yafara saukowa mutanen gurin ke kallonshi, motar da aka zo da ita danshi ya shiga bada jimawa ba suka bar gurin tare da tafiya da zuciyoyin al'ummar gurin.
Bada jimawa ba sai gasu sun isa masarautar koda suka isa kowa na tsaye bakin fada ana jiran isowar Yarima, wani bafade ne ya iso motar da Yarima yake da gudu ya buɗe ƙofar yana mishi kirari irinna ɗiyan sarauta,shikuma cikin izza yake saukowa daga motar fuskar shi ba alamar murmushi ko kaɗan.
"Takawarka lafiya Ɗan Sarki JININ SARAUTA jikan Sarki, Takawarka lafiya Yarima..."
Yarima bai bari ya ƙara sa ba ya ɗaga musu hannu alamar "ya isa haka" da haka kowa yaja jinin jikinshi.
"Ma sha Allah Yarima ya hanya?
Sai lokacin Yarima ya buɗe haɗaɗɗen Lips ɗin shi yafara dariya dariyar da kallo ɗaya zaka mata kagane bata cika hayaniya ba cike da izza yake ƙara sowa gurin mutanen gurin.
"Wallahi Aunty lafiya ƙalau na sameku lafiya?
"Lafiya ƙalau yaro na"
Da sauri Yarima ya nufi ɓangaren da ya hango Sarki tsaye yana isa ya rungume shi cike da soyayya ya ce,
"Wai na ma manta ashe fushi nakeyi da kai"
Yarima ya ida maganar cikin shagwaɓa,
"Haba kataɓa ganin inda ɗa yake fushi da mahaifinshi?
da sauri ya juya inda yaji maganar ya rungume ta tare da cewa,
"Ammi kema fushi nakeyi da ke ai"
"To ayimuna afuwa muje kafara hutawa sannan kagayamuna me muka yimaka haka"
da zallar farin ciki suka ƙarasa cikin fada sai farin ciki kowannensu keyi.
"Mamana waya taɓa min ke naga fuskarki ba fara'a ko kaɗan?
"Bakomai Dady gajiya ce kawai nayi"
badan ya yarda ba ya ce,
"To Allah ya hutar da gajiya"
da "Amin" ta amsa suka cigaba da tafiya.
Suna isa Beenah tayi hanyar ɗakinta tana isa toilet ta faɗa tayi wanka tare da ɗauro alwala ta fito, sallah tayi bata bar gurinba sai da tayi Azkhar sannan ta tashi ta shirya ta sakko indasu Momy.
*To be Continue* 💃🏻
*M.Lumu* ✍️
( *SHALELEN JAJIRTATTU* )✨💃🏻