WATA ALAƘA

SHA SHIDA

by @zeeeyybawa

*WATA ALAKA.*

*PAID BOOK*

*YAN TAGWAYE BIYAR*


ZAYNAB BAWA

&

STYLISH BCH



*SHAFI NA GOMA SHA SHIDA*



"Idan kikayi zancen yaje kunnen Takawa zaice toh kenan kin kasance daga cikin mutane masu jiran mutuwar sa. Duk wani abunda zai taɓa martabarki a idonsa bana so, shiyasa nakeso abi komai a hankali sannu-sannu bata hana zuwa. Kuma a halin yanzu baima kamata ki taso da wannan zancen akan yaran da har yanzu basu mallaki hankalin kansu ba Fulani. Har yanzu suna age din da suke bukatar kulawa da kuma basu ingantacciyar tarbiya ta yadda a nan gaba ma al'ummar jihar nan da kansu zakiji suna cewa abawa wane sarautar." Jikin Fulani ne yayi sanyi kenan da gaske jiran mutuwar mijinta da take yiwa ikirarin so takeyi? Tafara tambayar kanta cikin damuwa. Ajiyar zuciya ta sauƙe tace.


"Shikenan Yaya in sha Allah har zuwa lokacin daya dace bazan sake taso da znacen ba." Ciroma ya jinjina kai tare da cewa. 


"Toh Madallah Allah ya nuna mana girmansu cikin aminci." 


"Amin." Fulani ta amsa sannan suka shiga tattauna wani lamarin kuma daban. Sai da tayi la'asar a gidan kafin nan tayi musu sallama ta koma.


Giwar Ciroma kuwa gabaki ɗaya ta matsu Fulani tafita domin ta samu mijinta taji abunda suka tattauna. A zaune a palourn ta sameshi bayan ya dawo daga sallah yakoma bakin aiki yana duba wasu takardu da suke ajiye a gidan. Da sallama tashiga bayan ta ɗaura idonta akan abunda yakeyi ta ƙaraso tana faɗin.


"Aiki dai, aiki dai babu hutu ko yallaɓai? Yau ai tunda muka samu ka ƙwato sai kuma ka huta agidan." Murmushi yayi yace.


"Giwata kenan wayace miki mutumin daya tara iyalai yana ganin hutu? Ai babu batun hutu har indai inason saka farin ciki a zuciyar iyalina." Murmushi tayi sannan tace.


"Allah ya ƙara maka ɗaukaka akoda yaushe ai kana kan sakamu farin ciki." Amin ya amsa batareda ya ajiye takardun da suke hannunsa ba.


"Lafiya dai koh zuwan Fulani? Mun fara zancen da ita kuma saika dawo." Murmushi yayi cikin hikima ya sanar da ita yanda sukayi.


"Kai yanzu meka yanke mata?" Ta jeho masa tambayar.


"Toh yanzu nikam dai banace komai ba tukunna sai zuwa giramansu mugani Idan Allah yabamu aron rai da lafiya." Ɓata rai tayi sosai kamar ba itace yanzu take murmushi ba. Cikin sigar makirci da yanayin da tasan idan tayi magana yana ratsashi tace.


"Yallabai ɗina yaushe zaka farka ne? Yaushe zaka fara fahimtar abubuwa a yanda ya kamata ka fahimcesu?" Cikin rashin fahimta yake kallonta bata tsagaita ba tacigaba da faɗin.


"Har yanzu baka fahimci dalilin da Sunanka ya kasance Aliyu ba? Baka amshi saƙon Abba ba kenan? ko kuma ka fahimta ka amshi saƙon kawai amma bazaka cika masa burinsa akan wasiyyar daya barmaka ba ko? Da ace mutum yana mutuwa kuma ya taso idan Abba ya taso yaga yanda kayi burus da muradinsa haƙika saiya zubda hawaye. Kaga da farko nayi deciding na zuba maka ido amma na lura yallaɓai baka san zuru ba is hight time daya kamata ace ka farka." Nisawa Ciroma yayi ya fahimci inda ta dosa sai dai bai san a'ina tasan wannan muradin na Abbansa ba, wanda ya tabbata Abba shi kaɗai yabarwa wannan wasiyyar koshi bai daɗe da sani ba. Toh bayan ita mutane nawa suka san da wannan lamarin? Ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya ɗaga idonsa daga gareta yace.


"Kuna zancenku ne daga ke har ita, yanzu idan Allah yaga dama sai yabar Takawa akan mulki har wanda ake tunanin zasu hau karaga su mutu su barshi domin kaɗan ne daga cikin ikon ubangiji ya ɗauke duk wasu masu jiran karaga kafin shi. Idan Allah yaga dama sai yabarshi ya ƙara shekaru sittin ko saɓa'in yanzu haka akan nasa. Sannan idan Allah yaga dama saina mutu na barshi tunda naga kamar kunfi gane cewa ni zan bada mulkin." Cikin harzuƙa da zancensa Giwa tarasa inda ya kwaso sanyin hali gabaki ɗaya baida halayyar masu suna Aliyu ta miƙe tace.


"Shikenan ai saika jira ya mutu." Tafice daga ɗakin cike da fushi. Ajiyar zuciya ya sauƙe ya ajiye takardun hannunsa a gefe ya kwantar da kansa a jikin kujera yana maida numfashi.

___________


 Hydar yana barin wajan Takawa kai tsaye gidansu Hidaya ya nufa domin ya kwana biyu baiga Mami ba. A gefen gidan yayi parking motar ya fito ya kulle motar sannan yashiga ta ƙofar dake jikin gate. A bakin palourn Mami yayi sallama Maryam ce kaɗai da Auntyn su a palourn wato (Amaryar Abba) Maryam najin muryarsa ta taho da gudu ta buɗe ƙofar tana murnar ga Yaya Hydar. Ɗaukanta yayi yashigo ciki da sallama a bakinsa domin yana son Maryam sosai dan yana ganinta kamar ƙanwarshi Bilkisu duk da yasan a yanzu Bilkisu ta dawo ƴan mata domin tana kimamnin shekara na goma kenan. Hidaya wacce tashiga kitchen soyawa Auntyn su wainar flour saboda tafara laulayin ciki kuma tana son cin wainar flour idan ita tayi kuma bata iya ci shine Mami takan saka Hidaya tayi mata idan tana gida. Sannan dayake kansu ɗaya da Hidaya har Hidaya ma tafita girman jiki jininsu ya haɗu sosai, tunda suka gama cin amarci tagama ƴan ƙunshe-ƙunshe a ɗaki na amarci sai kuma tafara shigowa sashin Mami idan Hidaya tana nan domin tadawo kamar wata ƙawarta. Abba yana jin daɗin yanda yaga Hidaya da Hafsat sun shaƙu sannan hankalinsa a kwance yake fita yabarta a gida domin yasan ko abu take buƙata Mami zata tanadar mata dashi. Laulayinta bamai tsanani bane sosai kawai ƴan ƙwaɗayine na masu ciki sai abubuwan da baza'a rasa ba. Jin Ihun Maryam tana faɗin Yaya Hydar Hidaya ta fito daga kitchen, murmushi Hidaya ta saki tana kallon Hydar shima ita yake kallo, 


"Kayi kyau cikin shaddar nan Twin Bro." Tafaɗa kanta tsaye. Daɗin ya cika zuciyar Hydar jin Hidaya ta yabeshi kodan ita dama kanta tsaye take yaban duk wani abu daya jiɓanceshi. Ƙarasawa yayi cikin palourn ita kuma ta koma cikin kitchen tana jiyoshi suna gaisawa da Antynsu, wannan ne karo na farko da Hydar suka haɗu da ita tunda aka auro ta bai taɓa shiga sashinta ba sannan bai taɓa zuwa ya sameta a nan ba duk kuwa da baya sati baizoba dan idan ya kwana biyu Mami ta dinga damuwa kenan sai taga kamar bata riƙe amanar da aka barmata dakyau ba. Mami ce ta shigo palourn tana ganin Hydar ta faɗaɗa fara'arta ƙamshinsa ne ya sanar mata da zuwansa dake idan yazo haka gidan yake karaɗewa gabaki ɗaya da ƙamshinsa. Miƙewa Antynsu tayi tabi Hidaya cikin kitchen domin tana cike da tambayoyi da mamakin ganin balarabe yana yaran hausa tarr a bakinsa.


"Hidaya amma wannan saurayinki ne koh?" Dariya Hidaya tayi sannan tace.


"A'a Aunty Hydar nefa." Jijjiga kai Aunty Hafsat tayi ta sake jeho mata tambaya.


"Naga kamar ba ɗan ƙasar nan ba." 


"Ɗan kasar nan ne Aunty Umminshi ce ƴar Egypt Babanshi kuma shine SARKI ALIYU TURAD mai mulki a yanzu." Jijjiga kai tayi ta kai hannunta kan wainar flour din da Hidaya ta kwashe tafara ci tana faɗin.


"Ah lallai kam dole ma yayi kyau uwa balarabiya uba cikekken bafulani toh zallan familyn sarki ma kiji yanda ake zuzuta kyawunsu inaga ya haɗa ruwa biyu?" Murmushi Hidaya tayi tana gama ciro ta cikin kaskon tasaka a plate ta ɗauko mata suka fito. Zama tayi a kujerar da take kusa data Hydar tana faɗin.


"Twin-Bro baka cemin yau zakazo ba kuma ɗazu muka rabu." 


"Ba wajanki nazo ba ai shiyasa babu buƙatar sanar dake, Mami nazo gani that's all." Murmushi Mami tayi Hidaya kuma ta kyaɓe baki. A zahirin gaskiya kuma Hydar Hidaya yazo gani domin ko wuni zaiyi yana kallonta baiƙi a dawo da ranar baya ba yacigaba da kallonta ta sake ƙarawa a dawo da ita kawai. Shi kansa yasan yana yiwa Hidaya wata irin zazzafar ƙaunar da baya fata Allah ya jarrabeshi da rasata. Domin kwaƙwalwa bazata iya kintatar abunda zai biyo bayan hakan ba. Muryar Hidaya ya tsinta tana faɗin.


"Na ɗauka ma hira zaka tafi wajan Na'ima shiyasa kasaka manyan kayan nan." Ɓata rai Hydar yayi yace.


"Bazaki daina ba koh?" 


"A wane dalili zan daina twin Bro? Dazu mafa wayarka tana hannuna naga saƙonta ya shigo." Ɗan sirirn tsaki yaja ya kauda kansa Zuwa ga Mami dake tambayar 


"Yaron nawa budurwa ce dashi kenan?" Kafin Hydar yayi magana Hidaya tayi caraf tace.


"Ai Mami inaga a duk illahirin TURAD INTERNATIONAL ACADEMY babu wani mai farin jinin HYDAR TURAD. Dan ko a cikin fararen fatar school ɗinmu babu wanda yakai shi farin jini." Ta ƙarasa maganar ta sigar wasa.


"A'a gaskiya A'a ban yarda ba su ƙyalemin yarona tukunna ya nemo min baralabiya daga wajan Umminsa." Mami tafaɗa itama tana son tsokanar Hydar din. In a serious tone Hydar yace.


"A'a Mami nikam already ai kin haifomin mata." Su dukansu dariya suka saka, Hidaya tace.


"Eh lallai twin-Bro wato Maryam zaka aura ko?" Shareta Hydar yayi kamar baijita ba. Ya dubi Mami babu alamar wasa yace.


"Mami dan Allah idan ina so zaki bani?" Fahimtar da tayi cewa da gaske Hydar yakeyi sai itama ta cire alamun wasa a fuskarta ta shafo sumar kansa tace.


"In sha Allah yarona nayi maka alƙawari babu wani abu da nake dashi wanda zaka nema nakasa baka." Cike da jin daɗi Hydar yace.


"Nagode Mami Allah yaja kwanaki." Ta amsa masa da, 


"Amin." Hidaya ta miƙe tana faɗin.


"Wai Mami da gaske kikeyi? Yaushe zai jira Maryam kuma shima fa wasa yakeyi ko?" Mami tace.


"Da gaske nake mana Hidaya tunda nake da Hydar bai taɓa makamanciyar wannan maganar ba shi bamai magana bane na tabbata a wasa bazai faɗi wannan zancen ba" Taɓe baki Hidaya tayi ta shige kitchen Antynsu wanda ta fahimci Hydar ba akan Maryam yake magana ba ta miƙe ta bita kitchen din. Fridge ta buɗe ta ɗauko watermelon juice da Mami tayi wanda ba'a saka sugar a ciki ba ta ɗauko don tasan Hydar bai son Sugar. Juyawa tayi zata bar kitchen a lokacin Antynsu ta shigo. 


"Hidaya nifa inaga ba akan Maryam yake magana ba kamar ke yake nufi Hydar din." Cikin rashin fahimta Hidaya ta kalleta Antynsu ta ɗaura da faɗin.


"Naga irin kallon da yake miki idanuwansa cike suke da soyayyar ki." Dariya Hidaya tayi tace.


"Wai Hydar yana sona wayaga Hydar na sona, Eh tabbas nasani yana sona sosai amma ba irin wacce kike tunani ba. Anty duk yanda zan faɗa miki shaƙuwata da Hydar bazaki gane ba, Nafi shaƙuwa dashi akan kowa kuma shima hakanne, may be wanda bai sani ba zaiyi tunanin soyayya ce amma wannan WATA ALAƘA ce wanda ubangiji ya gina mana ita a tsakaninmu." Kai Antynsu ta gyaɗa bawai donta yarda da abunda Hidaya ta faɗi ba.


 Sunkuyar dakai Hydar yayi yana sauƙe ajiyar zuciya ba ƙaramin daurewa yayi kafin ya iya yiwa Mami wannan maganar ba, baya fata ace abubuwa sunzo masa ba'a yanayin tsarinsa ba shiyasa yafara shigo da Mami zancen tun a yanzu. Ajiye masa drink ɗin Hidaya tayi Mami ta dubeta tana faɗin.


"Abinci fa Hidaya?" 


"Yanzu zan kawo masa." Ta faɗa tana juyawa. Jawo Maryam dake jikinsa tayi tana faɗin.


"Sauko ki bashi waje Maryam yaci abinci." Sauka Maryam tayi zuwa jikin Mami, a lokacin Hidaya tafito masa da abinci, ta ajiye ta koma gefen Auntyn su ta zauna ahaka Abba yashigo ya samesu shima yazo ya zauna farin ciki yana ratsa shi. Jakarsa Mami ta amsa takai ɗaki tana barin wajan Abba ya dubi Antynsu Hidaya cike da kulawa yake tambayar jikinta. Kauda kai Hidaya tayi gefe tana mai jin kunya domin idan Abba yana nunawa matarsa kulawa kunyar idon Mami kawai yakeji yafi akira hakan da shakka. Mami tana dawowa ya miƙe yashiga ciki ita kuma ta ƙarasa dining domin haɗa masa abinci.


Sai bayan isha'i kafin Hydar yabar gidan tare da Abba suke fita sallah suka dawo. Da zai tafi Mami ta haɗa masa snacks da dambun nama kamar yanda ta saba yimasa, har bakin mota Hidaya ta rakashi tana riƙe da wasu package ɗin snacks ɗin bayan mota ya buɗe ta zubasu sannan ta dawo ta riƙe murfin motar suna magana. Zuciyar Hydar sai bugawa takeyi da sauri wani irin sanyi yakeji a zuciyarsa daɗi yakeji saboda irin yanayin da suke a yanzu kamar wasu saurayi da budurwa. Saurayi yazo hira zai tafi ta rakoshi duk wani abinda zai alaƙanta shi da Hidaya a matsayin masoya yana son hakan sosai. 


"Idan ka'isa gida zan kiraka." Tafaɗa tana ƙoƙarin juyawa. Harta juya ya kira sunanta, juyowa tayi fuskarta ɗauke da murmushi. 


"Yayaneh?" Ta tambaya. Ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya girgiza kai alamun babu komai, juyawa tayi tashige ciki saida yaga shigarta kafin yaja motar yabar wajan.

________


  Cikin tashin hankali Fulani ke kallon Hadimar Farouq, miƙewa tayi da sauri tana faɗin.


"Garin yaya baida lafiya amma tun ɗazu baku sanar min ba?" Tafaɗa tana fitowa daga ɗakinta. Ɗakin Faruq ta nufa sai kuka yake yana riƙe cikinsa kamar zai mutu. Hankali a tashe Fulani ta haura gadon ta kamoshi, cikin ƙaraji take faɗin.


"Meya sameshi tun yaushe yake cikin wannan halin?" Ɗaya hadimar tasa tace 


"Tun bai daɗe da dawowa daga sashin Yarima Hydar ba." A razane Fulani take kallonta, 


"Sashin Hydar? Da yaushe yaje sashin Hydar ɗin?"


"Bayan tafiyarki yace shi lallai sai an kaishi can tunda bakya nan." Cikin zafin rai Fulani tace.


"Toh ku mahaukata ne don yace ku kaishi saiku kaishi? Yaci wani abune acan ɗin?"


"Yafito yana shan chocolate bamu da masaniya ko yaci wani abu bayan ta." Gaban Fulani ne ya faɗi shikenan Hydar zai kashe mata ɗa. Takawa takira cikin tashin hankali tana kuka take sanar masa Faruq babu lafiya. Shima takawa cikin tashin hankali ya baro sashinsa zuwa nata, a gaggauce aka dauki Farooq akayi dashi asibiti basu daɗe da zuwa ba ciwon ya lafa. Sa'i-sa'i mai martaba yana kira yaji yanda ake ciki bayan sun gama bincike suka gano appendices ke damun Faruq amma Fulani bata yarda ba ita kawai Hydar ne zai kashe mata yaro. A daren aka shirya yimasa aiki Takawa yana jin haka ya taho asibitin shima. Fulani sai kuka takeyi tana faɗin Hydar ne zai kashe mata ɗa, Mai martaba yakasa fahimtar abunda take nufi. Sai da aka fito da Farouq daga theater kafin Takawa yadawo gida.


Washe gari da sassafe Hydar yaje gaida Takawa kafin yatafi school. Anan Takawa ya sanar masa abunda yafaru da Faruq din. Dayake a lokacin Takawa zai fita zuwa asibiti sai yace su tafi tare da Hydar daga can sai ya wuce school din dan Hydar yadamu sosai da ciwon yaron yana tuna zuwansa jiya wajansa. Driver ne yaja motarsa shikuma da mai martaba suka shiga mota ɗaya. Mai martaba ya lura da yanda Hydar ya shiga damuwa tunda ya faɗa masa Faruq baida lafiya, lura da hakan yasa Mai martaba ya fara kwantar masa da hankali har suka isa asibitin. A sashin VVIP anan aka kwantar da Faruq kai tsaye ɗakin suka nufa. Fulani ce zaune a bakin kujerar dake ɗakin fuskarta tayi fayau idanunta har kumbura sukayi da alamun tasha kuka ta ƙoshi. Sallamarsu ya sanyata ɗago kanta, wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne ya mamaye zuciyar Fulani ganin Hydar atare da mai martaba bayan duk abunda ya aikata saboda rashin kunya shine ya biyo shi nan zuwa yayi yasake ƙarasashi kenan? Idanuwanta sun rufe ko kallon mai Martaba dake gefe batayi ba ta miƙe ta nufesu tana isa batareda wani tunani ba ta wanke fuskar Hydar da mari. Wani irin tsawa mai martaba ya daka mata daya sakata yin baya Saida Faruq ya buɗe idonsa. Wani irin huci Mai Martaba yakeyi yana jin zuciyarsa tana masa wani irin zafi. Lokaci guda ya rikiɗe ya dawo Aliyu gadanga ƙusar yaƙinsa, idanuwansa suka canja launi yana jin kamar itama Fulanin ya wanke fuskarta da mari. Juyawa yayi ga Hydar wanda gefen fuskarsa tuni tayi jajawur kansa yana ƙasa har a lokacin. Cikin wani irin yanayi mai cike da tausayawa Takawa ya tallafo fuskarsa, amma Hydar yakasa ɗago ƙwayar idanuwansa da suka kaɗa ya kalli Mai martaba cikin raunin Zuciya mai martaba ya jawo Hydar jikinsa ya rumgune. Bubbuga bayansa yakeyi yakasa cewa komai. Hydar ma numfashi kawia yake fitarwa Fulani cikin ɓacin rai tace.


"Mugu azzalumi kawai. Ka fice min a ɗakin nan ko dawowa kayi ka kasheshi bayan niyyar da kayi bata cika ba? Bana buƙatar WATA ALAƘA tsakaninka da ɗana har Abada, sannan kuma bana son ganin ka kusanci ɗana har Abada kaji na gaya maka." Mai martaba gudun ya faɗi wata maganar da zasuyi dana sani kawai sai yaja hannun Hydar suka fice daga ɗakin. Sai da suka shiga mota kafin yafara rarrashunsa kalmar da yafi ambata itace.


"Koma menene yafaru nina jawo maka Abbana da ban bar mahaifiyarka tatafi ba da haka bata faru dakai ba." Hydar ajiyar zuciya kawai yake sauƙewa bai iya magana ba ko kukama kasa yi yayi. Makarantar da Hydar baije ba kenan a ranar, kuma wunin ranar a wajan mai martaba yayishi ko kalma guda ɗaya yakasa furtawa zuciyarshi na cike da kewar Ummin sa. Mai martaba shi kansa jiki a sanyaye yayi wannan wunin tunda yake ko murya bai taɓa ɗagawa Hydar ba saboda yanda yake jinsa kamar ransa amma yau Fulani ta ɗaga hannu ta mareshi, ji yayi inama ace shi Fulani ta mara ba Hydar ba da hakan sai yafi masa daɗi. Sai dare sosai kafin yabar Hydar ya koma sashinsa da tunanin yanda zai kasance shi ɗaya.


Hidaya takira Hydar harta gaji ba'ai picking ba, dayake wayar na cikin mota saida zai koma sashinsa kafin ya buɗe motar ya ɗauki wayar. Yana shiga ciki wani kiran ya sake shigowa. Amsawa yayi da sanyayyar muryarsa. Hidaya wacce itama duk jikinta yayi sanyi tana tunanin wani abunne yafaru saboda Hydar bai fashin zuwa makaranta kuma bai fashin ɗaukar wayarta. Cikin yanayin damuwa take tambayarsa abunda ya faru. Hydar sanar mata yayi akan bai jin daɗi Hidaya tashiga tashin hankali, daga yanayin yanda yake jiyo muryarta kamar zatayi kuka. Murmushi yayi ya koma yana rarrashinta duk da zuciyarsa bata masa daɗi. Wayar da Hydar yayi da Hidaya ta rage masa wani kaso daga ciki damuwarsa. 


Washe gari ma Hydar baije school ba saboda fuskarshi ta kumbura saboda marin da akai mata. Takawa ne ya shirya ya wuce sashin Hydar ganinsa ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba, babu yanda baiyi da Hydar din ba akan ya shirya suje asibiti amma yaƙi firr. Ganin haka kawai likita Takawa ya kira har gida ya duba shi. A ranar mai Martaba bai samu yafita Fada ba da Hydar ya wuni ko asibiti bai leƙa ba saboda baya son ganin fuskar Fulani akan abinda tayi. Yana ganin bai dace ba saboda sun zauna da ita kusan tsawon shekara talatin harda ƙari amma bai taɓa ganin baƙinta irin na wannan karon ba gabaki ɗaya tafice masa akai.


 Babban issue ne yayi rising akan wannan lamarin domin mai martaba kwana yakeyi bai runtsawa yana tunanin yanda zai hukunta Fulani dai dai da laifin ta. Washe gari Ciroma ya sanarwa yana son ganinsa bayan yazo ya shaida masa abunda Fulani tayi, sai da aka sallamo Faruq sannan Familyn mai martaba gabaki ɗaya suka haɗa zama babu wanda ya goyi bayan abunda Fulani tayi dan Ciroma ma Faɗa yayi mata sosai da sosai hakan yasa Fulani tasha kuka tana ganin kamar ba'ayi mata adalci ba an daketa kuma an hanata kuka. Har Hajiya da labari ya isar mata saida takira tayita faɗa domin itama ba ƙaramin so take yiwa Hydar ba. Tun daga wanann lokaci mai martaba yayi dedicating lokacinsa gabaki ɗaya wajan Hydar idan basa tare toh Hydar yana school koshi yana cikin fada. Kamar ranar sati kam har fada yake zuwa da Hydar. Wannan abunda Fulani tayi ya ƙara taso da wata binnanniyar soyayyar Hydar a zuciyar mai martaba sannan kusancinsu ya ƙaru sosai. Tausayinsa mai martaba yakeji na rashin mahaifiyarsa kusa dashi. Tsawon lokaci mai martaba ya ɗaukewa Fulani wuta gabaki ɗaya ya daina shiga harkarta hatta da turakarsa yayi mata iyaka da zuwa. Ta bashi hakuri amma abun ya faskara. Ƴan uwansa ta haɗashi dasu sukazo suma suka bashi hakuri kafin yabarta tacigaba da zuwa sashinsa amma bata samun sakin fuskarsa ko kaɗan.

______


 Akwana atashi babu wuya su Hydar sun fara shirye-shiryen zana jarabawar mock. A wannan lokacin ne kuma Hydar yafara shirin sanarwa Hidaya abunda yake zuciyarsa akoda yaushe tunanin ta wace hanya zai faɗa mata yakeyi don yasan lokacin da yakamata tasani yayi baiso yaja abun da nisa wani yazo yayi masa sakiyar da babu ruwa. Mai martaba ne zaune a Babban palournsa bayan yayi sallar isha'i yana jiran shigowar Hydar domin yasan tunda baizo sunyi sallah tare ba Maghreb da Isha'i ba toh wannan lokacin ne dai-dai lokacin zuwansa. Sallamar Hydar daya jiyo ya faɗada murmushin dake kan fuskarsa. Zama Hydar yayi kusa dashi yayi masa barka da hutawa mai martaba ya amsa cike da fara'a sannan yace.


"Ina dai komai lafiya ko Abbana? Yau gabaki daya najika shiru." Murmushi Hydar yayi yana shafa kansa da alamu akwai abunda yakeson sanarwa Abien nasa.


"Ina jinka maza faɗamin menene?" Waya Hydar yaciro ya ƙarasa kusa da mahaifinsa, wani diamond ring ya nuna masa Irin na hannunsa sai dai wancan na mata ne sannan Diamond ɗin dake jiki fari ne. Nuna masa yayi yace.


"Abie wannan ring ɗin nake so." Kallon ring ɗin Takawa yayi idan dai ba idonsa bane yaje masa hazo ba tabbas wannan ring ɗin na matane, cikin yanayin zolaya yace.


"Abbana wannan ring aina mata ne kodai proposing zakayi dashi?" Murmushi yayi wanda ke gaskata abunda Takawa ya faɗa. Kai Takawa ya jijjiga da yake nuni da yana kambaba girman lamarin yake faɗin.


"Eh lallai Abbana ya girma toh wacece?" Shiru Hydar yayi yaƙi faɗawa Abiensa wacece domin yafiso sai lamarin ya dai-daita kafin ya bayyanawa kowa yaji wacece dan ya tabbata Umminsa da abiensa sai sunfishi murna idan sukaji cewa Hidaya yakeso yakawo musu matsayin surika.


"Toh shikenan tunda bazaka faɗamin ba amma yanzu ka shirya aure kenan?" Ƙasa Hydar yayi da kansa cikin yanayi da yake nuni da yana jin nauyin maganar yace.


"Abbie Ina fatan zaka min?"


"Sosai kuwa Abbana mai zai hana aiko baka ƙarasa haka ba kace min kana son aure zanyi maka bare yanzu ka dawo saurayi this month fa zaka cika 18years kaga kuwa aika isa aure." Cikin jin daɗi Hydar ya miƙe yace.


"Abba wannan zoben ya zamana shine birthday gift ɗina." Dariya Takawa yayi yana faɗin.


"Kai Abbana anya wannan baiyi kaɗan a matsayin birthday gift din kaba?" 


"Kaduba kuɗinsa dai Abie kafin kace yayi kaɗan." Murmushi yayi yana girgiza kai. Yana jin daɗi yaga Hydar ya tambayeshi wani abun domin ba kasafai yake neman wani abun a wajansa ba akan ɗauki tsawon lokaci. 


  Within week ɗin Mai martaba ya yiwa Hydar order din zoben amma ba exact same colour da wanda Hydar ya nuna masa bane domin wannan har yafi kyau, wannan diamond ɗin dake jikinsa black and white ne kuma ga dukkan alamu yafi wancan tsada sannan kuma yafi kamanni dana hannun Hydar. Ba ƙaramin murna Hydar yayi ba dayaga zoben nan, ji yayi kamar ma Hidaya ta amshi soyayyarsa ta gama.


 Suna cikin zaman Exam ɗin mock birthdayn Hydar da Hidaya ya zagayo kamar yanda aka saba duk wanda keda birthday school na haɗa musu ɗan small celebration idan parent zasu ƙara wani abun sai suyi. Wannan karonma haka akayi, tun daga year ɗin da suka cika 3years daga Hydar har Hidaya tare suke celebrating gidansu Hidaya da Hydar gabaki ɗaya cake ɗaya ake musu da rubutun HBD HYDAR & HIDAYA gabaki ɗaya class ɗin kowacce shekara jiran zagayowar Birthday ɗinsu akeyi da zarar lokacin yazo gabaki ɗaya class ɗin murna suke bama suba cikin school ɗin kusan kowa yasan birthdate ɗinsu saboda yanda iyayensu suke Hidima. Suna gama paper ranar mock da suke zanawa aka fara celebrating birthday ɗinsu abun dai sai wanda yagani. Bayan sun kammala sunyi pictures da class mates ɗinsu sannan suka kama hanyar fita daga school din. Sai da ya kaita gida yayi parking sannan yaciro box na zoben ya miƙa mata yana faɗin.


"Happy birthday twinny." Amsa Hidaya tayi da fara'a akan fiskarta tace.


"Twinny birthday gift ɗina ne?" Kai ya jijjiga mata aalmun eh. Buɗewa tayi kyawun zoben ya sanyata faɗin.


"Ma sha Allah twin-bro Birthday gift ɗin yayi kyau Nagode sosai. Nima kazo da yamma zakaga birthday gift ɗinka." Girgiza kai yayi yace.


"No gaskiya nida kaina zan faɗa miki abunda nakeso a gift ɗina"


"Toh menene?" Hidaya ta tambaya.


"Kedai kawai kiyi alƙawari zaki bani idanna tambaya." Murmushi Hidaya tayi tana mai jin daɗin gift ɗin daya bata tace.


"Ai kaima dai kasan babu abunda zaka tambaya har indai ina dashi na hanaka" 


"Nidai kiyi alƙawari" 


"Nayi" Hidaya tafaɗa kanta tsaye batareda wani tunani ba tana ciro zoben. Sanyawa tayi a hannunta ba ƙaramin kyau yayi mata ba shi kansa Hydar kallon hannunta kawai yakeyi domin zoben ya matuƙar amsarta. 


"Kamar dominki akayi zoben twinny yayi miki kyau sosai" Murmushi Hidaya tayi tana kallon hannun nata. Fitowa sukayi su dukansu daga motar ya debo gift da Abienshi ya aiko mata dashi da wanda wasu daga cikin student da sauran teachers suka basu. Taimaka mata yayi suka kai cikin gida ya gaisa da Mami sannan yafito. Mami tayi mamakin zoben diamond data gani a hannun Hidaya kuma tace Hydar ne yabata. Da yazo gidan saida Mami tayi masa faɗa akan ɓarnatar da kuɗi. Cewa Mami Abienshi ne yasiya yabashi yabawa Hidaya jin haka yasa Mami ta daina faɗan.

______


 Akwana atashi babu wuya har su Hydar suka fara rubuta Jarabawarsu ta kammala secondary school. Karatu sosai Hydar da Hidaya sukeyi domin fitowa da sakamako mai kyau. Hydar kuma yagama yanke shawara ta hanyar daya kamata ya sanar mata da abinda yake ransa game da ita. Bayan sun kammala Exam suka fara shirin bikin Grdauation da school take haɗawa duk bayan yaye student ta gayyaci dukkan iyayen yara da sauran manyan baƙi. Graduation din yayi kyau sosai iyayen yara daga ƙasa-ƙasa suka halarci wannan graduation ɗin. Daga Hidaya har Hydar kowannesu ya amshi Award ta fannin dayafi ƙwarewa. Sannan gabaki ɗaya duk wani abunda za'ayiwa Hidaya a gidansu tare akayi mata da Hydar haka shima Hydar Komai Abienshi yayi masa tare yayi musu shida Hidaya. 




 Anyi bikin graduation da 3days aka fara shirin dinner event, Diner ta kasance na students ne kawai, Ranar diner har gida Hydar yazo ya ɗauki Hidaya da ƙannenta suka wuce wajan dinner, daga Hydar har Hidaya ba ƙaramin kyau sukayi ba seat kusa da juna suka zauna suna taɓa hira, Hydar jikinsa sai ɓari yakeyi gabaki ɗaya ana kallonsa za'a fahimci zullumin da yake ciki. Already ya sanarwa Hidaya akwai abunda zai faɗa mata ranar dinner ɗinsu, tun zamansu ta dameshi ya faɗa yace ba yanzu ba. Har saida aka fara gabatar da Award Hydar shine wanda ya karɓi Award na Most Handsome kuma intelligent student, sannan shida Hidaya tare suka amshi award na best friendship. Gabaki ɗaya award ɗin a hannun ƙannen Hidaya suka barsu Hydar da Hidaya suka fita domin sanar mata abunda yakeso ya sanar mata. Jikin motarsa sukaje Hydar ya ciro Gift ya miƙawa Hidaya yana faɗin.


"Congratulation twin-sis Allah ya taimaka yasa angama a sa'a" Amsa tayi tana murmushi haɗeda yimasa godiya tace.


"Thank you twin-bro wai dama wannan kakeso ka faɗamin? Toh wane alƙawarine kasa nayi maka kace zaka tambayi wani abu?" Nisawa Hydar yayi ya fitar da numfashi yazama dole a halin yanzu ya sanar da ita. Kallon fuskarshi tayi tace.


"Lafiya twin-bro?" Kai ya girgiza ya nemi duk wata dauriya da ƙwarin guiwa yace.


"Zuciyar ki nakeso zaki bani? Twinny Zuciyarki nakeso ki bani itace abunda nace kimin alƙawari a matsayin gift ɗina. Ina sonki Twinnny, ina miki irin son da ni kaina bansan irinsa ba, saboda ke ɗin kin kasance d'azuna, yanzuna da kuma gobena in sha Allah. Twine inaso idan natashi a bacci fuskarki ce zata kasance abunda zan fara gani a cikin idanuna." Yana magana gabaki ɗaya muryarshi tana cracking amma ya sake nemo ƙwarin guiwa yacigaba.


"Ban taɓa imagine rayuwa da wata mace bayan keba bazan taɓa iya auran wata bake ba saboda na buɗi ido da soyayyarki. Dan Allah twin-sis ki amshi soyayyata muyi rayuwa cike da sha'awa kamar yanda a halin yanzu muke bawa kowa sha'awa..."


_*TOFA ƙaraƙaƙaƙa yanzu fa aka fara buga wasan. Kundai ji batun da Hydar yazo mata dashi ko? Shin Hidaya zata amince ta karɓi soyayyar Hydar kuwa? Ko bazata amince ba? Yanzu idan Hidaya ta amince burin Hydar zai cika kenan? Yaya kuke ganin auren yara ƴan shekara goma sha? Lallai wannan labari yazo da salo na daban. Ko kuwa burin Hydar bazai cika ba?. Kodai itama Hidaya tana son Hydar ɗin?*_


_Wane irin Wasiyya mahaifin ALIYU UMAR TURAD yabar masa?_


_Kun dai ji batun da Giwar Ciroma tazowa mijinta dashi? Shin Fulani zata samu Cikar burinta kuwa?_


_Ina Ummin Hydar tatafi?_


_*Wannan labarin yana cike da sarƙaƙiya sosai fiye da yanda kukayi zato, domin samun amsoshin wannan tambaya da kuma warware wannan sarƙaƙiya saifa kun shigo daga ciki. 500 Naira kacal zata baku damar samun karanta cikekken wannan labarin. Hajiyata karki bari ayi babu ke domin bamuzo da wasa ba. Kunsan dai bama kawo labarin banza koh? toh karku bari abaku labari.*_



#WATA ALAƘA

#ZEEYY BAWA

#STYLISH BCH 

#YAN TAGWAYE..