{48..}
Washe gari tinda Hajar ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba sbd da wuri ta kwanta jiya, tana kwance kan carpet ta rufa da duvet da wayarta ta buɗe Alqur'anin tana karantawa, sai ƙarfe bakwai da rabi ta ajiye karatun, linke duvet din tayi ta maida kan bed, shima pillow da ta tada kai ta mayar dashi gado, bathroom ta shiga dan yin wanka, minti ashirin ta ɗauka tana wankan kafin ta fito ɗaure da towel da yazo mata har guiwa, sai ƙamshin tsadadden showel gel da tayi wanka ne ke tashi a ɗakin, gaban mirror ta tsaya kafin taja stool ta zauna, body lotion ta janyo ta fara rubbing a jikinta, a hankali take shafa man tunani iri iri na amsawa a brain dinta, da sauri ta dubi ƙofa jin alamar za a shigo, ido huɗu sukay da Nurain, yana riƙe da handle din ƙofar, Hajar ta zaro ido kafin ta fasa ƙara ta fara kare jikinta, ya ɗauke kansa fuskarsa a murtuke, da wani irin zafin nama ta tashi daga kan stool din ta wafci hijab dinta ta saka, ƙarasa shigowa ɗakin yayi ya ajiye pen da jotter din hannunsa, da haka ya doshi ƙofa zai fita, Hajar da jikinta yake mugun rawa sbd tinda take babu wani namiji da ya taɓa ganinta a haka, har ruwa idonta ya kawo, da kyar tace "malam ka dena shigo min haka nan without notice...", fita yayi daga ɗakin, ta bisa da sauri ta tsaya bakin ƙofa tace "kai da Allah da ka shigo min babu sallama...", tana kallonsa ya shiga part dinsa, ta juya ta koma ɗakinta zuciyarta na tafasa, wani irin yamutsa fuska tayi sbd kawai ƙamshinsa da ya bari ne ke tashi a ɗakin, ƙamshin da sam baya mata daɗi, ta ɗauki freshner ta hau feshe room din amma duk da haka pure men scent dinsa bai disashe ba, Shafa man da bata ƙarasa ba knn ta buɗe wardrobe ta ɗauki kaya ta saka, har ta gama shiryawa zuciyarta ba ta dena tafasa ba, knn yaga bati, a fili tace "shi ya isa yaga bati, wllh Allah ban yafe ba..", gaban mirror ta koma ta ringa kallon jotter da pen din da ya ajiye, ta taɓe baki kafin ta ɗauki biron, rubutun da bai wuce 5lines tayi ba ta yage papern tayi folding dinta, da papern a hannunta ta sauka downstairs, ta wurga takardar kan Centre table tace "wnn kaɗai nake buƙata a wajen ka malam..", kitchen ta shiga dan samawa kanta abinda zata ci, ta buɗe fridge tana kallon fresh vegetables dake ciki, ta rufe fridge din kafin ta buɗe freezer wacca take cike da nama da chicken ga kuma fish duk frozen, shawara ta yanke akan cewa anjima za tayi stew saita ajiye a fridge ta ringa amfani da abarta na ƴan kwanaki, ruwan shayi ta tafasa ta soya kwai guda biyu da haka tabar kitchen din, bata haura sama ba ta zauna nan palour, Centre table da Tv stand da kujerun duk sunyi ƙura, tin ranar da Hafsah ta gyara palourn rabonsa da ganin tsintsiya, taɓe baki Hajar tayi tace "uhmm tinda ba ubana ne ya zuba ba babu abinda ya shalleni..", ta ɗauki kofin shayinta ta fara sha tana gutsirar kwai, tana gama cin abincin ta tashi ta shiga kitchen, ta wanke kwanukan da ta ɓata ta mayar dasu position dinsu, tin kafin ta gama wanke wanken ma take kallon ƙofar backyard, Alla alla take ta gama ta fita can ta ɗan sarara, bakin door din ta isa ta murɗa handle, sake murɗa handle din tayi da ɗan ƙarfi jin ƙofar taƙi buɗewa, lokaci guda ta saki handle din ta kafawa ƙofar ido, shiknn a kulle take, sosai ranta ya ɓaci dan zaman backyard din nan sosai yake rage mata kaɗaici, ranta duk ba daɗi ta bar kitchen din, main door ta ringa attempting buɗewa itama dai a rufe. tinda aka kawota gidan duk wnn ranar tafi mata zafi, baccin rana ma kasawa tayi, babban abinda yafi tsaya mata a rai bai wuce na safe da ya shigo mata ba, bayan tayi sallar la'asar ta kira Umma, gaisawa sukay Umma ta tambayeta ya take, Hajar dai tace lfy amma dai a ƙasan ranta ba haka bane, har Sabra ta tambaya tana cewa yaushe za a kawo mata ita, Umma tace mata ba yanzu ba, da haka suka kashe wayar.
★Nurain na zaune bisa executive kujera dake office dinsa bayan ya gama attending last patient, ƙofar office din aka buɗe aka shigo, ya ajiye plastic heart like da yake wasa da ita ya ɗaga kai ya dubi wanda ya shigo, lokaci guda ya haɗe thick eyebrows dinsa, da sauri Haleema ta shigo office din itama gaba ɗaya a ruɗe take, ta kalli Ruqayyah tace "Maam please get out..", ko kallonta Ruqayyah ba tayi ba ta isa gaban table tana kallon Nurain tace "i can stand any humiliation as far as zaka saurareni Dearest....", Nurain ya maida dubansa ga Haleema yace "amm me na gaya miki ne...?", with due respect Haleema tace "don't let her in..", Calmly as if speaking to himself yace "bayan nan..?", Haleema tace "call security..", ya gyaɗa kai yace "good.." kafin ya ɗauki heart din da ya ajiye ya cigaba da wasa da ita, Haleema ta fita daga office din da sauri, Ruqayyah ta zauna kan ɗaya daga kujeru biyu dake gaban table din, kallonsa ta ringa yi babu ko ƙiftawa, kifa kanta tayi da table din ta fashe da kuka tana girgiza kai tace "na haɗaka da Allah, na haɗaka da manzon Allah, please talk to me Dearest, ko scolding dina kayi that will be better amma...", ta kasa cigaba da maganar tana kuka sosaii, a hankali yayi baya da kujerarsa ya tashi salum alum ya nufi door ya buɗe ya fita, Ruqayyah ta ɗago kanta ta bisa da kallo da jajayen idanunta, Office din Dr Marwan ya wuce, Dr Marwan na kallonsa yace "is there any problem Dr..?", Nurain yace "not at all, how is the patient..?", Dr Marwan yace "alhmdllh he is recovering gradually..", Nurain ya gyaɗa kai yace "how about his vital..?", Dr Marwan yace "great, Khaleel ya duba not too long ago", Nurain bai sake cewa komai ba yayi resting jikin kujerar, after few minutes of silence Dr Marwan yace "naji ana maganar Seminar wacca za aje Abuja nan da 1month, all thoracic surgeon must be there..", Nurain yace "am not going..", Dr Marwan yace "why..?", Nurain ya ɗaga shoulder yace "kawai.." da haka ya dubi wrist watch dinsa, tashi yayi ya yiwa Dr Marwan sallama, yana fita daga department din ya ciro wayarsa yayi dialing numbern Haleema, tana picking yace ta kawo masa briefcase dinsa yana parking lot, da haka ya kashe kiran ya cigaba da tafiya zuwa inda ya parker motarsa, buɗe motar yayi ya shiga, babu jimawa saiga Haleema da briefcase din tasa, ya amsa ba yabo ba fallasa yace "thank you..", tace "am so sorry sir about what happened, i tried to stopped her...", ya ɗaga mata hannu yace "it's okay..", tace "thank you sir", murmushi kawai ya mata ya sauke handbrake yaja motar yabar harabar hospital din, driving kawai yake saman titi amma bai san inda ya nufa ba, lokaci guda yayi murmushi yace "ironlady..", yana zuwa wani roundabout ya juya kan motar, yana zuwa gidan ya danna horn, mai gadi ya buɗe masa gate ya shigar da motar, fitowa yayi daga motar bayan ya gama parking, ta baya yabi inda direct nan ne zai kaika part din Hajiya, da sallama ya shiga palourn Hajiya, Hajiya na zaune kan darduma ƴar dattijuwar mai aikinta tana yanka mata papaya, Hajiya ta kalli Nurain ta saman kantamemen glasses dinta tace "ywwa ga likita ma Allah jefomin daga sama, Usuman cikina ne ya ɗaure kwana biyu ban kewaya ba, toh duk ya dameni ji nake kamar anyi min jeren marmaroni a kyuiɓi ko isasshen bacci bana samu, dana gaji da azaba shine nasa Umaru ya kwaso min gwanda kwallo uku, na sha kwallo guda da safe yanzu ma gashi ana yankan wata zan shanye, da daddare in Allah ya kaimu a yanke min gudar da ta rage itama na shanye, ai idan nayi hakan na huta da jarabar basir din nan, ba kaga da yaya na shanye wacca aka yankan da safe ba, cikina har baya kamar zanyi amai amma kuma ai lfy nake nema, yanzu haka har na fara tararrabin yadda zan shanye wnn..", Nurain yayi still yana sauraronta kafin ya samu waje ya zauna yace "karki sake shan wata ta safen is Okay..", Hajiya tace "Allah ko idan na sake sha zan iya tsurewa knn...?", ta dubi mai aikin tace "ke Asabe maza fita da ita duk warinta ya cikan hanci, kije can ki shanye rabonki ce", mai aikin ta ɗauki plate din papayan tayi waje da ita. Hajiya tace "na ganawa kaina azaba har yanxu gyatsar wnn aba nake, kai ina jin ma harna koma ga mahalicca na bazan sake shan gwanda ba duk ta gundureni", Nurain yace "ba kya jin komai daga wnn...?", tace "A'a ƙalau nake Usuman, haka kurum nace maka wani waje na min ciwo ka samu hanyar da zaka fara zuba min allurai..", yace "toh shknn tinda lafiyar ki ƙalau..", Hajiya tace "toh madallah ya gyatumar taka.." sai kuma ta tsuke baki tace "ji wani sakarci nida zan fara tambayarka matarka kuma na tafi wani wajen, Mami ai ba gida ɗaya kuke kwana ba yanzu..", shi dai baice mata komai ba, bayan ƴan mintina yace "bari na gaida Ummi.." da haka ya tashi ya buɗe wata ƙofa ya shiga, luckily ya tarar da Ummi na palour, ya gaisheta with respect, amsawa tayi tana tambayarsa aiki da iyali, shi dai ya shafa kansa ya amsa a takaice kafin ya mata sallama ya bar palourn ya koma na Hajiya, babu jimawa da zamansa saiga Abinci Ummi tasa an kawo masa, sosai Nurain yaji daɗin hakan, plate ya ɗauka zai zuba abincin Hajiya tace "wai ci za kayi kai Usuman na matarka fa..?", yace "shima zanci", ya faɗi hakan ne dan ya huta da surutunta ta barsa lfy yaci abincin kar ya dawo masa ta hanci. tin ɗaya da rabi sai uku da arba'in Nurain ya bar gidan, bai jira Farooq ba sbd baya dawowa aikin da wuri cause na Company ne. gidansu ya wuce, yana gama parking motarsa yaji ana kiran sallah, yayi amfani da tap dake compound yayi alwala ya wuce mosque, bayan ya dawo masallaci ya shiga ciki, part din Mami ya shiga ya gaisheta kafin ya fito ya haura room dinsa. bashi ya sakko ba sai biyar saura shima sbd Noor ne wacca ta takura masa akan project dinta, saida sukay chapter biyu snn ranta yayi fari tinda saura ɗaya ya rage su gama. ƙarfe bakwai da arba'in Nurain ya shiga wajen Mami, attention dinta ta mayar kansa, Nurain yace "Mami saida safe ni zan wuce..", Mami ta dubi agogo ganin lokaci tace "yawwa toh Allah ya tashemu lfy, ka ringa tafiya gida da wuri ai yafi son..", ya shafa kansa yace "tom Mami", Compound ya fita ya shiga motarsa, ya ciro wayarsa yayi dialing numbern Noor, tana picking yace "yi sauri malama", tace "Yaya gani nan..", few minutes saiga tanan ta ɓillo ta can baya da basket a hannunta, ta buɗe front seat ta ajiye basket din ta rufe door, Nurain ya gyara zama ya tada motar. saida ya tsaya wajen suya ya siyi kaza snn ya wuce gida, fitowa yayi daga motar yana amsa sannu da zuwan da mai gadi yake masa, ya buɗe front seat ya ɗauki basket din kafin ya nufi main building din gidan, keys ya ciro daga pocket ya buɗe door ya shiga ya mayar ya rufe still da muƙulli, ajiye basket din yayi nan palour kafin ya haura sama, wanka yayi ya saka Pajamas masu sweat pant masu shegen kyau, downstairs ya sakko da room slippers a ƙafarsa, kamar ce masa akay ya kalli wajen, ya ringa kallon papern dake kan Centre table, haɗe gira yayi kafin ya ɗauki papern ya buɗe a wulaƙance, beautiful handwriting din dake jiki ya fara karantawa.... "malam wai an gaya maka inada wata buƙata ne a wajenka in banda guda ɗaya, kawai ka sauwaƙe mana shine buƙatata..", tsaki yayi ya cukuikuiye takardar ya wurgar da ita, wani irin ƙauri ya fara perceiving, da sauri ya nufi kitchen, yana buɗewa yaja da baya ya toshe hancinsa, gaba ɗaya kitchen din ya gumame da hayaƙi da uban yaji, da hannu ɗaya ya rufe hancinsa ɗayan kuma ya ringa kore hayaƙin har ya samu ya shiga kitchen din, gaban cooking gas ya isa yana ƙoƙarin kashe wutar amma da yake hayaƙi yayi yawa baya gani sosai hannunsa ya jogali tukunya, da sauri ya janye hannun ya riƙe da other din, hkan ce tasa yayi perceiving ƙaurin har cikin lungs dinsa, tini ya fara tari at same time yana ƙoƙarin kashe gas din. Hajar ta saki pillow din hannunta bayan brain dinta ta amsa, shaf ta manta da kayan miyar da ta ɗora akan wuta, bata tsaya bi takan wani hijab ba ta gyara hular kanta ta fito daga room din, da sauri ta ringa sauka stairs har tana tuntuɓe, tin daga palour ta fara tari ga uban hayaƙi da ya rufe mata vision, gadan gadan kitchen ta shiga daidai lokacin da Nurain ya kashe gas din, da sauri ta juya kamar zata sa gudu sbd fitowar da tayi ba shiri, Allah yaso ma kayan baccin riga da wando ne kuma rigar ta saukar mata, tana fita daga kitchen din shima ya fito yasa ƙafa ya banke ƙofar, tana shirin hawa stairs taji an fixgo hannunta, figarta yayi zuwa dining area inda babu hayaƙin sosai, haɗe ta yayi da bango still bai sakar mata hannu ba fighting with his breathing, sosai ya shaƙi hayaƙin shiyasa numfashinsa har yanzu bai dawo normal ba, kiciniyar kwace hannunta ta fara yi tana turesa da iya ƙarfinta, sake matseta yayi da bango ta kasa motsi, heavily yake breathing har zuwa lokacin da yaji dama dama, a hankali take mayar da numfashi ta ɓalla masa harara tace "let go off me, ni ka sake ni..", ita babban tashin hankalinta kayan jikinta, muryarsa ma bata fita sosai yace "from today henceforth karna sake ganinki a kitchen, are you mad fire outbreak zaki ja min a gida, koda wasa na sake ganinki a kitchen saina sumar dake nonsense" yana kaiwa nan ya hankaɗeta saura ƙiris ta faɗi. da sauri ya nufi stairs ya haura sama don bazai iya ƙara koda 1minute a wajen ba, Hajar tabi bayansa da kallo zuciyarta ta ringa ƙuna kamar zata kama da wuta, zama tayi kan stairs din hawa dining ta haɗe kai da guiwa, after 10mins ta tashi ta haura sama kamar wacca kwai ya fashewa a ciki. washe gari da safe Nurain ya sauko downstairs, ta main door ya fita ya zaga can backyard ya kashe gas cylinder, cikin gida ya dawo bayan ya kashe gas din, ya shiga kitchen to make a cup of coffee, wani tsaki yayi ganin tukunyar dake kan cooking gas, tayi wani baƙi ƙirin ko kyan gani babu, cikin sink ya saka tukunyar ya sakar mata ruwa saida ta cika damm snn ya kashe pampon, ya jona coffee maker. A hankali Hajar ta ƙarasa sakkowa daga stairs idonta ƙur akan keys din dake jikin ƙofa, ta isa bakin ƙofar a hankali ta zare keys din, tana juyawa sukay ido huɗu dashi ya fito daga kitchen da cup a hannunsa, ta haɗe gira tayi sauri ta kunshe keys din a hijab, garin haka ji kake tass muƙulli sun faɗi a kan tiles, kallon keys din Nurain yayi snn ya kalleta, ta wani haɗe rai, yana kallon main door ita kuma ta samu opportunity ta sunkuya ta ɗauki mukullin ta kwasa a guje sai sama, a hannun kujera ya dungurar da Coffee din yabi bayanta da sauri, tana ƙoƙarin rufe ƙofa yasa ƙafa ya banke ƙofar, zaro ido tayi tace "na shiga uku" ta ruga can edge of the room ta boye hannunta a baya, daga bakin ƙofar ya tsaya yace "give me the keys..", ta murguɗa masa baki tace "wllh bazan bayar ba, ni ba tinkiyarka bace da zaka ringa kulleni", ƙofar bathroom ta kalla sai kuma ta kallesa tana banka masa harara, lokaci guda ta tafi da gudu zata shige bathroom din, ganin haka ya taho da speed ya fixgota ya haɗeta da jikin wardrobe, dunƙule keys din tayi a hannunta ta ɓoye a baya, tini ta ringa shaƙar scent dinsa da bata so, ta ɗaga lulu eyes ɗinta ta kallesa, shima kallon cikin idanunta yake da wani irin expression zuciyarsa na tafasa.......✍️