NIKAAH (Marriage for rent)

Rental marriage 2

by @hanaady



*NIKAAH* 

    *Marriage for Rent* 


           *By* 

       *HANAADY* 

    *Rahama Aminu Bala




 *WhatsApp* 

 ***** 


HE HAD THE COURAGE 

TO REMARRY.

WILL HE FIND THE COURAGE TO

LOVE AGAIN?



Marubuciyar

BAHAAR paid Book

And now NIKAAH(Rental Marriage)....... Free book





 *Page 2* 


__bakin k'ofar falon Dada ya toge ,kiran wayar Dada yayi,ta fito kad'ai ya iya furtawa katse kiran yayi Yana mai k'ara tamke fuska.


Kallon ta Dada tayi tareda cewa ki fita yana waje yana jiranki ,Allah ya baku zaman lafiya da zuria ta gari ,kanta a k'asa ta nufi hanyar fita .

Kallo d'aya yayi mata , d'auke kansa yayi tareda yin gaba abun sa, bata cikin hayyacin ta domin duk yau bata samu ta sakawa cikin ta abinci ba shiyasa bata da k'arfin maida magana ko masifa .

Bin bayan sa tayi jiki mace ,uffan baice mata illa inda take tunanin bedroom d'insa ne ya shige abunsa batayi mamakin komoi ba domin tuni tayi tsammanin fuskantar rashin mutunci fiyeda hakan .

Ganin tsayuwa bazata ficce taba yasa ta taka zuwa k'ofar bedroom d'insa.

K'ofar a bud'e take domin tana turawa ta bud'e kwance ta hango shi ya juya ma ganin ta baya sabida haka ita haryanzu baza tace ga kamannin sa, tabbas ta gane gidan da suka zo kawo kuka ne.


 kwana kin baya , bawai gidan ta gane ba aaa ganin part d'in Dada da haduwa da ita shine dalilin da yasa ta yanke wannan hukuncin .

D'aga kanta keda wuya ,gabanta mugun faduwa yayi ganin yanda bedroom d'insa yake manne da pictures d'insa shida wata kya'kyawar mata ,sunyi kyau sosai ,sai yanzu ta gane inda aka dosa ,sai yanzu ta gane waye aka aura mata .

Tamabayar data zo mata a zuciya itace shin yasan yanda aurensu ya kasance da sanin sa aka bama Baban Jummai ma'kudan kud'i ya siyar musu da ita ,shin wacece wannan matar wacce tazo har gidansu ta kafa mata sharudd'a akan shi,bata da mai bata anso shin tambayoyin ahalin yanzu ,amma tasha alwashin gano duk wasu amsoshin tambayoyin .

K'ara kallon pictures d'insu tayi , kallo d'aya zaka ma pictures d'in kagane tsantsar kauna tsakanin mamallakan hotunan .

Sunyi mata kyau matuk'a murmushi ne ya su'buce mata ,tana mugun son soyayya kawai bata da lokacine sabida yanayin rayuwa, bata tashi cikin sakin jiki da farinci a gidan Mahaifin taba ,tunda ta tashi ita dai a takure suke ita da mahaifiyar ta da sauran 'kannenta .

Ita tunda ta mallaki hankalin kanta nauyi ya hau kanta ,domin a kullun Mama cikin neman na kanta take wato bata zama babu sana'ar hannu wanda aikin Karime ne sayarda koma menene.

Shiyasa tuni jikinta ya saba da aikin wahala .

Ajiyar zuciya tayi tana mai kallon kayan jikin ta atamfar roba ce Mama ta d'inka mata ana gobe bikin ta, d'an satar kallon sa tayi still yana kwance ko motsawa baiyi ba , d'akin tabi da kallo aljannar duniya ta furta cikin ranta komai na d'akin farine da ratsin blue ,tsarin d'akin yayi mata kyau matuk'a , pictures d'insu ta D'an Kara satar kallon cikin ranta take mamakin toh ina matar tasa.

Wane irin dalili garesu da har zasu yi renting aure .

Cikin zuciyar ta take furta Allah shine ya jarabe tada Mahaifi mai mugun san kud'i lokutta da dama haka yake kwace dukkan kud'in da tayi wurin talla .


Ganin yanda kayan suka takura mata yasa ta fara baza idanuwa domin gano toilet dan ta d'an watsa ruwa 


Wardrobe d'insa ta bud'e abun sai Wanda ya gani, kaya kala kala shishshrye gwanin ban sha'awa.


Ganin babu irin kayan da take nema yasa ta rufe , d'aya bangaren ta bud'e shima haka, bangaren karshe ta duba annan ne taga jerin riguna na maza masu gajeren hannu , murmushi tayi domin abun ya burge ta , wato shi komai nasa a nitse yake kaman wata mace ita kanta bata da lokacin tsayawa ta gyara kayanta haka kusan ma ita ba d'abi'ar ta bace shirya kaya , anyhow take ajiye kayanta wani lokacin haka Mama zata tayi mata fad'a tana mai cewa watarana gidan wani zaki ba kowane namiji bane ke lamuntar mace mai irin wannan dabi'ar ta rashin kimtsa kaya da sakin su ko ina.


Toilet ta shiga domin watsawa ta dauki wasu lokuttan kafin ta kammala domin ta sha wahala kafun ta gado yanda zatayi amfani da abubuwan toilet d'in.

Da kayan shafarsa tayi amfani domin ita dai aiya saninta ba'a kawota da komai ba illa kaya jikinta ,bayan ta kammala farar rigar data d'auko cikin wardrobe d'insa ta saka .......


_______Hasken d'akin ta kashe tareda kwantawa saman couch , firgigi ya tashi tareda dafe kansa dake masa ciwo k'okarin tashi yayi but ciwon kan yayi tsanani nesa dashi ya hangota kwance ke... ya kira ta taji shi sarai ,banza tayi dashi sake kiranta yayi da ke still ko motsawa bata yiba ganin haka yasa ya Mi'ke tsaye naya mai dafe kansa dake sarawa hasken d'akin ya kashe mi'kewa zaune tayi tana mai binsa da kallo ,ta gabanta ya wuce zuwa saman bed kwanciya yayi yana mai ri'ke kansa da hannu.

Siririn tsaki tayi tareda mi'kewa tsaye direct hasken d'akin ta kashe , bud'e idanuwan sa yayi kansa ciwo yake masa, sam baya iya bacci idan akwai duhu yasan cewa babu kyau kwanciya da haske ,yaza yayi tunda ya rasa Sa'adatun sa baya iya bacci cikin duhu 

Please ki kunna hasken nan yace cikin yanayin azabar ciwon kanda yake fama dashi 

Bana iya bacci da haske ta fad'a cikin masifa ,baiyi mamakin furucin taba yasan zata aika duba da had'uwar su ta farko bataji kunyar yi masa rashin kunya ba .

Mi'kewa yayi da zimmar kashe hasken da kansa ,dafe kansa yayi, ganinsa ya nema ya rasa , ganin yana tangal tangal kaman zai fad'i yasa tayi saurin kawo masa d'auki ,taimaka masa tayi ya zauna saman gado still hannun sa yana saman kansa ya dafe ,duk rashin mutunci irin na Karime akwai tada tausayi , mi'kewa tayi cikin jarumta ta janye hannun sa daga saman kansa jijiyoyin kansa duk sun fito sabida tsananin ciwon kan da yake fama dashi 

Baiyi yun'kurin hana taba domin yasan yana buk'atar d'auki.

Addu'oi tayi masa cikin ikon Allah mai girma sai gashi ya sami sau'ki saidai abunda ba'a rasa ba 

Thanks ya furta can cikin ma'koshi , ta'be baki tayi domin ita dai bataji me yace ba , hasken ta kashe, k'okarin kwanciya take yace please ki kashe hasken nan idan kuma bakya iya bacci da haske ki koma falo.

Banza tayi dashi, kashe hasken ta kuma yi, bazai so ya biye mata ba ,rufe kansa yayi cikin bargo bai kuma kula taba....aikuwa Ramadan baka san Karime ba ba'a mata sanyi sanyi.


Kiran sallar farko ya tada shi ,ciwon kan ya ware ,hasken d'akin ya kunna kwance take ta barbaje zanin 'kugunta tuni yayi hanyarsa janye idanuwan sa yayi daga kallon inda take ,wanka ya watsa tareda dauro alwala, yanda ya barta haka ya kuma samun ta ,bacci take abunta .

Agurguje ya shirya domin zuwa massallcin dake cikin gidansu 


Mi'ka tayi had'i da sakin hamma wallahi yunwa nakeji ta fad'a tareda wurga idanuwan ta saman gado ganin wayam alamun ya tashi yasa ta furta please ki kunna mun haske bana kwana da duhu tsaki tayi tareda cewa sufa masu kud'i akwai su da iyayi.... 

Toilet ta shiga domin d'auro alwala ,ganin ruwa banza ,abunka da ba'a saba ba babu gidan father shiyasa ta hunce tareda watsawa .

Tsohuwar bra d'inta ta wanke had'i da tsohon d'an kamfanta ,wurga idanuwa tayi dole na sami inda zan 'boyesu bana son ya gansu domin bana d'aukar raini Wallahi ai dai d'an guntun katarin ka yafi sarika bani .

Bayan k'ofar toilet d'in ta sagala su fitowa tayi , direct wardrobe d'insa ta dosa shirt d'insa ta burkice saida ta za'bi rigar da tayi mata sanan ta rufe ,ninke wacce ta saka da dare tayi murmushi ta saki tareda cewa ai duk rigar dana d'auka ta zama tawa tunda yana da kud'i ya siyi wasu .


Tana cikin kokowa da rigar ya shugo da sallama a bakin sa , kallon d'aya yayi mata kauda kansa yayi tareda zama saman couch Qur'ani Mai girma ya d'auko ya fara karantawa cikin nutsuwa ,bayan ta kammala saka rigar salla ta kabbara .

Harya kamma karatun sa bata gama sallar ba abun ya d'aure masa kai wannan wace irin salla ce ,binta da idanuwa yayi domin yana mamakin lokacin da ta d'auka tana sallah.


ganin yanda take sallar ba dai dai ba yasa ya d'an gyada kai domin tausayi ma ta bashi . Wacce irin mace ce aka aura masa haka ?

Wata zuciyar tace menene naka aciki ,but ai matarsa ce hakkin addinin ta yanzu ya rataya a kansa .


A can bangaren Karime kuwa ganin yana karatun Qur'ani shine tace cikin ranta wa zaya nuna ma addini kowa ma ai ya iya dole na bashi mamaki domin sallar yau ta dabance .


Ganin yanda ta dage kuma bata da niyyar tsayawa yasa ya tashi tareda matsawa kusada ita waike wacce irin salla ce haka just raka'a biyu amma kaman wacce take sallar neman gafara .


Sallame sallar tayi tareda mi'kewa tsaye gittawa tayi ta gabansa saida ta kai daidai gadon sa sannan ta juyo ta kalle shi zaka koma bacci kona d'an shingida dan wallahi tunda na shugo d'akin nan nake marmarin hawa gadon nan .


Bud'e baki yayi da niyyar bata ansa maganar farko da ta fito bakin sa ita ce bazan koma bata bari ya idasa maganar saba tayi tsalle tareda fad'awa saman gadon .


Alhamdulillah gida babu ma'kota babu amma andace a gidan miji maimaitawa take tana wani zuyi ,he is speechless anya kuwa yarinyar nan kanta d'aya ,saman couch ya d'an shingida bacci yake ji sosai kuma baya son amfani da kowane daki a cikin part d'insa inba d'akin da sukayi rayuwa shida Sa'adar saba .


Ta kasa bacci sabida irin muguwar yunwar da take ji ,tashi tayi zaune tana mai tunanin abun yi ,shugowa Sa'ada tayi cikin d'akin nasu mamakin yarinyar take yanda ta shugo musu d'aki kai tsaye , direct wajen Mahaifin ta tayi ,Daddy ,Daddy ka tashi kada nayi late cikin yanayin baccin da yake mugun ji , kasancewar a jiya bai waniyi bacci mai dadi'ba ,sam baya iya samun natsuwa a cikin baccin sa if akwai haske,baya son biyema yarinyar da aka ce wai matarsa ce, da alama ita ma tilas tata akayi ta aure shi ,yasani shi mutum ne mai zafi but baya son karya al'kawarin da ya d'aukar ma masoyiyar sa ,wato Sa'ada,Allah ya ji'kanta da Rahama, shiyasa tun jiya baya biyewa shirmen Karime.


Dady kayi mun wanka bana son nayi late ,dafe kansa yayi da hannunsa cikin azabebben ciwon kan da yake fama yace Little please kije Nanny tayi miki wanka kaina yana mun ciwo , dire_dire ta fara , mi'kewa tsaye yayi tareda kama hannun ta zuwa toilet yasani sarai rigimar Little Sa'ada yawane da ita ,tura k'ofar toilet d'in yayi tareda shiga da addu'a a bakinsa ita Sa'ada haka ,bayan ya rufe k'ofar toilet d'in cin karo yayi da tsohon pant da bra d'inta k'asa yashe sun fad'o ,kallon sa Sa'ada tayi sannan tace Dady kayan wanene  ,cikin sauri ya saka hannu ya d'auke su tareda saka su cikin wani botiki........


Kasancewar shi mutunne mai 'kyen'kyami hand washi ya matsa a hannun sa tareda wanke hannuwan nasa.


Bayan ya kammala mata wankan fitowa suka yi , dama wani lokacin takan saka rigima adole shine zaiyi mata wanka .


Bayan ya shirya ta , toilet d'in ya koma domin shima ya watsa .

Duk hidimar da suke , idanuwa ta saka musu yanzu ta fahimci Sa'ada d'iyarsa ce toh ina mamar tata da za'a ce shine mai shirya ta .


Yarinyar akwata da son mutane sabida haka wajen Karima tazo tareda ce mata Dada tace wai daga yanzu ked'in Momy nace ,shuru Karima tayi na wasu y'an da'ki'kai sannan tace ina Momyn ki take da zakice nice Momyn ki .


Kallon hoton Mahaifiyar ta tayi kaman za tayi kuka sannan tace Momyna tana aljanna inji Daddy .

Allah sarki sai yanzu Karime ta gane inda aka dosa , yarinyar ta bata tausayi , hannuwan ta ta kama tareda cewa nice Momynki yanzu ko 


Gyada kai Sa'ada tayi sannan tace nema yanzu nayi momy a school d'inmu friends d'ina Momyn su tana zuwa ni kuwa saidai Dada taje ko Momyn Daddy.


Sosai yayi mamakin yanda suka saba lokaci 'kan'kane ,kaya ya d'auka cikin wardrobe tared komawa toilet dumin shiryawa .

Bayan ya shirya Sa'ada yayi wa magana Little mu wuce re'ke hannun Karime tayi sannan tace nidai Daddy yau na fasa zuwa school d'in.

Cikin mamaki Karime tace dama school zaki ??

Gayada kai Sa'ada tayi ,cikin mamaki Karime tace yau fa asabar , murmushi Sa'ada tayi sannan tace ai ba karatu ake mana ba muna zuwa ana koya mana drama da zamuyi ranar children day .

Oh na gane cewar Karime.

Kallon su yake fuskar sa babu yabo ba fallasa .

Mi'kewa tsaye Karime tayi sannan tace nifa yunwa nake ji tun jiya banci komai ba .

Shuru yayi kaman ba dashi take ba , ri'ko hannun ta Sa'ada tayi tareda cewa momy muje na nuna miki kitchen sai ki girka abunda kike so .


Da ido ya bisu har suka fice daga bedroom d'in .

Koda suka shiga kitchen d'in Hjy Karime kasa kunna gas cooker tayi , cikin kame_kame tace maza kirawo Daddynki ya kunna mana .


Da gudu Sa'ada ta fita zuwa bedroom ,takura masa tayi a dole ya taso .

Kama hannun Sa'ada yayi zuwa kitchen d'in bai shiga ba ,bakin k'ofa ya tsaya kije part d'in Dada abunda ya iya fad'a kenan ,d'aukar Sa'ada yayi tareda yin hanyar waje .


Rigima take masa akan ya sauke ta banza yayi da ita har suka isa parking space , bud'e motar yayi suka shiga.

Taji zafin yanda yayi mata magana ,ba tada yanda za tayi domin aronta Mahaifin ta ya bada.


Dagyal ta samu ta gano part d'in Dada domin bayan ta fito rikicewa tayi kasancewar gidane babba kaman wata Estate.

A gajiye ta isa cikin part d'in da sallama bakinta , magana tayiwa matashiyar yarinyar data iske cikin 'katon falon Dada , banza tayi da ita ganin haka yasa Karime tayi kanta tareda ci mata cola ke dan unbanki baki ji anayi miki magana ba zaki mayar da mutane y'an iska .

Jin hayaniyar su yasa Dada fitowa tana mai tambayar lafiya .

Still hannun ta na ri'ke da rigar yarinyar tace Dada ni yarinyar nan zata raina ma wayau ,tun dana shugo nake mata magana tayi banza dani.

Cikin lallashi Dada tace sakar mata riga kinji Karime ,sakin rigar tayi tana ta huci ,kallon yarinyar Dada tayi sannan tace ke Sailuba wane dalili gare ki da zaki 'ki ansa mata .

Kallon raini tayi ma Karime sannan tace Dada nayi tunanin ko irin masu zuwa maulane ,ko kuma masu zuwa bara ne

Baki Karime ta saki tana ji da kallon ikon Allah..

Cikin zafin zafin nama tayi kan yarinyar,sauri Dada tayi tareda tare Karime cikin lallashi tace Karime kiyi hak'uri bata son ked'in wacece ba .


Kallon Sailuba Dada tayi sannan tace wannan da kike gani matar Ramadan ce ,zaro idanuwa waje Sailuba tayi domin tasan wanene Ramadan 


Jiki na kyarma ta fara bama Karime hak'uri ,cikin wata sabuwar isa Karime tace bazan yafe miki ba sai kin fad'a mun dalilin da yasa kika yi mun kallon y'ar maula ko kuma mabaraciya.


Cikin yanayin tsoro tace wallahi Hajiya kayan jikin kine naga kodaini mai aiki bana iya saka su .

Kallon kayan jikin ta tayi sannan tace lallai yarinyar nan toh kayan jikina da kike magana akansu jiya na fara saka su .

Murmushi Dada tayi domin ta fahimci me Sailuba ke nufi ,mamaki tayi shin Hjy Sadiya ba tayi ma Karime lefe ba ..


Canza tunanin ta tayi , kallon Karime tayi muje ciki mana Karimatu .

Bin bayan Dada tayi zuwa d'ayan falon ta , wuri ta samu ta zauna tareda baza idanuwan ta tana kallon abun duniya .

Ita sam ba wani kallon part d'insa tayi ba sosai ,amma tasha alwashin duba sako da lungu na part idan ta koma .

Cikin sakin fuska Dada tace Hjy Karime kice way'annan kayan jiya kika fara saka su , murmushi Karime tayi sannan tace eh wallahi Dada Mamana ta d'inka munsu na na fitar biki.

Abun ya bama Dada dariya sabida haka darawa tayi kadan sannan tace ina mijin naki daya barki kika fito da sassasafe .

Hamma Karime tayi sannan tace Dada shiyace nazo part d'in ki domin na fad'a masa ina jin yunwa ,shuru Dada tayi domin abun yayi matuk'ar bata mamaki ,shin mi Hjy Sadiya ta d'auki auren yarinyar nan, tana cikin gidannan ace ba zata saka masu aiki suyi mata girki ba bayan haka ace ko lefe ba'a mata ba ,shine me Hjy Sadiya ta shirya akan aurennan dole akwai lauje cikin nad'i.

D'an basarwa Dada tayi,Sailuba ta k'wala ma Kira ,cikin ladabi ta bayyana gaban Dada .

Kiyi serving matar Ramadan breakfast , kallon Karime Dada tayi kije dining kiyi breakfast .


Cikin farinci Karime ta tashi zuwa dining ,bayan ta gyara cikin ta komawa tayi falon Dada ,anan fira ta 'barke tsakanin su .



Mu had'u next page


Please

Like

Comments


And share


 *Rahama Aminu Bala* *HANAADY*