NIKAAH (Marriage for rent)

Rental marriage 6

by @hanaady

*NIKAAH* 

    *Marriage for Rent* )


           *By* 

       *HANAADY* 

   *Rahama Aminu Bala* 




 *WhatsApp* 

 ***** 


 *Follow me on Whatpad* 

 *Rahama000* 

 *


HE HAD THE COURAGE 

TO REMARRY.

WILL HE FIND THE COURAGE TO

LOVE AGAIN?



 *Marubuciyar* 

 *BAHAAR paid book* 

 *And now* *NIKAAH(Rental Marriage).......* 

 *Free book* 


 *Page 6* 


______ya dad'e a cikin toilet d'in dan Karime bata son lokacin da bacci yayi awon gaba da ita ba ,jiki a mace ya fito daga toilet d'in kallo d'aya ya yayi mata,kauda kansa yayi tareda nufar wardrobe, shiryawa yayi zuwa wasu kayan baccin ,cikin mutuwar jiki ya nufi bakin bed d'in , already ta kashe hasken dakin baya iya bacci da haske but baya son takura mata , bedside table ya bud'e tareda d'auko wani photo album .


Wasu zafafan hawaye ne suka sauka saman fuskar sa, I LOVE YOU Sa'ada ya furta tareda rungume photo album d'in, kuka yake shabe shaye sosai yau mutuwar Sa'ada ta dawo masa sabuwa ,he is missing her kaman ba gobe , d'an abunnan daya shiga tsakanin su da Karime ba k'aramin tada masa soyaya da kewar matar sa Sa'ada yayi ba , ya kusa awa d'aya da rabi yana abu d'aya, dafe kansa yayi dake masa mugun ciwo zazzabi ne ya rufe shi cikin lokacin kankane jikinsa ya dau mugun zafi.

A can bangaren Madam Karime kuwa baccin ta take ta sarba abun ka da ba'a saba ba , sanyin AC na ratsa dukkan illahirirn jikinta , cikin baccinta ta fara jiwo nishinsa , saurin durowa tayi daga saman couch direct kansa tayi cikin nuna kulawa ta zauna bakin gadon tareda magana kaman wani saurayin kauye, wanda ke nesa ma zaya iya jiyota ,meke damunka Daddy ??



D'ago fuska yayi cikin hali ya kalle ta, kanta babu hula ,gashin kanta mai cika da waya duk ya barbazo janye kallon sa yayi daga kallon ta murya k'asa k'asa yace bana jin dad'i ne, please ki koma kiyi baccin ki .


Kyara zama tayi tareda daura hannun ta saman goshin sa kasancewar kwance yake yana dubar sama, jikinka da zafe sosai ta fad'a tana mai k'ara ta'ba jikin , cikin sauri ta mi'ke tareda nufar toilet , ruwa ta d'ebo cikin wani d'an k'aramin bucket had'i da k'aramin towel ,zama tayi sannan tace wannan zafin na jikinka yayi yawa barina d'an taikama maka da wanan , bai iya bata ansa ba lumshe idanuwan sa yayi kawai yana mai tunanin matarsa Sa'ada.


Nishi yake sama sama,sosai ya bata tausayi domin zafin jikin nasa ya shahara, cikin dauriya ya samu ya tashi zaune bedside table ya nuna mata tareda cewa ta d'auko masa magani, bayan ta d'akko maganin cikin sauri ta fita zuwa kitchen ,ruwan roba ta d'akko , maganin ya jefa baki tareda kora ruwa, Karime baiwar Allah sai sannu take masa .


Zaune take jingine da gado ,Ramadan na gefen ta ,nishi yake sama sama, sannu ta kuma yi masa,bai ansa ba illa k'okarin kwantawa da yake ,ganin zai kwanta ne yasa ta fara k'okarin sauka daga saman gadon,hannun sa ya daura saman jikinta , cikin yanayin ciwo ya kwanta saman cinyar ta, ba ta san ya zata misalta irin halin da take ciki,hannun ta ya kamo tared rungume shi cikin jikinsa, Nishi yake sama sama , ita kanta Karime ji take kaman ba lafiyar ne da ita ba domin yanayin jikin ta ji tayi ya canza mata.


A daskare take kaman kankara har bacci yayi gaba da Ramadan ba tareda sanin taba , bayan kaman awa d'aya Karime tace zan kwanta ?


Shuru taji, k'ara maimaita maganar tayi da zan kwanta shuru taji ,saurin duba shi tayi a tunanin ta ko baya numfashi ne ,ganin baccin sa yake hankali kwance yasa ta saki murmushi, cigaba da gadinsa tayi har bacci yayi awon gaba da ita.


Bud'e idanuwan sa yayi kwance yake comfortably saman cinyar ta , kallon ta yayi bacci take hankali kwance ,gashin kanta a barbaje saman fuskar ta kusan ma duk ya rufe fuskar, kaman wanda zai ta'ba abun tsoro haka ya saka tafin hannun sa ya fara tattara mata gashin, kasancewar Karime akwai gashi kuma gashin tana irin mai yawa ne ga kuma tsawo duk da tsawon sa baikai na matan Novel ba , bud'e idanuwan ta tayi tozali tayi da fuskar sa ,saurin janye hannun sa yayi daga cikin gashin ta tareda saurin tashi zaune ,dafe kansa yayi domin ji yayi still kansa na ciwo , sauka yayi daga saman gadon tared nufar toilet, domin watsa ruwa da kuma alwala kasancewar gari ya danyi haske sun makara sallar asuba.


Da ido ta raka shi har ya shige toilet d'in ajiyar zuciya tayi tareda fara k'okarin tashi ,saurin komawa tayi ta zauna domin ji tayi cinyar tana mata wani irin zugi ba kaman cinyar dama inda yafi sakarwa nauyi, d'an janye zanin jikinta tayi ta fara d'an murza wurin ,zafi yake mata sosai , fitowar sa daga toilet tasa ta fara k'okarin tashi , tafiya ta fara da dudduke ,da kallon mamaki yabi ta yau kuma wani sabon salon tafiya take ji, basarwa yayi ya fara k'okarin gabatar da sallah .


Wanka ta samu tayi tareda d'auro alwala, wanke zanin jikinta tayi domin shine kad'ai kayan sawar ta shiyasa sam bata wasa wajen ganin a kullun tsaftace yake, rigar data cire ta mayar a jikinta , towel ta d'aura a kugunta kaman zani haka ta fito toilet d'in tana tafiya cikin dauriya,ya idar da sallar ,zaune yake saman darmuma ya had'e kai da kwuiwa.


 Bayan fitowar ta daga toilet rasa abun d'aurawa tayi domin ta wanke zanin ta, wardrobe d'insa ta bud'e tareda dakko dogon wandon sa, yayi mata tsayi sosai haka tayi malegi ,bayan ta idar da sallar, mayarda wandon tayi cikin wardrobe saman gado ta zauna tana mai daddanna cinyar ta dake mata zugi, ta dad'e tana matsa cinyar ta , d'an satar kallon sa tayi ,mamaki tayi akan yanda ya sunkuyar da kansa for about 30 minutes, Mi'kewa tayi cikin dauriya , d'an nesa dashi ta zauna saman carpet ,cikin yanayin irin nata tace wai haryanzu jikinne ?


Shuru ya mata ganin haka yasa ta matsa kusada dashi, tallafo fuskar sa tayi , hawaye ta gani a saman kya'kyawar fuskar sa ,cikin nuna damuwar ta tace haryanzu jikinne, kallon ta yayi but still baice komai ba ,abun wani iri ace babban mutum na hawaye haka taji , ta fahimci yana cikin damuwa kuma al'amarin da alama babbab ne .


 share masa hawayen tayi da hannun ta sannan tace dan Allah ko menene ke damunka kayi addu'a tunda Allah ya hore maka ilimi ,gaskiya ta fad'a masa ,ashe yarinyar nan tana da hankali , boye damuwar sa yayi sannan yace thank you , janye hannu ta yayi daga fuskar sa tareda mi'kewa tsaye, bakin mirror ya tsaya tareda fara shafa lotion a jikinsa ,tashi tayi cikin dauriya ta fita zuwa falo domin ta fahimci shiryawa za yayi.



Bayan kaman 30 minutes bedroom d'in ta koma tsaye ta tarar dashi ya shirya tsaf cikin suits back color tie yake kyarawa ,bakin gadon ta zauna tareda d'an matsa cinyar ta , d'an kallon ta yayi yanzu ya fahimci da abunda ke damun jikinta,saida ya gama kammala Shirin sa tsaf kafun ya juyo, zan tafi office , ya furta , jin abunda ya fad'a yasa ta mi'ke cikin dauriya ,takowa tayi zuwa wurinsa sannan tace baka lafiya ,ta yaya kuma zaka tafi wajen aiki , su basa ma mutum uzuri ne?


Ganin yanda take tafiya cikin alamun ciwo yasa , cikin natsuwa ya matsa kusa da ita cikin sanyin murya yace lafiya naga kina tafiya kaman bakya jin dadi'?


Murmushi Karime tayi sannan tace wallahi cinyar nane ke ciwo, nasan jinne ya kwanta , let me see ya furta tareda da da taimaka mata ta zauna saman gado, , cikin natsuwa irin tasa ya fara yaye towel d'in kyawawan conyoyinta ne suka bayyana , slowly ya d'aura tafin hannun da tareda fara matsa mata su, rufe idanuwan ta tayi tana jin yanda zafi ke ratsata ,sosai ya daddana mata su , d'an kallon ta yayi idanuwan ta a rufe suke shiyasa ya Sami damar 'kare mata kallo , lips d'inta ya kallla , abunda ya faru tsakanin su jiya da dare ya dawo masa , saurin canza tunani yayi ta hanyar tambayar ta ,wai baki da wasu kaya ne ?


Still eyes nata a rufe ta bashi ansa da kala d'aya ne nazo dasu ,shuru yayi na wasu y'an da'ki'kai , if he could remember,Momy tayi requesting kud'i a wurin sa tace na kayane da za'a siya wa matarsa,kuma ya tura mata fiye da amount data buk'ata,why bata siya ba?


Maybe duk cikin plan nasu ne ita da Hjy Mariya wata zuciyar ta fad'a masa , tabbas ya yadda da abunda zuciyar sa ta fad'a masa hana Karime sutura is part of their plan , basa so tayi attracting nasa ta hanyar saka kaya masu kyau ne koko dai kayan ne basu iso na .


Canza tunanin yayi, he will talk to Sadiq about duk abunda ya faru ,he is very sure Sadiq zaya warware masa komai.



Tashi yayi ya d'auko wani maganin shafawa ,shafa mata yayi, bayan ya gama kallon ta yayi sannan yace ki kwanta ki hutu in sha Allah zaya bari toh ta ansa masa,jakkar system d'insa ya d'auka yana k'okarin fita , ba kayi kalaci ba ta fad'a cikin nuna kulawar ta akansa d'an tsayawa yayi sannan yace zanyi break a office,kije part d'in Dada kiyi breakfast tunda ba iya girki ki kayi ba ,jakarsa ya bud'e waya ya d'auko,takawa yayi zuwa bakin bed d'in mi'ka mata wayar yayi sannan yace duk wanda zaizo kada ki bud'e har saina Kira na fad'a miki , ta Yaya ake ansa Kiran ta furta tana mai kallon sa, kansancewar tunda take bata ta'ba yin wayar kanta ba hasali wayar Mama mai malatsai ce kuma wayar Aisha kawar ta ba irin wannan bace, y'ar karamar ViVo ce .


Hannu ya saka cikin aljihun sa tareda d'auko wata wayar ciran wayar daya bata yayi tareda nuna mata inda zata d'auka, d'auka, tayi tareda cewa hello, bud'e murya tayi sosai kaman ba mace ba,bai san lokacin da murmushi ya su'buce masa ba ,cewa yayi dana Kira anan ne zaki d'auka, murmushi tayi sannan tace toh nagane .


Tafiya ya fara harya kai bakin k'ofa ya zuyo make sure kina gama cin abinci ki dawo gidanki ,toh ta ansa masa ,ficewa yayi abunsa .



Ajiyar zuciya Karime tayi tared kallon wayar da ya ajiye mata ,sosai wayar ta mata kyau ,kirar Samsung ce ,gyara kwanciya tayi domin ta samu ta d'an rintsa, sam ba taji dad'in baccin jiya ba kasancewar a takure tayi shi.


Zaune yake cikin office,tarin aiyika ne a gaban sa but ko kad'an bai duba su ba ,yau d'innan ji yake he is not himself, babu sallama balantana knocking,kaman an jego shi haka ya shugo cikin Ofiice d'in , idanuwan sa a rufe suke ,ko rantsuwa yayi baya kaffara yasan Twin brother nasa ne wato Sadiq , kujerar da tafi kusanci da Ramadan ,Sadiq ya zauna ,banza yayi da shi still idanuwansa a rufe suke, kallo d'aya Sadiq yayi wa Ramdan,cewa yayi yane ?


Lover boy tunanin late Sa'ada kake ,banza yayi dashi dariya Sadiq ya kuma sannan yace yane ,yauma ta zone a mafarkin ka ?


Bud'e idanuwan sa yayi tareda tamke fuska sannan yace yaushe zaka girma ne ,eye Sadiq ? Dariya Sadiq yayi sannan yace randa ka daina haukan son matacciya, randa ka gane Allah d'aya ne , ma'ana randa ka bud'e zuciyar ka ga wata , a ranar ni Abubakar Sadiq zan yi hankali, jin furucin Sadiq tsaki Ramadan yayi sannan yace ,i doubt it baka san so na gaskiya ba .


Dariyar sha'kiyanci Sadiq yayi sannan yace ina da auren harda yaro ,kace ban san sona gaskiya ba , eh ? 


Hmm mata nawa kayi dating daga auren ka zuwa yanzu cewar Ramadan , murmush Sadiq yayi sannan yace gaskiya bana iya tunawa , murmusawa Ramadan yayi sannan yace my heart belongs to her , only her , kaine zuciyar ka ke son mata da yawa but ni Ramadan bana iyawa.


Dariya Sadiq yayi sannan  yace ni Sadiq Allah yasa ina matuk'ar so da kaunar mata ,ai mata duniya ne , ta'be baki Ramadan yayi sannan yace kaga banbancin na da kai 

Kai d'in mayen matane ni kuwa my heart belongs only to Sa'ada , matacciya Sadiq ya furta .


B'ata rai Ramadan d'in yayi sannan yace eh matacciya but my heart belongs only to her, dariya sosai Sadiq yayi sannan yace wallahi tausayi kake bani ace yanzu shekara har takwas kana rayuwa babu mace ,ina ai bana iyawa ,mata sune farincin duniya , amma Kai ka haramtawa kanka farinciki 


 baka san true love bane that's why kake irin wannan maganar cewar Ramadan, bayan haka , soyayyar matarka tafi taka yawane shiyasa har kake kula wasu matan tana saka maka ido if ace kaine ke mugun sonta ba zaka irin wannan rayuwar ba .


Ai kome za kace kace kula mata yanzu na fara ina dalili na takure kaina a mace guda , kaida kake haukan son matacciyaar matar ka Allah ya bada sa'a.


Hmm Allah ya shirye ka Sadiq , Ameen Sadiq ya furta , ina tausayin rayanka wallahi kuwa cewar Ramadan


 akanme kenan Sadiq ya fad'a cikin rashin fahimtar inda maganar Ramadan ta dosa , duk abunda ka yiwa y'ay'an wasu za'a ma naka ne , dariya Sadiq yayi sannan yace Allah abun godiya for now dai yarona namijine , zaka haifi matan watarana,cewar Ramadan .



Kaga banbancin mu a fuska muna matuk'ar kama da juna ,mutane da dama basa gane mu ,but sam halinmu ba d'aya bane kai din mata basa gaban ka ni kuwa ina matuk'ar kaunar su 


 tsaki Ramadan yayi sannan yace harna tuna a school lokacin da wata girlfriend naka tayi hugging d'ina a cafeteria , dariya Sadiq ya k'yalkyale da ita sannan yace babu abunda yafi bani dariya shine marin da ka mata , kuma fa Saida na fad'a mata bani bane domin sai da ta Kira wayana wai gani ta gani a cafeteria ,na fad'a mata ba nine ba but ba taji ba ,ashe rabon tasha marine dariya Sadiq ya k'ara .


Yauwa cewar Sadiq congratulations man, ashe finally Dada tayi nasarar aurar da mijin matacciya, dan ta'be baki yayi sannan yace Dada ko dai Momy ,I don't understand Sadiq ya fad'a ,kwashe komai yayi ya fad'a ma d'an uwansa akan yanda auren nasa ya faru ,sosai Sadiq yayi mamaki , Allah sarki ni yarinyar ma ta matuk'ar bani tausayi cewar Sadiq .



Wai meke damun Momy ne? Sadiq ya fad'a yana mai mamakin hali irinna mahaifiyar su, Anty Mariya itace matsalar Momy cewar Ramadan 


ita matar taka wane irin uba ne gare ta da zai iya sayar da farincikin d'iyarsa , baya jin komai d'iyar sa ta zama k'aramar jawara.



A yanda ta fad'a mun dama can ba wani damuwa da ita yayi sabida ta fad'a mun lokacin da mahaifiyar ta nada cikinta namiji yaso ta haifar masa ,sai Allah ya 'kaddara mace ce, kwashe duka labaran da Karime ta fad'a masa yayi ya fad'awa Sadiq , dariya Sadiq yayi sannan yace Abdulkarim ,Hhhhhhh b'ata rai Ramadan yayi zan daina fad'a maka labari kuwa if ka cigaba da yiwa matata dariya.


Dakyal Sadiq ya samu yayi controlling dariyar sa , baiwar Allah ashe auren aro aka mata , d'an ta'be baki Ramadan yayi sannan yace *MARRIAGE* *FOR RENT* .


 Wai Abdulkarim Sadiq ya kuma maimaitawa , wai ita Aliya har yanzu tana kan bakanta sai ta aureka ne?


She is my ex , ka sani ,da ita na fara soyayya ,kafun na had'u da Sa'ada ,kuma kafi kowa sanin dalilin rabuwana da Aliya .


Then zaka iya auren tane yanzu cewar Sadiq ?


Shuru Ramadan yayi na wasu y'an da'ki'kai sannan yace naso Aliya ,kafun na had'u da Sa'ada , but bana tunanin if soyayyar nan akwai ta , saidai if Momy ta umarceni dana auri Aliya zan aure ta for mom's sake .


d'an murmushi Sadiq yayi sannan yace enjoy your life bro , you have been suffering fa for 8 years , bana tunanin if ka k'ara hugging mace tun bayan mutuwar Sa'ada, lumshe idanuwan sa yayi ya bud'e sannan cikin taushin murya yace i hugged her yesterday , zaro idanuwa waje Sadiq yayi sannan yace wa kenan ?


My wife ya furta k'asa k'asa ,how cewar Sadiq ,she was crying so i don't know why nayi hugging nata and ya furta k'asa k'asa,and what cewar Sadiq ?


 And i kissed her , murmushi Sadiq yayi sannan yace then why can't you open your heart for her ?

 

Shuru Ramadan d'in yayi , mi'kewa tsaye Sadiq yayi tareda matsawa kusa da d'an uwan sa sannan yace since sunyi renting nata ganin cewa ita d'in ba cikakkiyar mace bace ,why don't make her complete.


Look bro cewar Sadiq, the whole world is looking at her as Abdulkarim ,why don't you make her Karima.


No Sadiq i can't do that , then tunda sakin ta za kayi why ba zaka taimaka ka mayar da ita Karime so that when you divorce her someone will recognize her ..

Shuru Ramadan yayi, murmushi Sadiq yayi sannan yace is she not beautiful??


A hankali Ramadan ya furta she is , then , please bro open your heart , please am begging you .


Kallon sa Ramadan yayi sannan yace ,if bud'e zuciya ta will you stop being womanizer?


Shuru Sadiq yayi , he want to see his brother happy ,he can sacrifice komai akan twin brother nasa 


saurin tarar numfashin Sadiq Ramadan yayi, look Sadiq kaman yanda ka sha fad'a mun womanizing a cikin jikinka yake haka soyayyar Sa'ada a cikin jinina take so please mu bar maganar nan


 Duk lokacin da ta buk'aci na sake ta, i will divorce her kaman yanda ta fad'a mun Aliya na dawowa zata buk'aci divorce a wurina.


Murmushi Sadiq yayi sannan yace fine , kallon tuhuma Ramadan yayi masa sannan yace ,tell me what are you up to 


nasan wannan fine d'in taka da abunda kake shiryawa, ko d'aya babu abunda nake shiryawa


 hasali ma na tuna akwai wata beb da zamu had'u ,wurin zaman sa ya koma tareda bud'e bag d'in system d'in da


 mirror ya fiddo Yana mai kallon fuskar sa , tsaki Ramadan yayi sannan yace Allah ya shirye ka Sadiq Ameen ya furta


 still yana duba mirror , kaga Ramadan nida Kai fa ba d'aya bane , kai d'in ka hak'ura da jij dad'in duniya ne but mu ai da tsinke muke cin abunmu , bayan haka duk abunda nake yi bana zina ,mugun gudu mu d'an yi romancing juna ne .

 Tsaki Ramadan yayi sam halayen su da dabi'un su ba d'aya bane da twin brother nasa , kuma ba karamar kama suke ba kawai banbanci su shine Ramadan ya d'an fi Sadiq kaurin jiki.


Wayar Sadiq ce tayi ringing,dagawa yayi tareda cewa beb ina hanaya , bayan ya katse kiran wani Kiran ne ya shigo , dagawa yayi tareda cewa my wife ,my everything, dan siririn tsaki Ramadan yayi.


Bayan ya gama wayar kallon Ramadan yayi sannan yace wai matatace take son zuwa gidanka , baice da Sadiq komai ba illa wayarsa dake gida ya kira.


Kwance take tana sarar bacci taji ringing d'in wayar, dagawa tayi cikin yanayin bacci tace ina ji ,a can bangaren Ramadan kuwa lumshe idanuwan sa yayi domin yanda muryar tata ta tafi da imanin sa , matar kanina Sadiq zata shugo ki bud'e mata kofa ,toh ta ansa masa still,cikin wannan murya , kasa katse kiran yayi, samun kansa yayi da cewa kinci abinci , bana jin yunwa ta fad'a masa ataikaice, shuru yayi na wasu y'an da'ki'kai sannan yace ya ciwon naki ?


Nishi ta d'an yi wanda ya jishi har cikin ransa ,cewa tayi Alhamdulillah na fara samun sauki .


Shuru suka yi ,baya son katse kiran bai san dalili ba can cewa tayi bari na fita zuwa falo kada ta buga k'ofa daganan bazan ji ba , k'ara lumshe eyes d'insa yayi he don't know why yau dad'in muryar tata yake ji .


Ido Sadiq ya sa masa , murmushi yayi shi kadai yasan me yake shiryawa d'an uwansa.



 *Mu had'u next page* 






* *HANAADY* 

*