Rental marriage 8
by @hanaady
*NIKAAH*
*Marriage for Rent)*
*By*
*HANAADY*
( *Rahama Aminu Bala)*
*WhatsApp*
*****
*Follow me on Whatpad*
*Rahama000*
HE HAD THE COURAGE
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?
Marubuciyar
BAHAAR paid book
And now NIKAAH(Rental Marriage).......
Free book
*Not edited*
Page 8
Su Hjy Karime a gaye aka dawo gida ,ga cikin ta sai kukan yunwa yake "ai kuwa koda ta dawo kayan da suka siyo ta baje saman bed,kallonsu take d'aya bayan d'aya murna da farinciki fal a cikin ranta,wata kya'kyawar rigar bacci ta d'aga mi'kewa tsaye tayi tareda d'aura ta saman jikinta ba doguwa bace bata kaima mata kwaiwa ba sosai rigar tayi mata kayau normal rigar bacci ce bata da wani tsaraice domin irin rigar baccin nan ce mai pictures d'in cartoon a jikinta , tun a can ta kagara taji rigar a jikinta sabida haka batareda tunanin komai ba ta fad'a toilet ,bayan ta fito wanka lotion ta shafa tareda fesha body spray mai kamshin dadi' zanin ta ta d'aura saman rigar tareda ficewa zuwa kitchen.
Juice ta d'auka cikin fridge tareda bud'e wata locker anan ne taga biscuits kala kala d'iba tayi iya yanda take tunanin zaya ishe ta bedroom ta dawo "bayan ta gama gyara cikin ta falo ta dawo tareda jiran dawowar Ramadan ita a tunanin ta baya gidan.
Sosai dare ya tsala domin 12:30 tayi bacci ne sosai a idanuwan ta , tunowa da wayar daya bata ne yasa tayi saurin fad'awa bedroom "Kiran number sa tayi bai d'aga ba kiran wayar ta cigaba dayi still no response , number Rumaisa ta kira kasancewar Rumaisa ta saka mata number ta bayan haka ta koya mata yanda ake kira "Dan Allah ko zaki tambayi mijinki inda Daddy yake har yanzu bai dawo gida ba cikin damuwa Karime ke maganar "kwantar da hankalin ki Karime mijinki yana cikin gidan ku amma kada kiyi kuskuren fuskantar sa a yau d'innan domin Sadiq ya fad'a mun cewa yana cikin damuwa kuma if yana cikin irin wannan halin babu mai ra'bar sa bangane me kike nufi ba cewar Karime "ina nufin yana saman bene Amma kada ki kuskura kije inda yake katse kiran Karime tayi tareda kwasawa da gudu saman bene , tunda tazo gidan bata ta'ba haurawa sama ba sai yau.
Koda ta shiga katon falo ne irin na kasa gyare yake tsaf kaman akwai mutane a ciki tsarin kujerun falon yayi matuk'ar kyau dube dube ta fara yi tana mai Kiran Daddy ,a tsora ce take but daurewa kawai take yi hankalin ta sam ba'a kwance yake ba gurin ta shine taga mijinta .
Ganin k'ofar wani bedroom a bud'e yasa tayi saurin fad'awa nishin sa ta fara jiyowa d'akin babu haske sosai zaune ta tarar dashi bakin gado rungume yake da hoton Sa'ada kuka yake sosai har muryar sa ta dashe , cikin tausayin sa ta matsa kusa dashi ,zama tayi daf dashi tareda dafa shi jin saukar hannunta jikinsa yasa yayi saurin mi'kewa tsaye itama tashi tayi tana mai cewa Daddy me aka maka k'okarin ta'ba shi take batai auni ba saukar tafin hannun sa taji a saman kuncin ta ji kake tas hannu yasa tareda ture ta bayabaya tayi zata fad'i saurin ri'ke hannun wardrobe tayi ,kallon sa tayi sosai tayi mamakin halin da yake cikin domin duk ya fita hayyacin sa .
Hawaye take domin ta maru iya maruwa but hankalin yana kansa k'ara matsawa tayi kusa dashi ture ta ya kuma yi wannan karan mamarsa tayi ta shige jikinsa ,hannuwan ta ta zagaya ta jikinsa tareda matse shi sosai , k'okarin zareta daga jikinsa yake zamewa sukayi saman gado shine a k'asa ita a sama tausayin sa take ya tausaya mata lokacin da take kuka ya saurari labarin har rungume ta yayi ,bayan haka har bakinta yayi ma abunda turawa keyi "k'okarin tashi yake hannu tasa tareda mayarda shi rufe idanuwan ta tayi tareda d'aura bakinta saman nasa iska take hura masa a baki a tunanin ta haka akeyi a nashi bangaren kuwa ji yayi kaman tana zare duk wata damuwa tasa "hannuwan sa yasa tareda k'ara matseta jikinsa kissing nata ya fara tareda juyawa ya dawo saman ta kissing bakinta yake da sauri sauri zame bakinsa yayi tareda yaye rigar jikinta zuwa can saman wuyan ta sosai Ramadan ya zage wajen sarrafa matarsa.
Komai ya tuna oho saurin janye jikinsa yayi tareda shigewa toilet" a bangaren Hjy Karime kuwa nishi take sama sama tana mai jin wata sabuwar kunyar Ramadan"ana shi bangaren ruwa ya sakarwa kansa yana mai jin haushin kansa akan me zai biye mata why ya kasa ture ta daga jikinsa lumshe idanuwan sa yayi yana mai tuna yanda moments nasu ya kasance anata bangaren kuwa tashi tayi zaune tana mai gyara rigar ta da ya yaye zaune tayi saman bed d'in tana bin k'ofar toilet d'in da ido.
Each and every moments nasu ya fara tariyo cikin ransa sosai ruwa ke dukansa haka zalika sosai yanayin sa ya canza "bukatace ta mugun taso masa bazai iya tuna when last irin haka ta faru dashi ba "jinginar da jikinsa yayi jikina bangon toilet d'in ruwa na mai dukansa idanuwan sa a rufe suke.
Picture d'in Sa'ada ta d'auka tana kallon ta murya a dashe tace kinyi sa'ar samun masoyi mai sonki da kaunar ki duk da bakya duniyar ,saukar hawaye taji saman fuskar ta Sosai tayi mamaki hawaye a fuskar toh wai kukan mema take ajiye picture d'in tayi tareda dafe zuciyar ta dake mata wani zugi.
Ganin ya d'auka lokaci bai fito ba yasa tayi saurin sauka daga saman gadon knocking k'ofar take Daddy lafiya na jika shuru Daddy kana lafiya?
Bud'e k'ofar yayi tareda fizgo ta cikin toilet d'in "jinginar da ita yayi jikin bangon toilet d'in jin yanda ruwa ke sauka jikinta yasa ta fara kyarmar sanyi sam Karime bata son shiga ruwa ,gashin kanta ya ji'ke sharkaf "matsowa yayi kusada da ita tareda had'e fuskar su tsinin hancin sa yasa yana mai gogawa saman fuskar ta jikinta kyarama yake kamar mazari abubu sunyi mata yawa ga ruwa na dukan su ga abunda yake mata ,zare rigar jikinta yayi cikin kyarmar jiki.
A haka ta tsaya kamar status tattabata yayi sarransa "tunda ta rufe idanuwan ta bata bud'e su ba tsayawa yayi da abunda yake kallon ta yake kaman yau ya fara ganin ta gashin kanta ya kallla yanda ya zubo a gefen fuskar ta gashi duk ya manne mata wani irin kyau tayi" ga yanda ruwa ke sauka a jikinsu sosai yanayin ya shagaltar dashi" saida ya gama kalle ta tas tukun' wannan karan cikin kasala ya bar toilet d'in wanda ita bata ma san ya fita ba .
Ta dad'e a tsaye still ruwa yana dukan ta " A bangaren sa kuwa tuni ya tsane jikinsa ya canza kaya zuwa kayan bacci na maza "gefen gado ya zauna tana mai ajiyar zuciya" kallon k'ofar toilet d'in yayi yanda ya barta a bud'e still haka take k'arar ruwa yake ji " da mamaki ya Mi'ke tareda nufar toilet d'in a tunanin tunda ya fito ai itama ta fito ta canza kaya .
Daga bakin k'ofa ya tsaya Yana kallon ta yanda ya barta still haka take saurin kauda idanuwan sa yayi daga kallon ta " baki gaji da ruwan bane muryar sa ta doki kunnen ta jin murya sa daga nesa yasa a hankali ta bud'e idanuwan ta bakin k'ofa ta hango shi harma ya canza kaya saurin janye idanuwan ta tayi "dan satar kallon sa tayi ita yake kallo hankali kwance tunowa tayi da ya cire mata riga fa tuni "aikuwa da sauri ta juya masa baya a nashi bangaren kuwa k'ofar toilet d'in ya rufe tareda saurin barin wurin .
Da lema haka ta d'auki ragar ta ta saka kashe ruwan tayi domin ta iya tun lokacin da tayi wa Little wanka a ranar ta iya kunna shower da kashe ta "kunyar fitowa take ji Amma sosai take jin sanyi ganin bazata iya fita ba yasa ta zauna saman kwamin wanka tana ta mazurai.
K'ofar toilet d'in ya bud'e tareda cewa me kuma kike jira ,saurin tashi tayi tareda saddar da kanta k'asa juyawa yayi simi simi ta fito daga toilet d'in .
Bakin toilet d'in ta tsaya sai kyarmar sanyi take inda take tsaye ruwane ke d'igowa daga rigar ga zuwa k'asa Kallo d'aya yayi mata ficewa yayi bayan wasu y'an minutes dawowa yayi dauke da mopper guge ruwan ya fara yi "ajiye mopper yayi tareda nufar wardrobe wani towel ne ya d'auko mata mai shegen kyau "mi'ka mata yayi cire rigarnan ki d'aura wannan ansa tayi cikin kunya .
K'okarin komawa toilet take "ina kuma zaki cikin inda inda tace zan koma na canza kaya kafeta da ido yayi sannan yace ki canza ana ganin fuskar sa ba alamun wasa yasa ta fara k'okarin canza kayan ajiye mofar yayi tareda jawota zuwa daf dashi "hannu yasa tareda cire rigar jikinta kare kirjinta tayi tana mai sunne kai k'asa a yau d'innan ji take duk kunyar duniya akan ta ta Kare "towel d'in ya d'aura mata tared cewa sa hannu ki ri'ke mana saurin d'aura hannuwan ta tayi tareda tallafe towel d'in. " Ki cire pant d'inki ya furta yana mai d'aukar rigar data jike " cikin kunya ta cire pant d'in inda taji dad'i cikin sabbin panties d'in da ta siyo ne yau "d'aukar pants d'in yayi toilet ya koma tareda dauraye rigar da pant d'in fitowa yayi dauke da su a hannun sa fuskar murtuke yace kiyi amfani da towel d'in ki tsane gashin kanki toh ta ansa cikin jin kunyar sa"ficewa yayi.
Lokacin daya shugo still tana tsaye sai k'okarin tsane gashin kanta take da towel d'in " saukar hannun sa taji saman hannun ta take goge gashin kanta towel d'in ya ja kaman yanda yaga tana yi cigaba da goge mata kan yayi ita kuwa k'okarin tatttare towel d'in take kada tsostai yasa ya su'buce domin iya shine a jikinta.
Fuska murtuke yace ina siyayyar da kika yo ? Cikin inda inda tace tana d'akin kwanan mu saki towel d'in yayi tareda cewa muje gaba yayi ri'ke towel d'in tayi tareda mara masa baya "saman couch ta ajiye su sabida haka yana zuwa dasu yayi arba zazzage su ya fara yi wata wa leda ya d'auka yana k'okarin bud'e ta cikin sauri ta fize ledar daga hannun sa cikin shan mur yace menen a ciki da bakya son na gani inda inda ta kama matsowa yayi daf da ita tareda fizge ledar daga hannun ta zazzage kayan cikin ledar yayi pants da brazier ne kallon ta yayi still fuskar murtuke hannu yasa tareda d'aukar bra d'aya da pants nunata yake dasu is this your size kai k'asa tace umm kallon sa ya mayar kansu ta nada boyayyan jiki zuciyar sa ta ayyana masa ajiye su yayi tareda cewa baki siyo hairdryer ba ne eh ta fad'a tana kallon sa alamun tana buk'atar karin bayani baki siyo abun busar da kai bane kanta na k'asa ta ansa da eh why baki siyo shi ba bayan kinsan kina da gashi haka shuru tayi tana sauraron sa ' lokacin da kina gida dame kike busar da gashin naki ?
K'ara gyara towel d'in jikinta tayi sannan tace nakan d'auki lokaci ban sakawa kaina ruwa ba kusan duk k'arshen wata nake wanke kaina why sai k'arshen wata? Kafe ta da ido yayi yana jiran ta bashi ansa saida ta d'an soshi kanta sannan tace duk lokacin da na gama period ne nake wanke kaina shuru yayi yana kallon ta still fuskar sa a murtuke take wardrobe d'insa ya bud'e wani towel d'in ya d'auka come here ya furta yana mai nuna mata saman bed .
Kai k'asa ta matsa cewa yayi ta zauna "zama tayi saman bed d'in"tsaye yayi a haka ya fara goge mata kan ba lafiya ya d'an fara shan iska towel ya nufa domin ajiye towel d'in da kallo ta bishi har ya shige "saman couch ta koma da zama sai raba idanuwan take "bakin gado ya zauna wata leda wadda ba'a bud'a ba ya kalla saurin bud'e ledar tayi washe baki tayi sannan tace kaga na siyo yadin Islamiyyar ka, d'inki kadai ya rage mun matar yayanka tace zata bama tailor d'inta ta d'inka mun .
Shuru yayi yana kallon ta tunowa tayi da canzin sa sabida haka mi'kewa tayi tareda nufar sa canzin ta mi'ka sama da mamaki ya bita da kallon Saida ta washe baki sannan tace ragowar kud'in kace shuru yayi na wasu y'an da'ki'kai kallon ta yake yana mai karantar ta ki ajiye wurinki cikin murna tace ka bani duka ne eh ya furta k'asa k'asa da murna ta koma saman couch d'in dai juya kud'in take"dama Saida Rumaisa tace su duka ya bata amma Karime ta'ki yadda wai hada canji zata mayar masa.
Standing fan ya kunna tareda matsoda ita saitin Karime "hannun sa ya d'aura saman kashin kanta tareda d'an yamutsa shi yanda zaiyi saurin bushewa.
Bakya jin sanyi ne ? Murmushi tayi wardrobe ya bud'e riga ya d'auko mata cikin rigunan sa da take sawa ga mamakin ta hannu yasa ya tattara gashin kanta waje d'aya bata gama dawowa daga duniyar mamaki ba ji tayi ya kama hannun ta zura shi yayi cikin riga haka ya saka kanta kyarmar jiki ta fara ita dai yau ta kasa gane yanayin sa duk wata kyautatawa da yake mata fuskar sa a murtuke take sam babu fara'a akan fuskar sa "rigar ya saka mata juya mata baya yayi zare towel d'in jikinta tayi tareda idasa saka rigar.
Towel d'in ya ansa tareda kai shi toilet " gado ya hau k'okarin kwanciya yake ji yayi tace na gode Dady alamu yayi mata akan tazo cikin jin nauyin sa ta matsa gefen sa ya nuna mata "zama tayi tana mai sadda kai k'asa "yaushe na haife ki da kike ce mun Dady jin yanda yayi maganar ta fahimci ya d'an sauko "washe baki tayi sannan tace ai itama Sa'ada haka take ce maka da mamaki yace Sa'ada is my daughter kefa shuru tayi ki daina kirana da Dady toh me zan Kira ka wannan ya rage naki shuru tayi na wasu y'an da'ki'kai daga bisani cewa tayi mijin Sa'ada da mamaki yace ban ganeba washe baki tayi sannan tace zan ringa kiranka mijin Sa'ada ok ya furta shuru suka yi na wasu y'an da'ki'kai .
Hannunsa ya d'aura saman kashin kanta ya fara bushewa ya furta k'asa k'asa murmushi tayi sannan tace shiyasa bana son saka mashi ruwa d'an Kankance idanuwan sa yayi sannan yace ya akai kike da gashi da yawa haka ?
Washe baki Hjy Karime tayi sannan tace Mamana tana da gashi sosai autar mu Sa'adatu itama haka take da gashi "kina da kanwa Sa'adatu eh ta ansa masa "ita ce autar mu Sa'adatu ya furta tareda d'an murmusawa satar kallon sa tayi ji tayi gabanta na faduwa wato sunanta kad'ai yana saka shi nishad'i maganar sace ta dawo da ita daga yanayin data shiga yaushe zata zo? Kaman mai shirin kuka tace tunda Baban Jummai ya bada haya ta babu Wanda na kuma gani cikin dangina Amma tunda kana son ganin Sa'adatu zanje gida na taho maka da ita fuskar ta ya tallafo sannan yace ina son Sa'ada sosai that's why duk mai suna Sa'adatu ina son kyautata Mata please kiyi k'okarin kawo mun ita murmushin ya'ke tayi sannan tace in sha Allah .
K'okarin mi'kewa take hannun ta ya ri'ke kallansa tayi baki tambaye ne ba akan abunda ya sakani cikin halin damuwa kyara zama tayi sannan tace ina ga kaman ba hurimi na bane shuru yayi na wasu y'an sec "kin manta yanda kika fad'a mun damuwar ki murmushi tayi sannan tace bani da kowa ne saikai shiyasa na fad'a maka hannun ta ya kama sannan yace by now banida kowa sai ke d'aga kai tayi tana bin sa da kallo ita ba yarinya bace dole ta fahimci halida take ciki dole ta fahimci yanda zuciyar ta ta dauke shi tuni ta fahimci soyayyar sa ta riga da tayi mata mugun kamu wanda Sam bata san lokacin da hakan ta faru ba .
Ki tambaye ni please ya furta yana mai matse hannuwan ta cikin d'aurewa tace me aka maka duk abunda ya faru tsakanin sa da Momy da kuma Sadiq ya kwashe ya fad'a mata karawa yayi da cewa Sadiq saiya aibata masa mata .
Kayi hak'uri kada kace zaka yi fushi da mahaifiyar ka koh d'an uwanka shuru yayi yana sauraren ta iyaye ba'a fushi dasu komai suka yiwa d'an su itace dalilinka zuwa duniya bugu da Kari aljannar ka tana karkashin kafar ta nasan ka fini sanin hakan domin Allah ya hore maka ilimin addaninmu "thank you ya furta cikin mutuwar jiki domin yasani ya san mahimmanci uwa da matsayin ta but baya shiga sabgar Momy tun mutuwar Sa'ada ya sani abunda yake ba dai dai bane but babu Wanda ya ta'ba tarar sa yayi masa tuni akan abunda yake sai yau "yau d'innan Karime ta zame masa abiyar shawar ta zame masa abiyar sa "shuru tayi tana kallon sa hannun ta ya kuma matsawa sannan yace thank you Karime zanyi k'okarin daina fushi da Momyna and bazan yi fushi da Sadiq ba murmushi tayi sannan tace toh mijin Sa'ada dare yayi muyi bacci koh .
Tashi yayi saurin ruk'o ta yayi murya k'asa k'asa yace please don't go "Best da mamaki tace nice Best yes ya furta you are my best friend now gabanta fad'uwa yayi wato bazai kalle ta a matsayin Mata ba sai dai kawa ba komai hakanma ta gode marairaice fuska tayi me kake so nayi kusa dashi ya nuna mata please come and sleep here "matsowa tayi a hankali ta kwanta inda ya nuna mata juya masa baya tayi murmushi yayi sannan yace thank you Best shafa gashin kanta yayi sannan yace please ki juyo ki fuskance ne "gyarawa tayi tana fuskantar sa mijin Sa'ada kayi bacci gobe akwai aiki ina son yi miki godiya ne thanks Best murmushi tayi sannan tace nima ina godiya mijin Sa'ada kissing kuncinta yayi tareda cewa good night Best juya mata baya yayi boyayyar ajiyar zuciya tayi tana jin wani sabon yanayi .
Sallar asuba ya tayar da ita da mamakin ta fuskar dauke take da murmushi murza idanuwan ta tayi tareda cewa wai har asuba tayi "tun d'azu take faman tada ki "k'okarin saukowa take kama ta yayi tareda cewa be careful murmushi ta mayar masa zan tafi ya fad'a cikin sakin fuska a dawo lafiya mijin Sa'ada murmushi yayi tareda ok Best ficewa yayi cikin sauri.
Ajiyar zuciya tayi tareda zaunawa saman bed duk abunda ya faru jiya ne ya dawo mata tayi tuanin if ya tashi zai cigaba da sha mata mur tunda ya sauka saman gadon ta tashi daga bacci tana jin lokacin da yake wanka toilet bata son ta tashi ne ya canza mata sai gashi still ya kirata da sunan da ya saka mata jiya .
A bangaren Ramadan kuwa bayan sun gama sallar had'uwa suka yi da Sadiq "sosai gaban Sadiq ya fad'i domin yasan tabbas d'an uwansa bazai masa magana ba haka zalika koya yi masa banza za yayi dashi but da mamakinsa hannu ya bashi suka gaisa and fuskar sa a sake take .
Aikuwa Yana komawa gida ya k'wala ma Rumaisa Kira rabari ya bata akan yanda Ramadan yayi masa magana harda murmushi sosai Rumaisa tayi mamaki domin sun san halinsa da mugun ri'ko idan aka masa abu.
Bayan sun rabu da Sadiq samun kansa yayi da son zuwa sashen Momy "zaune ya tarar da ita saman sofa nesa da ita ya zauna kasancewar gari baiyi haske ba kuma babu wani wadataccen haske a falon" ita a tunanin ta Sadiq ne cewa Sadiq kun had'u da Ramadan a masallaci ansa mata yayi da nine Ramadan saurin mi'kewa tsaye tayi tareda nufo shi hannuwan sa ta ri'ke tareda cewa ka yafe mun my son I don't know meke damuna wani lokacin na kanyi mamakin kaina sam kaman wani abu ke canza mun tunani ya wuce Momy na dama nazo na gaishe ki ne Allah yayi mak albarka Ramadan Ameen ya furta k'asa k'asa baya iya tuna when last Momy ta shi masa albarka gaskiya yayi kuskure no matter what take masa she is his Momy .
Momy zan koma aaa Ramadan tun yanzu eh ya furta yana k'okarin tashi " da kallo ta bishi harya bace mata da gani ajiyar zuciya tayi .
A bangaren Karime kuwa tayi mamaki da har yanzu bai shugo ba ta kasa samun natsuwa kad'an kad'an ta kalli k'ofa "jin alamun bud'e k'ofa yasa tayi saurin kwantawa tareda rufe ido
" Bakin gadon ya zauna hannun sa ya d'aura saman kashin kanta shafawa yayi tareda cewa Best bud'e idanuwan ta tayi tana amma Sam bata yadda suka had'a ido ba domin abubuwan data mata jiya sune cikin kwanyarta anshi bangaren kuwa bai bama zuciyar sa tariyo masa abunda ya faru ba all he can think of shi ne yanda ya iya yafe ma Sadiq da Momy lokaci d'aya.
Thank you Best naji dad'in shawarar ki mun gaisa da Momyna and Sadiq murmushi tayi sannan tace gaskiya na cancanci kyauta "hannunta ya kama fad'a mun me kike so washe baki tayi sannan tace wasa nake fa "But I'm serious ya furta shuru tayi na wasu y'an sec ka amince naje makaranta "kina son komawa school ne Islamiyya nake nufi ta fad'a oh na amince Best murmushi tayi nagode " maganar makarantar boko fa a ina kika tsaya " na gama makarantar secondary School duka a dagaske ya furta cikin mamaki ansa masa tayi da eh "then kina son komawa school bazan iya ansa maka ba yanzu
ok take your time ya furta tareda rungume ta" zara idanu ta fara yi tsakanin jiya da yau da kasa gane meya dauke ta zare jikinsa yayi tareda nufar wardrobe d'insa ta lura shiryawa za yayi sabida haka ficewa tayi zuwa falo .
A bangaren Aliya kuwa Koda Hjy Mariya tayi mata maganar dawowa Nigeria cewa tayi ita ba zata dawo ba har sai idan Ramadan ne ya buk'aci dawowar .
Mu had'u next page
*Please commitment*
*Like*
*And share.*
*Rahama Aminu Bala* *HANAADY*