Mrs HAMMAD

Arwa

by @youngmuslimahh

Arwa yarinya me jiji da kai takasance kyakkayawa kamar ita tayi kanta ga ilimi ga kuma kudi iyayenta Allah ya wadata su dashi

Arwa ba kowa takeson shiga harkarshi ba bata hada hanya da talaka haka kuma batada son mutane, macece me son kai da son dukiya.


shi kuma Hammad namiji ne Dan gayu me hankali, ga ilimi ga kuma tarbiya ya fito daga gidan tarbiyya da sanin yakamata

ranar litinin salma da imran sunje airport don tarar hammad daga dawowar sa daga china ya kammala karatunshi na digiri se mahaifinshi Albanian hafiz ya nemi yadawo domin fara gudanar da kasuwanci a garin abuja.


salma ce ta hango hammad yasaka tabaran sa da shigar sa ta qananan kaya wannan tace kalli chan ya imran

imran ya juyo yace ina ? Kalli chan wancan yaya ne

oyoyo oyoyo suka tashi cikin murna yaya sannu da xuwa sukayi hugging din juna suna farincikin sake haduwarsu

hammad ya kalli Salma yace naga kin girma yana me taba kanta murmushi tayi tace yaya na ma rame haka

budan bakin imran yace kaji ta kina cinye mana Abincin kaganta nan ita ke cinye kayan gidan kasan daddy dama yafisonta dani nifa kamar baqo nake a gidan gwanda ma mummy.

“kai imran fadi gaskia” Hammad ya fada yana murmushi



Allah Yaya hm danma bakaga basma ba hm! Kai dai muje yaya akwai labari!