MAI KWAƊAYI

4

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 4```



________Haƙurin Innar Halime da kawar da kai kan duk wani cin kashi da mutanen gidan su ke yi mata ne ya sanya ƙiyayyarta a zuciyar mafi akasarin su gushewa, suma ragowar ganinta da cikin Baba Shehu kamar yanda suke kiranshi ne ya sa ƙiyayyarta da ƴarta fara rikiɗewa zuwa soyayya. Ba su da wani haɗin kai tsakaninsu amma akwai shaƙuwa mai ƙarfin da Mahaifin su ya gina su akai tsayin shekaru duk da iyalan su sun so wargaza hakan.



Duk wanda ya tsokaneta a hanyarta na zuwa Makarantar Allo bata kulasu kuma har cikin ranta batajin damuwa kamar lokutan baya.


Duk ranar da sukazo giftawa da layin ita da Hindatu sai ta ƙara waiwayawa ta kalli tarin mabaratan dake jere a dogon layin da tafkeken gida daya ya cinye, shifiɗe da titi da bishiyu ma su kyau da birgewar da bazakace a irin Unguwar su ya ke ba.


"Hindatu wai me ake bawa waɗannan Matan suke yini a wannan wajen?"

Halime ta tambayi Hindatu tana ƙara waiwayarsu lokacin da suke ta rububin siyar awarar wata yarinya da bazata wuce sa'arta ba.

"Bara mana Halime,kuma an ce kuɗi suke samu sosai idan ma su gidan sukazo fitowa duk da an ce babu wanda yasan fuskokinsu sai dai na direbobin su amma tsabar kwaɗayi ko tsoro basaji,ai ni tsoro bazai barni na karɓi kyautar su ba" Hindatu ta faɗa tana taɓe baki.


Daga haka suka faɗa hirarrakin su na ƙuruciyar da rabinshi shirme ne.


Tunanin yanda suke rububin siyar awaran ne yafi tsayawa a ran Halime,sai take ganin kamar wani dama ta samu na shigarta Makaranta Boko,kuma tasan Innar ta bazata hana ba tunda ba yawon talla zatayi ba.


Har Halime ta zo kwanciya tunanin yanda Mabaratan nan suke rububin siyar awaran ya kasa barin ranta.amma tana tsoron kar Innarta taƙi amincewa.

"To su waye masu gidan? ko ƴan yankan kai ne kamar yanda taji mutane na yawan faɗa?to idan Mutanen ƙwarai ne maiyasa basa mu'amalantar mutanen Unguwa? Saboda su masu kuɗi ne" zuciyarta tabata amsa.

Da ire-iren waɗannan tambayoyin ta yi barci, ranta fal zullumin kar Inna ta hanata cikar muradinta.


★Cikin fargabar hukuncin da Inna zata yanke ta sameta da zancen zuciyarta na harbawa,tanajin wannan ne damarta na ƙarshe.


A nutse Inna take kallonta da tsananin tausayi, batada halin siyawa Halime kayan karatu saboda na cefane ma ba kullum Maigidan yake samun kawowa ba,wa su lokutan ma ƴan uwanshi ne suke taimakamai kuma tasha gwada sana'ar cikin gida amma basa siya sun gwammace su fita waje.

Bataso ta kashewa Halime burinta ko dan nakasunta, amma batajin zata ƙara barin Halime fita talla akaro na biyu,girgiza kai tayi kafin tafara magana cikin tsananin tausayinta.


" Halime kiyi haƙuri da kaina zantara miki kuɗin shiga Makaranta, amma banason ki ƙara ɗaukar talla ko nan zuwa ƙofar gida ne....✍🏻