NIKAAH 9
by @hanaady
*NIKAAH*
*Marriage for Rent)*
*By*
*HANAADY*
*Rahama Aminu Bala*
*WhatsApp*
*****
*Follow me on Whatpad*
*Rahama000*
*On Arewa book* *@hanaady*
HE HAD THE COURAGE
TO REMARRY.
WILL HE FIND THE COURAGE TO
LOVE AGAIN?
Marubuciyar
BAHAAR paid book
And now NIKAAH(Rental Marriage).......
Free book
*Page 9*
_________Fitowa yayi yana zuba kamshi da kallo ta bishi harya shige kitchen " shaf shaf ya soya egg tareda dafa indomie juyewa ta cikin plate yayi dining table ya nufa " kallon sa tayi tana mai had'e yawo Best ya furta aikuwa cikin sauri ta bayyana gaban sa zauna kiyi breakfast kaifa ba zaka ci ba bana breakfast da wuri "maganar Little ce tasa su duka saurin kallon k'ofa Momyna da gudu ta shugo tashi Karime tayi tareda nufar Little "kallo yake sosai yake mamakin shakuwar sa .
Hannun Mahaifin ta ta kama tareda cewa Dada tace wai tana da cikin ka "zaro idanuwa waje yayi tareda cewa watana saida ta d'an yi tunani sannan tace wata tara mena aikata haka har cikin ya kai wata tara murmushi Sa'ada tayi sannan tace Dada tace ka hana Momyna zuwa part nata and tace if kuka had'u saita cire maka kunne "dan kallon Karime yayi please make sure kinje part d'in Dada noding kanta tayi .
Hanyar waje ya nufa hannun sa ri'ke da Little Saida ta kai indomie baki tukun tabi bayan su da gudu bakin k'ofar falon taci burki ganin ya tsaya Yana binta da kallo "d'an susar kanta tayi dama tace zanje gidan yayanka "wani abu akeyi a gidan ?
Washe baki tayi sannan tace aaa dama tace zata koya mun girki kuma tace wai zata koya mun yanda ake kula da kai " d'an Kankance idanuwan sa yayi kula da kai kuma eh ta bashi ansa shuru yayi na wasu y'an sec ok adawo lafiya and please ki shiga ku gaisa da Momya " tsoro ne ya bayyana a kan fuskar ta " ita fa ta mugun tsorata da sha'anin Momy dafa kafad'ar ta yayi are you ok? Kina tsoron Momyna koh kai ta gyada masa d'an murmushi yayi you have to be strong kinji "for sure nasan zama da Momyna sai an daure so please just do as i say ficewa yayi abunsa da kallo ta busu harya shige mota da alama yau Little tare zasu tafi .
Jiki mace ta koma saman dining duk da tana cikin damuwa hakan bai hanata bud'e ciki ta cinye indomien ba tas "tattara plate d'in tayi zuwa kitchen "wanke plate d'in tayi tareda mayar dashi ma'ajin sa .
Gidan ga hau gyara kaman yanda Rumaisa ta koya mata " bayan ta kammala duk wani aikinta wanka tayi tareda bajewa saman gado sai bacci .
A bangaren Hjy Mariya kuwa sammako tayi zuwa gidan su Ramadan bayan sun gaisa da Momy fad'a mata yanda sukayi da Aliya tayi "wai ita Sam ba zata dawo Nigeria ba sai dai if Ramadan ne ya buk'aci hakan" yanzu menene mafita cewar Hjy Sadiya "ni a ganina ko zaki kwatanta yi masa magana akan ya kirata "shuru Momy tayi na wasu y'an da'ki'kai
Zan masa magana in sha Allah amma what i want you to understand shine haryanzu akwai soyayyar Sa'adatu aransa baya ganin ko wace mace a matsayin mace sai Sa'ada" bayan haka akwai abubuwan da baka isa kayi forcing mutum yayi su ba "d'aurewa Hjy Mariya kawai take domin tabbas sai yanzu ta fara yadda da maganar Fadila akan sihirin Hjy Sadiya ya fara barin jikinta.
D'an kyaran murya Hjy Mariya tayi sannan tace ni sam ban gane inda kika dosa ba " ina nufin auren Ramadan da Alia sam ba abu bane mai wahala domin shi baya da matsala ko mace nawa za'a aura masa saidai abunda nake gudu shine yaushe zai bud'e zuciyar sa ga wata mace " kina tunanin haka zamu aura masa Alia batared mun tabbatar da soyayyar ta a zuciyar sa "shuru Hjy Mariya tayi domin tabbas maganar Momy abun dubawa ce duk da ita dai ba wata soyayya bace a gaban ta arzikin sa take mawa but wani hanzari ba gudu ba tasan irin mugun son da Alia take wa Ramadan wani tunani ne ya zo mata murmushin gefen tayi sannan tace maganar ki tabbas akwai gaskiya a cikin ta yanzu abunda ya kama ta kiyi shine ki sami shi Ramadan d'in kiyi masa maganar kiran Alia I'm very sure zaya saurare ki and to cut story short try your best to talk to him about Aliar kiga shin wane reaction zai bayar ta haka ne zamu iya gane next move namu .
Sam Momy bata iya yiwa Hjy Mariya gaddama " da sallama ta shugo falon Momy "heartbeat d'in is not normal at all tunda ta doso hanya hakan ta faru da ita " tana mamakin irin yanda take jin nauyin Momy "lafiya Momy ta fad'a ba yabo ba fallasa saman fuskar ta k'araso tayi cikin falon gaishe dasu tayi cikin girmamawa " wannan fa Momy ta fad'a tana mai nuna Karime kallon banza Hjy Mariya tayi ma Karime wannan ai ba matsala bace komai ai yana tafiya according to the plan Alia na dawowa zata buk'aci divorce from Ramadan " kina ganin zaya aikata hakan cewar Momy why kika ce haka just like that " nina haifi Ramadan nasan halinsa da
Kafiyar tsiya .
You don't have to worry Hjy Sadiya agreement muka yi da Mahaifin ta" so ba zata ta'ba yadda hakan ma ta faru ba if haka ta fara her Father will go to jail "shuru tayi tana sauraren su.
Jiki mace ta baro flat d'in Momy direct gida tayi yau d'innan komai ya fice mata ba wai cin fuskar dasu Momy suka mata bane ya dagula mata lissafi ba and maganar auren Ramadan da Alia " she's aware about that but yanda taji suna maganar Ramadan ya bama soyayyar Alia second chance shine babbar damuwar ta " a lokacin data fara sanin ciwon kanta babban burin ta shine taga Maman ta da sisters nata cikin farinciki secondly shine Allah ya nuna mata ranar da wani d'an namijin da zai nuna ra'ayin sa akan ta ma'ana ya sota har abun ya kaisu ga aure
" a kullun addu'ar ta bata wuci hakan ba " d'an sabon da tayi da Ramadan ba k'aramin sakata farinciki hakan yake ba koba komai ba shi d'in ya yadda ita d'in macece ajiyar zuciya tayi ba tada abokiyar shawara ko aminiya Aishatu kad'ai ce yanzu kuma tayi mata nisa " shuru tayi tana mai share hawayen fuskar ta "Rumaisa ce ta fad'o mata a rai saurin mi'kewa yayi tareda zurar shoes d'inta sai Flat d'in su Rumaisa .
Bayan ta zauna cikin yanayin damuwa tace banida abiyar shawara ko wata aminya shine dalilin da yasa na yanke shawarar zuwa wajen ki "I'm all ears Karime ki fad'a mun duk wata damuwar ki in sha Allah zanyi iya k'okarina waje baki shawara ta gari " gyara zama Karime tayi tareda zaiyana mata duk yanda auren ta da Ramadan ya kasance ga mamakin Karime babu alamun mamaki akan fuskar Rumaisa saima murmushi da take hakan yasa Karime cewa kodai kin san komai ne ?
Hmm Karime kenan ba zan miki k'arya ba Mijina ya sanar dani komai saidai ban miki maganar bane sabida naga ked'in baki fad'a mun ba amma yanzu tunda zuciyar ki ta fara aminta dani Alahmududilahi "yanzu ki fad'a mun menene aranki gameda auren nan shuru Karime tayi na wasu y'an da'ki'kai ajiyar zuciya tayi tareda cewa maganar aurena yarjejeniya ce tskanin Mahaifina da kuma mahaifiyar Alia sabida haka nid'in bana tunanin akwai abunda zan iyayi " kin shirya rabuwa da Ramadan kenan if Alia ta dawo shuru Karime tayi tana bin Rumaisa da kallo " maganar na shirya ko ban shirya na bata taso ba domin ba'a bugatar ra'ayina " kama hanuwan ta Rumaisa tayi sannan tace wannan tsakanina ne dake shin are you ready to give up Ramadan to Alia kallon Rumaisa tayi cikin rauni tace bana son rabuwa dashi 'zanso ace na cigaba da rayauwa dashi harna kwanta damana abune wanda is impossible bayan haka a yau na tabbatar da cewa Alia tafi cancanta dashi ba niba duba da irin shakuwar dake tsakanin Momy da Mahaifiyar Alia .
Bayan haka naji ance ita d'in first love nashi sabida haka babu abunda zan iyayi besides ba wai sona yake ba haryanzu Sa'ada yake so " yanzu kuma I'm certain Alia zata iya nasarar maye gurbin Sa'ada tunda dama zuciyar sa ta ta'ba sonta nifa .
Sa'ada da Ramadan ba auren soyayya suka yiba cewar Rumaisa cikin rashin fahimta Karime tace ban gane ba kina son cemun ba auren soyayya suka yi ba you heard me right "i want you to give me all your attention a yau zan baki tarihin soyayyar Ramadan da Sa'ada bayan na gama baki labarin kina da damar yanke hukunci akan wannan auren naku bayan haka labarin da zan baki shine zaya baki dama either to fight for Ramadan ko kuma ki barma Alia is up to you Karime .
SEBRI AIRPORT NYSCE CAMP JALINGO TARABA STATE
Tsai tsaye muke a parade ground duk wani Corp member kallo d'aya zaka masa ka gane tabbas yana cikin nishad'i being a Corp member is the dreams of every graduate haka zalika is an experience da ko wane dalibi yake fatan samu " tafi 10 minutes tana kallon sa fuskar sa a murtuke take kaman baqara tsaye yake hannuwan sa cikin trouser bin mutane yake da ido .
Isowar sosojine yasa mutane saurin saka layi " sam ta kasa dauke idanuwanta daga kallon sa still fuskar sa a murtuke take "duk bayanin da ake bata san anayi ba kacokan hankalita yana kansa " kaman ance ya juyo kama ta yayi dumumu tana kallon sa k'ara tamke fuska yayi tareda kafeta da ido saurin janye idanuwanta tayi siririn tsaki yayi tareda juya fuskar .
Bayan an watse kasa tafiya tayi zuciyar ta ta'ki bata damar haka tsaye yake shida wani suna magana nesa dasu ta matsa tareda jingina jikin wata bishiya kallon sa take kaman ta samu tv "ganin sun fara tafiya ne yasa tayi saurin bin bayan su "ringing d'in wayar sane yasa ya d'an tsaya tareda fiddo ta from his trouser waya yake hankali kwance ganin haka yasa ta tsaya tana kallon sa "juyowar da za yayi nesa dasu ya hango ta murtuke fuska yayi tareda yin gaba.
Jan kafafuwan ta tayi zuwa Hostel nasa can ma kasa komai tayi sai tunanin sa murmushi ne ya su'buce mata tunowa da tayi ai platoon d'insu d'aya koma menene she is very sure gobe zata ganshi " bayan sun fito sallar asuba direct parade ground suka nufa tun da ta isa take baza idanu ko zata ganshi " Saida gari yayi haske sosai sannan Ramadan ya iso parade ground tafiya yake hankali kwance Sam bai lura da ita ba kasancewar already kowa yana cikin layi layi ya yashi yau d'innan kuwa mutun d'aya ne tsakanin su "tunda yazo ta saki baki ido da hanci tana kallon sa " she was lost a kallon sa ashe tuni ya juyo yana kallonta fuskar murtuke tsaki yayi tareda juyawa domin ya fahimci sam tayi nisa "shifa ya tsani kallo akan me yarinya zata mayar dashi abun kallon ta kaman wani sa'anta "a duk lokacin da ta had'u dashi haka zata saki baki tana kallon most especially a parade ground nanne wajen had'uwar su " yau ma hakan take kallonsa take tana murmushi juyowa yayi yana kallon ta murmushi ta k'asar ma abun ya matuk'ar bashi mamaki domin duk lokacin da suka had'a ido saurin janye nata take but a yau murmushi tayi masa aikuwa k'ara tamke fuska yayi tareda sakin siririn tsaki.
Tun daga wannan rana duk lokacin da ya juyo suka had'a ido murmushi take masa shi kuwa murtuke fuska yake" watarana haka ta tashi da zazzabi mai mugun zafi Koda taje clinic kwantar da ita su kayi domin BP nata ya d'aga sosai " tunda ya isa parade ground ya fahimci bata nan Wasa wasa kwana 2 bata nan hakanne yasa ya saka friend d'insa tambayar wata wacce yake ganin suna yawan tsayawa waje d'aya , fad'a ma friend nasa tayi bata jin dadi'tana Camp clinic kasancewar mutum mai tausayi yasa yaja friend nasa zuwa Clinic d'in time d'in da suka je bacci take ananne ake fad'a musu cewa jinin tane ya hau " kun tambaye ta dalilin haka Ramadan d'in ya tamabayi d'aya daga cikin corp member d'in dake kula da patient d'in bata fad'a musu komai ba duk tambayar da suka mata " ya tausaya Mata sosai ace yarinya k'arama da hawan jini .
Tunda tayi recovering ta koma yin duk wasu daily activities nata " yauma kallonsa take juyowa yayi yana kallon ga mamakin ta murmushi yayi mata gaban ta mugun faduwa yayi domin duk lokacin da suka had'a ido murtuke fuska yake but why yau yake mata murmushi " a nashi bangaren kuwa tunda ya gane tana da hawan jini yaji yana tausayin ta bayan haka ya fahimci yanda take murmushi if tana kallon sa tunanin sa shine if kallon sa yana saka ta nishad'i in sha Allah bazai kuma murtuke mata fuska ba wata zuciyar ta fad'a masa maybe ma ba shi take kallo ba kawai ana samu akasi ne ya juyo
Tunda ga wannan rana suka fara gaisawa dashi sosai suka shak'u "watarana suna zaune d'an nesa da juna zoben hannun sa ta kalla zoben hannun ka yayi kyau sosai murmushi yayi mata sannan yace had it been nawane dana baki shi cikin son karin bayani tace na wanene wayar ya nuna mata picture d'in Alia ne murmushi Sa'ada tayi sannan tace she is beautiful yes ya furta yana mai kallon picture d'in with admiration girlfriend d'in ka ce ?
No she is my fiancee and wannan zoben na engagement d'inmu ne da mamaki tace a tunanin Kai d'in bahaushe ne murmushi yayi sannan yace of course ni bahaushe ne yaushe hausawa suka fara saka ring a engagement Saida yayi dariya tukun yace matar da zan aura Mahaifin ta d'an Egypt ne so shine dalilin da yasa akayi mana engagement based on al'adar k'asar Daddynta .
Ok da ita kuke waya kenan yes ya furta yana murmushi kana sonta sosai gaskiya murmushi ya kuma yi sannan yace why kika ce haka it's very obvious Ramadan kai da baka cika murmushi ba but look at yanda kake ta murmushi daga maganar ta lumshe idanuwan sa yayi sannan yace adore her "when is your wedding Sa'ada ta furta zuciyar ta na rad'ad'i nanda 5 month ya furta congratulations Sa'ada ta fad'a tana mai murmushi thank you my friend ya furta da murmushi akan fuskar sa .
Haka suke gaisuwa wani lokacin ma a gabanta yake waya da Alia sam bata ta'ba sanin cewa soyayar Ramadan ta mata kamu ba sai bayan rabuwar su .
Tunda suka rabu basu kuma had'u ba hasali ma phone number nata baya aiki domin sace wayar akai "a kullun dashi take kwana dashi take yini kasancewar gidan kanin Babanta take zaune Babanta ya rasu Maman ta kuma tayi wani auren a wani kauye shi kansa kanin Baban nata ba haline dashi ba "a haka take rayuwa cikin kunci da kalubalen rayuwa dama kararun nata Mamanta ce tayi kokarin biya mata ta hanyar siyarda dabbobin ta anan Hassan Usman Katsina Poly tayi inda ta karanci Library and information .
Tunda maganar auren ta da Dikko yaron kawunta ,ta kunno kai ta shiga cikin muguwar damuwa domin Dikko ba miji bane mutunen da sam bai san inda rayuwa ta dosa ba baya da aiki sai shaye shaye da bin matan banza shine ake son forcing nata ta aura "tunda suka rabu bata k'ara ji daga gare shi ba asalima ko jahar da yake bata sani ba phone number sa kuwa tuni ta haddace ta Amma bata ta'ba gigin kiransa ba
A bangaren Ramadan kuwa time to time Sa'ada ta kan fad'o masa arai wani lokacin ya kan kira number ta bata shiga maganar soyayyar sa da Alia sosai suke gudanar da abunsu "
Ana kwana 2 saura bikin Sa'ada Dikko ya kama Sa'ada yayi mata d'an banzan duka sosai duk ya canza mata halittu
" A ranar ne ta ari wayar wata kawarta ta kira number Ramadan missed call biyar ta sama bai d'aga ba ganin haka ne yasa tace Sa'ada ta tafi da wayar Koda za'a kirata cikin ikon Allah saiga kiran Ramdan "Koda ta d'aga wayar bashewa tayi da kuka jin muryar sa yana tamabayar wake magana cikin sheshshekar kuka tace Sa'adatu ce wace Sa'ada ya fad'a domin shifa ya shafa'a da wata Sa'adatu ji tayi duk babu dadi'yanda ya nuna ya manta da ita
kashe Kiran tayi tana mai rera kuka " Kiran wayar ya kuma yi please dawa nake magana d'aurewa tayi tace Sa'ada ce Allah sarki ya furta domin yanzu 4 month kenan da rabuwar su kina lafiya fashewa tayi da kuka cikin yanayin tausayi irin na Ramadan yake tambayar ta dalilin kukan ta bayani tayi masa akan auren dole da ake son yi mata kwanaki biyu masu zuwa da yadda mijin da zata aura yayi mata dukan kawo wu'ka sosai ya tausaya mata " yanzu minene mafita Sa'ada cikin sheshshekar kuka tace Ramadan guduwa zanyi is better na shiga duniya da auren Bello banida gata saina Allah please Sa'ada kada ki k'ara maganar guduwa in sha zan nemo miki mafita kafun jibi " da wannan shawara suka yi bankwana .
A daren Ramadan sam bai runtsaba haka zalika Sa'ada lokacin 1 month ya rage bikinsu da Alia " ganin duk tunanin sa bai samu mafita ba yasa ya tunkari Sadiq da shawara first thing da Sadiq ya fad'a masa shine ya aureta da farko yayi gaddama sai daga baya ya amince "Dada ya samu da maganar bai boye mata komai ba cikin ikon Allah Dada ta goya masa baya ita da kanta ta sami Abba da maganar auren Ramadan da Sa'ada sosai Momy ta shiga tashin hankali Amma bakin alkalami ga bushe .
A bangaren Alia kuwa Ramadan yayi mata bayani akan taimakon Sa'ada daza yayi amma fafur ta'ki fahimtar sa karshe cewa tayi ita Wallahi ba zata zauna da kishi ba babu irin lallashin da Momyn ta da kuma Momyn Ramadan basu mata ba amma tak'i sauraren su .
A bangaren Sa'ada kuwa tun tana sa ran kiran Ramadan har ta cire rai ranar biki tana d'aki kwance kawarta wacce ta bata aron waya ta shugo ananne take fad'a mata number data kira ta kuma kira ta d'aga an tambaye ta address d'in gidansu da garin da take saurin anasar wayar tayi tabbas number Ramadan ce sosai farinciki da murna suka rufe Sa'ada" cikin ikon Allah time d'in da suka iso ba'a d'aura auren ba anane fa Daddy ya siye kawu da kudade masu yawa aikuwa ba kawu ba har mahaifiyar Dikko Saida ta amince "ana d'aura aure suka d'auki amarya Sa'ada sai garin Katsina kasancewar ita Sa'ada a garin Kankia take .
Murmushi Karime tayi sannan tace Allah sarki mijin Sa'ada gaskiya ya cika mutum mai tausayi " kona tsaya sai gobe ma cigaba cikin sauri Karime tace aaa dan Allah ki ciga mun ina son jin yanda aka k'are.
Tunda Ramadan ya auri Sa'ada koda wasa bai ta'ba nuna yana ra'ayin jikinta ba ita kanta ta sani ruhinsa da zuciyar sa Alia suke so " haka yake zama ya tusa pictures d'in Alia yana kallo wani time d'in har hawaye yake Sa'ada ce mai lallashin sa ita kanta Sa'ada tasha kiran Alia ta bata hak'uri but haka Alia zata zage ta zagin Sa'ada" duk wata kula yana bama Sa'ada saidai me koda wasa bai ta'ba kissing nata ba as time goes tuni damuwa ta yiwa Sa'ada yawa domin ta gane cewa gangar jikinsa ta aura " akwai watarana Sa'ada na wanka Ramadan ya shugo toilet d'in wai ya dawo aiki ne bai ganta taba shine yaji k'arar ruwa kai tsaye ya shige toilet d'in she was naked amma haka ya tsaya hankali kwance yana magana da ita akan wai ya mata 3 missed calls she didn't called him back kunya sosai ta rufe ta "kare kirjinta tayi da hannuwan ta ga mamakin ta takowa yayi tareda d'ibar ruwa a hannun sa saman bayan ta za zuba ruwan murya k'asa k'asa yace bayan da kumfa the same thing ya kuma Saida ya wanke mata kumfan tas then ya d'auki towel tareda rufe mata jiki hannunta ya kama suka fito waje soasi tayi mamakinsa ita duk a tunanin ta yau d'innan Ramadan bazai barta ba "bayan sun fito zaunar da ita yayi saman dressing chair lotion ya shafa mata duka jikinta babu inda bai shafa mawaba " da kanshi ya shirya ta amma ita dai bata ga alamun wai hankalin sa ya tashi ba ko ace taga buk'atar ta a idonsa tayi mamaki matuk'a .
Tun daga ranar ya koma koda tana babu kaya baya jin komai yake shugowa toilet ko bedroom d'in "haka zalika duk time d'in da ya shugo tana saka kaya ko make-up haka zai taya ta kada da kiyi tunanin cewa jikinta is not attractive duk wani qualities na d'iya mace tana dasu kawai abunda ta fahimci she was not sexually attractive to him and baya bama zuciyar sa damar kwodaituwa da jikinta .
Haka Sa'ada taita had'e damuwar ta akan mikinta bata ita yake ba a kullun sai Ramadan ya tusa pictures d'in Alia gana yana kallo "wula'kanci da tozarci babu wanda bata gani wajen Momy da Hjy Mariya haka zalika Alia takan shugo gidan tayi mata tas wani lokacin ma idan iskancin ta ya motsa har gida take iske Ramadan ga shigar banza tayi taita kad'a kugu yana binta da ido duk abunda Alia taya burge shi take sosai jikinsa yake reacting akan Alia Saida me Ramadan mutunne mai kiyaye aika alfasha da tuni Alia tayi nasarar gurbata shi "ana haka watarana Alia ta shugo falon su zaune suke suna fira sama sama Koda ta shugo direct Ramadan ta nufa d'agowar da za yayi had'e bakinsu Alia tayi a gaban Sa'ada aikuwa mi'kewa Sa'ada za tayi domin ta basu space fad'uwa k'asa tayi ba numfashi aikuwa ture Alia yayi tareda banka mata harara Koda wasa irin haka bata ta'ba faruwa ba tsakanin su ko hugging nasa ta take yi badan Yana so bane kawai yana mata uzuri akan kusan rayuwar ta a Egypt tayi ta duba da yanda al'adar su take .
Cikin tashin hankali ya nufi Hospital da Sa'ada ananne Likitoci ke fad'a masa jininta yayi mugun hawa bayan haka zuciyar ta isa weak "likatan ne ya umarce sha akan if matarsa ta farfado yay k'okarin tambayar ta problems nata domin a sami solutions .
Tun a Hospital yake tambayar ta meke damun ta but ta'ki ce masa komai whenever ya tambaye ta kuka take saka masa .
Bayan sun dawo ne gida ya kuma tambayar ta fashewa tayi da kuka sannan tace duk abunda ya same ni kaine sila zaro idanuwa waje yayi tareda nuna kansa yes 'you are the reason akan damuwa ta mana "kama hannun ta tayi cikin nuna tausayinta da kuma jin haushin kansa yace please ki fad'a mun duk abunda nake miki wanda bakya so I promise ko menene zan gyara "jin furucin sa ne yasa ta fara magana kamar haka "yau 6 month kenan da auren mu but a kullun baka da magana ko tunani saina wata d'iya mace a gabana "why don't you think about my feelings why don't you understand the love i have for you shuru yayi yana sauraren ta murya k'asa k'asa yace you love me yes ta furta tana mai dafe zuciyar ta " I'm in love with you but murmushin takaici tayi sannan tace but your heart loves Alia " i can't force you to love me ka aureni ka taimaka mun i can't ask for more ,why ba zaka aureta ba for how many time nake maka maganar ka aureta sai kace mum tace sai if kayi divorcing d'ina then what stopping you from doing so please Ramadan divorce me so that ka auri Alia please kana cutuwa zaman da kake sani your heart tana Matuk'ar kaunar Alia .
Rungume ta tayi tareda cewa then teach me how to love please Sa'ada teach me zanyi k'okarin cire Alia Alaina because i can't divorce you bana son Sa'ada ki koma rayuwar rashin y'anci da gata bazan miki k'arya ba ina matuk'ar kaunar Alia saidai me ita d'in bata min halacci ba ifa har tana sona yanda nake sonta she should have agree na aureta ba tareda nayi divorcing naki ba but ta'ki amincewa da haka sabida haka from today zanyi k'okarin fitar da soyayar ta daga zuciya ta .
Tun daga wannan ranar Ramadan ya fara k'okarin saka soyayyar Sa'ada a ransa as time goes on saiga shi Ramadan yana kaunar Sa'ada fiye da yanda yake son kansa " Sa'ada ko girki bata iya ba sai daga baya ta koya wajen Ramadan and me "duk wani aikin gida yi mata yake har abunda bakya tunani
Ramadan yana yiwa Sa'ada kafun mutuwarta sai da taje Makkha yafi a kirga haka zalika family nata tuni ya wadatar dasu " domin ba kananun kud'i Ramadan gare shi ba kasancewar Building ya karanta a k'asar Italy Sadiq kuma Architecture sai Khaleel kuma Qs wato Quantity survey" babban Construction company gare su a garin Katsina haka zalika shima Abba Building ya karanta yanzu haka yana Lagos acan yake managing companyn sa acan Lagos Yana da mata duk k'arshen wata yake zuwa Katsina babu yanda baiyi da Momy akan ta koma Lagos da zama amma tak'i ita tafi son Katsina .
Dafa ta Rumaisa tayi sannan tace Karima kinji tarihin soyayyar Ramadan da Sa'ada yanzu zaki iya yanke hukunci akan wether you will fight for Ramadan ko akasin haka .
Shuru Karime tayi na wasu y'an da'ki'kai what if zuciyar sa ta za'bi Alia Allah shine ke tabbatar da komai kedai kiyi iya k'okarin ki In sha Allah komai zai zama labari" meya kamata nayi cewar Karime shawarar da zan baki ita ce just be natural kin gane duk abund za kiyi ki tabbatar gaskiya ce kada ki ringa masa wani abu da is not real gaskiya bata ta'ba ta'bewa kin gane noding kanta tayi
Ki kula dashi kiyi k'okarin mayarda damuwar taki in sha Allah za kiyi nasara " a yanzu zuciyar sa a rufe take in sha Allah kice zaki bud'e ta but you have to be strong Kin gane nothing good comes easy in sha Allah Anty zanyi iya k'okarina gaskiya Sa'ada ba k'aramin k'okari tayi batry your best Karime in sha Allah you will succeed .
*Mu had'u next page.*
*Hanaady*