MAI KWAĆŠAYI

2

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 2```


_______Cikin tsananin tausayi ta ke kallon yanda Halime ke zumuɗin ɗaukar farantin dake shaƙe da gyaɗa marau-marau da tuɓus-tuɓus duk girman tsanar da ta yiwa ɗaukar talla.


Tana ƙoƙarin barin ɗakin ta kirata cikin sanyin da muryarta ya yi,"Halime"

A kaikace ta juyo sai dai ganin yanayin Mahaifiyar tata yasanyata dawowa baya.

" Tayaya kuɗin ribar gyaɗa zai ishe ki zuwa Makaranta?, ina jin tsoron kar wani ya illatamin ke Halime, talla bashida wani riba sai danasani a ƙarshe"

"Inna za su isheni zuwa na gwamnati mana, kawai fa littafi da Uniform zaki siyamin sai jakar Makaranta da takalmi,ni basai kin bani kuÉ—in kashewa ba kuma In sha Allahu ba bu abinda zai sameni" ta faÉ—a tana dariya.

"Allah ya bada Sa'a"

"Ameen Inna"


Tun tanada ƙwarin gwiwar bin gidaje har ta gaji tanemi waje ta zauna cikin sagewar gwiwa domin ko rabi bata siyar ba.


Bayan ta huta taƙara ɗaukar harama sai dai har duhun magriba ya fara kunno kai ba'a ƙara siya ba,lungu da zai kaita gidan su ta laɓe tasha kukanta,amma batajin zata gajiya har sai burinta ya cika in sha Allahu kuma zatayi nasara.


Muryoyin Matasan gidan su da ta jiyo zuga gudane ya sa ta fara ƙoƙarin barin wajen tana goge hawayenta.


"Ke tsaya nan" ta jiyo Muryar É—aya daga cikin su na faÉ—a. Jikinta na rawa ta tsaya da duk addu'ar dayazo bakinta.

Cikin rashin kwaÉ“a da tarbiyyar da Yusha'u bai samu daga wajen Mahaifansa ba yake Ć™are mata kallo da farantin kanta.

"Daina kallona da wannan ƙwala-ƙwala idanuwan naki kafin in tsiyaye miki su"


Cikin fargabar kar ya yi mata wani mugun abun ta yi ƙasa da kanta.

Gyaɗar farantin ta suka sawa wawaso,kamar zatayi kuka ta ɗago tana kallon su.cikin rashin imani Yusha'u ya soka ma ta ɗan siriri ƙarfen da ke hannun shi a ɗaya idonta da ke kusa da shi,saboda gargaɗin da ya yi ma ta bataji ba.


Ihu da kururuwar neman taimakonta ne yasa ragowar da shi kanshi Yusha'un guduwa.


Cikin tashin hankali aka sanar da Innar Halime,

"Ga Halime can an tsiyayar ma ta da idanuwa",ta yi kuka mai zafi da ciwo lokacin da likita ya tabbatar mu su da ido ɗayan Halime ya tsiyaye.bazata ƙara gani da shi ba.


Yusha'u É—an babban Yayan su Mallam Shehu ne basa son laifin shi kuma su suka horar da shi kan tarbiyyar dayake kai ,rantsuwa ya yi da abinda zai kashe shi,shi bai ga ko Halime a hanya ba balle har ya yi mata wannan muguntar.

Inna da Halime suna ji suna gani zancen ya bi ruwa.


Sai Sunan Halime ya koma kashi uku wasu su kiranta da aihinin Sunanta wa su suce agolar gidan Shehu wa su kuma su kirata da sabon Sunan da suka sa mata Halime kanne manne....✍🏻


Ku yi following É—ina domin samun Update kullum