Page 04
by @nanameera08
*BA ITA BA CE!..💖💖*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
*@Nanameera08* _wattpad_
*nanameera08* _arewabooks_.
*Nanameera ce!*
*Daga marubuciyar*
*NAANAH*
*TSAKANINMU*
*SHEIKH HEESHAM*
*FATTOMAH*
*nd now*
*BA ITA BA CE!*
# *SQUAD 2024*
```Page 04```
Kallonsa Mommy take da tsananin tashin hankali kwata-kwata ta kasa fahimtar abinda yake faɗa kwakwalwarta ta tsaya cak!, Miƙewa tayi dan fita daga gidan saidai kafin takai kofar zauren tayi baya luuu zata waɗi da sauri Farooq ya tare ta hankali tashe kuma yake furta "Mommy!! Mommy!! Mommy" tuni jikinta ya saki hakan yasa kawai ya yi waje da ita, kallonta ya yi hannunsa riƙe da goran ruwan sai sauke numfashi take a hankali shi kansa dauriya kawai yake amma tabbas abun ya tabashi sosai, riƙo hannunsa Mommy ta yi murya bata fita sosai ta ce"Farooq ka fahimci abinda malamin nan ke faɗa kuwa? ni ban fahimta sosai ba, nufi yake duk abinda mukayi ya tashi a banza kenan?, muna tareda silar rugujewar burikanmu, nashiga ukuna Farooq idan General ya fahimta wlh mun kaɗe har ganyenmu ni wlh..."
"Mommy dan Allah ya isa haka kina neman fasamin kai kema, please abar wannan maganar muje gida doctor ya dubaki maybe ma jininki ya hau baki sani ba, zamu yi maganar ko zuwa gobe ne"
Batada wani zaɓin hakan yasa dole tayi shiru badan tagama faɗar abinda ke ranta ba sanin kuma halin Farooq na fusata yasa tayi shirun, fita ya yi ya koma front sit ɗin ya tayar ya motar, tafiya kawai sukai yana furzar da wani irin numfashi sai wuci yake haka har suka ƙarasa gida.
*MAI ZAMANI POV*
Kamar bazai magana sai kuma ya ce"meya sameta?" kansa ƙasa ya ce"wlh Father wai jininta ne ya hau" miƙewa General ya yi ya ce"okay Allah ya bata lpy zuwa anjima kazo zamuyi magana akan tafiyarka Paris" ya juya ya fita. Bin bayansa Mami tayi har bedroom ɗinsa, zaune ta taddashi yana waya hakan yasa ta zauna kan bedside drawer tana kallonsa saidai ya kammala sannan ya juyo yana kallonta yana murmushi ya ce"Madam ya dai?" shiru tayi bata bashi amsa ba hakan yasa ya miƙe cikin takunsa na isa ya ƙaraso inda take hannunta ya kama sannan ya koma ya zauna ya zaunar da ita bisa cinyarta yana kallon kyakkyawar fuskanta ya ce"Gimbiyata yau gida aka tuna ne?, Sarautar ce ta tashi?" da sauri ta rufe fuskarta a ƙirjinsa tana dariya ta ce"kai kam bakada dama wlh" dariya shima ya yi sannan ya ɗago fuskar tata yana kallonta cikin ido ya ce"kema ai kin sani banda ma yanzu kina hanani" turo baki tayi kamar wata ƙaramar yarinya ta ce"to ai kai bakasan ka girma ba" jan kumatunta ya yi ya ce" to kenan dan mutum ya girma bazai enjoying lfy ɗinsa ba?" girgiza kai kawai tayi sanin halin mijin nata ta ce"ai shikenan".
*YOBE STATE*
*BANI KURA RESIDENCE*
Kallon Falmata ta yi da mugun mamaki ta ce"wai me kike nufi nifa bangane ba?" tsaki Falmata ta yi ta ce"ke daÉ—ina dake rashin fahimta wlh, yanda nace miki haka zamuyi idan dare ya yi yau malam aikin dare zai yi kawai sai mu koreta ni a tunanina hakan shine kaÉ—ai mafitarmu"
"Aikuwa bazaku taɓa samun nasara ba Allah yafi ƙarfin ku"
Da sauri suka juya suna kallon Bani kura wanda yake tsaye ya ɗage labule" a matukar razane suka miƙe tsaye suna kallonsa duk idanunsu sun fito waje, ƙarasowa ya yi yana kallonsu idanunsa sun rune na zallar ɓacin rai ya ce"kunji kunya wlh kuma kun bani mamaki, wace irin tsana kuka yiwa wannan yarinyar ne?, me tayi muku da zafi haka da har kuke shirin rusa rayuwarta?, idan tabar gidan nan ina take dashi inda zata zauna?, to wlh ku kuka da kanku ku sani duk abinda kuke aikatawa Allah na kallonku kuma da sannu zai yi maganinku sannan magana ta ƙarshe na yanke shawarar zan auri Aishatu saboda na inganta rayuwarta tunda akwai aure tsakanin mu daga nan babu wanda ya isa ya ce zau takata a cikinku dan itama sunan matata zata amsa". Da sauri Muhaira ta toshe bakinta tana girgiza kai inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun Baba ne zai ce zai aureta?, kenan saboda batada gata haka rayuwarta zata kasance?, da sauri tayi ɗakinta saboda jin muryarsa yana ƙoƙarin fitowa daga ɗakin, tana zuwa ta faɗa kan tabarmar tana rushewa da wani irin kuka mai taɓa zuciya tabbas rayuwarta batada amfani kuma zuwa yanzu dole ta ɗauki matakin daya dace dan ko a mafarki bazata taɓa iya auren Bani kura ba bare kuma a gaske dole ta samu wata mafitar wacce zata ɓulle mata saidai batasan mene ne abinda zata yi ba!. Shi kuwa yana fitowa daga ɗakin ya yi waje dan zai je wajen Mai unguwane ya shaida masa idan yaso zuwa gobe da safe sai a ɗaura auren kuma ya yi hakan ne saboda ya samar mata da ƴanci cikin gidansa.
*11:30pm*
Wani irin baƙin hadari ne ya haɗo a sararin samaniya lokaci ɗaya garin yayi wani irin jaaa kasancewar lokacin damuna ne ga kuma dare, a hankali kamar wata ɓarauniya haka ta fito daga ɗakin tana sanɗa dan ko takalmi bata saka ba a hannunta ta riƙeshi babu kowa a tsakar gidan sai kukan gyare da kakeji ga kuma kukan iska wanda yake haɗe da ƙura da sauri ta fice daga gidan bayan ta zare sakatar ƙofar a hankali yanda wani bazai jiba, tana fita ta sanya takalmanta ta kuma sake riƙe jakarta sannan ta fara wani irin gudu kamar wacce ake binta. Gudun da take ya tsananta hakan yasa numfashinta ya fara janyewa saboda gudun da kuma ƙurar iskar dake tashi ta ko'ina, ƙarfinta ne ya fara ƙarewa a hankali ta fara rage gudun nata zuwa lokacin kuma an fara yayyafi, hakan yasa dole ta nemi waje ta tsaya sai a sannan ta lurada a cikin kasuwa take amma duk shagunan mutane a rufe suke hakan yasa ta samu rumfar wani shago ta shiga dan fakewa ruwan.
*MAITAMA DISTRICT*
*MA'EESHA POV*
Kallonta Mami tayi sai kuma ta ce"then yaushe zakuyi tafiyar?" cikeda fara'a ta ce"ranar Friday Mami kuma kwana uku kawai zamuyi dan Allah ki bari naje" numfasawa ta yi ta ce"Ma'eesha bawai hanaki nake ba saboda banason ki fita A'a ina gudun abinda zai je yadawo ne kawai" turo baki gaba ta yi ta ce"Ayyah Mami wlh ba abinda zai faru kinga ai da ƴan department ɗinmu duka zamu tafi nidai kawai ki yarda tunda Father ya yarda" harararta Mami tayi ta ce"oh sai kin tura min baki gaba zan yarda?, ko shagwaɓar taki zaki min?" girgiza kai tayi tana murmushi ta ce"sorry Mami nidai please ki ce Eh" ganin yanda ta marairaice fuska yasa ta ce"shikenan Allah ya tsare hanya Amma ki kula sosai sannan banda shan ruwan sanyi Ma'eesha" rungume Mamin tayi tana dariya ta ce"yawwa Mamina Allah ya bar min ke" taɓe baki Mami ta yi ta ce" wa Allah ya bari da zai barni kedai ki yita shashancinki" dariya ta yi Mami ta ce" idan yaso bayan kin dawo sai ki shirya dan mai martaba yanata tambayarki" da sauri ta miƙe tana tsalle ta ce"yeee Mami zani masarauta?, harda ke Mami?" girgiza kai Mami ta yi ta ce" Allah ya baki nutsuwa, Maybe hardani maybe kuma ke ɗaya zaki" da sauri tayi waje tana cewa"bari na faɗawa yaya Farooq" murmushi Mami tayi tana nemawa ƴar tata addu'ar shiriya wajen ubangiji.
*FAROOQ POV*
"Mommy nace miki ki kwantar da hankalinki na tabbata ba za'a samu wata matsala ba domin nasan wanda nabawa aikin kawai yanzu zan nemo hanyar da zata fita ne amma ba tare dani ba yanda babu wani wanda zai yi zargina da zarar nasamu wannan to komai fa zai zo ƙarshe zamu gama da General cikin sauƙi batareda munsha wata wahala ba" ajiyar zuciya Mommy ta sauke tana sanye cikin wani less peach colour mai manyan zane ɗinkin Bubu tayi ɗaurin ture kaga tsiya, ga mata iya mata amma sai mummunar zuciya, cikin sanyin jiki ta ce"to Allah yasa muyi nasara dan ni wlh abun ya fara damuna koda wasa ban taɓa tunanin haka zata kasance ba, na ɗauka munyi abinda ya kamata kuma zamu samu sakamako mai kyau amma sai ta sauya zani" wani killer smile ya yi ya ce"Mommy nace miki ki saka a ranki cewa angama komai domin ni nasan halin wanda na bawa aikin nan wlh koda da wasa baza'a taɓa samun wani abu wai shi matsala ba, infact ma Mommy shi baya taɓa kuskure cikin aikinsa bayan haka kuma ya rigada ya turon kuɗaɗen kinga munci riba biyu kenan" murmushi ta yi daidai lokacin Ma'eesha ta turo ƙofar bedroom ɗin ta shigo, a ɗan tsorace suka kalleta amma sai sukaga tana murmushi hakan yasa Mommy ta ce"shalelen Father ce kuma?" murmushi Ma'eesha ta yi tana kallon Farooq ta ce"yaya guess what?" lumshe ido ya yi ya buɗe ya ce"Father ya siya maki chocolate" girgiza kanta ta yi tana murmushi ta ce"baka canka baaa" murmushi ya yi ya ce"shikenan naji I'm looser now tell me" rufe idanunta tayi sai kuma ta buɗe ta ce" ranar Friday zamu tafi excursion" baki buɗe da matukar murna ya ce"awwwn wane waje?" tana dariya tace "National museum Damaturu nd kuma Father ya yarda hakama Mami" wani ƙayataccen murmushi ya yi yana kama hannunta ya ce"wowww amma naji daɗi shalelen Father gaskiya zo mu fita let's celebrate" murmushi tayi sannan suka fita daga bedroom ɗin tana cigaba da bashi labarin.
*YOBE STATE*
*GASHUA MARKET*
*MUHAIRA POV*
Dakyar take tafiya cikin kasuwar duk jikinta ya yi weak, wajejen ƙarfe 12pm na rana ne duk mutane sun fito suna hada-hadarsu wata Irin yunwa take ji dan rabonta da abinci tun jiya da rana gashi ƙirjinta yana mata ciwo jikinta kuwa kamar wacce aka naɗawa duka haka takeji, wani mutum tagani yana gashin masara hakan yasa ta ƙarasa wajen, tsugunawa tayi cikeda ladabi ta ce"Baba ina yini" kallonta tsohon mutumin ya yi aikuwa ya saki baki dan shi bai taɓa ganin mai kyau irin haka ba duk zatonsa ma aljana ce, ganin bai amsa mata ba yasa ta ce"Baba dan Allah ka taimaka min da masarar nan yunwa nakeji" da sauri ya ɗauki guda uku ya sanya mata cikin leda ya miƙa mata dan shi ko magana ma ya gagara yi dan tsoro yake kar yaje ba mutun ba ce, sosai Muhaira tayi murna cikin sanyin murya ta ce"Allah ya biyaka da gidan aljanna Baba Nagode" kai kawai ya gyaɗa mata dan tsorone ya ƙara kamashi sanda yaji muryarta, miƙewa tayi ta cigaba da tafiya dan ta samu wani wajen ta zauna ta ci masararta hankali kwance, Wani tebur ta samu gefen wani mai kayan awo ta zauna a hankali tayi bismillah tafara cin masararta. Duk wanda ya zo shigewa sai ya kalleta ganin yanda tayi wani irin kyau dukda ita ba'a cikin nutsuwarta take ba, irinsu Muhaira ne idan suka samu hutu tofa basu ganuwa saboda kyau da kuma tsarin halitta.
*BANI KURA RESIDENCE*
Tsaye suke cirko-cirko kowa ya yi shiru shi kuwa Bani kura ya zauna kan dakalin ɗakinta ya zuba uban tagumi yama rasa ta ina zai fara, ko ina Muhaira ta tafi?, yaushe tabar gidan?, Allah shine masani, taɓe baki Falmata ta yi ta ce"wama ya sani ko yawonta data saba ta tafi daman ai duk irinsu ƙarshensu yawon banza" a fusace Bani ya ɗauketa da wani lafiyayyen mari yana kallonta ya ce"dallah rufe mana baki wama ya sani ko kune kuka koreta kamar yanda kuka shirya, ku sani zan fita neman Aishatu amma duk abinda ya samu rayuwarta Allah bazai barku ba jahilan banza kawai!" yana gama faɗin haka ya fice daga gidan kamar zai tashi sama, da harara Ya'acca ta Bisa sannan ta ce"can kaje gayyar tsiya kuma in sha Allahu bazaka taɓa ganinta ba mun rabu da wahala shegiyar yarinya tana gidan nan ubanma zai zo ya auri ƴaƴanmu ai gwara data tafi Allah yasa mota tabi ta kanta ta markaɗe" tuntsirewa sukai da dariya Kulu ta ce"wlh kuwa Umma rannan Salisu cemin yai wai shi wannan ta gidan namu yakeso" kwafa Falmata ta yi ta ce"yoo daman wannan ai annoba ce shiyasa shima baban naku yace zai aureta ai wai mu zaiwa duniyanci heheheheeeeeeee!" Tsaki Ya'acca ta yi ta ce"ai wlh da ya aureta ya jaza mata bala'i dan Allah watarana saina kasheta kowama ya huta, daman ɗiyar Fulani ai mugunta garesu ni bansan mema ya haɗashi abota da ubanta ba" Allah dai ya kyauta cewar Falmata sannan ta cigaba da wankin da take.
# *BA ITA BA CE!*
# *Human trafficking*
# *Destiny*
# *Unconditional love*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce!*.