{46..}
Nurain was extremely angry at that moment, yana mata wani kallon barazana yace "maimaita abinda kika ce..", ta ja da baya zuciyarta na lugude tace "bazan maimaita din ba, idan baka ji ba kai ka sani...", da sauri ta durƙushe ƙasa ta ajiye cup din ruwan ta damƙe cikinta tana murƙususu, fashewa tayi da kuka tana yarfe hannu tace "na shiga uku cikina", tsuke idanunsa yayi ya matsa daga kusa da ita yana kallonta, after looking at her for few seconds yace "hey get up..", banza tayi dashi ta cigaba da kukanta a hankali, folding hands dinsa yayi yace "ke tashi daga nan...", duk da irin azabar da take ji hakan bai hanata ɗaga kai ta zabga masa harara ba, ya koma kan kujera ya zauna gami da ɗaukan remove ya ƙure volume din Tv don baya son ya cigaba da jin sautin kukanta, saida cikin ya lafa mata bayan kamar minti goma ta tashi tana goge fuskarta, ta ɗauki kofin ruwan ta haura sama tana tafiya a hankali, bayanta yabi da kallo bai san lokacin da wani tsaki ya kufce masa ba, ya tashi ya kashe Tvn gaba ɗaya, kitchen ya shiga yana ƙare masa kallo, ya buɗe store ya duba ko ina, yadda ya ajiye foodstuffs haka ya gansu ba a taɓa ba, carton din Noodles kawai ya gani a bude kuma shima pack ɗaya aka ɗauka, ya fito daga storen ya buɗe fridge shima dai babu abinda aka taɓa, ganin bottle water shima ko ɗaya ba'a taɓa ba murya ƙasan maƙoshi yace "what.. toh wane ruwa take sha..", bottle water ya ɗauka ya rufe fridge din snn ya bar kitchen din, upstairs ya haura zuwa part dinsa, direct bedroom ya shiga ya kunna lights, yayi drawing bedside drawer ya ɗauki wani satchet na drug, tashi yayi ya fito daga bedroom din snn ya fita daga part din, tsaye yayi a corridor yana kallon ƙofar ɗakinta, after standing for few seconds ya haɗe gira ya murɗa handle din ƙofar ya shiga, ƙasa ƙasa yayi sallama wanda ta tsaya iya lips, kwance ya ganta kan carpet ta rufa da duvet har ka, ya ƙarasa cikin ɗakin bayan yabar door a wangale, controlling ɓacin ran dake taso masa yayi, chest of drawers ya bubbuga yace "hey", ta yaye rufar da tayi ta tashi zaune, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kanta, fuskarsa a haɗe ya ƙara four steps towards her, dungurar da bottle water din yayi a gabanta, ta juyo ta kalli ruwan ta ɗaga kai ta kallesa, ya ajiye satchet din drug din yace "take it..", ta haɗe gira tace "bazan sha ba...", one step ya kara getting even more closer to her, tayi sauri ta muskuta ta bada space a tsakaninsu, taɓe baki yayi yace "an gaya miki nayi hakan ne sbd ke, hmm you don't worth it ba dan ke nayi ba, darajar Abba kika ci, tinda an riga an liƙa min ke babu yadda zan iya and now we are living in the same roof, so listen tinda kema kin nace kina son auren nan toh ga fili ga mai doki, zaki zauna anan amma kuma bazaki jamin matsala ba, na fita haƙƙina na ajiye miki foodstuffs, you are free ki shiga kitchen ki dafa abinda za kici idan kinga dama, don babu wanda zai miki gage, secondly you see this room da downstairs palour and kitchen are the only places da kike da damar shiga daga su kar kiyi gigin shiga wani wajen, and if you need anything bance kimin magana ba, ki nemi pen da jotter ki ajiye duk sanda kike buƙatar wani abu ki rubuta ki ajiye kan center table a palour, i will give that idan baki da shi, am done with you...." da haka ya isa gaban mirror ya ɗauki cup din da ta ajiye, girgiza kai yayi yana kallon ruwan kafin ya juyo ya dubeta yace "for your own heath tap water ba shine ruwan sha a nan ba...", ƙofa ya nufa zai fita yaji tace "malam ka gama, dawo ka ɗauki tarkacen da ka zube min a nan who are you to give me drug, kai tinda aka kawoni wnn ƙaddararran gidan na taɓa mka magana ne da farko da kake cewa wani kar na maka mgana, kaga malam nifa ba mara galihu bace da zaka ringa giggillamin sharuɗa sai kace wata ƴarka, ni nan na fika tsanar wnn jarababben auren wllh, da zaka sauwaƙe mna da ka huta..." ta ƙarashe tana murguɗa baki gami da hura siririn hancinta, bai motsa daga inda yake tsaye yana kallonta ba, tana lura da reaction din fuskarsa zuciyarta ta buga da ƙarfi, tayi sauri ta yaye duvet din da ta lulluɓe jikinta ta miƙe tsaye fuskarta a haɗe, lokaci guda ta dubi kanta, kayan bacci ne a jikinta riga da wando, ai kam da sauri ta durƙusa ta yayibi duvet din ta rufe jikinta, kamar me ƙirga takunsa haka ya fara walking towards her, ganin haka yasa ta fara tafiya da baya tana banka masa harara, da gudu ta shige bathroom tana taɗewa da duvet din, tayi sauri ta saka lock tana sauke numfashi, Nurain ya sauke ajiyar zuciya yana bin ƙofar bathroom din da kallo kafin ya juya ya fita daga ɗakin, jingina Hajar tayi da jikin ƙofa, ta hura hanci tace "Wllh ka gayamin ajali sai na gaya mka mutuwa, haka kurum ba zaka danƙaramin magana nayi shiru na kyaleka ba zuciyata ta buga, kai da kanka zaka koma wajen wnda ya ƙulla wnn jarababben auren ya kunce sa ehe, dan billahillazi la'ilaha illa huwa yanxu na fara musguna maka a gidan nan, kai ka isa ka aureni kai asuwa...", ita kaɗai ta ringa huci sai kace wata kububuwa, bayan kamar minti goma ta buɗe ƙofar a hankali, ta gama surveying ɗakin da idanunta kafin ta fito, tsaki tayi taje ta rufe ƙofarta, tasa ƙafa tayi fatali da bottle water da satchet din maganin dake kan carpet, ta sake yin wani tsakin tayi kwanciyarta, tsakar dare ciki yace ba sai kiyi baccin na gani ba, duk da sanyin AC gumi ne ya ringa tsattsafo mata a goshi, ganin alamar dai cikin nan ba lafa mata zaiyi ba ta tashi zaune, a gigice ta fara laluben maganin tana rarrafe, taci sa'a kam ta hango sa a karkashin mirror, ta ƙarasa bakin ƙofa ta ɗauki ruwan da ta wurga can, da sauri ta buɗe bottle din ta ɓalli 2tablets ta afa a baki ta bisa da ruwa, within minutes Allah ya taimaketa cikin ya lafa, ta ringa kallon satchet din maganin kafin ta tashi ta ajiye bisa mirror ta koma ta kwanta. washe gari wajen ƙarfe takwas da rabi Hajar ta fito daga ɗakinta bayan tayi wanka ta shirya, downstairs ta sauka zuwa kitchen, tana buɗe ƙofar kitchen sukay ido huɗu da Nurain da ke making coffee, da sauri ta rufe ƙofar ta haura sama, Nurain ya kashe coffee makern bayan ya gama haɗawa, zai ɗau cup din Coffeen knn wayarsa ta fara vibrate, da asuba ya dakkota daga mota bayan ya dawo masallaci, ya duba yaga babu wani missed call kuma luckily wacca tasa ya tsani wayar bata kira ba kuma bata turo message ba, ya ciro wayar daga pocket yayi picking ganin Dr Marwan, fita yayi daga kitchen din still yana wayar, Nurain yace "alright send it now..", Dr Marwan yace "Okay", Nurain yace "when is it going to start..?", Dr Marwan yace "12noon insha Allah...", Nurain yace "Neh, i will be there before then..", Dr Marwan yace "thank you Dr..", Nurain ya katse wayar ya haura sama ya shiga part dinsa, Laptop dinsa dake jone a charge ya ciro ya zauna yayi switching dinta on, tana gama booting ya buɗe WiFi, it connected automatically with the house router, ai kam sai ga mail daga Dr Marwan, Nurain ya bude mail din yana duba hoton jiki, almost 30mins yana examining picturen, it is a human chest diagram, a zuciyarsa wondering yake who is this patient with a damage lungs. Hajar ta sake sakkowa ƙasa don yunwa take ji sosai, plain Noodles ta dafa ta juye a plate, tinda ta shigo kitchen din take kallon Cup din dake cike da Coffee, bayan ta gama tafasa tea ta juye a cup ta zuba sugar da lipton, har zata fita da shayi da Noodles dinta a hannu sai kuma ta dawo da baya, ta ajiyesu kan kitchen island, store ta shiga ta ɗakko ledar gishiri ta fito, farke ledar tayi ta ɗauki spoon ta matsa wajen Coffeen, ta zuba cokali biyar cikakku na gishiri a Coffeen tana murmushi, ta mayar da gishirin store ta fito tana kakkaɓe hannunta tace "Asha shayii lfy.. counting from today..." kafin ta ɗauki plate din Noodles da kofin shayinta ta fita. Nurain ya shigo kitchen din bayan fitar Hajar da minti biyu, direct Coffeen sa ya ɗauka, ya ringa kallon coffeen ganin kamar ya ƙara yawa, gashi kuma it is not hot but warm, tinda it is warm he can take it, Sipping yayi domin yaji temp din dai a bakinsa, guntse wanda ya kurɓa yayi ya yamutsa fuska, lokaci guda ya isa gaban sink ya zubar ya kunna tap ya wanke bakinsa, har lokacin wani irin taste yake ji a bakinsa wanda ya kasa gane masa, ya ringa kallon Coffeen kafin ya sheƙar dashi ya bar kitchen din, yana zuwa ɗakinsa ya wuce bathroom ya shiga wanke bakinsa da mouth wash har saida yaji taste din ya ragu sosai.
★Tin daga soro Sa'adatu ta fara zabga sallama harta shiga cikin gida, wani kallon hadarin kaji ta watsawa Umma dake zaune kan ƙaramar kujera tana shafa manja jikin gwangwanaye, ɗakin Maama ta shiga, Maimuna dake zaune kan gado ta bita da kallo tace "kin dawo..?", Sa'adatu ta saki baki tana kallon Maimuna kafin ta yakice hijab din da ta zumbula a jikinta, wasu irin matsattsun kaya ne jikinta wanda ya bayyana shape din bom bom dinta da ƙirjinta, ta zauna kusa da Maimuna ta sake ƙare mata kallo tace "ke kuma wa ya mayar dake wnn mummunar halittar, babur ne ya bigeki...?", Maimuna ta shafa goshinta tace "idan na gaya miki Allah yasa ki yarda.., wai fa Mu'azzam ne yamin haka..", Sa'adatu ta hangame baki tace "Mu'azzam din ne ya miki haka...?", Maimuna da takaici ya kuma maƙureta tace "shifa..", Sa'adatu tace "chaɓɗi jamm, wato har dasu kaza acin danƙo, ke me ya haɗaki da wnn jakin har yayi miki haka...?", Maimuna ta kwashe kaf abinda ya faru ta gaya mata, Sa'adatu ta ringa jinjina kai tana hura bubble da chewing gum din bakinta, Maimuna ta kwashe cinya tace "kinga walmukalafatun da Baba yayi min..", Sa'adatu tace "karki yarda wllh tllh, toh aiko shinkafar ɓeran kika zuba iya abinda za a miki knn, karki haƙura wllh..", Maimuna tace "ke ko ce miki akai zan haƙuri zaki yarda ne, dan na rantse da zabbatin Ubangiji bazan yarda ba..", Sa'adatu ta karyar da kai tace "wllh karki haƙura wannan halittar da ya mayar dake ai ya cuce ki, fuska duk ta suntuma, ji fa yadda idanunki suka koma ciki sai kace fuskar biri bukka, kibi dare idan ya kwanta ki rusa masa taɓarya a ka..", Maimuna tace "A'a ni bazan taɓasa da hannuna ba, dafa kuɗina a ƙugu, ƴan daba zan biya su lakaɗa masa duka su sassara banza su jefar a layii", Sa'adatu ta sheƙe da dariya tace "hakan yayi... wai ina Maama da waccan mai kai a tukunyar...?", Maimuna tace "Maama ta fita bansan inda taje ba, Nabilah kuma ta fita auno shinkafa...". babu jimawa Maama ta shigo gidan bayan ta dawo daga gidan Balaraba, ganin Sa'adatu Maama ta yaƙe haƙora tace "Sa'adatun Maama kin dawo...?", Sa'adatu tace "nadawo Maama..", Maama tace "ai kinga haka yafi kin cika alƙawari, kinga gobe ma sai nasan ƙaryar da zan shiryawa malam idan ya tambayeki, ina ƴan albarkar ƙawayen naki kuwa...?", Sa'adatu tace "suna nan kalau Maama sunce ma na gaisheki..", Maama ta washe haƙora tace "Ahh ina amsawa kuwa..", Nabilah ta shigo hannunta riƙe da baƙar leda, kallo daya ta yiwa Sa'adatu ta ɗauke kanta, hijab dinta ta cire zata fita Maama tace "haba Annabilatuwa biki ga ƴar uwarki ba", Nabilah ta juyo tace "Au sannunta toh" da haka ta fice a ɗakin, gawayi ta zuba a kurfotu ta tashi wuta, tana fifita wutar Naseer ya shigo, ta masa sannu da zuwa ya amsa a taƙaice, Maama ta leƙo tace "A'a Nasiru sannu da zuwa..", Naseer ya ajiye doyar da ya shigo da ita ya russuna ya gaisheta, Maama tace "lfy lou, ya wajen aikin..?", yace "Alhmdllh an gode Allah..", bai tambayi Baba ba sbd yasan dai a wnn lokacin Baba ya fita aiki, ganin haka yasa Nabilah tace "Yaya Baba yana nan fa..", yace "toh" ya shiga ɗakin Baban da Sallama, Maama ta zabgawa Nabilah wata harara tace "naga ranar da wnn munafikin canjin naki zai ɗore..", bayan Naseer sun gaisa da Baba yace "Baba ko dai jikin ne..?", Baba ya numfasa yace "Nasiru duk ranar da kuka wayi gari bani toh mahaifiyarku ce sila..", Naseer ya kasa cewa komai tsabar ydda mgnar Baba ta dakesa, can dai yace "Ayi haƙuri Baba, Allah ya huci zuciyarku..", Baba yace "haƙuri ai ya zama dole tinda ta gama zubamin virus ta haifeku...", Naseer dai kawai haƙuri ya ringa basa duk da cewa bai san me ya faru ba.
★Kamar yadda Nurain yace kafin 12noon zai iso hospital, 11:40 ya isa hospital din, yana shiga office dinsa yasa Haleema ta kira masa his team members, har zai wuce sai kuma ya dawo yace "exclude A Nurse, call Nurse Amina instead..", Haleema tace "yess sir", ta ɗauki landline ta shiga kiran members din, babu jimawa kam All of them suka hallara a office din, Nurse Amina ce kawai ba tazo ba, briefing dinsu Nurain yayi akan surgeryn da zasu shiga, daga nan suka fita to get ready, Nurain na wanke hannunsa kafin ya shiga surgery room din Khaleel ya da already dressed up in surgeon gown da nose mask a fuskarsa amma bai rufe hancin ba ya iso wajen yace "Boss everyone is here banda Nurse Amina, kuma i informed her tace tana zuwa..", Nurain na cigaba da wanke hannunsa yace "lets wait for her since the surgery is not yet started...", Khaleel yace "sure..", Nurain na gama wanke hands daman already ya sanya surgical Scrub. Surgery room din ya shiga, wani Nurse dake riƙe da surgeon gown ya ƙaraso kusa da shi helping him to wear the gown, Nurain ya saka nose mask da hand gloves kafin ya isa position dinsa na head of the surgery ya tsaya, patient din daman tintini aka masa anesthesia. Ruqayyah na zaune Nurse station duk abin duniya ya isheta, tinda tazo babu wani aikin arziƙi da tayi kawai safa da marwa take tsakanin Nurse station da Office din Nurain, taje office din yafi sau biyar saita tarar baizo ba, Nurse Amina ce ta shigo station din in a hurry tace "please Ruqayyah ki kulamin da ward C ina dawowa..", Ruqayyah tace "ina zaki haka..?", Nurse Amina ta dafe goshinta tace "Dr Uthman ne yake nemana a surgery room..", miƙewa Ruqayyah tayi tace "surgery zaiyi knn..?", Nurse Amina tace "eh..", wani irin ɗaci Ruqayyah taji ya taso mata daga zuciya, she is part of the team toh me yasa ake neman wata Nurse din bayan gata, Nurse Amina tace "Please Rukky..", Ruqayyah ta girgiza kai tace "A'a gaskiya bazan kula miki da ward ba saidai ke ki zauna in shiga surgeryn", Nurse Amina tace "ai kwa da na fi son hakan ma, nagode sosai..", Ruqayyah tace "don't mention" da haka ta bar station din walking fast, surgery gown ta ɗora kan uniform dinta ta saka nose mask da gloves kafin ta shiga surgery room din kanta a ƙasa, with respect ta ɗan russuna tace "sorry Dr..", Khaleel yace "come closer..", ta ƙarasa ciki tana satan kallon Nurain, surgery tray ta dauka ta tsaya position dinta, ta ɗauki Scalpel ta miƙawa Nurain, da haka aka fara surgeryn, kawai aikinsa yake cike da nutsuwa yayinda Ruqayyah ta kafa masa idanu tamkar zata cinyesa, wani sa'in ma sai yace ta basa instrument snn take basa sbd rashin nutsuwa, a haka dai har suka gama surgeryn, bayan an fita da patient din sauran doctors din ma sun fita Nurain ya cire hands gloves yayi disposing, sauke nose mask din fuskarsa yayi ya wuce zai bar room din, Ruqayyah tace "Dr...", ya juyo yace "yess Nurse Amina...", idonta yayi rau rau ta kai hannu ta zame nose mask dinta....✍️