Rental marriage 1
by @hanaady
*NIKAAH*
*Marriage for Rent*
*By*
*HANAADY*
*Rahama Aminu Bala*
Follow me on Whatpad
Rahama 000
*WhatsApp*
*****
HE HAD THE COURAGE
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?
*Marubuciyar*
*BAHAAR*
*And now* *NIKAAH(Rental* *Marriage).......*
page 1*
A kowane lokaci na kanyi tunanin shin akwai macen da tafini sa'a, cikin yanayi mai nuna matuk'ar damuwa take maganar
K'ara hugging nata yayi tareda cewa nima haka but for now please ki cigaba da addu'a duk tsanani yana tareda sau'ki
Murmushi Sa'adatu tayi ka tuna lokacin da muka fara haduwa a Camp
Murmushi ya mayar mata sannan yace yes how can i forget our first meeting
Jare jikinta tayi daga jikin sa tareda d'aura hannun sa saman katon cikin ta cikin dauriya irin tata tace ina son babyn nan fiye da rayuwa ta
please my man ka kula da babyn nan bayan raina
Dan b'ata rai yayi please Habibty you should stop irin wa y'annan maganganun
in sha Allah zamu rayu da babynmu lafiya
Hmm I have to dole nayi irin maganganun nan zasuyi amfani nan gaba
Why kike sakawa kanki mutuwa cikin karaya Ramadan yayi maganar
Murmushin k'arfin hali Sa'adatu tayi case d'in haihuwa ta mai wahala ne kana gani Nigeria sun tsorata da case d'ina
sune suka turo mu k'asar India
Kana tunanin zan rayu kuwa
Shuru yayi wannan kara yarasa mai zai fad'a mata
Hannuwan sa ta ri'ke please My man don't give up on love
Please open your heart to love again
Hawaye yake sosai wannan karan abun yayi masa yawa baya son yana nuna mata shima he give up on her
Case d'inta is very complicated su kansu Doctors d'in sun fad'a masa they are not sure if Sa'adatu za tayi surviving .
Shugowar Nurse ne yasa yayi saurin tashi daga saman bed d'in
Kallon sa Sa'ada tayi tareda cewa i will always love you
Please don't forget to give your next wife my dairy
Please kayi k'okarin bama ko wacece zaka aura akwai alots of sirrika da nake son sharing to her
Kad'a kansa yayi tareda cewa No Habibty babu wata wacce zan aura ke kadaice kuma dake zan spending my whole life so please ki daina fad'a mun haka
Cikin tausaya ma masoyan Nurse d'in tace it's time
Lumshe idanuwan ta tayi tana mai zubar hawaye
A hankali ya fara dosar k'ofar fita
Kiran sunansa tayi
Juyowa yayi tareda matsawa kusada ita yes Habbty
Cikin yanayin jin jiki tace please if you remarry treat her nice , don't be rude on her ,treat her with respect ,nishi tayi kadan sannan tace please try your best to love her
Please can you do that for me
Shuru yayi na wasu y'an sec please ta kuma furtawa
A hankali ya furta i promise to treat her nice but ,a hankali ya furta i can't promise you to love again
You are the only one i love ,you are my heartbeat my choice,my happiness,my life, my everything
I don't think if zan iya son wata mace bayan ke so please don't force me
Murmushin k'arfin hali tayi sannan tace look at me ,
K'asa yayi da kansa kaman wanda yaje wajen surukkan sa
Please ta furta
D'ago kansa yayi Yana mai kallon ta cikin yanayin rashin lafiya tace i want to you to be Happy koda bana tare da kai, Koda bana duniyar nan so please don't say no to me
Cikin rauni ya ri'ke hannunta tareda cewa baza ki mutu ba zamu rayu da juna please just keep on praying in sha Allah surgery naki will be successful
Please sir it's time Nurse d'in ta kuma fad'a
Sakin hannun Sa'ada yayi tareda fara tafiya
Cikin yanayin rashin lafiya Sa'ada tace please ka turo munsu Dada
Kai ya gyada mata domin baya iya magana .
Bayan fitar sa tana mai zubar da hawaye ta furta i love you ,i will always love you
Ganin fitowar sa daga d'akin da take yasa su duka yo kansa ji yayi baya gani sosai jiri na d'e'barsa kaman zai fad'i cikin zafin nama Khalid yayi saurin ri'ke yayan sa
Zaunar dashi sukayi suna mai lallashin sa akan ya yarda da Allah ne ke komai in sha Allah Sa'adatu will make it
A hankali ya fad'a musu cewa tayi requesting ganin su
Ganin lokacin Surgery nata yayi yasa sukayi saurin shiga
Cikin fara'a irin ta Sa'ada take yi musu magana akan kada su damu in sha Allah watarana sai labari
Su duka saida suka zubda hawaye tuni sun san condition nata ,sun san cewa ba dole bane tayi surviving
Ko wanen su da hawaye ya bar d'akin
Kiran sunan Dada tayi dawowa Dada tayi tareda cewa kina buk'atar wani abu ne??
Ri'ke hannun Dada tayi tareda cewa please Dada bayan raina kiyi k'okarin saka shi yayi aure i know him zaya iya spending rayuwar babu aure if aka saka masa ido
Cikin tausaya mata Dada tace Dan Allah Sa'adatu ki daina irin wannan maganar in sha Allah zaki tashi ai ciwo ba mutuwa bane
Gilgiza kant tayi tareda cewa please Dada kiyi mun alkairin saka shi yayi aure
Please Dada ta kuma maimaita maganar kaman zatayi kuka
Cikin tashin hankali Dada tace in sha Allah nayi miki alkawari
A matsayina na wacce ta haifi Mahaifin sa zanyi iya k'okarina domin cika wasiyyar ki
Cikin wasa irin Wanda suka saba Dada tace Amma if kika tashi zanyi k'okarin cika alkawarina still
Kinga kuwa da anga suna sai musha biki
Dariya Sa'adatu ta k'yalkyale da ita
Haba Dada ayi haka
Anyi ma an gama cewar Dada
Ganin Nurse ta kuma shugowar yasa Dada cewa barina wuce kafun tace na cika naci ,kowa ya fita saini
Murmushi Sa'ada tayi she will her family wato familyn mijinta masu sonta da 'kaunarta duk da ita d'in ba kowa bace .
**************************************
Lokacin da Likitocin zasu fito yayi har ya gota but still shuru sosai hankalin su yayi matuk'ar tashi ,an sami 'karin kaman 30 minutes sannan suka fito kallo d'aya zaka musu ka gane akwai problem domin su duka basa tareda kuzari
Cikin kyarma sukayi kansu domin sanin halinda ake ciki
Cikin damuwa babban likitan yace we are sorry but we couldn't save her
Tashin hankali ba'a saka masa rana Allah sarki Sa'ada lokaci yayi Allah ya jikanta da Rahama
Zubewa k'asa yayi ,kansa sukayi but baya numfash taimakon gaggawa aka bashi
cikin dauriya Momy wato Mahaifiyar tace babyn tana raye
Eh tana raye but tana buk'atar wasu treatment kafun ku ganta cewar wani Likita
____________________________
______________
Firgigi ya farka daga wahalallen barcin da yake, mafarkin yau na daban ne domin gaba d'aya scenarios d'in mutuwar tane suka dawo masa ri'ke kansa yayi da yake masa ciwo bayan kaman 10 minutes, tashi tayi tareda shigewa toilet ruwa ya watsa ya fito
Bakin gado ya zauna naya mai tuna mafarkin da ya zame masa jiki it has been long da rasuwar Sa'adatun sa
but a kullun jin mutuwar ta sabuwa yake, he misses her
Hawaye ne masu zafi ke gangarowa daga fuskar sa ,jin ana goge masa hawayen ne yasa ya bud'e eyes d'insa
Ganin ta a tsaye yasa yayi k'okarin 'kir'kiro murmushi
Daddy ta furta murmushi ya kuma yi mata tareda cewa Sa'ada
Ri'ke masa hannu tayi sannan tace Daddy you should pray for her tafi bu'katar prayers kan amata kuka
Kumatun ta yaja a kullun k'ara wayau kike ,alamun tunani yayi sannan yace sometimes na kanyi mamakin wayau irin naki but ba abun mamaki bane tunda kullun kina li'ke da tsohuwa ai dole kiyi wayau .
Dariya Sa'ada ta k'yalkyale da ita .
Kallon pictures d'in iyayen tayi a hankali ta furta i missed you Momy , how i wish na sanki nayi rayuwa dake
Ganin Sa'ada ta fara shiga damuwa yasa yace kinfi kama da Momynki
Murmushi tayi sannan tace nafi kama da kai Daddy saidai ita Momyna farace sosai kai d'in kuma chocolate ne ,ni kuma hasken ta na d'ebo shine banbancin mu
Fira suke sosai ,duk wanda ya gansu yasan tabbas akwai sha'kuwa mai tsanani tsakanin su
____________________________
Dada , da fatan lafiya naga 3 missed calls d'inki Hajiya Sadiya ta fad'a tana mai sunkuyar da kai , remote ne a hannun wacce aka Kira da Dada channels take canzawa abun ta kota d'aga kai ta kalli Hajiya
Bayan kaman minti goma Dada tayi kyaran murya cikin izza irin tata tace a ina aka tsaya akan dawowar wannan gantalalliyar d'iyar kawar taki
Cikin ladabi Hajiya Sadiya tace wallahi Dada still babu wani feedback akan dawowar ta k'asar nan
Yanzu Sadiya farinciki , da kwanciyar hankalin 'kawar ki ya fiye miki na d'anda kika haifa
Yanzu a haka zaita zama cikin kewar Sa'ada if yana da mata damuwar ba zata masa yawa ba but ke kin za'bi farantawa kawarki rai
Cikin ladabi Hajiya Sadiya tace Dada yarinyar tana matuk'ar son Ramadan tun kafun yasan Sa'ada, babu yanda banyi dashi ba akan ya aure ta yak'i ,ashe wacce yake son ba mai dorewa bace
Wai shin ke bakya damuwa kan farincikin sa ,wane irin karatu take da haryanzu baya da niyyar 'karewa
Yanzu fa shekarar Sa'ada takwas da mutuwa ace har yanzu yaron nan yana cikin 'kunci
Tun bayan rasuwar Sa'adatu nake k'okari akan yaronnan yayi aure,duk yun'kurin da nayi sai kinbi kin lalata abun , na kasa gane dalilin daya sa bakya son ya auri kowa sai d'iyar Mariya.
Ki saurare ni da kyau Sadiya na baki kwana 8 duk abunda za kiyi kiyi Ramadan yayi aure cikin kwana 8
Zaro idanuwa tayi tareda cewa haba Dada kwana 8 yayi kad'an ,gyara zama Dada tayi sannan tace ok if a wurinki yayi kad'an toh ni a wurina bai ba
A yau idan naga dama zan samo masa mata but ina son fita shari'a ke d'in mahaifiyar da ce so bana son tauye Miki hak'ki
ta k'are nan da kwana 8 if kika kasa samo masa mata ni zanyi
Kije kiyi shawara da mijinki ,koda yake nasan halinki abiyar shawarar ki zaki nema
Cikin nuna ba haka bane Hajiya Sadiya tace ai Dada bazan fad'a Mata ba
Tsaki Dada tayi sannan tace ai Hajiya Mariya ita ke juya ki ,kullun gaki nan kaman mai hankali Amma babu shi
Kina barin wata can tana controlling rayuwar ki ,idan yayi auren if d'iyar kawar taki ta dawo kin sa ya aure ta tunda dama shi d'in d'ane mai biyayya
Tashe Hajiya Sadiya tayi tana mai sa'kawa da warwarewa
Da kallo Dada ta bita tana mamakin hali irin na Hajiya Sadiya Sam ita bata abun kanta kawayen tane masu juyata
________________________________
__________________________________
Ai kuwa Koda ta koma d'aki Hajiya Mariya ta Kira , kwashe duk abunda ya faru tayi ta fad'a mata
cikin tashin hankali Hajiya Mariya tace yanzu tsohuwar nan abunda zata mana kenan , nace yaushe ita zata dawo ashe bata ma san yaushe d'iyar kawar tata zata dawo k'asar ba
Cikin yanayi nasu na y'an duniya Hajiya Mariya tace very soon zata dawo yanzu dai wace shawara gareki ??
Wallahi ba nida abun cewa yanzu dai abunda za'ayi ki nemo mana mafita duk abunda kika zo dashi zan amince Hajiya Sadiya ta fad'a cikin fara'a
Bayan sun gama wayar tsaki Hajiya Mariya tayi sannan ta kalli wata mata yanzu dillaliya samo mana mafita
Cikin yanayi irin na tsaffin y'an duniya dillaliya tace Hajiya ai dole ayi mun bayani domin bansan inda kuka dosa ba
Kyara zama Hajiya Mariya tayi maganar auren Alia da yaron wajen Hajiya Sadiya ne
Oh wai har yanzu kina kan bakan ki akan auren nan
Murmushin mugunta Hajiya Mariya tayi
Auren Alia da yaron Sadiya shine abu na farko dana saka a gaba yanzu ,kin san zamu huta duk lokacin da Alia ta hauri Ramadan
Ai ba banza ba kika ga na li'ke mata auren kawai nakeso ayi but wannan tsohuwar tana son kawo mana cikas
Yanzu ita Alia yaushe ne dawowar ta ??
Ajiyar zuciya Hajiya Mariya tayi sannan tace nan da 9 month
Yanzu menene abunyi Dillaliya kin wani dameni da tambayoyi just ki kawo mana mafita
Gaskiya Hajiya wannan abun sai anyi tunani akai
Nidai a ganina ko zaku bari tsohuwar ta masa auren daga bisa ni sai ita uwar yaron tasa a saki matar
Murmushin takaici Hajiya Mariya tayi duk lokacin da muka bari tsohuwar nan ta kawo mata da kanta
babu maganar Sadiya tasa asake ta domin yanda kika ga ina juya Sadiya toh haka uwar mijin ta ke juya ta kasancewar ta yaya ce a wajen Mahaifiyar Sadiya ,wannan ba mafita bace
Hajiya ki bani kwana 2 in sha Allah zan zo da mafita
________________________________________________________
Nace ina zamu sami kuka mai kyau Hajiya Sadiya ke tambayar Hajiya Mariya wacce suke zaune falon Hajiya Sadiya suna fira
cikin mamaki Hajiya
Mariya tace yo shan kukan dole ne kice a dole sai kin nemo kuka a yau d'innan
Wallahi kin gani aikin Dada ne tasa rigima adole miyar kuka take son sha gashi an siyo ta kasuwa tace bata buk'atar ta wai suna mata had'i
Bari na kira Dillaliya maybe a samu a unguwar su
Bayan kaman 5 minutes ta kira Hajiya Sadiya tareda fad'a mata cewa an sami kuka yanzu haka zata shugo ita da d'iyar ta su kawo
__________________________________________________________
Daidai Katafaren gidan mai napep ya ajiye su ,Dallalilaya na gaba suna binta a baya ,baki sake suke kallon gidan aljannar duniya Aisha ta fad'a ita kuwa Karime bata ce 'kala ba
Ku jirani anan bance kuyi abunda zai ja mana magana ba kallon Karima tayi sannan tace ba kaman ke Karime ki kama kanki domin nan dai ba unguwar mu bace da kika raina kowa
Bayan shigar Dallalilaya kallon Aisha Karime tayi tareda cewa gaskiya dole na kashe kwarkwatar idona zauna ke ki jirata kinga kaman haihuwar ki tayi
Dariya Aisha tayi inda sabo ta saba ganin drama tsakanin Abiyar zaman Mahaifiyar ta da kuma Aminiyar ta
Wata hanya tabi hango wani ke'bataccen wuri tayi can nesa da ita ganin shuke shuke ne da'alama wuri garden ne dole naje na yagi rabona .
Wurin ta dosa direct swimming pool ne a wajen mai girman gaske .
Zaune ta hango shi yana mai latsa system kirar Apple .
Wata beautiful cat ta hango daf dashi kuma daf da ruwa kaman zata fad'a cikin ruwan
ganin haka yasa tayi sauri domin taimaka mata su duka cikin ruwan suka afka ita da kuliyar
Bata iya ruwa ba sama take tana k'asa
but still bai daina abunda yake ba .
Ganin abunda ke faru daga isowar ta yasa tace yanzu tsakani da Allah rashin imanin ka harya kai haka Ramadan
murtuke fuska yayi sannan yace Dada yanzu menene laifi na
A gaban ka rai zai fita baka iya kawo d'auki
Cikin swimming pool d'in ya fad'a ,d'auko ta yayi kaman wanda ya d'auko kayan wanki su duka d'igar ruwa suke ri'ke take da Kuliyar ita kanta Kuliyar ta fita hayyacin ta
Memokon ya ajiye ta ,sakin ta yayi tim kaman ya saki abunda ba'aso a k'asa
Dafe mazaunan ta tayi tareda binsa da mugun kallon
Cikin tsiwa da rashin kunya irin ta Karima tace Allah ya isa anyi girman banza
Fasa d'aukar laptop d'insa yayi cikin zafin nama ya juyo tareda cewa what me kika ce ??
Cikin rashin tsoro tace nace anyi girman banza
Ganin yayo kanta gadan gadan yasa Dada tace k'arya ta fad'a
Anyi mutum sai rashin mutunci yanzu inda yarinyar nan ta mutu me zamu fad'a ma hukuma
Kallon Karima Ramadan yayi sannan yace Dada ta mutu for all i care
Rufe mun baki marar ta ido ko ubanka ya isa ya fad'a mun magana balanta Kai
Kallon Dada Karima tayi sannan tace cikin tsiwa nima ceton rai ya kawo ne Yana ganin Kuliyar nan zata fad'a ruwa Amma ko motsi baiyi ba
Salati Dada tayi yanzu Ramadan kana ganin Kuliya ta ,ta fad'a. ruwa
Kai a yanzu baka damu da rayuwar kowa ba .
Baka 'ki kowa ya mutu ba tunda Sa'ada ta mutu
to bari kaji rayuwa cikin duniya yanzu muka fara saidai bakin ciki ya kashe ka
Gaba yayi abunsa domin yasan rigimar Dada
Kallon Karima Dada tayi tareda cewa y'ammata daga ina
Cikin ladabi Karime tace ai kuka muka zo kawowa to shine fa na hango Kuliyar zata fad'a ruwa nace barina taimaka mata
Dariya Dada tayi tareda cewa yanzu muje ciki ki canza kaya kinji d'iyar kirki
Da mamaki Aisha ke kallon Karime lafiya wannan kallo haka?
Kaman yau kika fara ganina cikin mamaki still Aisha tace ina kika sami kaya meya faru wai
Labartama Aisha abunda ya faru tayi kinga wallahi kayan marmari na hango
su naje tsinkowa ashe guy d'in nan na zaune a geden d'in toh anan fa na hango Kuliyar zata fad'a ruwa shine taje taimako
Suna cikin tattaunawa Dalliya ta fito muje tace dasu kallon Karime tayi sannan tace wallahi tunda muka taho tare dake nasan sai kin d'auko mana magana
Allah yaso wannan karon abun kirki kika jawo kud'i ta fiddo y'an dubu dubu mi'kama Karima tayi anshi wannan dubu shabiyar ce Dada tace abaki sauran sai mu raba dina Aisha tunda ta dalilinmu kika shugo digan
Ganin Dillaliya zata raina mata wayau yasa tace bari naje wajen tsohuwar naji nawa tace abani ,ganin dagaske Karime take yasa Dillaliya cewa anshi matsiyaciya
Dubu biyar ta cika mata wai suda Aisha saisu raba dubu goma kasancewar kud'in dubu talatinne
Haka suka taho cikin Napep suna harar juna ita dai Aisha bata ce komai ba ,domin Anty Dillaliya da Karime sun saba takon sa'ka
Koda akace ana buk'atar kuka gidan su Karime aka siyota ganin zasu je kai kukar ne Dalliya tasa rigima adole da ita za'a tafi tunda ita tayi musu hanya ,tasan dole za'a sami wani abu
_____________________________
______________
Mama ina ta sallama, hankali ki na wani wuri Karima ta fad'a tana mai zama kusada Mama cikin damuwa Mama tace wallahi Karime abubu sunyi mun yawa a kullun ina cikin tunanin halinda muke ciki.
kud'in kukar ta mi'kawa Mama ,cikin farinci Mama ta anshi kud'in ..
Yanzu ki huta sai ki anso mana garin rogo
Zun'buro baki tayi gaskiya Mama yau baza muci gari ba
Baki sake Mama ke binta da kallo ,yanzu Karime abun naki harya Kai haka .
Kud'in da Dada ta bata ta fiddo, cikin mamaki Mama tace ina kika sami kud'i haka, feeling proud Karime ta kwashe yanda akayi ta fad'a wa Mama ,ansar kud'in Mama tayi tana mai 'kirgawa cikin farinci
Fizge kud'in yayi cikin tashin hankali su duka suka bishi da kallo shikenan sun sara su
Cikin rashin mutunci irin na Baban Jimmai yace ina aka sami kud'i masu yawa haka ??
Badai karuwanci kika fara tura d'iyar taki ba ,figit Maman Jummai ta fito daga d'akin ta mai fad'in hayaniyar me nake ji
Kud'in ya nuna mata tareda cewa ai Hadiza ta fara tura Karame karuwanci dariya Maman Jummai tayi sannan tace gado girman d'a
Karime kasa jure rashin mutuncin su Maman Jammai tayi mi'kewa tayi tareda cewa eh karuwanci nayi na samo su aidai hak'ki nane to abani abuna .
Da gudu Baban Jimmai yayi kanta zai doke ta , d'aki ta shige tareda sayo k'ofa.
Bud'e k'ofar nice cewar Mama wacce keta buga k'ofar d'aki
Bud'e k'ofar tayi, Karime yaushe zaki daina yiwa Maman Jummai rashin kunya
Mama kina gani kud'in mu ya anshe har tana sakawa mutane baki .
Ya isa haka daga yau kada naji kada na gani duk da nasan ba bari zakiyi ba .
Bayan fatar Mama turo baki tayi tana gunguni .
Safa da marwa Hajiya Mariya take ,takai ta komo kaman wacce aka fad'a ma sako mutuwa na hanyar zuwa gidan ta
Hajiya ki kwantar da hankalin ki duk kin bi kin tada hankalin ki cewar Samira
Nace ko naje gidan Dillaliyar na dubo lafiya
Aaa Samira dole naje da kaina domin wannan sako yafi k'arfin ki
Mayafi taja tareda ficewa tana sababi
Driver neke jan motar ita kuwa Hajiya Mariya sai faman kiran number Dillaliya take a akashe
Nesa da gidan Dillaliya yayi parking lafiya Hajiya Mariya ta tambaye shi ??
Cikin ladabi yace Hajiya cuncoson mutane yayi yawa a layin nasu bazan iya shiga da motar nan ba
Cikin Masifa Hjy Mariya tace maza yi parking na wuce da 'kafa ta .
Kusan hanyar da mutun zaya wuce wahala take duba da yanayin yawan mutanen da suka taru akan layin
Coller rigar sa ta ri'ke tana ta kumfan baki adole saiya biya ta kud'in ta , domin dama halinsa ne ,duk lokacin da yara suka zo shagon sa siyayya hakance ke faruwa
Domin shagonsa k'ofa biyu ne dashi, fita yake ta k'ofar ciki ,ya dawo bakin k'ofar waje ya nuna wa mutum bashi bane
wani lokacin ma kayan jikinsa yake zuwa gida ya canza ,yau Allah yasa ya fad'a hannun Karime .
Dakyal Hjy Mariya ta sami hanyar wucewa .
Bayan yaji wuya dole ya fiddo kud'in ta ya bata aikuwa mutanen layin ehu suka hau yi masa suna tsokanar sa .
Gidan su kawar ta Aisha ta wuce tana ta sababi .
Koda ta shiga gidan d'akin Dillaliya ta fad'a babu sallama
Wai Karime yaushe zakiyi hankali
Dakata Anty Dillaliya ba wanna ya kawo ni ba garin kwaki zaki bani na d'ari biyu .
Kallon Karime Hjy Mariya tayi tana mamaki ga mace har mace amma babu nutsuwa tattare da ita .
Magana kanta kaman wani saurayi ke magana , dressing d'in ta ta kalla jeans ne jikin ta sai hijab ,a tsaye take amma hannun ta na cikin aljihu yanda maza keyi .
Bayan fitar Karime Hjy Mariya tace na jiki shuru gashi a yau saura kwan biyu.
Wallahi kuwa Hjy nayi iya tunanin da zanyi amma mafita d'aya ce rak na iya samu
Cikin 'kosawa da zaman d'akin Dillaliya Hjy Mariya tace wace mafita ce
Kewa nayi ko zaki duba ta wajenki ,ki sami wata yarinya ki bata kud'i yanda za'a ayi auren da ita ,kinga da Alia ta dawo zata iya neman saki wajen yaron cikin sauki .
Shuru Hjy Mariya tayi tana mai tunani akan maganar Dillaliya.
Banida wacce zani kawo cewar Hjy kallon Dillaliya tayi tareda cewa kinsan irin wannan aikin sai matsiya ta kodai yarinyar da ta fita nan zata iya saina bata ko nawa take so .
Cikin sar'kewar harshe Dillaliya tace wa Karime aaa Hjy wannan ba abu bane mai yuyuwa ba, baki san Karime ba wallahi bazata yadda ba.
With confidence Hjy Mariya tace ita kadai zata iya kinsan meyasa .
Aaaaa sai kin fad'a Dillaliya ta fad'a tana mai sauraron abunda Hjy zata ce .
Na lura yarinyar kafi d'aya ce ma'ana bata damu da iyayi na mata ba ,
Dariya Dillaliya tayi tareda cewa gaskiya Hjy kina da brain mai kyau kaman kau kin sani Karime ai mata sunyi kudu ita kuma tayi arewa .
Amma maganar gaskiya Karime bazata ta'ba yadda da wannan offer taki ba .
Shuru Hjy tayi na wasu dan lokuta , mahaifiyar tafa itama haka , mahaifiyar ta bata da san abun duniya .
Mahaifin tafa dariya Dillaliya tayi sannan tace Baban Jimmai wannan babu abunda baya iyayi dan kud'i
Murmushi Hjy Mariya tayi sannan tace
Turo shi muji nawa zaya bamu auren d'iyar sa ,na d'an lokaci.
Koda Dillaliya ta sami Baban Jimmai da wannan zance ai bai gusa ba Saida yace ta kaishi gidan Hjy Mariya haka kuma akayi .
Ciniki sukayi akan Million biyar ,cash haka aka bama Baban Jimmai yaso tayi masa transfer wasu a bank ta'ki
A cewarta irin wannan business d'in ba'a yinsa da bank sabida tsaro
Takarda aka bama Baban Jimmai yayu signing domin shaida .
Basu san wainar da ake toyawa ba saiji Mama tayi Baban Jimmai na yawa da mutane wai gobe daurin auren Karime.
Koda ta tunkare shi da maganar baiji tsoron komai ba ya kwashe yadda sukayi da Hjy Mariya ya fad'a mata.
Tayi kuka kaman ranta zai fita amma shi ko ajikin sa .
Ana gobe biki Karime bata son wainar a ake toyawa ba tuni kawar ta Aisha taji labari amma ganin Karime bata mata maganar ba yada ta kama bakin ta tayi shuru .
Lokacin da Hjy Sadiya tazo ma Dada da maganar an sami mata ,Dada ta nuna dole akaita gidansu yarinyar jin Hjy Sadiya ta fad'a mata cewa yarinyar da tazo kawo mata kuka ce yasa Dada tayi farinciki da hakan domin dama yarinyar ta shiga ranta .
A bangaren Ramadan kuwa koda Abba yayi masa magana baiyi gaddama ba domin tuni sunyi magana da Momyn sa .
Bayan haka shi baya da matsala da auren da suke shirin yi masa ,domin baya da lokacin b'ata akan wata .
_____
Tana sheshshekar kuka tace yanzu Mama tsanar da Baba yake mun harta kai ya siyar dani, ya siyar da mutuncin d'iyar sa akan kud'i
Kiyi hak'uri Karime kowane d'an Adam da tashi kaddarar
Kiyi k'okarin tallafar taki da hannu biyu biyu .
Ki share hawayen ki in sha Allah hakan alkairi ne a gare ki
Kallon Karime Sa'adatu tayi tareda cewa Anty Karime kiyi hak'uri kinji
Rungume autar su tayi tana mai zubar hawaye.
Ki tashi ki shirya anjima zasu tafi dake gidan mijinki .
Su Maman Jammai ne y'an Kai Amarya ,baza idanuwan sukaita yi suna Kallon abun duniya
Part d'in Dada aka kaita sosai Dada tayi musu tarbar arziki .
Basu wani dad'e ba Maman Jummai ta matsa su tafi gida domin tuni ranta yayi mugun b'aci
Koda suka isa gida masifa Maman Jummai taita yiwa Baban Jummai wai Yana sane ya Karime gidan hutu ai da ta sani da Jummai suka bada .
Cikin lallashi yace haba Maman Jummai na fad'a miki auren na wata tara ne nayi miki bayani ya kamata ace a halin yanzu kin fahimta.
Kallon Mama tayi bushewa da dariya Mama Jummai tayi sannan tace wallahi kuwa Baban Jummai na manta ashe aro aka bada ta Hhhhhhh anayi muna shan kallo ana bari muna jin haushi.
Kanta a k'asa Dada tace ki cire mayafin ki sha iska.
Cikin jin nauyin tsohuwar ta d'an janye mayafin ta
Murmushi Dada tayi tareda cewa barka da zuwa cikin ahalina murmushi Karime tayi cikin jin nauyin Dada.
Fira Dada ke mata sosai firar ta rage mata damuwar ta .
Misalin k'arfe 10: 30 na dare Dada ta kira wayar da cikin yanayin bacci ya d'aga
Sannu bacci ma kake ,cikin yanayin bacci yace Dada what do want cikin daren nan??
Minti biyar na baka ka bayyana a bangaren na koni nazo na iske ka shasha .
Sababi Dada take ,a d'aura maka aure a kawo maka sabuwar mata Amma kaje kana kwasar bacci .
Ita dai Karime bata ce komai ba .
Tunanin sharudd'an da Hjy Mariya ta kafa mata take, tace ba make up gidan mijinta tace ,ba gaishe dashi, bayi masa dariya ballantana murmushi
wasu abubuwan ma bata iya tuna su
D'an sirirn tsaki tayi cikin ranta domin ita dama abubuwan da Hjy ta lissafo basa gaban ta .
Mu had'u next page
*Rahama Aminu Bala......* *HANAADY*