RAYUWATA (WRITTEN IN HAUSA LANGUAGE)
Part 3
Saukowa halima tayi daga sama da ruwa hannunta hajiya nafisa ta kalleta tace Halima! Hakane ko ? Hajiya Khadijah tace yeah itace
"Wow Masha Allah kai this girl is very beautiful matso Halima" Halima ta matso ta ajiye ruwan sannan ta miqo gaisuwar ta "ina kwana Aunty" Lafiya qlw Halima, ya karatu?
Lafiya lau anzo lpy?
Ah Alhamdulillahi!
Mahmud dake gefe yana xaune cikin nutsuwa yana binsu da kallo
"Ga mahmud nan dana ku gaisa"
"Oh ina wuni, ya hanya, Halima, Humaira da Salma suka gaidashi
Shi kuma yayi murmushi yace sannunku!
Hajiya Nafisa tace ina Abdul?
Shi kadae ne bangani ba
"Ah yaje ya karbo min wasu kaya wajen friend Dina yanxu xaki ganshi oh! lemme call him ma inji if he's on his way
Ta dauki wayarta ta danna don kiran Abdul se sukaji qarar mota ah! I think shine ma
Me gadi ya bude mishi ya shigo da mota sannan ya shigo cikin gida inda suke suka ga juna suka gaisa.
Hajiya khadija tayi musu iso wajen cin abinci yayin da su Halima suka kawo abinci qamshi ya cika gidan.
Bayan sun gama cin abinci hajiya Khadija da hajiya nafisa sun bar wajen sun kebe domin suyi maganganunsu ma zumunta.
Bayan sun gama se sukayi sallama domin zasu tafi sannan tace ita tanaso su ziyarce ta
Hajiya Khadija "Ai zaki ganni qawata Akwai abubuwan da xamu sake tattaunawa se dai mun hadu.
Tom yar uwa bye bye!
Sukayi sallama sannan suka nufi gidansu
Bayan tafiyarsu da daddare Halima tayi sallah sannan ta xauna dakinta ta dauko wayarta ta kira Khalil se taji shigowar mummy dakin se ta ajiye
"Salamu alaikum"
"Wa alaikum assalam mummy, sannu da hutawa"
"Yww" sannunki dai
Em yw! Kindai ga mahmud ko ?
He is a nice guy and sunada kudi, hajiya nafisa batada matsala she's my close friend
Kuma kina ganinshi akwai ilimi tattare dashi
Bama a Nigeria ya girma ba and I think chan xai tafi dake after marriage.
Shiisa nace yau tazo dashi ya ganki ki ganshi kafin a hada muku zama na musamman
"Mummy I don't get it"
"Okay lemme make you understand Halima, mahmud's mom and I mun yanke hukunci zamu hadaku aure.
Yanada budurwan da yake so a chan kasar waje but hajiya nafisa bataso ya auro mata wata da ba yar Nigeria ba nima kuma mahmud yayi min nace mata kawai a hadaku ayi auren da wuri tunda wancen shashashan bai alamun fitowa ba.
"Mummy munyi magana dashi yace zai turo ko a san dashi kafin yasamu ya kawo kudi please mummy give him some more time Wlhi he's trying his best yaga yayi yadda xaiyi kuma mun kasance tare for almost 5 years"
"Oh! Bari kiji in ma kiranki yake ya kashe ki da kalaman banza to wallahi I won't take it daga yau karna sake ji kunyi magana dashi ko ta what's app, idan nasake ji zaki fuskanci bacin rai!
Kinji ko?!
Ba 5 years ba ko tare aka haifeku dole ku rabu yww!
"Tohm mummy Dan Allah kibani yau muyi magana"
Halima ta fada idonta cike da ruwa
"Oho miki"
Hajiya Khadija tafada ta fita da dakin cikin fushi
Halima ta dauki wayarta ta danna number din khalil tana kuka
Khalil ya dauki kiran ya fara yi mata kalamai kamar yadda ya saba kullum