NIKAAH (Marriage for rent)

Rental marriage 5

by @hanaady

*NIKAAH* 

    *Marriage for Rent* )


           *By* 

       *HANAADY* 

    *Rahama Aminu Bala




 *WhatsApp* 

 ***** 


 *Follow me on Whatpad* 

 *Rahama000* 

 *


HE HAD THE COURAGE 

TO REMARRY.

WILL HE FIND THE COURAGE TO

LOVE AGAIN?





Marubuciyar

BAHAAR paid book

And now NIKAAH(Rental Marriage).......

Free book


 *Not edited* 



 *Page 5* 


_________Tafiya ya fara cikin takunsa Karime baki ya mutu domin har yanzu yana ri'ke da hannun ta , bedroom ya shiga kwance suka tarar da Little ba bacci take ba but eyes d'inta a rufe suke , shugowar suce tasa ta bud'e idanuwan ta tana mai murzarsu , Dady bacci nake ji ,sakin hannun Karime yayi tareda matsawa kusada Little zaunawa yayi sannan yace bacci za kiyi ?Da kai ta bashi ansa saman cinyarsa ya d'aura ta sannan yace nayi miki wanka anan zaki kwana koh ??

Cikin yanayin yarinta Little tace aaa Dady bazan kwana anan ba Why ya fad'a k'asa k'asa ,Dada tace yara saba kwana da manya wai , murmushi yayi sannan yace a yaushe ta fad'a miki haka bayan mun saba kwana tare, Dada tace yanzu kai ba gwowro bane kana da mata sabida haka bazan kuma kwana da kai ba zaro idanu waje yayi yana mai saurin kallon Karime ,ita kanta Karime tayi mamakin furucin Little.


Saukowa tayi daga saman jikinsa wurin Karime ta nufa hannun ta ta kama sannan tace Dada tace yanz tareda Momyna zaku rika kwana ,kuma tace zaku samo mana saban baby .

 kallon Karime ya kuma , had'a idanuwa sukayi saurin janye nata tayi tana mai ce ma Little haba d'iya ta tare zamu kwana Dada tana miki wasa ne.


Aaa Momy Dada da gaske take tace idan ina kwana tare daku ba zaki kawo mun baby ba ni kuma ina son ki kawo mana baby koh Dady ta idasa maganar da kallon Mahaifin ta ,shidai he is speechless tsohuwar can bata jin magana taya zata rin'ka irin wad'annan maganganun da karamar yarinya.


Cikin jin kunya Karime tace Sa'ada muje na miki wanka ,da kallo ya bisu har suka bacce masa da gani ajiyar zuciya yayi , tareda zama saman couch.


Bayan ta kammala wa Little wanka shirya ta tayi cikin kayan bacci kasancewar akwai kayan ta a dakinsa.


D'aukar Sa'ada yayi saman kafad'ar sa ,baice da Sa'ada komai ba ganin ya fita ,yasa tayi saurin bin bayan ,kallo d'aya ya maita ya mayar da kallonsa kan hanya ,tafiya suke suna fira shi da diyarsa da kallon burgewa take ta kalle su , Allah sarki ta ayyana cikin ranta yanzu da mahaifiyar ta nan da farinciki su tafi haka, Allah sarki Sa'adatu,sosai Karime taji tausayin Ramadan da kuma diyarsa Little,ta fahimci they are not complete, suna buk'atar wani abu a rayuwar su ,suna buk'atar farincikin da yafi haka ajiyar zuciya tayi, tasan yanda aurensu ya kasance ita d'in aronta Mahaifin ta ya bada shin ita wacce zata zo zaya sota kuwa ?? Menene dalilin da yasa Hjy Mariya ke son had'a auren d'iyar ta da Ramadan ?


Why Momy ke goya mata baya a matsayin tana mahaifiyar sa ta yaya zaya amince ayi renting mata wa d'an ta ,?? 


Bata tunanin farincikin sa .

Dole ta samo ansoshin wad'annan tambayoyin nata.


Wurin wa ta furta a hankali??


Tana can duniyar tunani bata san har sun kusa part d'in Dada, ganin sun d'an yi mata nisa yasa ya d'an jirata ,saurin karasowa tayi ,tare suka shiga,ba kowa falon sabida haka bedroom suka nufa shine a gaba ita kuma tana binsa baya,zaune suka tarar da Dada tana zan carbi zama suka yi tareda gaishe ta cikin sakin fuska ta ansa musu , Sa'ada muka kawo tace ba zata kuma kwana a part nawa ba cewar Ramadan.

Washe baki Dada tayi sannan tace kwarai kuwa yarinya taji magana ta yoo akan me zata ringa kwana da akai tunda yanzu kai d'in ba gwauro bane ,kana da matarka ai kwana tareda Sa'adatu ya kare ,cikin jin kunya Karime tace Allah Dada data ri'ka kwana acan d'in.

Kallon Karime Dada tayi sannan tace a ina ake haka ai dole ta dawo nan da kwana kada taje ta gano ma kanta abunda yafi k'arfin ta ,saurin sunkuyar da kai Karime tayi shikuwa yasan k'aramin aikin Dada ne ,haka take musu shida Sa'ada bata jin kunyar yanko wata maganar .

Mi'kewa yayi tareda cewa Dada Saida safe ,kallon sa tayi sannan tace tunda anyi aure adai harraka a samo mun wasu jikokin ,jin abunda tace yasa Sa'ada tace eh Dady ina son sister da brother ,bai tsaya basu ansa ba yayi gaba abunsa.

Na dawo kanki Hjy Karime cewar Dada kiyi k'okarin jawo hankalin sa ki samu ki samo mun jika,mijinki dole sai kin had'a da dubarunmu na mata ko kina samun kansa domin kacako tunanin sa da hankalin sa suna kan marigayiyar matarsa wato Sa'adatu, sabida haka dole ki hanzarta,idan kuma kin san kina da matsala toh ki fad'a mun domin na samo miki magani, bayan haka idan baki san yanda ake jan hankalin miji na koya miki.


Momyna ba tada lafiya ne cewar Little banza Dada tayi da ita kallon Karime tayi sannan tace kinde ji abunda na fad'a miki ,maza ki tafi ,cikin sunne kai Karime ta fito daga part d'in Dada,tsaye ta tarar dashi yana jiranta , d'an nesa dashi ta tsaya tana mai k'ara sunne kai sabida sosai maganganun Dada suka sa kata jin wata muguwar kunya.


Ganin yanda take sunne kai da kuma yanda ta d'an dad'e bata fito daga part d'in Dada ba yasan definitely akwai maganar da Dada ta fad'a mata ,he is very curious akan abunda ta fad'a mata sabida haka kallon Karime yayi cikin natsuwa yace me Dada tace Miki ne ?


Kallon sa tayi,kara sunne kai tayi tana dariya ,kyara tsayuwa yayi sannan yace fad'a mun mana me tace miki , dariya ta kuma yi tana mai rufe bakinta da hijab d'inta.

Ba zaki fad'awa mijinki ba ,jin abunda yace yasa ta tsagaita da dariyar da take cikin kunya ta fad'a masa yanda sukayi da Dada murmushi yayi har fararen ha'koransa suka bayyana ,oh Dada kenan ya fad'a still murmushin fuskar sa bai gushe ba ,tunda tazo gidannan bata ta'ba ganin yayi wa wani murmushi irin haka ba idan aka cire Little.

Tafiya suka cigaba dayi,shuru ya d'an gitta kaman wasa taji yace lokacin da Sa'ada tana da cikin Little a haka Dada ta saka mu gaba dole Sa'ada ta koma part nata da zama ,haka take koroni if naje part d'in ta ganin matata cikin yanayin dauriya ya idasa maganar.

Allah ya jikanta Karime ta furta ,Ameen ya ansa mata.

Tafiya suke kowanen su ya kama bakinsa ,Dan satar kallon sa tayi , fuskar da babu yabo ba fallasa,daurewa tayi tace ina son nayi karatun addini , d'an tsayawa yayi daga tafiya,juyowa yayi yana fuskantar ta ,cikin yanayin sa yace a wacce Sura kika tsaya ??

Cikin jin kunya tace a iya izu biyu nake ,shuru yayi na wasu y'an minutes,shekarar ki nawa ya kuma tambayar ta , d'an murmushi tayi sannan tace nifa ba yarinya bace yanda wasu ke tunani , shekara ta ashirin da biyar ,yayi mamakin shekarunta ,shifa duk a tunanin sa she is 19 to 20 murmushi ta kuma yi sannan tace Jummai kanwa ta na bata shekara bakwai tayi aure tuni har tana da yara biyu ,kallon sa tayi shima ita yake kallo ,janye idanuwan ta tayi daga kallon sa sannan tace a garinmu yamma ta suna aure da wuri, kawata Aisha ma anyi mata baiko nan da wata ukku za'ayu bikinta, kuma fa na girme ta a haihuwa, kusan shekarun su d'aya da kanwata Mariya ,shuru yayi yana kallon ta ya fahimci she want to shere wasu labarai akan ta ,but babu abokin firar ,ya fahimci tana missing family nata, ya san mahimmanci mutun ba dadi'ya nuna rashin interest akan labaranta .

D'an kyaran murya yayi sannan yace why ke ba kiyi aure dawuri ba ? Murmushin takaici tayi sannan tace laifin Baban Jimmai ne,waye Baban Jimmai ? Mahaifin na ta bashi ansa ,ta k'ara ta dacewa maganar Baban Jimmai akai na ta zagaye kauyenmu akan cewa shi ba za yayi mun kayan d'aki ba duk wanda zaya aureni babu maganar kayan d'aki da akewa ko wace d'iya akasar hausa .

Wannan ne dalilin da yasa samarin garinmu suke guduna sabida yanzu mutane auren jari suke yi babu wanda zaya auri macce ace babu kayan d'aki.

Mahaifiyar ki sai tayi miki ya fad'a yana mai kallon ta , murmushi ta kuma yi sannan tace Mama bata da hakin yi mun kayan d'aki.

Shuru yayi na wasu y'an da'ki'kai .

Can yaji tace dama can samarin ba wani sona suke ba kasancewar a garin masu kallon saurayi suke mun ,cikin mamakin furucin ta yace bangane ba , k'asa tayi da kanta sannan tace nice babba a d'akin mu , mahaifiya ta yaranta duka matane ,Baban Jimmai baya son yara mata ,Maman Jummai tana da yara ukku maza ,idan Baba zaya gona nice jagaba wajen zuwa domin tun dana tashi Baban Jimmai ya mayar dani damiji ,duk wani aikin da namiji za yayi shi yake saka ni ,tun ban sababa har abun ya bi mun jiki.


Ji yayi tausayin ta ya shige shi lokaci d'aya.....

Murmushin takaici tayi sannan tace aikin gona dani ake yin sa ,bayan haka duk lokacin da Baban Jummai yaje kudu neman kud'i ya kanyi mana tsara ba ,kasan wani abu ta fad'a tana mai maida kallon ta akansa ?

Kai ya gyada alamun aaa murmushi tayi sannan tace kayan maza yake siyo mun wando jeans da rika mai dogon hannu sune tsaraba ta ,yayi mamakin wannan labari .

Sune kayana wanda har yanzu banida kayan da suka wuce su sabida dasu na saba , tunda ina JSSS 1 nake saka kayan maza ,ada na kan saka su batareda hijab ba ,sai daga baya dana fara mallakar hankalin kaina na gane tabbas ni d'in macece sabida haka dole na suturta jikina .


Basu farga ba ashe ,har sun iso part nasu ,bayan sun shiga direct kitchen ya fad'a wani d'an bowl mai matuk'ar kyau ya d'auko tareda flask,zama yayi tareda cema mata ki d'auko mun cup a kitchen, toh ta ansa masa tareda tafiya fakan fakan kaman zata tashi sama, da kallon tausayi ya bita domin tabbas sai yanzu ya fahimci ko tafiyar ta sam bata mata bace ,kaman daga sama yaji tace ga cup d'in saurin dawowa yayi daga duniyar tunani ansar cup d'in yayi sannan tace ki Karo d'aya , still cikin tafiya irin ta samarin kauye tayi hanyar kitchen d'in.


Bayan ta kawo masa d'ayan cup d'in tea ya had'a musu kiran sunan ta yayi ,bayan tazo wuri ya nuna mata d'an nesa dashi zama tayi tana mai kallon sa tea d'in ya mi'ka mata tareda nuna mata cake cikin bowl , fara cin abunsa yayi hankali kwance yanayi yana korawa da tea ,sam ita dai had'in bai mata dadi'ba ko dan bata saba bane ,ya lura kaman bata jin dad'in had'in ,bayan ya take cikinsa mi'kewa yayi tareda cewa muje kitchen gaba yayi ,cikin sauri tabi bayan sa ,gas cooker ya nuna mata yanda ake kunnawa ,indomie ya dafa mata tareda soya mata kwai.

Bayan ya juye mata indomien a cikin plate , Mika mata yayi sannan yace idan kin gama ki wanke plate din ki saka cikin kitchen wear ,da Kai ta ansa masa ficewa yayi zuwa bedroom.


Bayan fitarsa ajiyar zuciya tayi sannan tace ohi Karime meya hau kaina na cika bawon Allah da surutu , murmushi tayi sannan tace ashe yana da kirki haka .


Wanka yayi ya shirya cikin kayan baccin ,zama yayi saman gado yana mai karanta wani littafin addini.



Da sallam ta shugo d'akin ,ansa mata yayi still idanuwan sa suna kan littafin da yake karantawa, toilet ta shiga domin ta watsa ruwa,bayan kaman minti goma ta fito , wardrobe d'insa ta bud'e riga da gajeren wando ta d'auka , toilet ta kuma komawa domin ta shirya ,bayan ta shirya cikin jin kunya ta fito daga toilet d'in domin kayan da ta cire ta wanke su ,a haka ta fito wandon ya sauko mata haka rigar ma ta d'an sauko mata , ya canza hasken d'akin daga mai haske zuwa mai d'an duhu.


Bakin mirror ta tsaya , hannun ta saka tareda zame ribbom d'in kanta ,yawa da cikar gashin ta ni kaina abun ya matuk'ar bani mamaki , ashe Karime nada gashi har haka , kaman ance ya d'ago,sosai yayi mamakin waya da tsawon gashin ta ,taje gashin take , bayan ta gama tajewa ribbom ta saka, dakyal ta d'aure gashin , wata hula ta saka saman kanta ,irin mai kwantar da gashi, d'auke eyes d'insa yayi daga kallon ta sosai yayi mamaki kodai karin gashi tayi wata zuciyar ta fad'a masa but ta yaya yarinyar dake abu kaman namiji zata k'ara gashi .


D'an nesa dashi ta zauna bakin bed , hankalin sa yana kan littafin da yake karantawa, ji yayi tace Baba Jimmai har Abdulkarim yake ce mun 


Da mamaki ya furta Abdulkarim?? Murmushi tayi sannan tace wallahi kuwa a kauyenmu ma akwai masu ce mun haka ajiye littafin yayi tareda bata dukkan natsuwar sa , cigaba da cewa tayi ,tun ina k'ara Baban Jimmai idan zai kirani zaice Abdulkarim kuma dolena na ansa ,a haka duk lokacin daya kirani yafi son na ansa masa da babbar murya , kaman ya Ramdan ya tambaya yana mai k'ara tsareta da ido murmushi tayi sannan tace baya son na ansa kaman yanda mace take magana saidai na bud'e murya kaman namiji ,da haka na saba komaina kaman na mazane .


Babu aikin k'arfin da Baban Jimmai baya saka ni , d'ebo ruwa cikin baro na kawo gida ,noma ,shuka hud'a,girbi babu abunda ban iya ba ,haka zalika aiyi kan cikin gida suma duk ina yi , talla kuwa duk rana sai nayi nayiwa Mamana nayi wa Maman Jummai.


Maganar samari kuwa babu saurayin da keso na sabida basa mun kallon d'iya mace,wannan shine dalilin da yasa nake duk wasu dabi'u na maza domin tuni na amince cewa ni d'in kaman namiji nake.

Danbe kuwa ko namiji albarka domin bana jin tsoro ko shakkar kokowa da maza.

Cikin murya irin tasa yace Allah yayi ki mace har kuma kike fad'in kin yadda ked'in namiji ce , d'agowa tayi ta kalle shi ,saurin janye idanuwan tayi domin bata iya kallon sa ido cikin ido, cikin yanayin damuwa tace nasan nid'in macece sai dai me duk wasu dabi'u na mata bana tunanin idan na iya su ,ban ta'ba sha'awar koyon wani abu daya danganci Mata ba , Baban Jimmai namijj yaso a haihafa masa sai Allah ya bashi ne a matsayin d'iyar sa ta farko bayan an haife ni shine yayi nasarar mayar dani namiji.

Cikin tausayi yace bana miki kallon namiji ,domin ni dai mace ce a gabana yanzu , murmushin takaici Karime tayi sannan tace ban ta'ba tunanin zanyi aure ba, kasan meya sa ??

Da ya gyada alamun aaa, murmushi tayi sannan tace sabida babu namijin da zaya auri mace irina , Amma sai gashi wasu mutanen sun biya kud'i domin a basu aurena , kud'i?? Kaman ya jin abunda yace yasa tayi dana sanin furuncin ta domin bata son fad'a masa yanda auren ta dashi ya kasance.


Matsowa yayi kusada ita a cikin murya k'asa k'asa yace please ki fad'a mun duk abunda kika sani game da auren mu cikin zubar hawaye tace sunce kada na fad'a maka please ya furta ,a hankali ta fad'a masa komai ,sosai yayi mamakin wannan d'an aiki dama tunda Little ta fad'a masa yaso ya fahimci wani abu ,ya bar maganar ne akwai sabida ya san bincike baya da kyau.


Ta yaya ita Anty Mariya ta san Baban ki ??

Share hawayen fuskar ta tayi sannan tace , a gidan su kawata na fara had'uwa da ita anan ne taga nice na dace da ka aura kafun d'iyar ta ta dawo 

Kasan meyasa ta fahimci nice na dace ??



Aaa ya furta k'asa k'asa murmushi Karime tayi sannan tace sabida ni d'in ba mace bace , tana da tabbacin cewa ba zaka ta'ba Sona ba sabida banida suffar da namiji zaya soni , bayan haka ban san hanyar da zan ja hankalin namiji ba ,kaga kuwa nafi kowace mace dacewa da wannan aikin , a gabana Hjy Mariya ke fad'awa Mamana aurena, na d'an lokacine kafun d'iyar ta ta dawo ,haka Maman Jummai tayi ta yiwa Mamana dariya.


Zan so na canza labarina ,zan so labari na ya canza ,saidai kash ,kaddara ta riga fata , ,yaushe Baban Jummai zai nuna mun cewa nima d'iya ce .


Baban Jimmai na kasa gane wace irin tsana yayi mun ba da har zai iya sayar dani , mi'kewa tsaye tayi tareda zuya masa baya fashewa tayi da kuka mai cin rai ,saman couch ta kwanta tana kuka mai cin rai , sosai tausayin ta ya kama tashi a hankali ya taso zuwa wurin ta ,kaman mai tsoron wani abu ya d'aura hannun sa saman bayan ta kasancewar ta zuya masa baya ,jin lallausan hannun sa a jikin ta yasa a hankali ta tashi zaune tana mai share hawaye da tafin hannun ta, muryar ta har ta fara dishewa ban ta'ba ganin mutum marar sa'a a rayuwa ba irina cikin kuka tayi maganar, ta k'ara da cewa Maman Jummai tace suffata ma kanta bata mata bace nafi kama da maza .

Kallon sa tayi tana zubar hawaye tace wai dagaske bana kama da mata?



A hankali ya d'aura tafin hannun sa saman fuskar ta , cikin yanayin tausayin ta yace , you are a woman Karima ,duk wanda ya kira ki da Mai suffar maza ki fad'a masa cewa ni Ramadan mijinki nace you are a woman and a very beautiful one ,shafa girar ta yayi a hankali ya furta girarki tana da kyau sosai, hancin ta ya ta'ba murya k'asa k'asa ya kuma furta shima Yana da kyau sosai lumshe idanuwan ta tayi a hankali ya gangarowa zuwa la'b'banta,cikin wata murya mai dad'in sauraro yace suna da matuk'ar kyau ,bud'e idanuwan ta tayi kallon juna suke , muryar k'asa k'asa yace Karima you are very cute and beautiful , ajiyar zuciya tayi tana mai k'ara kallon sa , kallon ta yake shima a hankali ya fara matso da fuskar sa kusa da tata, had'e fuskar su yayi ya kasa hana kansa abunda zuciyar sa ke k'okarin saka shi ,baya tunanin komai sai abunda zuciyar sa ta saka shi .


A hankali ya d'aura bakinsa saman la'b'banta lumshe idanuwan tayi hawaye na mai zubowa daga eyes d'inta , cikin natsuwa yake kissing la'b'banta, jikinta yayi sanyi jin sabon al'amari a rayuwar ta .


A hankali ya zame bakinsa kallon ta yayi still idanuwan ta a rufe suke , zame hukar kanta da ribbom yayi saka hannuwan sa yayi cikin gashin kanta cikin natsuwa ya fara shafa kanta kyarma jikinta yake kamar mazari, ganin yanda jikinta ke kyarna yasa ya daina abunda yake , hugging nata yayi , ajiyar zuciya yayi tareda k'ara shigar da ita jikinsa .


Bayan kaman 5 minutes zare ta daga jikinsa yayi ,juyawa yayi zuwa toilet ,zaunawa tayi saman couch kaman wacce bata da lakka a jikinta , la'b'banta ta shafa da hannun a hankali ta saki ajiyar zuciya, mamakin abunda ya faru nake ,ashe hausawa ma suna irin wannan abun ta furta cikin ranta ita duk a tunanin ta fararen fata ne kad'ai ke irin haka domin ta ta'ba ganin Jummai na kallo a wayar ta kafun tayi aure wai mijin da zata aura ne ta turo mata kasancewar Lagos yake zuwa neman kud'i .

Sake ta'ba la'b'banta tayi murmushi ne ya su'buce mata saurin rufe fuskar ta tayi da tafin hannun ta.


A Bangaren Ramadan kuwa shower ya sakarwa kansa tareda lumshe idanuwan sa mamakin kansa yake why ya aikata haka ? Why ya kasa hana zuciyar sa ? Why ya kasa controlling kansa rabon da irin haka ta faru dashi shekara 8 kenan tun Sa'adar sa na raye .

Lumshe idanuwan sa yayi ruwa na ratsa dukkan jikinsa.



Mu had'u next page.


Please like

Share

And comments.