Rental marriage 4
by @hanaady
*NIKAAH*
*Marriage for Rent*
*By*
*HANAADY*
*WhatsApp*
*****
*Follow me on Whatpad*
*Rahama000*
HE HAD THE COURAGE
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?
Marubuciyar
BAHAAR paid book
And now NIKAAH(Rental Marriage).......
Free book
*Page 4*
Da taimakon ma'ikatan gidan Allah yasa ta gane inda Islamiyyar take
Yanayin ginin ya matuk'ar burgeta d'aga kanta tayi domin karanta sunan Islamiyyar, *SA'ADATU HUSSAIN* *MEMORIAL ISLAMIYYA* .
Allah sarki ta furta domin tuni Dada ta d'an bata wasu labarai akan mariganya Sa'ada, kutsa kai tayi cikin makarantar ,tafiya ta fara kanta tsaye ji tayi wata kakkaurar murya ta kira ta da ke, kallo d'aya tayiwa mamallakin muryar yasa ta gane shid'in jami'in tsarone kasancewar uniform ne a jikinsa .
Lafiya ina zaki ? Da izinin wa kika shugo makarantar nan.
Kallon raini da katskanci yake binta dashi ,yanayinsa yasa ta mayar da duk wasu kayan yakinta domin ta lura wannan ba irin mutanen data raina bane .
Cikin rage murya tace bawon Allah ina ga b'atan hanya nayi .
Cikin kallon raini yace ta yaya kika shugo cikin gidannan ko kina cikin masu hidimawa gidanne ,taji haushin furuncin sa d'aurewa tayi , sannan tace eh ina ciki , kyara tsayuwa yayi sannan yace toh ke ai sai an baki uniform tukun zaki fara zuwa sauran 'yan uwanki basu fad'a miki ba .
Gaskiya mutunennan yaci mutuncin ta wato shima kallon y'ar aiki yake mata.
Baki ta washe sannan tace gaskiya basu fad'a mun ba ,amma dai a yanzu ayi mun afuwa na shiga .
Dariya yayi sannan yace a haka zaki shiga yana magana yana mai nuna ta da hannu.
Kallon kanta tayi domin ita dai bata ga ai bun shigarta ba hasali ma kayanta sabbine .
Cikin dauriya da wula'kanci sa tace yo menene laifin sutura .
D'an rage murya yayi sannan yace wannan Islamiyyar akwai y'ay'an masu hannu da shuni sabida haka if kika shiga haka ai sai hankali su ya tashi .
Cikin jin haushin maganar sa tace kace Islamiyyar babu talakawa irinmu .
B'ata rai yayi,ashe talakawa irinmu ,irinki dai domin ni nan da kike ganin albashina mai tsoka ne .
Jin furuncin yasa wani tunani yazo mata kace suna biya sosai murmushi yayi sannan yace sosaima kuwa ,ai yanzu haka mutane da dama nasan samun aikin gadi a Islamiyyar nan ko kuma wani aikin a cikin gidan nan domin Oga Ramadan yana biya sosai.
Jin abunda yace yasa tace shi Ramadan d'in shine mai d'auka masu aikin?
Da kai ya bata ansa murmushi tayi sannan tace na gode ,gaba tayi tana mai dosar classes d'in.
Saurin shan gabanta mai gadin yayi ,wai ina zaki?
Murmushi tayi sannan tace zan dan kashe kwarkwatar idona ne.
Kalle kalle take ,ta kalli nan ta kalli nan ,kallon jerin motoci tayi cikin san Karin bayani tace ,nace wa d'annan motocin fa ? Na dalibanne domin na fad'a miki akwai y'ay'an masu hannu da shuni sosai a Islamiyyar nan .
Sosai mamaki ya rufe ta ,kyawo da tasrin motocin take kallo ,fakar idon sa tayi ta shara da gudu ,bai farga ba Saida ta d'anyi nesa dashi ,aikuwa bin bayan ta yayi da gudu , k'ara speed d'in gudun tayi ganin ya biyo ta .
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Ajine na gani na fad'a abun sai Wanda ya gani domin baka ta'ba cewa wai Islamiyya ce yanda aka kawata ta ajin ,kujerun cikin ajin kansu abin kallo ne ga Ac ta wadata .
Zaune yake saman wata kujera mai kyau da tsari ,karin Qur'ani mai girma yake musu ,cikin zazzakar muryar sa , kacoko hankali sa na kan abunda yake yi ,cikin ikon Allah dai dai k'ofar class d'in da yake taci burki .
Le'kawa ta fara yi saurin ja baya tayi , again ta kuma le'kawa kaman ance ya d'ago ,gilmawar fuskar ta ya gani abun ya d'aure masa kai kodai yarinyar nan gizau tayi masa he is very sure babu abunda zaya kawo ta cikin Islamiyyar nan bayan haka dokar Islamiyyar ce ba'a shugowa babu uniform,bayan haka yasan Musa mai gadi bazai barta ta shugo ba.
Maida hankalin sa yayi kan karantun sa ,ya kasa samun natsuwa shida ,gani yake tabbas ya hango fuskar ta.
Isowar Musa maigadi yasa tayi saurin kama kanta , magana yake mata akan ta koma inda ta fito ba'a shiga kuma saida ya fad'a mata.
Jin hayaniyar Musa mai gadi yasa a hankali bayan ya kai aya ya ajiye Qur'ani cikin mutuntawa . Tafiya ya fara cikin takunsa da kallon so Zuby ta bishi tana mai had'iye yawu,tabo ta Meme tayi haba Zuby ki ri'ka kama kanki mana , soyayya hauka ce kinga yanda mutanen class d'innan ke binki da kallo,siririn tsaki Zuby tayi sannan tace I don't care duk abunda zasu ce suce nidai abunda na sani shine am crazy about him , ina mugun son sa ,ta idasa maganar tana mai lumshe idanu.
Ki fad'a masa mana ,wannan dakon soyayar tasa da kike yi ya fara zauta ki cewar Meme.
Murmushin takaici Zuby tayi sannan tace ina naga fuskar tunkarar sa na fad'a masa haka,mutum fuska kaman ta baqaratu , dariya Meme tayi sannan tace a haka kuma kike son sa mutum babu fara'a ko kad'an ,sai dai akwai mutunci da kuma mutunta mutane.
Rashin fara'ar sa yana d'aya daga cikin abun da yasa nake 'kara durmiyawa cikin kaunar sa , wayar ta ta fiddo ,hoton Ramadan ne ya bayyana ,sosai yayi kyau dumin a picture d'in yayi murmushi.
Lips d'inta ta d'aura saman screenn d'in tsadaddiyar wayar ta , kissing lips d'insa tayi a hankali ta furta ina matuk'ar kaunar lips d'innan , a kullun da mafarkin su nake kwana.
Murmushin takaici Meme tayi sannan tace wannan soyayyar taki kada fa ta koma sha'awa!
Ajiyar zuciya Zuby tayi sannan tace ba'a soyaya babu sha'awa ,a tunani ki ba Meme ta fad'a ,ta k'ara da cewa soyayyar da aka ginata a tafarkin addini da tarbiyya akan yi k'okarin boye sha'awa, sabida kiyaye sabon Allah .
B'ata rai Zuby tayi sannan tace kin fara halin naki na wa'azi koh ,ni dai nayi nisa bana jin kira sabida haka ki ajiye wa'azin ki maybe za yayi miki amfani.
Meme ba taji dad'in furucin kawarta ba ,amma dole ta daure domin tana son cire kawar ta daga halin halaka ,tuni ta fara wasiwasin soyayar Zuby akan Uncle Ramadan gani take kaman sha'awa tafi yawa akan soyayyar da take yi masa.
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
A bangaren Ramadan kuwa,koda ya fita da mamaki yake kallon Karime tsaye take ta kama kugu ita a dole ba zata tafi ba ,a cikin ranta tsoro take ji but tasan cewa koda ta kacame Ramadan zaya ji su.
Takowa yayi cikin takun sa ,ganin tahowar sa yasa Maigadi ya k'ara wutar yi mata rashin mutunci, bata lura cewa harya iso inda suke kasancewar ta bama wurin baya shi kuwa Musa mai gadi wurin yake kallo.
Maganar sa taji daga bayan ta saurin matsawa tayi kusa dashi cikin washe baki,Musa maigadi ne yayi saurin cewa Oga sannu da zuwa , kafun Musa Maigadi ya kuma cewa wani abu tayi saurin cewa tun d'azu nazo amma yak'i ya barni na shiga ,sosai Musa yayi mamakin yanda Karime ke yiwa Oga Ramadan magana.
Saurin gaishe da Ramadan Musa yayi yana mai nuna Karime sannan yace yarinyar nan tun d'azu nake ta fama da ita akan kada ta shugo ,daga hannu Ramadan yayi alamun ya tafi ,tafiya yayi yana mamakin yanda ya ga Karime ta saki jiki a gaban Ramadan ,a iya saninsa da Oga Ramadan bai ta'ba ganin makaman cin irin haka ba ,duk wasu y'an mata dake haukar sonsa Musa Maigadi ya sani sabida wani lokaci ya kanji su suna fira a kan Ramadan d'in.
Kafun Ramadan yace wani abu tuni tace da izinin Dada nazo wurinnan ,sabida haka muje ciki ka cigaba da koyarwar ka ,danni nan a shirye nake.
Bai katse taba har ta kai aya.
Waya fad'a mike Islamiyya wurin biki ne ko kasuwa , zun'buro baki tayi sannan tace menene laifina daga zuwa ne man ilimi
Juyawa yayi ya fara tafiya ,bin bayansa tayi cikin sauri ,tsayawa yayi tareda cewa wai ina za kije ne ??
Aaa wai duk baka fahimci bayanina bane , d'an kallon ta yayi ,ya fahimci yarinyar nan kauyenci yayi mata mugun kamu ..
D'aure fuska yayi sannan yace ki koma gida if na dawo mayi magana ,aaa ni babu inda zani tunda nazo toh sai fa an koya mun karatu ko ina barin wurin nan , shuru yayi na wasu y'an da'ki'kai , gaskiya an had'a shi da aiki shi sam baya son takura saidai me a duk lokacin da ya nuna wasiyyar Sa'ada ya kanyi k'okarin boye fushin sa , yanzu ina littafin da za'a koya miki karatun ya fad'a yana mai kallon ta?
Banida littafi ta fad'a , d'an murmushi yayi sannan yace kije wurin Dada kice ta baki littafin dana bata ajiya ,zan jira ki ki dawo.
Murmushi ta saki ,bari nayi sauri naje na dawo ta fad'a tana mai tafiya .
Da kallo ya bita ajiyar zuciya ya saki baya son sa ido irin na d'aliban makarantar sa ,komai su abun gulmane .
Number Musa Maigadi ya fira tareda bashi umarnin ya rufe gate da key ,ta yanda ko ta dawo zata ga k'ofar a rufe .
☘️☘️☘️☘️☘️☘️
A can bangaren Karime kuwa zagewa tayi taita sauri harta isa part d'in Dada ,sallama ta tsala da k'arfi,cikin mamaki Dada tace aa Karime ya naga kin dawo ko kin fasa karatun ne?? Aaa Dada nazo na anshi littafi a wurin ki ,cikin rashin fahimta Dada tace wani littafi kuma,yace mun nazo wurinki na anshi littafi ba'a karatu ba littafi , murmushi Dada tayi domin ta gane Ramadan wayau yayi ma Karime.
cewa Dada tayi ki zauna ki jira shi idan ya dawo ya d'auko littafin da kansa danna manta a ina ya ajiye shi .
Sosai suka sha fira abunsu yau dai Dada ta sha dariya sosai a wurin Karime. Bai shigo part d'in Dada ba sai bayan sallar isa lokacin Little ta tashi ,koda ya shugo ma'kale take da Momynta wato Karima.
Bayan ya gaishe da Dada bai kuma cewa komai ba ,zaune yake fuskar sa ba yabo ba fallasa , firarsu suke abunsu yana dai jinsu , labari take bama Dada irin wawtar da take a kauyensu .
Da sallam Khaleel ya shugo part d'in Dada matarsa Fadila na take masa baya sai kisisina take ,gaisawa sukayi cikin mutunta juna, kusada Ramadan Khaleel ya zauna ,Fadila kuwa direct wurin Dada tayi tareda hugging d'inta cikin sakin fuska Dada tace barka da dawowa manyan baki ,cikin yanga da iyayi Fadila tace yauwa our granny .
D'an kallon Karime Fadila tayi sannan tace sabuwar mai aiki aka kawo miki tana magana ta mai yatsina baki kaman taga abun kyama.
Kallon banza Karime tayi mata , ke uban waye ubaki a garin Katsina da har zaki harare ni, harara kuma da wane idon kika kalle ni da zakice na harare ki cikin tsiwa itama ta mayar mata ,ya isa Fadila cewar Khaleel kallon Karime yayi sannan yace ke kama gaban ki
da mamaki ta kalli Khaleel,magana nake maki ya fad'a cikin tsawa banza tayi dashi ya isa haka Dada ta fad'a wai Dada ina kika kwaso mana wannan shashashar cewar Khaleel , saida Karime ta murguda baki sannan tace wallahi nidai ba shashasha bace.
Tunda suka fara yake latsa wayarsa domin dama can haka Fadila ta takura ma Sa'ada, d'akin ya dau shuru na wasu y'an lokutta , fita daga d'akin Dada tayi domin ansa waya .
Ganin Dada ta fitane yasa Fadila ta cigaba da zagin Karime ,ta fara kaita bango sabida haka mi'kewa tsaye tayi tareda nuna Fadila da yatsa sannan tace duk rashin kunyar ki , ki kyara kalaman ki kada kiyi kuskura ki k'ara gigin zagin iyayena ,ni kike fad'a ma haka eh an fad'a miki ko akwai abunda zaki iya .
Murmushi k'asa k'asa Ramadan yayi domin yau d'innan Karime ta matuk'ar burge shi if Sa'adatun sace ba zata ta'ba maida magana ga masu tozartata .
Hannu ta d'aga zata mari Karime ri'ke hannun tayi sannan tace nid'in ba kanwar lasa bace ,mi'kewa Khaleel yayi tareda cewa wai ke uban me kika taka kallo d'aya tayi masa d'auke kanta tayi tareda kallon Ramadan had'a idanuwa suka yi sauren janye nata tayi sannan tace kayi wa matar ka fad'a ba matar wani ba cikin mamaki yace matar wani uban waye mijin naki da yatsa ta nuna masa Ramadan saurin kallon yayansa yayi baki sake yace I'm sorry yaya wallahi ba nida masaniya cewa matarka ce d'an ta'be baki yayi sannan yace ai yanzu ka sani.
Mi'kewa yayi tareda cema Karime muje , gaba yayi abunsa yana mai kama hannun Little.
Kallon Karime Khaleel yayi sannan yace please Anty I'm so sorry murmushi Karime tayi sannan tace wai nice Anty Kai ya gyada, ki yafe mun ke matar yayana ce dole na nemi tafiyar ki because ina ji da yayana fiyeda tunanin mai tunani .
Murmushi tayi sannan tace na yafema ka kallon Fadila tayi sannan tace shi d'an Adam a duk yanda ka gansa darajane dashi tana idasa maganar ta tayi waje abunta.
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Zama tayi jagwab saman sofa she can't believe it wai yau ita wata marar kunya y'ar kauye ke fad'a ma magana ,shi kuma Khaleel hada wani bata hak'uri,fuu Fadila ta fita daga part d'in Dada direct part d'in Momy tayi ,zaune ta tarar da Momy tana kallo hankali kwance , tsaye tayi kerere cikin yanayin rashin tarbiyya tace Momy plan namu ya fad'i bangane ba Momy ta fad'a, akan matar Yaya mana tsaki Momy tayi sannan tace meya faru ne kwashe k'arya da gaskiya Fadila tayi ta fad'awa Momy , yanzu me kike so ayi Momy ta fad'a tana mai maida idanuwan ta saman screen d'in tv.
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Momy kije kici mutuncin ta ,naga alama Dada itace mai goya mata baya take wa mutane iskanci ,shuru Momy tayi na wasu y'an da'ki'kai sannan tace bawai bana son ci mata mutunci bane tsohuwar can takai k'arana wajen Alhaji bayan fitar ki ya kirani yayi ta mun masifa,kin san halin Dadyn Ramadan ba sau'ki ne dashi ba .
Yanzu shikenan ta zageni a banza Fadila ta fad'a kaman za tayi kuka.
Ficewa tayi daga falon kaman kububuwa ,tsaki Momy tayi sannan tace anyi yarinya sai mugun abu ya haliki ya halin uwarki , kullun saidai kici kiyi zubar toilet kin kasa haihuwa mitsw ta kuma jan tsaki.
Da murmushi akan fuskar ta shugo falon hannun ta d'auke da wasu food flasks masu kyau da tsari, dining table ta nufa tareda ajiyesu cikin natsuwa ,irin matannanne wanda kallo d'aya zaka musu ka gane gayu da ilimi sun anshe su ,cikin girmamawa ta gaishe da Momy tareda zama k'asa saman carpet ,yau dai cikin sakin fuska Momy ta ansa mata Rumaisa Momy ta kira sunan ta me aka kawo ma Momy cikin sakin fuska still Momy tayi maganar , pepesoup d'in kayan ciki ne Momy nasan kina so sosai sai kuma fara dana soya miki ,
Momy tuni taji yawun ta ya tsinke, aaa gaskiya kin kauta ina Sadiq d'in ko bai dawo bane .
Cikin kunya tace kinsan yau ake bikin friend d'in sa Mujaheed ,kice ana can ana shagali cewar Momy ,fira suka an ta'ba bankwana Rumaisa tayi wa Momy tareda tafiya bangaren su .
Yau Rumaisa taji dad'in ganin canji a wurin surukar tasu ,dama ba kowane lokaci take masu rashin mutunci sai idan aminiya ta wato Hjy Mariya nanan ,wani lokacin ta kanyi tunanin anya Hjy Mariya banza tabar Momy abun kaman hada sihiri sabida yanda take juya tane amma akwai lokuttan da zaka ga Momy kaman ba ita ba.
A bangaren Fadila kuwa Hjy Mariya ta kira cikin makirci tace Mom kaman fa Sadiya ta samu,meya faru Hjy Mariya ta tambaya ,bayan Fadila ta gama fad'a ma uwar tata abunda ya faru ,cikin jin haushi tace ba wani abunda ya warware kawai dan Mijin nata yayi mata fad'a ne kin san akwai tada tsoro amma kada ki damu gobe xan shugo gidan ,kidai ki cigaba da saka musu ido so nake wannan gantalalliyar ta dawo ko anyi bikinsu da Ramadan ,kinga duk da kina auren Khaleel dole mu dage Alia ta auri Ramadan tunda shine mai dukiyar .Fadilq taji haushin furuncin uwar ta duk lokacin da tace wai Ramdan ne mai duniyar sai taji haushi.
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Rumaisa da farinciki ta koma part nasu , zame mayafin kanta tayi tana mai sakin ajiyar zuciya, ruguwa Adil yayi ya fad'a jikinta rungume d'anta tayi tana mai farinci, d'agowa yayi cikin magana irin ta yara yace Ammi kina murna yau Momy bata saka ki kuka ba murmushi Rumaisa tayi sannan tace Momy tana sona wancen ranar ma da kaga ta sa kani kuka laifi na mata , sosai take farinciki domin bata iya tuna when last Momy tayi mata tarbar mutunci a kullun suka had'u ita da Momy sai zagi da rashin mutunci........
Kiran Number mijinta tayi tareda labarta masa , shima yayi murna sosai domin babu wanda zaiso ace babu jituwa tsakanin mahaifiyar sa da kuma matarsa.
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
A can bangaren Karime kuwa tunda suka koma gida take sababi wai ta lura mutanen gidannan sun riga da sunga wurin kwanan ta ,banza yayi da ita har ta gaji tayi shuru . kitchen ya shiga domin samar ma kansa abunda zaya ci ,zaune suke ita da little suna Kallon tv ,fitowa yayi daga kitchen d'in hannun sa d'auke da abincin, nesa dasu ya zauna saman dining table , abinci yake ce hankali kwance ,
Little zaki ci abinci Karime ta tambaye ta murya k'asa k'asa dan kada ya jita No momy bana jin yunwa , taji haushin ansar Little dan wallahi yawunta sai tsinkewa yake taso ace Little tace tana jin yunwa .
Suna cikin kallon Karime ta mi'ke direct hanyar dining d'in tayi cikin basarwa tayi kaman wucewa za tayi d'an satr kallon abincin tayi , nama ne ta hango zako zako kaman su fita waje suyi magan saurin had'e yawu tayi ,tunda ta taho yake satar kallon ta yana mamakin hali irin na Karime.
Ya lura tsaf abincin take son ci amma tana jin kunyar nuna maitar ta fili ,kai ya d'an gilgiza baka iya predicting halin Karime yanzu zaka fahimci wani abu a gare ta ,yanzu zata baka mamaki wai ta'ba tunin tana da kawaici ba sai yanzu.
Mi'kewa yayi ya fara tafi cikin sauri Karime tace abinci fa kake ci ina zaka hannun Little ya kama baice mata komai ba bedroom ya shige .
Ganin ya bace mata da gani yasa ta zauna tareda cafka hannun ta cikin abinci ,nama ta fara kaiwa bakinta , wai Allah ni Karime dadi' iya dadi'
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Sama gado Sa'ada take zauna tana mai karanto masa littafin sa'al wa jaba daya koya mata, shi kuwa wardrobe ya bud'e tareda fiddo wani d'an k'aramin box, password ya saka bayan ya bud'e box d'in wani d'an k'aramin dairy ya d'auko shuru yayi yana kallon shi bai ta'ba gigin bud'e shi ba domin bata bashi izinin karanta ko menene a ciki ba but tunda ta bashi dairy d'innan yake mamakin wace irin wasiyya ce
Sa'adatun sa ta barwa matar da zaya aura ,shuru yayi na wasu y'an da'ki'kai
a hankali ya furta Karime bata da natsuwar da zaya bata wanna abun mai mahimmanci a wurin Sa'ada tashi kansa .
But dolen sa ya cika wasiyyar Sa'ada ,fita yayi zuwa falo domin ya bata dairy d'in, gyatsa tayi sannan tace Masha Allah yau dai Alhamdulillah naci harna barshi ,ko mai tuna gani yayi yanayin ta ya canza cikin yanayin damuwa tace Allah sarki Mamana kome kika ce ayanzu ko wane hali kice ce ,tagumi tayi tana mai tunanin wane hali mahaifiyar ta take ciki ,siraren hawaye ne suka fara fitowa daga idanuwan ta.
A hankali ya taka zuwa dining area d'in kujera ya d'an ja tareda zaunawa ,shuru yayi na wasu lokutta ,murya k'asa k'asa yace kina son ganin mahaifiyar kine ??
Saurin kallon sa tayi tareda gyada kai , mi'kewa tsaye yayi cikin natsuwa ya mi'ka mata hannu sa ,kallon sa tayi na wasu y'an da'ki'kai , mi'ka masa hannun tayi tareda mi'kewa tsaye.
Mu had'u next page
Yawan comments yawan typing
*Please
Like
Comments and share*
*Rahama Aminu Bala* *HANAADY*