NIKAAH (Marriage for rent)

Rental marriage 7

by @hanaady

*NIKAAH* 

    *Marriage for Rent* )


           *By* 

       *HANAADY* 

    *Rahama Aminu Bala* 




 *WhatsApp* 

 ***** 


 *Follow me on Whatpad* 

 *Rahama000* 

 


HE HAD THE COURAGE 

TO REMARRY.

WILL HE FIND THE COURAGE TO

LOVE AGAIN?







Marubuciyar

BAHAAR paid book

And now NIKAAH(Rental Marriage).......

Free book


 *Page 7* 


________Cikin dauriya ta fita zuwa bakin gate d'in gidansu kasancewar kowane flat na gidan yana da get nasa , bud'e k'ofar get d'in tayi tareda fara baza idanuwa ko zata hango wacce yace tana hanya zuwa flat nasu ,nesa ta hango ta cikin shiga ta alfarma ,cikin fara'a Ramaisa ta karaso kallon Karime tayi sannan tace dan Allah tace Amaryar gidannan tana ciki?


Sam Karime bata ji dad'in furucin Rumaisa ba saidai me ganin cewa akan rashin sani tayi maganar kuma babu alamun raini cikin maganar tata yasa Karime tace muje ciki , Karime na gaba Rumaisa na take mata baya har suka isa cikin gidan ,Allah sarki Rumaisa ji tayi hawaye suna k'okarin saukowa daga idanuwan ta ,bata iya tuna when last ta shugo part d'in kawar ta kuma Aminiyar ta wato mariganya Sa'ada .


Ki zauna mana Karime tace tana mai kallon Rumaisa ,zama tayi saman sofa cikin mutunci Karime tace na kawo miki ruwa ? Allah sarki wallahi bana buk'atar ruwa a yanzu but in sha Allah kafun na tafi maybe zan tambaya .


Toh Karime ta ansa mata shuru su kayi nace ina matar gidan Rumaisa ta kuma tambaya d'an murmusawa Karime tayi sannan tace ai nice matar gidan ,cikin inda inda Rumaisa tace I'm so sorry wallahi ba'a sane na miki haka ba , d'an murmushi Karime tayi sannan tace kada ki damu ba kece ta farko data fara mun kallon Mai aiki ba .


But ked'in kya'kyawa ce kawai ina ga problem d'in daga dressing naki take , d'an kallon kanta tayi sannan tace a anan garin ba amma a kauyenmu babu wanda zaima suturata kallon banza domin sabuwace gal nina fara saka kayana.

Murmushi Rumaisa tayi domin ta fahimci tabbas kauyen ci na d'awainiya da Karime , kina da baki cewar Rumaisa kaman ya?


Ina nufin bakida tsoron magana ba kaman mariganya Sa'ada ba ita macece mai nauyin baki da hak'uri , Allah sarki Karime ta fad'a tana mai jin tausayin Ramadan .


Sosai suka sha fira , akan yanda gidan nasu yake ita dai Karime ta cikin ta take domin ba karamar yunwa take ji ba d'an mi'kewa tayi tareda cema Rumaisa dan Allah bari na d'auko waya ki d'an Kira mun maigidan ,aaa basai kin d'auko waya ba bari na kira mijina am sure suna tareda , komawa tayi ta zauna tana mai jiran Rumaisa..


Bayan sun gaisa tambayar Sadiq tayi ko suna tareda da Ramadan ansa mata da eh yayi ,matarsa tana buk'atar magana dashi ne ok Sadiq ya furta tareda mi'kawa Ramadan wayar ,da hannu ya tambayi d'an uwansa akan waye Abdulkarim Sadiq ya furta yana mai kunshe dariyarsa ,banka masa harara yayi tareda fizgar wayar daga hannun sa.


Batareda ta gaishe shi ba tace zanje sashen Dada yunwa nake ji , bakuwar taki fa anan zaki barta ki tafi cin abinci flat d'in Dada , aaa ai idan zata tafi saimu tafi tare , ina wayar dana baki why baki kirani da ita ba zun'buro baki tayi sannan tace yo ai baka koya mun yanda ake kiran ba ,shuru yayi mata d'ago wayar tayi daga kunnen ta kallon Rumaisa tayi wai shin koya kashe kiranne duba mun naji shuru ,ansa Rumaisa sa tayi tareda dubawa mi'kawa mata tayi aa yana kan lafiya ,murya ta bud'e sosai hello baka jinane janye wayar yayi daga wurin kunnen sa sabida ji yayi maganar ta na shirin lalata masa dodon kunne .


Mayarda wayar yayi sannan yace kice ta kunna miki gas cooker d'in sai ki girka da kanki aaa nidai ka bari baje inda zanci daga sama , wallahi bana iya komai a yanda nake yanzu ciwon da nake fama dashi ba kad'an bane ok sai kin dawo ya fad'a tareda mi'kawa Sadiq wayar ,magana take abunta ba tareda ta kashe wayar ba dama ba iyawa tayi ba kaji shi wai bayaso naje sashen Dada naci abinci daga sama inani ina fara girki da waccan abar naje na kone fuska dariya sosai Rumaisa keyi yau dai Karime ta matuk'ar bata dariya.


A bangaren Sadiq kuwa yaji komai , xolayar d'an uwansa yayi tayi karshe tashi Ramadan yayi ya bar masa office d'in.

Bayan ta mi'ka ma Rumaisa wayar bedroom d'in su ta shiga wayar daya bata ta d'auko muje koh tace ma Rumaisa , murmushi Rumaisa tayi sannan tace ga shawara muje part nawa saina baki abincin shuru Karime tayi na wasu y'an da'ki'kai sannan tace d'an kira mun shi na fad'a masa wayar ta bama Rumaisa , zaune yake cikin mota ya jingina kansa idanuwan sa a lumshe kiran Hajiya Karime ne ya shugo , dagawa yayi tareda cewa menene ?


Aaa Dady ka mayarda wukaken mana yaushe na haife ki da zaki kirani da Daddy I'm not your Daddy sosai ya taso yana mata fad'a shuru tayi tana sauraren sa tsaki yayi tareda katse kiran ,bayan ya katse kiran ne ya tuna yanda ya rufe ta da fad'a toh me tayi masa ne wata zuciyar ke tambayar sa ajiyar zuciya yayi why ya sauke fushinsa akan ta ,shi takamaimai bai san fushin me yake ba kawai yaji ransa ya b'aci.


A bangaren Karime kuwa shuru tayi kaman ruwa ya cita ,dafa ta Rumaisa tayi kiyi hak'uri duk wani tsanani yana tareda sau'ki bayan haka Ramadan mutunne mai wuyar zama kafun ka fahimce shi if kika fahimce shi yafi mutane da yawa dad'in zama ,kallon Rumaisa tayi sannan tace tunda nazo gidannan bai ta'ba mun irin haka ba yana kyautata mun bisa gwargwadon iko amma yanzu ban masa komai ba ya rufeni da fad'a


Maybe akwai abunda ya b'ata masa rai ne cewar Rumaisa sake kira mun shi Dan Allah ,ansar wayar Rumaisa tayi tareda Kiran number Ramadan ,saurin mi'kama Karime wayar tayi d'aga kiran yayi amma baice komai ba, kayi hak'uri naga kaman kana fushi dani ,me kika mun da zanyi fushi dake ?

Toh ko wani ya b'ata maka raine , shuru yayi yana mai sauraren ta tunda baka so na fita bazan fita ba kayi hak'uri , I'm trying to protect you ne Karime bana son kina fita bananan but tunda kince yunwa kike ji and ba girki kika iya ba zaki iya tafiya , dan Allah meke damun ka ,cikin mamaki furucin Karime yace ban gane ba ,yanayin ka ya canza kaman kana cikin damuwa , baisan lokacin da yayi murmushi ba duka yaushe kika sanni da zaki iya gane yanayina ,a d'an zaman da nayi da kai zan iya fad'in wani abu game dakai ,canza maganar yayi ta hanyar cewa bakuwar taki ta tafine ?

 


Aaa tace na bita sashen ta zata bani abinci , cikin nishad'i tayi maganar adowa lafiya ya furta tareda katse kiran , murmushi yayi k'asa k'asa yarinyar nan akwai ta da abun dariya .


Koda suka isa flat d'insu Rumaisa sosai Karime ta shgala da kallon tsari da kyauwo irin na falon , komai na gidannan irin naku ne kawai banbanci ku yanzu bangaren Ramadan ne kuke amfani dashi bangane ba cewar Karime kyara zama Rumaisa tayi sannan tace lokacin da cikin mariganya Sa'ada ya fara girma a lokacin ne ta dawo wannan d'akin da zama sabida hawan bene yana wahalar da ita , kasancewar anan sukayi rayuwa kafun mutuwar ta yasa sam baya iya amfani da kowane d'aki sai wannan d'akin dake k'asa, Allah sarki cewar Karime , kin ta'ba zuwa dakunan saman ? 


Aaaa ban ta'ba ba hasali tunda nazo gidan daga kitchen , falo da d'akin bacci kad'ai na sani kuma banyi karambanin shiga sauran dakunan ba , Sadiq ya fad'a mun a duk ranar juma'a yake shiga part d'in ya kyara da kan sa bayan haka duk wasu abubuwa da Sa'ada ke amfani dasu sunan a cikin d'akin .


Cikin yanayin tausaya masa Karime tace gaskiya yana kaunar matar nan tasa dariya Rumaisa tayi sannan tace Sosai ma kuwa , Sa'ada tayi dacen miji ban ta'ba ganin mijin irin nata ba, sun shak'u sosai Allah yasa ita d'in ba mai dad'ewa bace , Sosai suka sha fira , bayan ta zuba mata abincin cewa Karime tayi tunda yana da waya zata ajiye wa mijinta ,Koda ta dawo part gyara gidan tsaf ,kaman yanda taga gidan Rumaisa a gyare haka ta zage ta gyara gidan sosai duk da dama ba wani daud'a yayi ba, bayan ta watsa ruwa atamfar ta, mayar , gama mirror ta tasaya tana mai taje kanta ,da sallama ya shugo falon jin shuru baa ansa ba yasa ya kunno kai cikin bedroom d'in sallamar ya kuma yi ansawa tayi cikin fara'a tareda cewa sannu da zuwa bai ansa mata sallamar ba illa binta da kallo da yake ajiye matajin tayi tareda takowa zuwa gareshi jakara hannun sa ta ansa sannan ta kuma cewa sannu da zuwa ,ya shagala sosai da ganin tsawo da kuma wayan gashin Karime,ayyanawa yayi cikin ransa wai ashe tsawo da yawan kashin Karime harya Kai haka sosai abun ya bashi mamaki ganin baice komai ba yasa tace Dady sannu da zuwa wannan karan da k'arfi tayi maganar firgigi ya dawo daga duniyar tunani basarwa yayi tareda fara cire coat d'in suit d'insa, ajiye jakar inda taga ya dauke tada safe tayi tareda saurin fita da kallo ya bita ,tunda tazo gidannan bai ta'ba ganin ta haka ba wato kai ba hula ko dankwali , zama tayi saman couch yana mai k'okarin cire safar kafarsa , ba sallama ta shugo direct wurin dan k'aramin fridge d'in dake bedroom d'in tayi ,ruwan roba ta d'auka tareda tsiyaya shi cikin cup d'in glass data d'auko kitchen , cikin kazar kazar ta matsa kusa da shi,ruwan ta mi'ka masa, kallon ta yayi na wasu y'an da'ki'kai ansar ruwan yayi tareda furta thanks k'asa k'asa yayi maganar sabida haka bata ji mai yace ba ,dukawa tayi tareda fara cire masa safar kafarsa da mamaki yace why are you doing this , d'ago fuskar ta tayi cikin fara'a tace meka ce ?


D'an siririn tsaki yayi tareda mi'kewa , toilet ya shige yana mai banko k'ofa da k'arfi , ajiyar zuciya Karime ta sauke tareda tambayar kanta kodai har yanzu fushi yake da ita ,babu wanda ya sakata yi masa haka kawai labaran da Anty Rumaisa ta batane akan rayuwarsu da Sa'ada shine taji aranta tasan son kwatanta yi masa domin sosai tausayin sa ya shigeta .

 A bangaren sa kuwa ruwa ya sakarwa kansa why zata masa irin abubuwan da Sa'adarsa ke masa ,me matar Sadiq ta fad'a mata da har zata fara k'okarin yi masa shishshigi, yau acting d'in Karime ba k'aramin fama masa ciwo da rad'ad'in da zuciyar sa ke masa ba.


Jikinta a mace ta mi'ke zuwa falo zama tayi saman sofa tareda had'e kanta da gwaiwa zuciyar ta bugawa take da sauri da sauri, sam ta kasa samun natsuwa ganin yanda ya rufe k'ofa da k'arfi Sosai abun ya tayar mata da hankali , a rayuwar ta saba fuskantar wula'kanci da tozarci a wajen Baban Jimmai da Maman Jummai but yau d'innan duk sai take jin kaman zuciyar ta bata iya zure wula'kancin Ramadan ma'ana zuciyar sosai ta shiga hali da kuma damuwa mai tarin yawa.

Bayan ya fito daga toilet shiryawa yayi cikin casual shirt kalar brownda wando jeans kalar baki , fitowa yayi zuwa kitchen domin girka abunda zaya ci maganar Karime ce ta doki kunnen sa juyowa yayi tareda binta da kallo fuska d'aure kaman mai shirin dukanta , ganin yanda ya tamke fuska yasa tayi k'asa da kanta murya kaman mai shirin kuka tace ga abinci a nan , abinci ya furta cikin ransa , toh ina ta samo abinci shidai yasan ba girki ta iya ba ,ya fahimci kaman tsoronsa ya shigeta duba da yanda yaga tana sunne kai k'asa bayan haka muryar ta tuni tayi masa bayanin halinda take ciki , samun kansa yayi da takawa zuwa dining .


Zama yayi tareda cewa aina kika samo abinci , murmushi tayi sannan tace gidan yayanka ,matar sa ta zuba mun, shine na ajiye ka dawo kika ajiye na dawo ya fad'a da mamaki akan fuskar sa ansa masa tayi da eh ina jira idan kaci ka rage sai na cinye sauran ,shuru yayi yana mai kallon ta ko Sa'adar sa bata jiran dawowar sa kafun taci abinci but look at this village girl wai tana jira yaci ya rage mata ,gayran murya yayi tareda nuna mata d'aya daga cikin kujerun dining d'in zauna ya fad'a murya a tausashe yayi maganar zama tayi tana mai fara'a ,bai kuma cewa komai ba illa food warmer daya bud'e jallof rice ce data sha kayan lambu ga naman zaka kaman yayi magana , had'e yawu Karime tayi ,shi kansa tsarin abincin ya matuk'ar burge shi sosai suka saba da abincin Rumaisa lokacin da cikin mariganya Sa'ada ya tsufa sosai Rumaisa ce mai masu girke kasancewar shi baya cin abinci masu aiki shiya Sa'ada har ta koma ga mahaliccin ta bata ta'ba marmarin mai aiki ba.

Ganin yanda yake kallon abincin yasa Karime tace ko baka son irinsa ne?


 Abicin ya fara zubawa cikin flate batareda ya ansa mata tambayar ta ba , tashi tayi , batareda ya d'ago ba yace ina kuma zaki ? 


Zuyowa tayi murmushi dauke da fuskar ta tace zan saka dankwali ne kada gashi ya shiga cikin abincin kallon ta yayi na wasu y'an da'ki'kai come here ya furta , takowa tayi zuwa dining table d'in d'an nesa dashi ta tsaya, seat ya furta yana mai nuna kujera mafi kusanci dashi ,zama tayi tana mai zara idanu d'an satar kallon ta yayi abincin daya zuba a flate ya tura gabanta eat ya furta yana mai tsareta da ido, d'an murmushi Karime tayi sannan tace kaifa ba zaka ci bane wani flat d'in ya d'auka tareda zuba wani abincin ,shuru tayi tana mai kallon sa yau sam babu fara'a akan fuskar sa , abincin ya fara ci hankali kwance, ganin ba sarki sai Allah yasa ta saka hannu tana mai kai katuwar loma baki,cikin mintunan da basu kai hudu ba Karime ta share abincin ta tas mi'kewa tsaye tayi tareda cewa Alahmududilahi kallon ta yayi tareda maida kallon sa saman empty flate d'in data gama cin abinci mamaki ne kwance saman fuskar sa, kallon abincin gaban sa yayi ko rabi sai ciba but Hjy Karime ita harta share nata .


D'an susar kanta tayi ganin yanda yake kallon flate d'in da taci abinci, cigaba da cin abinci sa yayi ita kuwa zama tayi tana mai k'okarin d'aure gashin kanta, knocking k'ofar su ake mi'kewa yayi tareda nufar k'ofar, Sadiq ya furta cikin mamaki lafiya naga ba wani dad'ewa muka yi da rabuwa ba murmushi Sadiq yayi sannan yace ki matso mana sai a lokacin Ramadan ya gane Sadiq tare yake da matarsa ,gaishe da Ramadan tayi cikin mutunci ansawa yayi tareda tambayar ta yaro yana part d'in Dada Sadiq yayi saurin bashi ansa ,zaka bamu wuri mu shugo koka, mu kama gabanmu ,jin furucin Sadiq matsawa Ramadan yayi domin Rumaisa ta shiga ,aikuwa cikin farinciki Karime ta tarbi Rumaisa zama Rumaisa tayi suna mai gaisuwa cikin mutunci, yaka babbake hanya ne ko baka so na shugo g cewar Sadiq ganin Ramadan bayada niyyar bashi hanya ya shugo, d'an matswa yayi tareda cewa Bismillah.


Koda suka shugo cikin mamaki Karime ta tsaya tana mai binsu da kallo kasancewar fitowar ta kenan daga kitchen lemun kwali ne ta d'auko musu cikin fridge haka taga Rumaisa ta mata da taje part nasu shiyasa itama ta kwatanta .


Kallon su take sosai shigarsu iri d'aya ce d'an rad'a Sadiq yayi wa Ramadan it seems Abdulkarim munyi confusing nashi ta'ba rai Ramadan yayi domin still kanta a bud'e yake gashi sai wani kallon su take ,ganin yanda take kallon su yasa Rumaisa mi'kewa cikin fara'a ta dafa kafad'ar Karime sannan tace wanene mijinki a cikinsu d'an kallon Rumaisa tayi sannan ta mayar da kallonta kansu


 Mutunen naku sai uban Shan mur yake ganin d'an uwansa ya had'e rai yasa shima Sadiq ya tamke fuska he is very sure if yayi murmushi za tafi gane su easily , k'okarin matsawa ciki Ramadan yayi saurin ri'ko shi Sadiq yayi domin ya fahimci b'ata musu wasa yake son yi 


 Sa'ada lokacin da ta fara ganinsu tare kasa gane su tayi haka zalika Rumaisa itama kasa gane su tayi Hjy Karime kuwa sosai ta mayarda hankalin ta kansu shigarsu iri d'aya ce ,dama kusan kaya iri d'aya suke saye but yanda suka saka sutura iri d'aya duk da ba a gida d'aya suke ba shine abunda yafi bama Karime mamaki a wajen Rumaisa kuwa inda sabo ta saba tun tana mamakin yanda suke saka sutura iri d'aya harta daina domin tuni ta fahimci abun nasu a zuciyar su yake .


Murmushi Karime tayi tareda takawa zuwa inda suke hannun shi ta kama tareda cewa ko a mafarki zan iya banbance ka wani abu yake ji wanda sam bai san ya zaya misalta shi ba dariya Sadiq yayi haka zalika Rumaisa , matse hannunsa tayi sannan tace kayi tunanin bazan gani ka ba d'an kallon ta yayi amma baice komai ba ka bata ansa mana cewar Sadiq gyaran murya yayi sannan yace fad'a mun ta yaya kika ganeni


Murmushi tayi mai ma'anoni tareda zare hannun ta daga nasa zan fad'a maka amma ba yanzu ba, gaba tayi abunta da kallo ya bita yana mai kallon yanda gashin kanta ya sauko sosai ta bayan ta ajiyar zuciya yayi tareda bin bayan zama tayi nesa dasu kasancewar yanzu Sadiq yana manne da Rumaisa .


Kujerar da take zaune ya zauna but d'an nesa da ita , Sadiq ne mai fad'in amarya ya bakunta murmushi tayi sannan tace Alahmududilahi ,Masha Allah ya furta yana mai kallon d'an uwansa Wanda ke ta uban bak'in rai , Rumaisa ce ta d'an ta'bo Sadiq gyaran murya Sadiq yayi sannan yace wai my queen ba fita za kuyi ba kada fa dare yayi muku , murmushi Rumaisa tayi sannan tace Amarya kin shirya Kuwa kallon mununta tayi sannan tace wallahi na shafa'a ashe yaune kika ce za niyi miki rakiya zuwa kasuwa murmushi Rumaisa ta kuma yi sannan tace Green house zaki rakani ,kallon Ramadan Karime tayi sannan tace zan raka ta , baice komai ba illa tashi da yayi tareda shige bedroom ,kallon Rumaisa Karime tayi kaman mai shirin kuka alama suka yi Mata akan ta bishi ciki.


Zaune ta tarar dashi ya juya mata baya sabida haka ba zatace ga ainafin abunda yake yi ba , come here ya furta yana mai kallon ta , matsawa tayi ido cike da kwalla tunda ya shugowar sa d'aki ranta ya gama bata bazai barta ta yiwa Rumaisa rakiya ba kuma wallahi tana matuk'ar son fita waje ita sam bata saba zama wuri d'aya irin haka ba ,a duk ranar duniya Karime saita fita waje but tunda ta shugo gidannan ko waje bata le'ka ba yau kwana 5 kenan shine yanzu ta samu damar fita yana son yi mata buk'ulu.


D'an nesa dashi ta tsaya, rakiya zaki mata ke bakya ra'ayin siyan komai ne ,washe baki tayi "eh ai kaga ba kud'i ne dani ba batareda ya kuma magana ba , mi'ko mata bandir d'in y'an 1500,000 yayi , sa'ko gareka ne cikin washe baki tayi maganar ,tafiya ya fara yi harya kai bakin k'ofa juyoww yayi tareda cewa kiyi sauri kina b'ata muku lokaci.


Lokacin da ta fito falon duk sun fice kasancewar sai data d'an b'ata lokaci kafun ta fito , waje ta nufa cikin sauri, daga nesa ta hango mijinta"jingine yake jikin mota d'an nesa dasu Sadiq "hannuwan sa cikin aljihun jeans d'insa kallon su Rumaisa yake ba zaka iya gane yanayin da yake ciki ba ,Sadiq ne rungume da Rumaisa magana suke cikin shakuwa da kuma soyayyar junann su tunda ta fito take kallon mijinta sosai tausayin sa ya mamaye zuciyar ta yanayin yanda yake kallon su da yanayin ya yanda ya jingina da motar sa ,duk wani farincikin zata fita ji tayi ya bar jikinta tausayin sa ne ya mamaye zuciyar ta "cikin mutuwar jiki ta k'arasa inda yake bai mata magana ba haka zalika ita ma .


A bangaren Sadiq kuwa driver seat ya bud'e ma Rumaisa kafun ta shiga saida suka kuma rungume juna , kissing forehead d'inta yayi a dawo lafiya Beb ansa masa tayi da in sha Allah,ganin Rumaisa ta shiga mota ne yasa Karime kallon sa tareda cewa saina dawo a dawo lafiya yace still bai kalle ta ba "tafiya tayi jiki a mace motar ta fara k'okarin bud'ewa sam bata ta'ba shiga mota irin haka ba that's why ta kasa bud'e ,juyowa tayi tana kallon sa alamun ya kawo mata d'auki , ganin tana kallon sa yasa ya kauda fuskar sa daga kallon wurin , ta ciki Rumaisa ta bud'e mata k'ofar ,bayan ta shiga murmushin ya'ke tayi " mai gadi ne ya bud'e musu get cikin kwarewa Rumaisa ta d'au hanya sai Green house.


Tunda suka d'au hanya tsit Karime tayi kaman ruwa ya cita "jefi jefi Rumaisa ke bata labari da um sai aaa kawai take iya fad'a " koda suka isa Green house d'in ba wani sakin jiji tayi ba damuwa ce fal a cikin ranta , kud'in hannun ta ta mi'kawa Rumaisa tareda cewa gasu ya bani Dan Allah ki siya mun abunda kika ga ya dace d'an murmushi Rumaisa tayi"wai meke damun kine Amarya naga baki d'aya yanayin ki ya canza , cikin yanayin damuwa tace wallahi bana son ganinsa cikin damuwa ne a yau d'innan naga duk ya canza mun dafa ta Rumaisa tayi sannan tace kiyi hak'uri mu gama siyayya kinga dare keyi mayi magana a hanya "yanzu fad'a mun abubuwan da kike ra'ayi ina buk'atar kayan sawa Kinga wad'annan kayan na jikina su kad'ai gareni ,cikin rashin fahimta Rumaisa tace Bangane ba , kina son kice mun bakida wata sutura sai wannan " haka nake nufi shuru Rumaisa tayi na wasu y'an sec ba'a miki lefe bane "dagani sai kayan jikina nazo gidan ku sabida haka ke taima mun na siye kaya ,sai yanzu ta fara fahimtar abun tabbas akwai lauje cikin nad'i,ta tuna lokacin da Sadiq ya dawo aiki ya fara mata bayani kan auren Karime da Ramadan but ya dai me mata auren Ramadan da Karime Momy ta had'a shine da wata manufa ,ajiye duk wani tunani tayi "muje Karime na taya ki siyayyar.


Haka kuwa a kayi domin Rumaisa ta taya Karime siyayya,duk abunda tasan zata buk'ata shi suka siya.



A can bangaren su Ramadan kuwa ba rabuwar arziki su kayi ba shida d'an uwansa sosai yau suka sha fad'a duk akan Sadiq ya kushe Sa'adatun sa ne , kuma shi Sadiq cikin wasa yayi Maganar amma haka Ramadan ya rufe shi da fad'a .

A falon Momy suke zaune bayan tafiyar su Karime Sadiq ne yaja d'an uwansa zuwa part d'in Momy sosai tayi murnar ganin sa , kasancewar tun mutuwar Sa'ada sam baya son shiga harkar Momy kyautata mata kuwa yanayi duk abunda zata buk'ata ya kanyi mata amma baya ga haka kullun nisantar kansa yake da ita ,tuni yaso tashi daga gidan su Abba ne yak'i amince masa,a cewar Abba Koda zai koma tabbas ya tabbatar da yayi aure tukun. da tuni ya koma sabon gidan da ya gina wanda ya gina gidanne su koma shida Sa'adar sa .


Fira suke sama sama cikin wasa Sadiq ya furta hakanan kake haukar son Sa'ada wallahi muni yayi mata yawa kawai dan tana da haske ne da bata ganuwa " aikuwa sosai Ramadan ya zage Sadiq tas hada mi'kewa kaman zai dake sa.

Momy ce mai faman bashi hak'uri ganin kaman hak'uri da take bashi kaman k'ara zuga shi take yasa ta fara yi masa fad'a tareda zage Sa'ada ta uwa ta uba baice da Momy komai ba sai uban hawaye dake , kanka farau mutuwar mata asane nake da kai tun mutuwar Sa'ada ka rage damuwa dani ,ka dauki son duniya ka d'aurawa matacciyaar matar ka toh ka saurareni da kyau Aliya na dawowa k'asar nan auren ku zaya tabbata kuma duk lokacin ka shiga hakkinta Allah bazai barka ba , ina ma amfani duk kabi ka susuce akan kyamisasshiyar yarinya sabida hauka har fad'a kake da d'an uwanka akan matacciya.


Hawaye shabe shabe ya dawo part nasu direct d'akin sama yayi "rungume picture d'in Sa'ada yayi yana kuka kaman ransa zai fita .


Mu had'u next page

 * HANAADY

*