3
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 3```
_______Halime kanne manne shine Sunan dayafi yiwa Innar Halime ɗaci a cikin zuciyarta, daga Inna har Halime sai zaman tsakar gidan ya fara gagarar su saboda habaicin Inna Huwaila da baya ƙarewa.
Kullum idan ta kalli mudubi ta ganta da ido É—aya sai taji burinkanta na bin iska, tayaya zatayi ilimi da ido É—aya tsokanar Æ´an Unguwar su kaÉ—ai ya isheta.
Makarantar Allo ma sai yafara yiwa Halime wahalar zuwa saboda kullum da kuka take dawowa.
Ƙawarta Hindatu mai zurfin buri kan tayi ilimi mai zurfi irina Halime ne, ta bata ƙarfin gwiwar komai zai zama nasara a rayuwarka to sai mutane sun maka dariya karta karaya kuma ita ba nakasasshiya bace kamar yanda mutane su ke yawan faɗa,har me ta rasa? Kawai dan tarasa ido ɗaya.
A karon farko da Halime ta daina jin haushin dariya da kuma tsokanar da mafi akasarin mutane suke yi mata,sai dai ko da ta tuntubi innarta kan sha'awar komawarta talla domin yin tarin kuɗin Makaranta, faɗa ta rufe ta dashi ta kuma nuna ƙin amincewarta.
Rayuwar kaɗaici da tsangwamar da Halime take fuskanta daga ɓangarorin mutane da dama idan ka cire Hindatu,Innarta,da Mallam Shehu ba bu wani mai son ya mu'amalance ta har ƙawayenta na baya sai suce kunya sukeji agansu da ƙawa mai ido ɗaya, Halime sai ta fara ƙanƙancewa tasawar da yara sukeyi sai ta daina, maimakon ta ƙara tsaho ko jiki sai ta fara ramewa kamar batacin abinci. ƙaton cikin da kowa ya wayi gari yaga Innar Halime da shi ne ya ɗaga hankalin kowa.
Halime tuni ta manta da damuwarta saboda murnar cikin da taga Innarta da shi.
Inna Huwaila daina zaman tsakar gidan ta yi sai yawon biye-biyen yanda cikin Innar Halime zai salwanta ko ta haifa babu rai, wannan dalilin ya sa Halime ta fara samun sakewar zamar tsakar gidan har ta yi Æ´an wasanninta
#MAYSARAH
#HALIME
Follow me for more update