Page 21
by @billysfari
TS 21.
Cike da girmamawa da kuma mutuntawa mm ya sinne kai yana ƙoƙarin gaishe sa, ɓuɗar bakin sa keda wuya ya daka masa wata uwar tsawa tare da dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu,
"Look bana buƙatar gaisuwar ka, baka ji mena faɗa bane?"
"Yi haƙuri Abba, ni masoyin 'yar ka Janan ne.." tun kafin ya ƙarasa Abba ya yayi saurin runtse idanuwa alamun kalmar cin zafin kalmar, haka ya ci gaba da sauraren mm zuciyarsa na tafarfasa akan Janan data kawo masa mutum maƙasƙanci irin wannan da har yake iya tsayawa gabansa don tsarin idanuwa yana faɗa masa cewa shi masoyin 'yar sa ne, "Sunana Muhammad Muhriz, ni ɗane awajen mahaifina dake da ƙaramin ƙarfi a ƙauyen caranci, amma yanzu ALLAH yayi masa rasuwa, nazo gidan nan ne bisa dalilin soyayyar da nake yiwa 'yar ka Janan.." cike da ɓacin rai Abba yayi saurin ɗaga masa hannu yana faɗin,
"Kai wane irin bagida je ne haka, tambaya ɗaya zuwa uku nayi maka amma don rashin hankali ka zauna kana bani labarin rasuwar mahaifin ka, wannan ba shine damuwata ba, yana da rai ko ba ya da rai buƙata ta kawai inji in kana da arziƙin iya zamowa surukin cikin gidan nan, saboda haka tunda baka da shi kada ka kuskura na sake ganin ka da 'yatah, haka ma gidan nan kar in ƙara ganin ƙafar ka aciki, wannan gargaɗi ne, idan kuma ka ƙi zan sa a fahimtar da kai ta ƙarfi da yaji, don haka maza ka ficemun daga gida yanzun nan" ya ƙare maganar yana nuna masa hanyar fita,
"A'a Abba kada kayi haka don ALLAH, wlh ina son sa ko sau ɗaya ne ka tsaya ka saurare shi.."
"Will you keep quite my dear ko sai nazo na tattaka ki a wajen?" Abba ya faɗa da ƙarfi haɗe da yowa kanta, wata irin zabura tayi haɗe da fashewa da kuka tana bubbuga ƙafa, "pls dad wlh shine rayuwata, ina son sa bazan taɓa iya rabuwa da shi ba"
"Haka ne Abba, don ALLAH kayi haƙuri ka amince da soyayyar mu, son gaskiya nake yimata kuma zan tashi tsaye wajen nema iya ƙarfina don na kula maka da ita" mm ya ƙare zancen haɗe da duƙawa a gaban sa, wani irin mugun kallo ya bishi dashi yana ganin gaba ɗaya ma mm ya rena masa da wayo, banda laifin da yayi na shigowa rayuwar 'yar sa da matsayinsu bai zo ɗaya ba, ya ƙara da laifin saka 'yar sa na ƙoƙarin ja in ja dashi abunda ko a mafarki bata taɓa gwada yi masa ba, juyawa yayi ga guard ɗin sa da ke tsaitsaye fuskar nan ba imani ya yiwa babban su signal da idanuwa, kan kace me ya dira gaban mm tare da finciko wuyan rigar sa, Janan na gani haka tayo wajen mahaifinta,
"A'a Abba don ALLAH kada kasa ayi masa komai, kace su ƙyalesa don ALLAH Abba" ta ƙare zancen tare da zubewa gaban sa tana kuka ganin sun fara kai masa duka,
"Leave this place Janan before I slap you"
"Pls Abba.."
"I said leave" ya faɗa da ƙarfi, ganin irin dukan da suke yiwa mm da shi gaba ɗaya ma hankalin sa baya kansu ya shagala da kallon Janan dake kuka tana roƙon mahaifin nata yasa cikin rashin tsoro ta miƙe haɗe da yowa kan guard ɗin dake dukan sa tana tutturesu haɗe da cewa,
"Ku dena dukan sa nace" in ta ture wannan ta ture wancan haka tayi ta biyar su tana turesu haɗe da yi masa garkuwa ta tsaya agabansa tare da haɗe hannayen ta waje ɗaya tana riƙon su,
"Ku ƙyalesa haka na roƙeku don ALLAH, ku ƙyalesa zai tafi"
Tsananin takaici yasa Abba yi masu tafi dake nuni da su ƙyalesa haka tare da wucewa cikin gida, kai tsaye sashen sa ya wuce ya dinga aafa da marwa a cikin falon nasa yana tunanin wane mataki ya kamata ya ɗaukarwa Janan kafin ta jawo masa abun kunya akan waccan talakan da bai ma san cikakken asalin sa ba,
Wata shawara ce ta faɗo masa a rai da sauri ya ciro wayarsa ya kira wani aminin sa ambassador Hussaini Salam dake zaune a ƙasar chardi, sun jima suna waya da shi kafin daga ƙarshe suyi sallama da shi yana faɗin,
"Ok ba damuwa sai ya iso"
Wannan wayar ita ta ɗan kwantar masa da hankali saboda yasan kaso tamanin cikin ɗari na damuwar sa ya gama magance ta,
Ita kuwa Janan mayafinta ta cire ta shige gogewa mm jini a gefen baki da suka fasa masa tana kuka,
"Kayi haƙuri hubbin ruh, wannan kaɗan kenan daga cikin abinda mahaifina ke iya yi maka akan soyayyar mu, shiyasa kaga na shiga damuwa ɗazu, kar ka sake zuwa nan mm ka bari kawai muci gaba da haɗuwar mu makaran ta don ALLAH"
Riƙe mayafin yayi yana kallon cikin idanuwan ta haɗe da sakar mata dariya har yana riƙe ciki ganin yanda duk tabi ta ruɗe, kafin yace,
"Meye haka Janan!?, Kar dai ace har kin karaya akan wannan ɗan dukan da aka yi mani?" Mayafin ya sa ya share mata hawayen dake kwance a fuskarta tana ƙare masa kallon cike da mamaki tamkar ba shi ne aka daka ba ya ci gaba da cewa, "share hawayen ki ranki shi daɗe tawan!, Ai in dai akan wannan ɗan dukan da aka yi mani ne bazan dena zuwa ganin ki ba aduk lokacin dana buƙaci hakan matuƙar za a barni na gane kin, ban da abunki ma ai nan ya kamata naci gaba da zuwa muna ganin juna bawai a makaranta ba matuƙar na amshi sunan cikakken masoyi, buri na kawai kada ki bari faruwar hakan ya raunata soyayyar mu, kuma kada ki bari ya ɓata maki rai ko kaɗan don shi zai sa ƙwarin guiwar da nake dashi akan ki ya ragu kin ji ko Janany tawan" ya ƙare zancen yana kashe mata ido ɗaya, ɗan turo leɓen ta na ƙasa tayi tana son sake fashewa da kuka ya girgiza mata kai,
"Kar kiyi hakan bana so, fitar wuɗan nan tsadaddin hawayen naki yafi azabtar da zuciyata fiye da dukan da aka yimun, saboda haka ki dena kin ji ko?"
Murmushin dole ta ƙaƙaro haɗe da cewa,
"Kai maƙura ne mm, ina matuƙar ƙaunar ka"
"Kema haka ranki shi daɗe, bari naje kafin ƙattin can su wai wayo ni, don kuwa ba kaɗan suka iya mazga da sambaɗa ba" ya ƙare zancen yana zazzaro idanuwa haɗe da kallon gefe da gefe kamar mai tsoron dawowar tasu da gaske, dariya Janan ta kwashe da ita ganin yanda yayi tana faɗin,
"Ashe dai zaka ji tsoron su shine ka ƙi guduwa ɗazu"
"Ai indai kina akusa dani, ba wani tsoron su da zan ji don ko sanin suna wajen bazan yi ba, amma kinga idan kika tafi na bawa ƙafafuwan nan nawa iska ai sai dai su kamoni a bakin titi, shima ɗin idan na tsaya sun riskeni a wajen" sosai ta riƙa yin dariya har dimple ɗin ta na loɓawa, ganin ta ɗan saki akan ɗazu da ta shiga damuwa ya sa mm cewa,
"To Madam bari ni naje gida na samu na gasa jiki na, wannan soyayyar taki mai tsananin tsada ce na ciyo Janany" dariyar ta koma yi haɗe da cewa,
"Sannu, zan biya duka wannan da kyakkyawan TUKUICIN SO agare ka"
"Kin tabbata hakan?"
"Sosai ma kuwa, ka ƙara haƙuri pls kuma don ALLAH ka yafewa mahaifina"
"Ki manta da wannan, ai nima mahaifina ne ko kuwa?" Wata irin kima da ƙaunarsa ta ji sun ƙara shiga ranta kafin ta kashe idanuwa tana kallon sa haɗe da shagwaɓe murya, tace
"Ok to shikenan nagode, bye bye, ALLAH ya kai ka lafiya mintin zuciyata, hasken idaniyata, muradin raina"
"Iyyeeeee, duka wuɗan nan suna yen wani kaɗai? Ko dai na sake dawowa gobe na ƙara shan duka ko zan samu wasu irin su?"
"Laaa...ba sai kayi hakan ba ai, in dai irin sune, to kasa a zuciyarka yanzu ka fara saurarar su daga bakin Jananyn ka"
"ALLAH kuwa?, To godiya nake yi nima nurul albi na, ko zaki raka ni ki taya ni gasa jiki na?" Ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya, da sauri tasa hannayen ta ta rufe fuskar ta cike da jin kunya ta bar wajen aguje, shi kuwa dariya yayi sannan ya juya ya fice daga gidan yana jin shi yanzu ma ya fara son Janan a zuciyar sa, Forward ever, backward never....
Daidai lokacin Nihal ita kuma ta fito ganin yanda mahaifin nasu ya shigo rai a ɓace, tana yimasa sannu amma ko jinta baiyi ba wanda hakan ya sa tabi bayan sa zuwa sashen nasa, maganar da taji yana yi da ambassador Hussaini Salam ita tasa ta fitowa don ganin halin da saurayin na Nihal da Abba ya cewa aminin nasa yasa anyi masa duka yake ciki, don kuwa ji tayi ya bata matuƙar tausayi, kusan karo suka yi da ita kasan cewar ta zo aguje, da sauri Nihal ta riƙe mata ka faɗu tana regen mm dake ƙoƙarin fita da bayan sa kawai take iya hangowa.
*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU 👏😭*