1
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```NA```
```NAFISAT ALIYU SASAAL```
```Page 1```
```BISMILLAH```
_____Babbar Macen da shekarunta za su haura arba'in ne take ta zarya ciki da wajen Asibitin.
Dayawan waÉ—an da take wucewa kallo suke bin ta da shi saboda surutan da take yi ita É—aya kuma babu alamun ciwo hauka a tattare da ita.
Komarwa Asibitin akaro na uku ne ta samu dangin Mahaifin Halime, fuskar kowanne su shimfiɗe da matsananciyar damuwar da idan ta rantse bazatayi kaffara ba na ƙarya ne.
Cikin Kuka da hargowa son ta kore su ta nufe su,Indo ƙanwarta ce taja hannunta gefe,cikin taushin lafazi da son kwantar mata da hankali take tausar ta.
Fitowar Nurse ta na neman Æ´an uwan Halima Haladu ne yasa Innar Halime da Indo matsowa a hanzarce.
Albishir É—in samun Baby girl É—in da Halime ta haifa ta yi mu su,cikin tsananin farin ciki Inna da Indo suka rungume juna suna hamdala haka suma Æ´an uwan Mahaifinta.
"Halime fa tana lafiya dai ko" Inna ta tambaya zuciyarta na tsinkewa.
MAFARI
Babban gida ne da rai sama da hamsin suke rayuwa a sassa daban-daban na gidan kuma duk sun fito ne daga tsatson mutum ɗaya,baƙin hali, tsananin son zuciya da KWA'DAYI su ne abinda yafi yawa a zuƙatan mafi yawanci yaran su da manyan su.
Mallam Shehu shine na uku acikin su Taran da Mahaifin su Mallam Idris ya haifa, kuma shine mai ƙaranci samu acikin su.
Matarsa Huwaila ita take juya akalar zamanta da Mallam Shehu wannan dalilin ya sa ita kaɗaice bata da abokiyar zama ta kuma sha alwashin ƙare rayuwarta batare da Mijinta ya ƙara aure ba duk da har lokacin ba su samu haihuwa ba.
Kwatsam Mallam Idris Mahaifin Mallam Shehu ya nema mishi auren ƴar ƙaninshi da Mijinta ya mutu a ƙauye, da ƴarta ɗaya Halime.
Babu inda bataje ba kuma babu wani barazana da batayiwa Mallam Shehu ba, amma cikin hukunci Ubangiji aka É—aura auren Mallam Shehu da zankaÉ—eÉ—iyar baffulatar Amaryar shi Saude.
Baƙaramin artabu akayi da dangin Mahaifin Halime ba kafin su amince da tafiyarta birni,amma da alƙawarin zata dawo ƙauye ta yi aure, saboda sun fison ta auri na gida yanda za su fi jin daɗin morewa dukiyar da Mahaifinta ya bari.
Agolar gidan Shehu shine sabon sunan da ahalin gidan suka raɗa mata, Mutanen Unguwa kowa ya ɗauka,tanajin ciwon sunan, wa su lokutan sai taji kamar ta koma ƙauye wajen dangin Mahaifinta sai dai bazata iya ba saboda tarin burinka dake danƙare acikin zuciyarta.
Tsangwama da ƙyara take fuskanta daga kowanni sashe na gidan hakama Inna Huwaila kullum cikin takalar Innar ta da faɗa ta ke.
Bata zuwa Makarantar Boko sai Makarantar allo duk da zurfin burin da take da shi akan ta yi ilimi mai zurfi amma Innarta batada wannan halin.
Dalilin fara tallar gyaÉ—ar Halime kenan saboda ta tara kuÉ—in zuwa Makarantar Boko...
#MAYSARAH
#HALIME