BA ITA BA CE

Page 02

by @nanameera08

*BA ITA BA CE!...💖💖*


   *MIKIYA WRITERS ASSO...*

     

    *Follow my account both arewabooks nd Wattpad*


*nanameera 08* _arewabooks_

*@Nanameera08* _wattpad_.


  *Nanameera*




# *SQUAD 2024*.



```Page 02```


   *Rugar Jama'are*


Durƙushe take gabansa ta zuba masa idanu tana kallonsa ƙaramar yarinya ce ba zata shige 4 to 5yrs ba tana sanye da kayan Fulani Blue colour as usual gashinta dake zube a gefenta wanda aka kalbaceshi irin manyan kalbar nan guda biyu yabi da kallon a hankali kuma ya sake lumshe idanunsa shi kaɗai yasan irin tsananin azabar da yake ji, kamar zatayi kuka take kallon mahaifin nata cikin wata siririyar murya mai Matuƙar zaƙi da ɗaukan hankali take cewa"Papina sannu zaka samu sauƙi kaji sannu dan Allah" bata rufe bakinta ba aka ɗaga labulen wanda ya kasance asabari ne suka shigo da sauri kuma cikin ɗaga murya Dada ta ce"Baba kura zo ki dubashi aradu mun higa uku ya Gani sannu Allah zai tashi kafaɗunki" da sauri wanda take cewa Baba kuran ya ƙaraso yana zuwa ya zube a gabansa hannunsa ya kai ya taɓa wuyansa sosai yaji zafi a jikinsa hakan yasa duk hankalinsa ya ƙara tashi a matuƙar razane kuma ya miƙe ya fice daga cikin bukkar, da kallo suka bisa kafin Dada ta kalleta da idanunta wanda suka sauya launi ta ce"kai Muhaira ɗebo ruwa a bashi yasha" da sauri ƴar ƙaramar yarinya ta miƙe ta ɗauki ɗan ƙaramin jallan ruwan tayi waje saidai kafin ta fita ta juya a hankali tana kallon fuskarsa ga mamakinta sai taga shima ita yake kallo wani tattausan murmushi ya yi mata dukda yanda bakinsa yake a bushe wanda ke nuni da asalin ciwon da yake ciki a hankali itama ta mayar masa da nata kyakkyawan murmushi ya ilahy wani irin sihirtaccen kyau ƴar yarinya ta yi tamkar wata ƴar aljanu haka ubangiji ya yi mata kyau kwayar idonta blue colour ce irin mai hasken nan sai wani irin sheƙi suke saɓanin na sauran mutane da suka kasance baƙaƙe. Da hannunsa ya yi mata alama da tazo hakan yasa ta ajiye jallan ta ƙara sa gabansa ɗan ƙaramin hannunta ya kama a hankali kuma ya buɗe bakinsa wanda yawo yake shirin ƙafewa daga cikinsa ya ce"Baddon Papi!" da sauri ta ɗaga kanta tana kallonsa wasu zafafan hawayene suka shiga gangarowa kan kuncinsa da sauri ta saka ɗaya hannun nata tana goge masa kwaɓe fuska ta yi cikeda shagwaɓa ta ce"Papi kadaina kuka kaji dan Allahhhh" shafa fuskarta ya yi hannunsa na kakkarwa ya gyaɗa mata kai dan bakinsa ya yi masa nauyi, Bani kura ne ya shigo bukkar shida wani mutum a bayansa da alama kuma mai magani ne. Bayan sun zauna ya kalli Papi sai kuma ya kalli Muhaira dake gefensa ya ce"Baddo maza jeki gidana ki karɓon ƙwarya" miƙewa Muhaira tayi ta fice tana tafiya da a sauri a hankali kuma take waiwayen bukkar tasu.


   Tafiya kawai take da sauri da sauri dan ko wasa bata tsaya ba haka har ta baro rugar tasu, kasancewar su a cikin gari suke ya sanya ta É—an yi tafiya mai yawa kafin ta Æ™araso Æ™ofar gidan, "Wundo!! Wundo!! Wundo!!" turo baki Muhaira ta yi bata ce komai ba har sannan, da sauri ya'acca ta kalleta cikin É“acin rai ta ce"ke kam Muhaira bakida mutunci ko?, banda iskanci ki shigowa mutane gida babu sallama sannan kuma ji ana waye kinyi tsif abinki ko?" sosai yarinyar ta tsorata da tsawar da tayi mata bakinta na rawa ta ce"unn...uhhhmm...dan...daman Bani kura ne ya ce a bashi Æ™warya" tsaki ya'acca ta yi ta ce"shine zaki tsaya kina mana shashanci" sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba amma duk a tsorace take, shiga É—aki ta yi ta É—auko Æ™waryar ta mika mata, da sauri Muhaira ta karÉ“a sannan ta juya da gudu tayi waje, tsaki ta yi tana kallonta ta ce"shashasha kawai".




    Da sauri ta shigo cikin bukkar hannunta riÆ™e da Æ™waryar saidai me?, babu Bani kura wanda ya aikata haka zalika babu mai maganin da aka É—auko sai Dada wacce ke zaune gefensa banda kuka babu abinda take yayinda Papi aka rufeshi da wani tsohon bargon, da sauri ta Æ™arasa wajensa tsugunawa tayi gaban Dada tana cewa"Dadana Papi ya yi bacci?" kallonta Dada ta yi amma bata ce mata komai, sosai idanunta sukayi jajur ko ba'a faÉ—a maka ba kasan ba Æ™aramin kuka tasha ba, kuka ta fashe dashi tana murza idanunta da kallo kawai Dada ta bita dan ita tama gagara magana ganin Dada bata kulata ba har sannan yasa ta kwanta a wajen tana birgima, Bani kura ne ya shigo shida masu maza a bayansa suna zuwa kai tsaye inda Papi ke shimfiÉ—e suka nufa ganin yanda take kuka yasa Bani kura ya ce"Aishatu ke dawa?" daga yanayin muryarsa zaki fahimci irin damuwar da take tare dashi, da sauri Muhaira ta tashi jin ya kira sunanta ta Æ™arasa wajensa har Sannan kuma kuka take ta ce"Bani koba Dada bace" janta ya yi jikinsa ya rashe mata hawayen fuskarta sannan ya ce "to kiyi haÆ™uri zauna anan" shiru tayi ta zauna a gefensa tana kallon bargon da suka rufe Papi. 


 

   Æ˜arasawa suka yi bayan sun yaye bargon suka kamashi suka fita daga cikin bukkar duk wannan abun da ake banda kallo babu abinda Muhaira ke yi dan ita bata gane ba mene ne abinda ya faru ba, Dada kuwa Æ™ara sautin kukanta ta yi jikinta na wani irin kyarma, tashi Muhaira ta yi ta koma kusada ita ta zauna amma bata ce komai ba sai kallon mahaifiyar tata take, ita kuwa Dada tunanin yadda rayuwarsu zaka kasance take, tunanin rayuwar Muhaira take, zuciyarta cike take da tausayin tilon Æ´ar tata, tabbas Æ™addara ta riga fata domin Papi ya tafi ya barsu a lokacin da suka fi bukatarsa. Tunawa da wannan yasa ta sake rushewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya ita kuwa Muhaira bata fahimtar komai Æ™anÆ™antar shekarunta da kuma Æ™arancin shekarunta sune suka yi tasiri wajen gazawa kwakwalwarta ta fahimtar da ita duk a tunaninta Papi É—in wani waje zasu kaishi wanda zasu dawo mata dashi. Amma saidai abinda bata sani ba shine Papinta ya tafi kenan tafiyarda duk wanda ya yi ta baya taÉ“a dawowa,tun tana tambayar Dada ina Papinta har ta fahimci cewa Papinta ya bar duniyar a hankali mintuna ke komawa awanni awanni ke komawa kwanaki kwanaki ke komawa sattituka sukuma suke juyewa izuwa wattani wattani kuma ke juyewa izuwa shekaru, tafiya ta tafi a Æ™alla Papi zai yi shekaru uku da barinsa duniya zuwa wannan lokacin kuma Muhaira tanada shekaru 8 a duniya.



    Wani irin sanyin ake mai ratsa É“argon da jijiya sanyinne irin wanda ke haddasa cuttukan musamman Asthma, pneumonia, sickler dama wasu ciwukan, safiyar ranar juma'a ce gabaÉ—aya rugar Jama'are tayi tsit kowa yana cikin bukkarsa da iyalansa, tsugunne take gaban wata tukunya wacce aka É—orata akan dutsuna guda uku wanda suka zama sune murhun da take girkin akai sosai take haÉ—e jikinta yayinda numfashinta ke wani irin fuzga ita kaÉ—ai tasan azabar da take ji amma kuma burinta bai shige ta gama damawa Dada kokon ba. Cikin mintuna Æ™adan ta kammala ta juyeshi cikin wani tsohon kofi sannan ta tashi da gudunt ta shige bukkar, tana nan yanda ta barta a kwance idanunta a rufe suke amma ba bacci take ba ajiye kofin hannunta ta yi sannan ta shiga kamata tana faÉ—in" Dada tashi, tashi kinji na dama miki kokon tashi kisha sai kisha magani" dakyar Dada ta buÉ—e idanunta ta kama hannun Muhaira ta miÆ™e daga kwancen É—ora kan Dadar tayi akan Æ™irjinta dukda nauyin da tayi mata amma ko kaÉ—an hakan bai dameta haka ta É—auki kofin kunun ta kai mata bakinta, girgiza kai Dada ta yi tana riÆ™e hannunta ta ce"A'a Muhaira bazan iya sha ba akwai abinda nakeson na faÉ—a miki tabbas wannan cutar tawa bata tashi ba ce saida... wani irin jan numfashi ta yi tana saukeshi a hankali runtse idanunta tayi hawaye suka shiga rige-rigen sakkowa kan kuncinta alama ta yi mata data bata kunnenta a hankali Muhaira ta kara kunnen nata kusada fuskar mahaifiyartata dan taji me zata faÉ—a mata. Above 5mins tana yi mata magana zuwa lokacin kuma banda hawaye babu abinda Muhaira ke yi gaba É—aya tunaninta ya tsaya cak batada wata sauran dabara zuwa sannan kuma bata iya fahimtar abinda mahaifiyar tata ke faÉ—a mata. Shirun da taji Dada tayi yasa ta kalleta wata irin razananniyar Æ™ara ta fasa wacce ta yi daidai da shigowar Falmata cikin bukkar da sauri ta Æ™araso tana kallonsu duka ganin yanda Muhaira ta Æ™amÆ™ame Dadan har sannan kuma kuka take yi kallo É—aya Falmata ta yi mata tasan cewa Ubangiji ya karÉ“i abarsa, ikon Allah kenan babu yanda mutum ya iya kamar yanda Papi ya mutu haka yanzu itama Dada tabi bayansa


"Dadata! dan Allah dan Annabi ki tashi karki mutu ki barni banida kowa Dadaaaa...ki taimaka ki tashi Dada ko kinfi son nayi kuka har ƙarshen rayuwata?, banida kowa Dada kema kuma bakida kowa Papina ya tafi har yau bai dawo ba kema shine zaki bisa??? kenan duk baku sona? meyasa Dada?, me nayi muku?, ina zani yanzu? wane zai kula dani Dadaaaaa..." maganar ta tsaye a maƙoshinta sakamakon wani irin nauyi da zuciyarta tayi da gudu ta miƙe ta fita daga bukkar saboda wani irin amai daya tawo mata saidai me???? madadin amai na abinci ko kuma na ruwa wani irin guda-gudan jini ne ya shiga fitowa daga bakinta sai kuma ta faɗi nan ƙasa sumammiya.

     

    Allah sarki rayuwa tabbas babu abinda ke É—orewa sai ikon Allah cikin É—an lokaci Æ™alilan Muhaira tarasa iyayenta guda biyu wanda hakan shine mafarin Æ™addararta, tabbas labarin rayuwarta akwai taÉ“a zuciya, musamman daya kasance tanada Æ™arancin shekaru Hakazalika kuma babu wani wanda zata kama ta ce wannan danginta ne kasancewar iyayen nata Fulanin tashi ne, tarasa gatanta tun tana jaririya sannan kuma ta sake rasa waÉ—anda suka maye mata gurbin wannan gatan data rasa ya zatayi??dawa zata rayu?? wace irin Æ™addara ce ke bibiyar rayuwarta??...


*17 years*.



*Maitama district, Abuja*

    *No:113*.


 *Mai Zamani pov.*


Wani zazzafan numfashi ya sauke bayan ya saki curtain ɗin, a hankali cikin tafiyarsa mai nuni da isa ya ƙaraso gefen kujerar dake gaban gadon ya zauna sanye yake da wata Polo T-shirt white colour sai kuma wani Cargon Three-quater black colour a jikinsa ba wani fari bane can haka zalika kuma ba baƙi bane yana dai da haskensa dai-dai misali, ɗan ƙaramin tsaki yaja sannan ya buɗe system ɗin gabansa ya shiga dubawa. Duba da irin yanda yake kallon system ɗin zaka fahimci tabbas wani abu mai matuƙar muhimmanci yake gabatarwa, turo ƙofar ɗakin tayi bakinta ɗauke da sallama a ciki ya amsata sannan ta ƙaraso gabansa zama tayi gefensa tana sanye cikin wani material black colour mai adon flower pink ɗinkin doguwar riga A-shape mug ɗin gabanta ta ajiye masa gefen table ɗin gabansa ta cigaba da kallon abinda yake, above tens minutes sannan ya kammala ya rufe system ɗin sai a sannan ya ɗago yana kallonta fara ce tass kuma asalin kyakkyawa dan ko ba'a faɗa maka ba kasan ita ɗin ba ta kasance cikin ƙabilar Hausawa ba ganin irin kallon da yake mata ya sanya ta sunkuyar da idanunta ƙasa tana wasa da fingers ɗinta masu ɗauke da zanen flower wacce tayi matuƙar amsar farar fatarta taɓe baki ya yi sannan ya ɗauki mug ɗin data ajiye a hankali kuma yakai tea ɗin bakinsa wani runtse ido ya yi saboda wani irin zaƙi da yaji har cikin kansa da sauri ya ajiye mug ɗin yana mata wani hargitsatsen kallo ya ce "Ma'eesha I'm play with you?" kallonsa ta yi fuska a kwaɓe ta ce" A'a yaya I'm sorry wlh banson sugar ya yi yawa ba I'm so sorry" kallonta ya yi from head to toe sannan ya yi tsaki ya tashi bai tsaya cigaba da jin abinda take faɗi ba ya ɗauki wayarsa ƙirar iphone 14pro max ya yi waje. Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe ƙirjinta sanin halin yayan nata sai kuma ta miƙe itama tabi bayansa.



    A nutse take taka stairs É—in benen har ta sakko gaba É—aya, ya rabbi wani irin haÉ—aÉ—É—en parlon ne irin mai tafiya da imanin mutum É—in nan komai na cikinsa golden colour ne tun daga kan kujeru, curtains, carpet, center table even bulb da suke parlon golden colour suke bayarwa banda sanyin A.C babu abinda ka keji a parlon sai kuma wani irin daddaÉ—an Æ™amshin da yake fita daga kowace kusurwa ta parlon ko ba'a faÉ—a maka ba kasan wannan parlon bai yi kamada na Æ™ananan mutane ba ko kuma basu ji da Æ™aramin arziÆ™i parlon ne irin wanda koda a cikin Villa yake sai ance ya haÉ—u iya haÉ—uwa, parlon ne na irin manyan nan wanda suka jiÆ™u da manyan kuÉ—aÉ—e, a hankali ta Æ™araso cikin parlon inda ta hangin iyayen nata. Zaune yake kan kujera Three seater yana sanye da wata dakakkiyar shadda Madam gezner blue black É—inkin jamfa da babbar riga idanunsa maÆ™ale da wani farin tabarau yayinda yake kallon jaridar dake hannunsa da alama kuma karantawa yake duba da yanda ya bada full attention É—insa a wajen magidancin mutum ne dan aÆ™alla zai kai irin 60yrs É—in nan amma idan har kayi duba da yanayi na siffarsa zaka iya cewa bai fi 46yrs saboda kwarjini da kuma hutu wanda ya zauna masa. Major General Ibrahim Tijjani mai Zamani kenan wanda ke riÆ™eda muÆ™amin shugabannin sojoji na Æ™asa kuma sanannen É—an kasuwa mai tashen arziÆ™i mamallakin Companyn mai Zamani corture indai magana kake ta kuÉ—i to tabbas M.G Ibrahim Æ™arshene sannan kuma uwa uba ya kasance mutum mai taimakon na Æ™asa dashi wannan shine dalilin daya sanya yake da mabiya daga kowacce fuska. Da sauri ta zauna gefensa tana shagwaÉ“e fuska ta ce" Father narhhhh!!" murmushi É—auke a fuskarsa yake kallon tilon Æ´ar tasa kallo mai nuna zallar so da Æ™aunar da yake mata shafa kanta ya yi cikin kamilalliyar muryarsa ya ce" Shalelen Father what's wrong uhn" turo baki gaba tayi ta ce" Father ko ba yaya Farooq bane" da sauri Farooq wanda yake zaune kujerar dake opposite tasu ya É—ago yana kallonta amma bai ce komai ba, murmushi Father ya yi sanin halin rigimarta ya ce"keda yayan naki ne kuma yanzu?, To kiyi haÆ™uri bazai sake ba ya tuba" taÉ“e baki ta yi sannan ta ce"Father kace masa ya kaini saloon É—in" dafe kansa ya yi yana zare glasses É—in idanunsa ya ce" ohho!! Shalelen Father rigima ko?, Ki tambayeshi da kansa idan yaga zai rakaki fine idan kuma yanada wasu uzurin sai ki tafi da guards zasu jiraki" girgiza kai tayi ta ce"nooo! nasan ma zai rakani" kallon Farooq ta yi wanda yake kallonsu tun É—azu ta ce"yaya zaka rakani ko?" da sauri ya gyaÉ—a mata kai ko babu komai ya samu damar da zai gasa mata aya a hannu, murmushi É—auke a fuskarta ta kalli Father ta ce"yawwa Father kaji ko ya ce zai rakani" numfasawa Father ya yi ya jinjina mata kai sannan ya miÆ™e yana riÆ™e da hannunta ya ce"na tayaki murna amma karku daÉ—e zan fita byee" gyaÉ—a masa kai ta yi tana murmushinta mai kyau ta ce"ok Allah ya tsare hanya Father narh" kissing goshinta ya yi sannan ya yi waje.



# *BA ITA BA CE*

# *Human trafficking*

# *Destiny*

# *love*.

# *SQUAD 2024*


# *Nanameera ce!*.