Chapter 05
*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*
*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
*Page 5*
_Monday 5rd March, 2022. Gidan Talabijin na Karamchi_
*10:04am*
A shashin al'amuran labarai na yau da kullum na gidan talabijin mai tashe a jihar gombe. Wani shashi ne mai girma a gidan talabijin ɗin mai ɗauke da babban falo tare da ofisoshin manyan ma'aikatan bangaren.
Irin su news manager, editer da sauran su shi kuma babban falo mai ɗauke da kowani rukuni kamar an ƙawayanta ma kowa bangaransa ne. Kowa kuma akwai ƙaramin teburinsa da kayansa a kai sai kujeran inda kake da muhallin ijiye komai naka, daga gefe akwai ɗan aninin da ke nuni da sunan mai wajen. Daga can kusa da office ɗin new manager wajen zaman Broadcaster ɗin gidan talabijin ɗin ne, daga gaba can kuma waje zaman camera man tare da reporters ne, da kuma ɗalibai masu sanin makaman aiki wato yan Intern.
Dole bayan sun haɗa rahottnni da kuma labarai wato bayan camera man da reporter sun gama aikin su kenan akwai bukatar editer ya duba ya kuma ta ce sahihancin labarin. Bayan ya gama dubawa kuma sai news manager ya duba ya cire kalmar da ya ga ba ta dace ba, dole dai sai an bi matakai kafin labarai ya kai ma masu kallo ko masu saurare. Kuma abuin da mutane wasu ba su sani ba, labaran da ake karanta su a gidan talabijin live ne, ko da an mai maitashi to sake karan tashi aka yi ba recording ba ne.
Sannan broadcaster zai iya zama reporter, amma ba kowani reporter ke iya zama Broadcaster ba, kamar yadda Salim Bunza ya kasance a gidan talabijin na karamchi Reporter ne, sannan kuma shi ɗin Broadcaster ne.
Mimi ce kaɗai ce ta kasance Broadcaster kaɗai kuma a tsarin gidan talabijin ɗin su biyu ne Broadcaster ɗin
Kowani na karanta oabarai sau hakwai a sati tunda kwanaki bakwai sai tsarin ya kasance kowa ya na yin adadin rabin kwanakin da zai kasance a sati. Tun da safe da yammah ne, su ma suna shan wahala kwarai tunda suna da tsare tsare kafin ma a fara ɗaukan labaran live a haska ma mai kallo. A kwai bukatar camera man tare da masu makeup tunda abu ne da duniya zata ri ƙa kallo a matsayin majigin gani da ido akwai bukatar gyara ga mai karanta labaran.
A can baya kafin Mimi ta fara aiki da su wata Cindera ce ta yi aiki da su yar Lagos ce, komawa ta yi garin su ya sa ta saki aiki da Karamchi a tsarin su, suke ba da kayan sawa in da zaka karanta labarai amma zuwan Mimi ta ruguza wannan tsarin ta ce ita da kayanta zata rika amfani tunda kuma yar ma su da shi ne daga ganinta kasan ba tsiya a jikinta kuma ta na da kyau ga iya ɗaukan wakan da kwalliya sai suka amince da tsarinta.
Abu ɗaya ake yi mata kafin a fara ɗaukan live shine makeup man ya gyara mata fuskarta ya ɗan kara mata hoda shikenan.
Duk da ba ta daɗe da fara aiki da su ba ta zama tauraruwa a gidan talabijin Karamchi saboda fuskar Mimi, ta kasance mace mai fara'a da farinjini manyan mutane sun sha kawo ziyara suna mai ya ba mata.
Sannan ga zaƙin murya ga turanci da ya zauna a bakinta, wanda in ta juya harshe sai ka rantse bata taɓa jin yaren hausa ba.
Daga office ɗin editor ta fito zuwa mazauninta in da ƙaramin oaptop ɗin ta ya ke da sauran tarkacenta ta ja Kujera ta zauna ita kaɗai ce a bangaren sai daga nesa kuma sauran reporters ɗinsu ne ke nuna ma ƴan inten wasu abubuwan.
Salim Bunza sai dare ya ke da karanta labarai bai riga ya shigo ba tukunnah.
Sanye ta ke da doguwar rigar atamfa mai adon zanen golding a jikinta ta sanya mayafinta mai raga raga a saman wuyanta da ya ji sarka mai kyau da yarari, hannunta sanye da zabbunanta na zinare guda biyu kafarta sanye cikin wani bakin Booth ɗin takalmi kalan na mata. Saukakkiyar kwaliya ce a saman fuskarta amma kallo ɗaaya zaka yi mata kasan ko ba ta yi kwalliya ba ita ɗin mai kyau ce. Ta zauna kenan wata matashiya daga cikin ƴan inten ta zo kusa da ita cikin girmamawa lokaci ɗaya tana faɗin.
"Barka da aiki Anty Mimi."
Ta juyo Cikin fara'a kafin ta ce"Yauwa Safina kina bukatar wani abu ne?
Safina ta karisa kusa da ita tana nuna mata takardan hannunta lokaci ɗaya tana fadɗn"kan wannan ne, ina bukatar karin bayani." Cikin kwarwaarta kan abin da ta karanta ta fara mata bayani har sai da ta gamsu. Cikin jin daɗi ta ce"Na gode Sosai Anty Mimi"
Gyaɗa mata kai ta yi cikin irin mirmishinta kafin ta ce"Kar dki damu aikina ne."
Cikin jin daɗi Safina ta wuce wajen ƴan'uwanta kamar daman ita su ke jira sai aka zagayeta ta fara kora musu bayanin da Mmi ta kora mata yanzu.
Ta na kallonsu a cikin ranta tana jin wani iri, dama ita ce dama dama ace zata iya maida hannun agogo baya. Su ɗin ta san ba su da wata matsala a rayuwarsu ba kamar ita da ciwon dake ckin zuciyata yake taso mata ookaci bayan lokaci ya hanata sukuni ba.
Ajiyar zuciya ta sauke lokaci ɗaya tana buɗe jakarta da ke kan desk ɗin dake gabanta, ta dauko wayarta ta na latsa hasken wayar sai ta ga Missed call har guda uku da sauri ta ja ta duba, sai ta ga Mommy ce ta kirata bata gani ba. Da sauri ta yi kokarin nemanta sai ga kiran Mommy ya shigo kamar yadda ta yi mata saving acikin wayar. Da Sauri ta ɗaga kiran cikin fara'a kafin ta ce" Barrister Murjanatu Soron ɗinki" Mommy daga can bangaren Ta ce.
"Na'am, Fatima kabir Dabo."
Sai Mimi ta saki dariya kafin ta ce"Mommy mun ta shi lafiya? ya Abi ya tashi?
Annuri na bayyana a saman fuskarta Ita fa Mommy yar ba ruwanta ne.Sunan kowa da sunan uban shi take yi masa saving a wayarta har Korafi ta taɓa yi mata ita kuma ta ce sunan su ne cikakke ko suna kyamatar sunan ne? Mimi tace a'a Mommy ta ce to ba za ta sauya ma kowa ba, to ba ma su kaɗai ba kowa haka ta ke yi masa saving acikin wayarta.
"Lafiya kalau muka ta shi, Habibi ne ma tun jiya ya(e ta kiran sunan ki shi ne nace bari na kira ki na faɗa miki.."
Mimi na dariya ta ce"Allah Sarki Abi Mommy ba shi wayar mu gaisa"
Mommy ta mika ma Abi wayar dake kwance a kan gado sai dai ta saka masa filo ta kara masa daga bayansa kansa ya ɗan ta sa sama. Cikin yanayin Muryan sa da ta sha jinya ya ce"Mimin Abi."
Da sauri Mimi ta ce"Na'am Abin Mimi ya jikin ka? Abi ya amsa mata da cewa yaji Sauki ya karishe da faɗin "Honey tana kula dani sosai na gode mata Allah ya yi mata albarka." Mimi ta amsa da Amin Amin.
Sun gaisa cikin fara'a da tambayan aiki ta ce gata ma a wajen aiki.
Cikin yanayin muryansa ya ce"Mimi ki yi hakuri da rayuwar nan kin ji ko?
Mimi ta amsa da cewa" In sha Allahu Abi Allah ya baka Lafiya."
Abi ya amsa mata da Amin kafin ya ce" yaushe za ki zo?
Da sauri ta ce"Abi kana son ganina ne?
Abi ya gyaɗa mata kai kafin ya ce"Eh ina son ganin ki, ki zo in kin samu dama."
Mimi ta amsamai da faɗin" In sha Allahu Abi Allah ya kara maka lafiya da tsawon kwana." Ya amsa mata dai dai ookacin da Mommy ta shigo bedroom ɗin ɗauke da Mug a hannunta damn tana bashi wayar ta fita zuwa Kitchen.
Tana zuwa kusa da shi ta sauke mug ɗin hannunta saman Side drower ɗin gadon dai dai ya na miko mata wayar ta amsa ta na karawa a kunne ookaci ɗaya tana faɗin.
" later lokacin karya wan Habibi ne."
Mimi ta ce"Mommy sai an juma."
Daga haka suka yanke kiran a lokaci ɗaya
Mimi ta bi wayarta da kallo tana ɗan Mirmishi, Abi da Mommy kenan sai ta tuna shekaru a can baya in ran Abi ya ɓaci Murjanatu ya ke kiranta kai tsaye Honey sai lokaci bayan lokaci. Amman yanzu komai ya sauya tsarin rayuwar da komai shi ya sa rayuwar nan duk babu tabbas a cikinta.
Yau fari ne gobe kuma baki, in yau ka ji daɗi gobe kuma akasin sa zaka shiga.
Tunani ta shiga yi, tunanin wani irin nema Abi yake yi mata, ko da yaushe tsakaninsu ban hakuri, ita kuma har acikin ranta ba ta taɓa rike Abi acikin ranta ba komai ya yi mata shi uba ne kuma duk abinnda ya yi domin ya inganta rayuwarta ne, ba taɓa fushi da shi Saboda abijbda ya faru a baya ba, Tana kaunar Abi domin mahaifinta ya wuce sauran mahaifa ya kuma yi mata gatan duniya nan, abin da ya faru wani kaddaren al'amari ne daga Ubangiji da bawa bai isa ya kauce ma faruwarsa ba.
Hankalinta ya yi nisa ba ta san Rukky ta shigo ba, sai kawai ji ta yi ta saita dai dai kunnenta ta ƙwala mata kira.
"Mimii..!."
Firgigit ta yi gabanta na faɗuwa domin ta ji tsoro sai ta ci karo Rukky da ta na mata dariya cikin jin haushi Mimi ta ce"Rukky Why? Kin bani tsoro ba ki ji yadda kirjina ke faɗuwa ba" Rukky na dariya ta zauna saman desk tana kallon Mimi kafin tace"Tunanin wa kike yi ne da ba ki san shigowa ta ba?
Mimi ta lumshe ido kafin ta buɗe tana faɗin" Me ya faru? Domin daga ganin bakin ki akwai mgana."
Rukky ta ce"Maganar dai da muka fara ta waya, ki zo mu tattauna yadda zamu shirya bikin Bibi."
Mimi ta kalleta a karkace kafin ta ce"Saboda ita Bibi ba ta da ƙawaye?
mu fa yayye ne Baby ina ruwan mu da tsara biki wannan ai sai ƙawayenta."
Rukky ta ce" Bibi ta ce mu tsara komai kinsan fa ba ta da wasu kawaye, sai wasu yan makarantar su kuma kinsan yadda zamu tsara al'amarin ba kamar su ba."
Mimi ta yi shuru kafin ta kara mgana Rukky ta shagwabe fuska ta na faɗin" Haba mana Hajiya Mimi ta."
Mirmishi ta yi kafin tace"Yaudara! Zan shigo gidan sai mu yi mgana."
Rukky tace" Yauwa ko ke fa? yaushe to za ki shigo ? Ko yau kawai ki jirani na tashi sai mu tafi tare." Mimi ta taɓe baki kafin tace"Yau daga nan ina komawa gida zan dauki Hajiya mu je gidan Daddy kinsan Mama ta kwanta asibiti jiya aka sallamo ta sau ɗaya naje na duba ta shi ne yau zan kai Hajiya mu kara dubata."
Rukky ta jinjina kai kafin tace"Shike nan Allah ya ba ta lafiya."
Nan suka cigaba da hiran su Rukky na faɗa mata yadda za su tsara Bikin ya yi kyau sosai. Mimi na dariya tac e"Kina ta tsare tsare Baby, shin angon nan zai fitar da kudaɗe ne masu yawa ya baki?
Rukky tace"Ba ma dolen shi ba, ai na yi mgana da shi yace ba matsala akwai abokansa da suke tunanin ɗaukan nauyin yin dinner, mu dai nan kamu kaɗai Ummi tace zata ɗauki nauyi."
Mimi ta gyaɗa kafin ta ce"Good! Allah ya nuna mana ookacin da rai da lafiya."
Rukky ta jima har sai da aka kira wayarta sannan ta bar wajen Itama Mimi bata jima ba ta kwashi tarkacenta ta shiga office ɗin manajansu ta kai masa takardun hannunta suka yi mganar da za su yi ta ce mai ita ta tashi sai gobe da yammah tunda sai karfe bakwai din gobe take da karanta labarai amman zata shigo zuwa la'asar. Daga nan ta fito ta yi sallama da sauran ma'aikantan bangaren su. Ta fita zuwa babban falon da ke ma'aikan ana mata mgana ta na amsawa da sakin fuska. Na Misau ta hanga yana ta hira da wani ɗan siyasa acikin shirin Nageria a siyan ce. Daga masa hannu ta yi ta cikin gilashin da ya raba wajen shi kuma sai ya jinjina mata kai.
Ko bangaren su Rukky ba ta biya ta fita zuwa haraban wajen ta kunna motarta bayan ta ijiye jakarta a kujeran mai zaman banza ta zagaya ta shiga bangaren direba ta zauna da bismillah a bakinta. Sannan ta yi ma motar key ta juya ta fice daga gidan talabijin ɗin megadi na faɗin a sauka lafiya Hajiya." Itama sai ta ɗaga masa hannu cikin fara'an da ke saman fuskarta.
Bata da chanji ne acikin jakarta sai dai gobe in ta dawo. Mimi mai kyauta ce abun hannunta baya rufe mata ido in tana da shi ta ba ka in bata da shi ta ba ka hakuri.
Gida ta koma ta iske Hajiya ta yi barci sai Baaba Uwani kaɗai a gida tana ta zirga zirga sannu da gida ta yi mata sannan itama ta shige cikin ɗakinta. Kaya ta sauya zuwa masu sauki na gida sannan ta haye gado ta kwanta ta na motsa jikinta domin tana jin jikinta duk gajiya ya saukar mata.
Har ta kwanta sai kuma ta mike ta isa kan Dressing mirror ɗin da ke ɗakin ta buɗe jakarta ookaci ɗaya ta ciro wayarta ta koma ta kwanta. Faceebook ta shiga ta sauya Account ɗin ta na Asali na Fatima Kabir sulaimam Dabo(Mimi).Zuwa wanda ta buɗe na sirri da suna MIAJ Kuma account ɗin bai da suna ko wani bayanan da za'a iya gane ko wani jinsi ne. Da ɓoyayyen account take bibiyan Aji kuma da shi ne ta tura masa friend request tun shekaru huɗu da suka gabata kuma ya karɓeta sannan tana following ɗin GOMBE UNITED nan t ke ganin wasu abubuwan
Tun da shi ba chart yake yi ba, ta sha masa sallama bai taɓa buɗewa ba ballantana ya amsa ta ba, sai dai ta na bibiyan shi ta hanyar club ɗin sa. A nan ne ma ta samu hoton sa da ta kai aka yi ma babban elegerment, anan take ganin in suna da wasa da garin da suka je anan kuma take ganin irin cigaban da ya samu bayan rabuwar su. Ba za ta taɓa manta lokacin tana Kano tana Master ɗinta ba , ta taɓa haɗuwa da ɗaya daga cikin abokansa mai suna Nasir. A bakin shi ta fara jin Aji yanzu ƙwallo yake yi, ta daɗe ta na mamaki sai da ta gani sannan ta tabbatar. Shiga ta rika yi hotunan da Club ke ɗorawa yawanci na yan wasan su ne, har akwai hoton da aka ɗauka da Aji tare da Coach ɗin su ookacin da ya yi singing contract da su.
A nan take samun ganin rabin ranta ta kuma kalle shi son ranta, komai nashi na nan a yadda ta san shi sai dai yanzu ya rage fara'a sannan fuskar nan a kimtse kamar wanda ke cikin bacin rai, ya kara dai girma tunda shekaru sun ja, wani hoto da ya yi mata kyau sai da ta ɗauke shi. A Studion ne aka ɗauki hoton yana sanye a blue din kayan kwallo a jikinsa ya duka kamar zai taso daga sujjuda zufa duk ya cika fuskarsa a wannan hoton ta ga dariyan shi.
Har ga fararen hakoransa nan sun bayyana.
Kamar kuma a wani gari ne da suka je kwallo, sai da ta duba rubutun ƙasan Hoton ta ga an saka. Kaduna da date din sannan an Rubuta Captain Aji baka dariya sai ka kada masu gida. Itama sai da ta murmmusa a sanin da ta masa a baya yana dariya.
Sai dai ta san masifaffe ne, abu kaɗaan sai ya harzuƙa sa ya fara masifa. Ga zuciya da kafiya in ya kafe akan abu baya sauya ra'ayi. Tana kai hoton da ta ɗauka wajen da take adana hotunan sirinta ta furta a fili" Ko yanzu ya daina faɗa? Ko wasu hallayansa ne suka sauya bayan mun rabu?
Sai ta kasa ba ma kanta wannan amsar, sai kawai ta kashe data, ta sauka daga kan Account din ta kashe wayarta ta sauke a gefenta ta koma ta kwanta tana sauke numfashi. Ya jima ta na ta tunane tunane kafin barci ya kwasheta. Ba ta tashi ba sai da Hajiya ta shigo tana buga mata kafa da cewa an yi azahar. Sannan ta iya tashi a kasalance ta shiga tiolet tayi alwala ta zo ta yi sallah sannan ta fita fallo ta iske Baaba Uwani da Hajiya suna hira.
Kirchen ta nufa tana faɗin "Baaba me kika girka mana yau?
Baaba Uwani ta ce"Alala Hajiya ta ce tana jin ci yau, shi na yi."
Mimi ta daka yar tsalle kafin ta ce"Kai Hajiyata Allah ya saka ki a gidan Aljannah, kamar kin shiga raina daman na ce sai weekend na zauna nayi Alala na kwana biyu ban ci ba." Ta faɗa tana shiga kitchen ɗin cikin farinciki.
Hajiya na mirmishi ta ce"Daman nasan kina so, rashin samun zama ya sa ba ki yi mana mun ci ba, da Uwani take tambayata abin da za a dafa na ce ta yi mana Alala kawai." Ta na jin maganar Hajiya daga cikin madafin , miyanta har tsinkewa yake yi sanda ta ga alalan gwangwani da manja.
filet ta samu ta zubo guda huɗu ta saka yaji kaɗan mai daɗi da Yaddiko da aiko ma da Hajiya ta kuma tsiyayi soyayyan manja a gefe. Ko da ta fito falo mirmishi kawai take yi cikinta na wani yamutsawa.
Gefe ta samu ta zauna kan cafet ta yi bismillah ta fara ci loma daya biyu ta ɗago tana kallon Hajiya dake kallonta kafin ta ce"Hajiya ke ba za ki ci ba ne?
Hajiya na yar dariya ta ce"Sai ya sha iska zan ci kar na ci da zafi ya lalatamin ciki."
Mimi ta ce"Hmm hajiya da zafi ya fi daɗi."
Baaba Uwani ta saka dariya tana faɗin" Binta ko na saka waigi ne?
Mimi ta jinjina kai kafin ta ce"Baaba na manta kafin ki saka waigin haɗomin da ruwa wayyo daɗi Hajiya."
Ta ke faɗa tana cin alalanta tana santi Hajiya da Baaba Uwani na yi mata dariya.
Baaba Uwani ta tashi ta ɗauko mata ruwa mai sanyi da kofi ta kawo mata.
Mimi na ta buga santi suna ta mata dariya tas ta Cinye ta sha ruwa kafin ta ce"Baaba Uwani Allah ya yi albarka ya sa a gama da duniya lafiya."
Baaba Uwani na dariya ta ce"Amin Binta."
ta mike ɗauke da filet ɗin hannunta tana faɗin"Baaba Uwani cikin Albashina na wannan watan kina da dubu goma cash tukwaicin Bintan Hajiya ne."
Baaba Uwani ta ɗaga hanci ta rangaɗa guɗa kafin ta ce"Ina godiya uwar ɗakina Allah ya saka da alheri Allah ya tsare gaban ki da bayan ki Allah ya rabaki da sharrin makiya da mahassada, Allah kuma ya bama babanki lafiya." Mimi na gabda shiga madafi ta ce"Amin Amin Baaba Uwani da kika yi min addu'an Allah ya ba ma Abi lafiya kamar na ce na ƙara miki wata duban goman""
Ta faɗa ta na yar dariya Baaba Uwani ta kara karkacewa ta yanka wata guɗaa kafin ta ce"Gaba salamun baya salamun yar lelen Hajiya da ba kamarta Allah ya kara arziki da wadata Na gode kwarai"
Hajiya na gefe da cashaba a hannunta tana ja cikin mirmishi ta ce"Da kin kara da addu'an Allah ya kawo ranar auran Binta da wuri wuri da na cike miki kudin sun zama dubu hamsim"Baaba Uwani na jin haka ta yi zaman dirshan gaban Hajiya tana faɗin"Allahu Akbar Uwar marayu, kin goya na gida kin goya bare, ai ban gama addu'an ba, tana tafe Allah ya nuna mana auran Binta Allah ya bata miji nagari kyakyawan kamarta mai kyan hali da mutumci kamar ita.." Hajiya na dariya ta ce"duk da kin makara na dai ƙara miki dubu goma."
Baaba Uwani ta ɗaaga hannu alamun jinjina kafin ta ce"Allah ya kara nisan kwana Hajiya, Allah yasa ki dade a duniya kina goya marayu irin mu."
Hajiya ta ce"Uwani ai duk sona da duniya sai na mutu na barta ballantana ai bazan iya rama shekaruna na baya a duniya ba, ke dai Allah yasa mu cika da kyau da Imani."
Uwani ta amsa mata da Amin Mimi ta fito ta na taɓa cikinta lokaci daya tana faɗin.
" Hajiya mu bar tafiyar mu gidan Daddy sai anjuma lokacin cikina ya sassaɓe"
Hajiya ta kaɗa kai kafin ta ce"Daman ai sai rana ta yi sanyi."
Baaba uwani na gefe ta ce"Hajiya nima ina son zuwa na duba mai jikin."
Hajiya ta ce"Ba matsala duk sai mu tafi tare.
tashi ki zubomin alala ya kara wucewa kafin na gama lazimi."
Baaba Uwani ta mike ta na faɗin "Angama Uwar marayu." Mimi kuma dakin Hajiya ta shige ta je ta kunna talabijin. Tunda bayan falo akwai wani talabijin ɗin a ɗakin Hajiya.
Mbc Bollywood ta saka sai ta ga a wani Film ɗin da ta ke matukar so mai suna HIKCHI
FiLM ɗin Rani murkarji ne. Cikin jin daɗi ta gyara zama ta cigaba da kallo.
Ba su samu tafiya gidan Daddy ba sai bayan la'asar, gidansa na anguwan Abubakar Habu Hashidu Estate ne, Hajiya na gidan gaba Mimi na driving Baaba uwani na gidan Baya. Sanda suka je gidan sun iske Jaheed ya zo garin tunda mahaifiyarsa ce Mama sai Amaryanta da suke kira da Anty.
Gidan Alhaji Hamza Sulaiman Dabo gida ne na rayuwar yan boko, kowa kuma abin da ya ga dama shi yake yi shi ba mutum ba ne mai zama ɗan siyasa mai jama'a, kuma ba shi da takura da matsawa rayuwar boko zallah kawai iyalansa ke gudanarwa.
Ko da suka shiga ɗakin Mama Jaheed suka iske kwance kusa da Maman kamar zai koma cikin cikinta. Ga kanwarta nan a cikin ɗaakin amman bai saka shi ya fita ba.
Ya juya yana ta magana a waya sai da yabji mganar Mimi da Hajiya ne ya yanke wayar da ya ke yi ya juyo ya na sakin Mirmishi ya ce"
"Hajiyata Amaryata."
Hajiya ta balla masa harara tana faɗin"Ni ai ba na mijin da kai, tafi can soloɓiyo kullun kwance ɗakin uwa kamar wani jariri, ke Hansa'u hala nono kike ba shi ne?
Gabaɗayan su ka fashe da dariya shi kuma sai ya hau shafa kansa. Mama ta ba ma Hajiya wajen zama na saman kujera guda ɗaya da ke cikin bedroom ɗin ta.
Kanwarta mai suna Hajiya Turai ta kada baki ta ce"Ai Jaheed jin sa ya ke kamar Yaya bata yaye shi ba."
Mama ta yi dariya ba ta yi mgana ba, saboda ita macece mai kaunar ya'yanta haka zaka ga ko masu auran in suka zo Jikiko su hau jikinta iyayensu su kwanto kan Jikinta. Ita Anty ma ba ta taɓa haihuwa ba sai dai suna zaune lafiya sai dai kishi na halitta.
Bayan an gaisa da yambayan jki Mama ta ce ta samu sauki, Hajiya ta ce"Sannu! Allah ya kara lafiya.'
Ta amsa da Amin Jaheed kuma kusa da Mimi ya koma ya zauna kamar zai shige jikinta ta yi saurin matsawa kusa da Hajiya Turai daman a gefen gadon ta zauna a kusa da ita. A cikin kunnenta ya yi mata raɗa" Me na yi miki ba ki ɗaukan wayata?
Mimi ta kalleshi ta na masa inkiya da su Mama sai kawai ya ɗaga murya yana faɗin" Mama ga Mmin ba kin ce za ki yi mata mgana ba? Mama ni fa Mimi ta ce ba ta sona me na rasa mene ne bazan yi mata ba in mu ka yi aure?
Ya faɗa cikin yar shagwaɓa Mimi kunya ya kamata sai ta yi saurin tashi, Mama kuma idon Hajiya ya sa ba ta yi magana ba sai Hajiya Turai ce ta kalli Mimi tana faɗin" Mimi miye aibun Son da ba ki son shi? gaye na nunawa daga nan har london?
Ta karishe faɗa cikin zolaya Mimi ta kasa mgana kanta dai na kasa Hajiya sai Mirmishi ta ke yi ba ta ce komai ba.
Baaba Uwani ta ce"Ai daga nan har gaba da london ma Hajiya, wane mutum.."
Mirmishi ya yi kafin ya mike ya na fadin"To na rasa me ya sa ba ta so na"
Yadda ya faɗ kamar zai yi kuka, Hajiya ta taɓe baki kafin ta ce"Ba dole ta ce bata son ka ba, kana mgana kamar wata mace. Ni kuma Binta na namiji take son aura ba yaron mama ba." Kamar magana ce Hajiya ta sakarma Jaheed ɗin da uwarsa amma sai ba wanda ya nuna
Dariya kawai aka yi, sai ya nufi Hajiya zai mata shagwaɓa ta mike tana faɗin"Ni matsa tafi wurin uwarka ita zata iya da wannan lagen wuya naka kamar wata mace mai laulayi." Mimi sai da ta saka dariya shi kuma sai ya tura baki.
Hajiya Turai ta ce"Ko dai hajiya na kishi ne."
Ta karishe faɗa cikin zolaya Hajiya ta wuce gaba tana faɗin"Allah ya tsareni ko tsohon mijina Sulainmnu kafin ya bar duniya duk tsufansa ya fi min wannan lange langen ɗan naku. Allah ya kara lafiya Hansa'u Binta mu je ko? Hajiya ta faɗa tana kallon Mimi daman kamar akan ƙaya take ta yi saurin fita daga ɗakin.
Mama da Jaheed suka biyo bayansu suna faɗin" Tun yanzu za su tafi ba za su bari Alhaji ya dawo ba?
Hajiya na cigaba da tafiya ta ce"Wani Alhajin kuma? Hamza ko da safe ya zo mun gaisa."
Jin haka suka yi shuru Anty jin tafiyar su, ya sa ta fito suka yi sallama har bakin mota Jaheed ya rakasu.
Ya za ga ya ta bangaren Mimi cikin yar shagwaɓa ya ce," In zo gobe?
Mimi ta ce"No ina wajen aiki?
Da sauri ya ce" Sai na same ki acan mana."
Mimi ta yi saurin cewa"A a ka bari in na dawo zan kira ka."
Karya wuya ya yi kafin ya ce" Jibi zan koma saboda haka promise"
Ya faɗa har ya na mika mata hannu sai taki kamawa sai kawai ta girgiza kai kafin ta ce"In sha Allahu zan kira ka."
Sai lokacin ya yi mirmishi ya zaga ya wajen da Hajiya ke zaune ya zaro kuɗi Sabbi daga aljihun Jeans ɗin da ke Jikinsa ya ɗorama Hajiya a saman cinyarta, sannan ya sagala Hannu ya mikama Baaba Uwani nata ta karɓa tana masa godiya.
Sai kawai ya ce"Baaba uwani addu'a zaki yi min Allah yasa Mimi ta so ni."
Baaba Uwani ta ce"Da ikon Allah zata so ka ɗan Alhaji kuma kun bala'in dacewa da juna." Ta faɗa tana yar dariya, Jin haka ya sa ya kara dumbuza mata kuɗi ya mika mata ta karɓa tana saka albarka da addu'an Allah ya ba shi Binta.
Mimi ta ji hauahi ya isheta ta yi ma motar ta key, ya ɗaga ma Hajiya hannu yana fadin"Amaryata sai na zo, na ba da kudin cefane ba na son gori."
Hajiya ta ce"Sai ka zo tunda kana yi da ni ai shik enan Allah ya yi albarka."
Yana ɗaga musu hannu har suka bar haraban gidan.
Sai da suka hau titi Baaba uwani na dariya ta ce"Dubu ashirin ne ɗan Alhaji ya bani Hajiya"
Hajiya ta ce"Kin gode kuwa."
Mimi na tuki ba ta ce komai ba, Baaba Uwani na soke kudinta a haɓan zaninta ta ce"Binta ina laifin ɗan Alhaji? ga shi ɗan uwanki don Allah ki saurareshi mu yi tuwo na maina"
Mimi na jin ta ba ta yi mgana ba Hajiya ce ta ce"Ai Babanta ma ya ce tunda ba ta so a bar mganar, kuma Ya faɗa ma Hamza, shi dai yaron ne ya kasa hakura."
Baaba Uwani ta ce"Wayyo wallahi ya na son Bintar ki Hajiya ki saka baki ta saurere shi."
Hajiya ta ce" Ba ruwana ai ba ni zan zauna ma ta da shi ba, in sun daidaita kansu zan fi kowa murna da haka."
Mimi na jin haka ta kaɗa kai kafin ta ce"Baaba uwani ni fa Jaheed baya cikin, irin jerin mazan da nake son aura ni da shi ba bambamci ya yi ta wani abu kamar ba namiji ba, ko maganarsa irin na mata ne fa ba ki ji ba?. Ta faɗaa cikin marairacewa, Baaba Uwani ta ce" kuma fa hakane yana abu shima kamar na mata."
Hajiya na dariya ta ce"Ai na matan ne, ko ba ku ga yadda yake nane da uwarsa ba."
Daga Mimin har Baaba Uwani sai da suka saka ma mganar Hajiya dariya.
Ita kuma ta ce"To ina mamakin yaran zamanin nan, kamar sun fi kowa sanin darajan Ƴaya mu namu ƴaƴan ba ƴaƴa ba ne." Mimi na dariya ta ce" Hajiya ta kenan."
Hajiya ta yi mirmishi ba ta dai yi mgana ba.
Suna tafe suna hira har suka isa gida, ammh sai da suka tsaya a hanya Mimi ta siya kayan marmari saboda na su ya ƙare kuma mai kawo cefanan wannan watan ya yi nuƙusa ni, daga gidan Daddy ne kila gobe ko Jibi za'a kawo kayan abinci da cefane.
Washegari kafin Mimi ta je wajen aiki Rukky ta dameta da kira dole ta shirya ta fita gabaɗaya, ta fara biyawa ta gidan su Rukky sannan da la'asar ta tafi wajen aiki, rigimar Rukky ce da ba ta karewa.
Dole wai sun shiga bikin ƙanwarsu sun yi kane kane, to ya ta iya? In bata saka kanta ba, nacin Rukky kaɗai ya isa ya hanata barci cikin salama.
*****
*7rd March, 2022*
11:40pm
Ɗakin Inna Meri cike yake da baƙi mutanen Kano ne suka zo garin tn jiya Mu'azzam da matarsa Hibba da ɗansu mai sunan Baba Danjuma suna kiran shi Junoir. Anty Amina itama tun safe ta zo ita da nata gayyar ƴaƴan, sai kuma Bintu tare da ƴan biyunta.
Sai Anty Halima itama da nata gayyar Ƴayan. Sai Hibba da Walida sai Mariya a ɗakin Inna Meri ya cika da hayaniya, ita kuma daman abin da take so kenan..ta yi nan ta yi nan duk domin ta ga ta farantama ƴaƴanta da jikokinta da suke tafe bin ta wannan ya ce Inna zan sha tea sai wannan ya ce Inna zan sha ruwa. Uwayensu na zaune ita ke tsaye kan kafafunta a kansu.
Iyaye nasu na zaune suna hira suna dariya.
Magajiya na tsakar gida tana shanyan yan kayanta da ta wanke sai kwafa take yi, bakin ciki ya kusa kasheta in ta jiyo shewan Ƴaƴan Inna Meri daga bangarenta.
Gaje ce ta shigo daga bangaransu da botiki a hannunta duk da an raba ƙofa amma itama jin hayaniya ya sa ta wanke wasu kaya ta shigo shanya domin ta ji gulma.
Tana ganin Magajiya na shanya sai ta wayance da cewa"Au ke ma wanki kika yi, nima tun safe na ke wanki igiyan can ya cika sai na ce bari nazo na shanya anan."
Magajiya ta taɓe baki kafin ta ce"Nawa ba su da yawa, ki shanya daga gefe."
Daga haka ta cigaba da shanyanta tana tsaki ita kaɗai. Gaje ta zo ta fara shanyanta lokaci ɗaaya ta na nazarin Magajiya kafin tace" Hala mariya ba ta gidan ne?
Magajiya kamar ta na jira ta fara faɗin" Ta na nan, ammh ta na ɗakin uwarta Meri tunda taji zuwan su Amina da safe.".
Gaje ta rike haɓa kafin ta ce"ashe su ne su ka zo shi ya sa na yi ta jin hayaniya, ke ko dan'uwansu ya zo mana jiya mun sha tsaraba an gode Allah ya ba da lada."
Magajiya ta sake yin kwafa kafin ta sauke ajiyar rai ta na faɗin"Uhm!
Daga nan ba ta kara mgana ba, sai dai jefi jefi ta na ta sakin tsaki ƙananu.
"Salamu Alaimkum.."
Muryan Jummai ya shigo tsakar gidan lokaci ɗaya da bayyanarta a tsakar gidan fakan fakan ta shigo gidan ga goyo ga Ƴaƴanta guda uku kai da kai suna bin ta a baya Magajiya ta dakata da ƙokarin zuba ruwan da take yi za ta yi wanka.
Gaje ce ta tari Jummai da faɗin"A' a Jummai ce a gidan." Jummai na zama saman tayels ɗin dake Kofar ɗakin Magajiya lokaci ɗaya tana faɗin "E Gaje, Magajiya ina kwana, wai Mu'azzam ya zo garin nan ƴaron nan munzali ya ke faɗa min ya ce da safe ya ganshi"
Ta faɗa tana nuna ɗan babba ciki ƴaƴanta.
Magajiya bata yi mgana ba Gaje ta ce"Eh ya zo jiya, kin makara har mun cinye tsaraba."
Jummai tace"Kan uba har kun ma isa, Magajiya ina tsaraban mu?
Magajiya ta kalleta a fusace kafin ta ce"Sai ki shiga ɗakin uwarsa ki tambayeta domin duk abin da ya zo da shi shashenta aka shiga da shi, sai abin da ta ga dama ta aikomin da shi." Ta faɗa tana nuna bangaren Inna Meri ta na jin wani bakin ciki na yi mata suya acikin ranta.
Jummai ta rufe baki kafin ta ce"Wai kaɗan ta baki magajiya?
Kafin ta yi mgana, Gaje ta yi saurin cewa" To ai daman haka take yi, ta wani tattare komai sai kace agolan ɗan ta ne ya kawo, ai ba ita ta haifi Mu'azzam ɗin ba, balle ta rika tattare komai in adalci zata yi sai ta fito da shi ayi raba dai dai.".
Ta karishe faɗa a na waige waige na munafunci jummai ta sauke numfashi ta kwanto goyon ƴarta ta buɗe rigarta daman tuni ta cire hijabi, nono ta jawo wani yaraf kamar tsumma a yamushe ta tura ma yarinyar nono a baki Lokaci ɗaya tana faɗin"Ta wani fannin da ƴar gaskiyarta fa gaje, kin manta lokacin da Maman Mu'azzanm ta rasu, Baba ya yi ya yi da Magajiya ta rike su ta ce ba zata rike ɗan kowa ba, bayan ya auro Inna Meri ya ba ta su ta kuma karɓe su ta riƙe su da Amana to anan fa banga laifinta in ta kankane komai ba, da Magajiya ta rike su da yanzu komai suka samu yana bangarenta ne."
Magajiya kamar ta kai ma Jummai duka haka ta ji, cikin ƙufuluwa da ɗaga murya ta ce"Eh din,na faɗa na kara faɗa bazan riƙe ɗan kowa ba ni ma kaina Ƴaƴana sun ishe ni." Jummai ta ce"Hmm!
Kafin ta mike yarinyar ko gama shan nono ba ta yi ba, ta warceta ta saba a kafaɗa lokaci ɗaya tana faɗin" Bari naje shashen Inna Meri na samo tsarabata."
Harara magajiya ta bi ta da shi kamar Idanuwanta za su faɗo ƙasa. Gaje ta rakata da faɗin" Za ki samo kam, domim Meri ba daga nan ba wajen kyauta."
Magajiya ta kalleta a wulakance kafin tace"Gaje ba kin gama shanyar ba?
Gaje na rawan baki ta ce"Eh dama..!
"To kama gaban ki gaje, kinsan halina bana son Munafunci yanzu sai aji mu da ke."
Take faɗa lokaci ɗaya tana zuba ruwa a botiki rabi ke shiga ciki rabi na zuɓewa saboda bakincikin an yabi halin kirkin Inna Meri, magajiya mace ce mai bakin kishi da hassada da ƙyashi. Gaje ta ɗauki botikin ta kama hanyar fita tana faɗin"Abun bai kai ha ka ba Magajiya sai an juma."
Daga haka ta fice ta na taɓe baki.
Magajiya ta ja tsaki sai a lokacin ta ga munzali yaron jummai.
Tsawa ta daka masa kafin ta ce"Ta shi ka bi uwarka kafin na mare ka."
Sumu sumi ya mike ya bi bayan uwarsa kamar yadda kakarsa ta faɗa ita kaɗai ta shiga ɗakinta Lokaci ɗaya ta na dage labulen ɗaakin ganin shi kaca kaca.
Kyafci ta yi lokaci ɗaya tana faɗin"Sai na yi ma mariya bugun tsiya, yar iska yarinya kawai." Take faɗa ta na faman kaye kaye ta na tsaki ita kaɗai.
A shashen Inna Meri kuma ya kacame da hira, Jummai daman akwai zence in ta zauna kaf sai ta zazzage asirin gidanta kullun cikin babu, ba ranar da Jummai za ta zauna ta faɗi alheri a kan mijinta sai dai ta ce ba ta da shi Saboda a taimaka mata.
Mu'azzam in yazo gari haka ya ke fama da babun ƴan'uwansa marasa godiyan Allah, Mansoor dai ba ma ganinsa suke yi ba shi ya fi yi ma mazan matan ma wata sai ta yi shekara bata ganshi ba tunda ya fara harkan ƙwallon nan. Kuma sun fi sakewa da Mu'azzam Mansoor daman shi tuntuni sun ɓata garinsu a wajensa mata ba ta isa ta tare shi da wata mgana ba.
Jummai ke ba da labarin a anguwarsu wani gidan ɗan majalisa yana raba tallafin kayan abinci da suka je bin layi sai da ta yi faɗa da wata mata. Hibba na zaune ta ce"Kai yaya Junmai dambe a titi ba girman ki ba ne."
Bintu ta yi dariya kafin ta ce"Baki san Yaya Jummai ba ne shi ya sa."
Hibba sai kawai ta kaɗa kai ta ce Allah ya kyauta wayarta mai tsada ta ɗauka ta tura ma Bobo ɗinta sakon tana Jiran sa zai zo ya kaita gidan su ne yau can zata kwana.
Daman auran zumunci ne tsakaninsu da Mu'azzam ɗiyar kanwar mahaifiyar Mu'azzam ce aka yi haɗin zumumci.
Yanzu can bolari zata fara biyawa babban gidansu kafin ta wuce tudun wada gidansu.
Sai ya ce mata yana tare da Mansoor in sun gama gashi nan zuwa. Amina ta kalleta kafin ta ce"Kun fasa tafiya can tudun wadan ne? Sai ta girgiza kai kafin ta ce"Ya ce yana wajen Yaya Mansoor in sun gama zai taho."
Bintu na jin an ambaci sunan shi ta yi saurin cewa"Baban Inna, uhm ban faɗa muku abin da ya yi min ba?
Nan ta shiga ba su labarin faɗan da yaje ya yi mata a gaban kishiyarta da mijinta.
Cikin takaici Binta ta ce"Ni ba abin da yafi ban haushi sai cewan da ya yi sai ya yi biji biji da ni na kara mgana a wajen."
Jummai ta ce "Kan uba, shi fa daman masifaffe ne, har yanzu bai daina masifarsa ba." Halima ta ce"Ya rage masifa amma ya kara ninka bakar zuciyarsa."
Hibba na jin su ta na dariya sau ɗaya ya taɓa zuwa gidanta na kano sai dai su hadu in sun zo garin nan. Ta san shi tun suna yanmata tunda suna zuwa gida nan.
Ita dariyansa ne ba ta taɓa gani ba, Kamar baya son zama acikin mutane ne.
Nan aka buɗe caftan Baban Inna ana ta gulmansa.
Hibba na saurare tana dariya farar mace ce doguwa mai kyau da ita ga gashi da ka ganta ka ga bafullatan gombe.
Suna cikin mgana Inna Meri ta leƙo tana faɗin " Duk ina jin ku, ku gama za ge min Babana na gode."
Sai gabaɗaya suka saka mata dariya har da Jummai tana faɗin"Ni dai inna ban da ni kar ki hanani tsaraban Mu'azzam"
Domin jummai akwai son abun duniya zata iya kwantar da kanta saboda abun duniya.
*An samu kuskure a page 1, in da na ce Mimi ta karanci Mass communication a Faculty of Sciences, kuskure ne zan ce ne a Faculty of Social Sciences*
*Janafty*