Chapter 14
๐๐_*RAMIN K'ARYA*_ ๐๐
NA
IKILIMA ADAM
*( Kyauta daga Allah)*
Marubuciyar da ta nishandantar daku a littafanta kamar haka:
Kai ka jawa kanka
Kanwata
Rai daya ( Jan zaki)
Rudani
Makauniyar shari'a
And now
Ramin karya yan karin magana suka ce kurarre ne , mu je zuwa.
Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai .
SHAFI NA SHA HUDU
Zumbur prince ya mike tsaye . Murya na rawa ya ce ,
" Na san maganar nan daga bakin Lailat ya fito" ya fada yana mai tuna kalaman ta , na zata tari Sarki da wannan maganar.
" Hakan da kayi ya tabbatar min da gaskiyar abun ake fada, haba ina ilimin ka na arabi dana boko yake , ina maka kallon mai ilimi da wayewa ashe kallon mai saman ruwa nake maka" cewar Sarki cikin zafafan martani.
Ciza labbansa prince yayi yana mai murza idanunsa ,kansa na mugun sara masa.
" Zan tafi kai na ke ciwo" ya fada yana mai kokarin barin fadar.
Har ya sa kai ze fice .
" Dakata " cewar Sarki cikin kakkausar murya .
Cak ya tsaya be waigo ba .
" Karka kuskura ka samu Lailat da wannan batu, wannan tsakanina da kai ne , kaga ciki ne da ita ba'a son bata ran masu ciki, kuma ai tana da gaskiya, a cikin addini babu boye _ boye , in tayi shiru cutar da kai ne ".
Jidda dakyar ta daga kafafunta har ta iya tashi.
Prince be baiwa Sarki amsa ba , ya fice cikin hanzari . Jidda sallama tayiwa Sarki , kana ta iske baiwar dake kula da sashinta , tayi mata jagora har zuwa dakinta.
Bangaren Ummi , sanye cikin kayan barci riga da wando , kujerar falo ta kwanta kamar yanda ta fara tunda aka kawo ta , kallon agogon dakin tayi karfe tara na dare.
Hakan ya sanyata kara rufa zani akanta , adu'oi take karantowa cike da nutsuwa hade da shafe jikinta.
Kashe Gari.
Prince Adamsy tun da asuba sai mursu mursu yake a gado , cikin mafarkinasa , wata matashiyar yarinya ce , ta taho gabansa , murya mai dadin sauraro , rike hannayensa tayi , kana kanta a kasa dan taki yarda su hada idanu , duk da suna cikin sahara.
" Prince " ta kira sunansa , yayin da ,iska mai dadin gaske yake kadawa.
Lumshe idanunsa yayi yana mai kara matse hannunsa , idanu ya zuba mata , hade da jiran me zata fadi.
" Ina sonka , ina sonka , don Allah karka min kishiya a soyayya" ta fada cikin wani irin murya mai kashe jiki.
" In har kin yi alkawarin ba zaki barni ba , kamar yanda Maryam ta barni ba , zan baki zuciyata ke kadai".
" A'a ita Maryam haske ce , kuma ta tafi , ni kuma annurinka ce , ka rikeni kamar yanda uwa take rike danta " ta fada tana mai kokarin kiss dinsa a baki.
Kiss din ta masa ya sanya shi , maida mata martani suna kiss din juna yana jin kansa yana shawagi a sararin samaniya , karar alarme din wayarsa ne ya zaburar dashi. A kidime ya bude idanunsa yana kallon kansa saman gado, karamin tsuki yaja yana shafa sajen fuskarsa , hade da fara karanto aduar tashi daga barci. Lumshe idanu yayi yana tariyo mafarkin da yayi, kana a zahirance yana jin kamar a zahiri ne . Barin wani tunanin yayi ya sauka daga kan gadon yana mika hade da salati a bakinsa .
Koda ya fito daga bandaki Jallabiya ya zura domin tafiya masalaci , har ya sakai ze fice daga Masarautar , maganganun mai martaba ne suke masa yawo kwanyar kansa. Juyawa yayi yayi sashin Lailat cikin hanzari , knocking yayi , jin shiru ba'a bude ba ,ya sanya shi bude da kansa . Falon nata yake bi da kallo yanda aka masa kaca-kaca ba'a gyara ba alamun tayi baki a daren jiya. Plate da abinci ciki a yashe a kasa , kawar da kallonsa akai yayi yana mai ci gaba da tafiya zuwa dakin nata.
Yana bude dakin nata , ya kunna madannin haske , kallonta yake yanda take barci bilhakkin.
" Ki tashi ki yi sallah" ya fada kamar me jin kashi.
Bude idanunta tayi ta gansa da mamakinta , dan be taba shigo mata daki irin wannan time din ba ,sai da kwakwaran dalili .
Kara bude idanu tayi ta tabattar shine.
Ganin ta bude idanu ne ya sanya shi juyawa , ba tare da ya kara waiwayarta ba , kai tsaye dakin Jidda ya nufa , yana shiga ya duba ko ina be ganta ba , rike da kugunsa yana tunanin ko ina ta shiga ne . Fita dakin yayi ya zarce dakin yara. Yana shiga dakin ya iske su a falo suna nafila , Jidda tana rike da hannun Hassana gudun kar ta fadi.
Tsaye yake yana kallonsu kusan mintuna uku ya dauka, sosai ya ji nutsuwa na saukar masa , a hankali ya juya tare da rufo kofar ba tare da sun san ya shigo ba.
Karfe goma daidai ya fito daga dakinsa, sanye bleu black din boyel tsadadde ya sanya hula mai kalar hade da daki , takalmin sa baki ne , wayoyinsa ne ahannunsa , suna gogar agogon diamond dake makale a tintsiyar hannunsa.
Kai tsaye dakin Maman Nura ya nufa domin yana son ganinta .
Yana bin sashin dakinta , bayi suna ta zuwa masa gaisuwa , isowar sa ne ya sanya aka bude masa .
Yana shiga dakin yake bi da kallo yanda bayi suke ta kai kawo ana ta ajiye kayan brek akan dinner table.
" Barka da zuwa prince Adamsy" cewar ma'aikaciyarta .
Be bata amsa ba
" Ina Umma " ya fada ba yabo ba fallasa
" A'a Adamu, kai ne yaushe rabon da na ganka ka shigo tun rasuwar Maryam , sai yau.
Kallon ta yake yanda take baza kamshi taci habaya Egypt , mai kalan ruwan kwai , alkyabba ne a saman sa , kana hannunta na karar warwaron zinare.
" Eh sai yau , Allah ya bani ikon zuwa " ya fada yana mai kallon agogon hannunsa.
" Zauna mana mu gaisa" ta fada fuska a sake.
" Hakan ma yayi, da fatan dai kina Lafiya ".
" Lafiya lau Adamu na" ta fada tana mai mamakin yanayinsa.
" Daman na zo na gayamiki , ko in jaddada miki wani abu , ki jawa Nura kunne dan bana son na na fara ja masa , kuma ki sanar masa , aman da yayi ya kamata ya lashe " ya fada a zafafe.
Cikin tsananin tashin da damuwa ta ce ,
" Ban fahimci me kake nufi ba , Adamu " .
" Karatun na yan hausa ne , ke kuma yar turai ce " ya fada yana kokarin barin falon.
Cikin tafasar zuciya ta ce , " ai Adamu wallahi kayi kadan ka gasa min magana ka wuce" .
Cak ya tsaya tare da waigowa fuskarsa dauke da murmushin yake .
" Ba gasa miki magana nayi ba , kawai dai bakya gane karatun kurma ne ". Yana fadin hakan ya fice daga dakin nata , kai tsaye dakin Gimbiya Zainab ya nufa.
Ya iske ta zaune bayi na mata fifita.
Bayan sun gaisa ne ya nemi a basu wuri.
Dan taba hira suka yi , kana ya tashi domin tafiya.
" Har zaka tafi" ta fada tana murmushi.
" Eh zan je nayi brek , yau a falo zanyi break ya fada yana mai fita.
" Sai mun fito " cewar Gimbiya Zainab.
Yana fita ta fara gyada kai tana aune aunen abun yi.
___________________
Zaune a ma'aikanta na sabulu , gefensa sakatariya ce zaune hannunta dauke da file.
Tana sanye cikin riga da wando mayo kalar omo wanda ya kama jikinta , kana kana ganin sharp dinta duk da a zaune take , kyakyawa black beauti ce , bakinta dauke da jan baki pin color .
" Yallabai daman PA ya ce yau be samun zuwa aiki , Dan mamarshi ba lafiya" ta fada tana mai kallonsa.
Kamar ba ze magana ba , yana ta rube_rube a file.
Kallonta yayi kana ya sauke kai kasa.
" Kashe min AC " ya fada ,yana mai jin sanyi na shigarsa.
Tashi tayi tana juya mazaunai, tana kada su da gangan , kana ta kashe , tafiya take kamar me gasar miss kana ta karaso tare da komawa mazauninta.
Kallonta yake , yana mai fadin " Oh tunda be zo ba , ki zo min da file din abunda akayi jiya , kana ki cewa , Zahradeen ina son ganinsa" ya fada cikin kaduwa dan sanyi yake ji sosai.
" Sir lafiya kuwa?". ta fada tana kokarin taba shi.
Hannun ya mata alamun dakatarwa cikin bacin rai.
" Am sorry wai karka fadi ne ?".
Murya na rawa ya ce " kira mun shi nace ko!!!". ya fada yana mata wani irin kallo " .
A hanzarce har tana tuntube ta je , ta kira shi. tare da suka shigo dakin , shi kuwa , hanzarta karasawa gabansa yayi .
" Lafiya kuwa ?". ya fada hankali tashe.
" Kai ni gida sanyi nake ji" yana markakata.
" Sanyi ko zazzabi"?. Deen ya tambaya , fuska babu walwala .
A wahalarce ya ce , " har da zazzabin ma ". ya fada yana mai ciza bakinsa.
Kama shi Deen yayi dakyar ya kama shi , da taimakon manager Aminu suka sakashi a mota , ma'aikata sai sannu ake ta jero masa.
Koda isar su Masarauta ne docto ya zo ya duba shi , kana ya kalli Deen da Abdullahi da Aliyu har da Sumayya .
" Ku dan bamu wuri zanyi magana da Deen , dan maganar ba irin taku bace " ya fada yana mai neman hakan.
" Haba doctor mu fa kannnensa ne ?". Cewar Aliyu ,ransa a bace
" Na sani" docto ya bashi amsa.
Domin kauda cece ku cen , Deen ya ce , " kawai ka fada a gabansu babu komi" ya fada cikin bukatar hakan.
Gyada kai Aliyu yayi tare da fadin " Atoh gaya masa ".
Ajiyar zuciya ya sauke kana ya kara kallon Aliyu.
"Don Allah ku fita , ai yayanku ne , akwai abunda shi kansa ba ze so ace kun ji ba , duk da ku kannensa ne , amma abokinsa daidai suke da junansu " ya fada ransa ya dan soma baci. Ya kara da fadin
" Kuma na san waye Adamsy , sannan don Allah ,cikin matansa a kira mutum daya ".
Ajiyar zuciya Abdullahi ya sauke kana ya furta " na fahimce ka docto " sai ya kalli kannensa, ku zo mu je , ke kuma Sumayya , ki je ki taho da amaryarsa ina ze fi bukatan hakan". Ya fada cikin mutuntaka, tare da tasa keyar Aliyu suka fita . Sumayya take musu baya tayi.
Koda ta je dakin yara iske Jidda tayi zaune tana karatun al'kurani mai girma tana zubar da kwallah.
Jiki a sanyaye ta karasa dakin. Dago kai Jidda tayi tana kallonta tana mai goge kwallah.
" Mu je dakin yaya Adamsy bashi lafiya" . Ta fada.
Ajiye al'kurani mai girma tayi cikin tsinkewar zuciya, kana tana tuno kalaman Sarki na jiya.
" Lafiya kuwa ?".ta fada cikin tsoro.
" Meye abun damuwa ai dakin Mijinki ne , bashi da Lafiya kila zaki taimaka masa da abinci ne , ko wani abun" cewar Sumayya tana mai kallon yaran dake zaune saman kujera.
Itama Jidda su take kallo , gabansu ta isa ta manna musu kiss a goshin su , kana ta dauki hijab ta sanya.
" Mu je , inna kai ki, sai na dawo wajen yaran nan" Sumayya ta fada tana mai yin gaba , Jidda na bin ta a baya.
Daga cikin dakin.
" Yanzu fa shekaru shida kenan, Adamsy be kusanci iyali , haka ya fada min kwanaki da bakinsa , ya kamata a nusar dashi yarda da kaddara, kuma ciwon maran da yake yawan yi, shi ke haifar da komi , tunda ya kara aure me yake ......" sai yayi shiru ganin Jidda da Sumayya sun shigo. Sumayya juyawa tayi ta fita , ita kuwa Jidda gefe daya ta samu wuri ta zauna tana kallon Prince Adamsy kwance saman kujera yana barci alamun yana jin jiki.
" Yawwa madam , gara da kika shigo " cewar docto yana dawo da kallonsa akanta.
Zura masa idanu take tana mai jiran jin abunda ze fada
" Ya kamata ki bar Mijinki ya kusance ki , in har ana son wannnan lakurar ta kau ce .
Kallonsa take kamar bata fahimtar me yake fadi.
" Ina nufin ina son ki amince kuyi kwanciyar aure ke da mijinki" ya fada cikin gwari gwari.
Tashi tsaye tayi tana kallon Adamsy tana kallon doctor.
"Ina zaki je , ki zauna a miki bayani " shiru docto sakamakon ganin.......
Taku har kullum kyauta daga Allah