5
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 5```
______"Dan Allah Inna karkice haka babu abunda zai ƙara samuna"
Halime ta ƙarasa faɗa hawaye na zubo ma ta.
"Ki bari zanyi shawara kinji" Inna ta faÉ—a tana shafa kanta
Ba don Halime ta gamsu ba ta saki ranta.
Tun daga ranar Halime sai ta mayar da layin gidan abin kallon kamar ta samu Tv.
Hindatu tun abun na bata haushi harta dawo yi mata dariya.
ShuÉ—ewar kwanaki har zuwa wata É—aya Innarta batace komai ba,bayan kullum da fargabar shawarar da Innar zata yanke take kwana,
washe garin data yanke shawarar tambayar Inna hukuncin data yanke Allah ya sauki Innarta lafiya ta haifi É—anta Namiji kyakkyawa mai kama da ita.
Farin ciki da zumuÉ—in samun sabon jaririn da sukayi ne ya danne damuwar Halime.
Babu wanda bai yi farin cikin haihuwar Innar Halime ba sai Inna Huwaila,ƙarara ta fito da baƙin cikinta, duk da kowa ya san rashin haihuwa da ciwo amma Allah ne yake bayarwa.
Ranar Suna yaro yaci Sunan Mahaifin Baba Shehu Idris sunayi mishi kara da Babangida.
Kamar Halime jira take yi Innarta ta samu ƙarfin jiki ta sako ma ta zancen kai Awararta gidan bayan layin su.
A wannan karon uzurin batada kuÉ—in jarin da zata bawa Halime ta kawo.ta É—an samun kuÉ—in Æ´an barka sai dai ba wasu masu yawa bane yawanci daga masu bata hamsin,ashirin harda ma su Naira goma. dudu data haÉ—a kuÉ—in ba su fi dubu É—aya da É—ari biyar ba kayan sawa ne suka samu balaifi da É—an yawa.
Cikin wannan damuwar dake danƙare aran Halime su ka shiga watan Ramadan,bata fashin zuwa Sallar asham kuma duk zuwa sai ta yi addu'ar Allah yasa ta samu Barka da Sallah mai yawan da zai isheta ɗan jari koda ya ya ne.
Allah baya barci,a wannan Sallar Halime ta tara kuÉ—i ma su yawan da zasu isheta É—an jarin da zata fara da shi.
Kamar anyi mata albishir haka ta wuni cikin farin ciki.
Bayan an gama hidimar Sallah Inna ta yiwa Halime awarar dayasa Inna Huwaila dariya harda kifawa"meye wannan dole ne yin sana'ar abu kamar na rowa Allah dai ya rabamu da irin wannan talaucin" ta faɗa tana riƙe haɓa haɗe da ƙarewa farin roba dake kan Halime kallo wanda duk yaji jiki alamun ba sabo bane.
Da fitar Halime bai fi da minti talatin ba saigata ta dawo da empty roba bakinta kamar zai yage tana sosa idonta ɗayan dayake manne.hakan data shigo tanayi da ɓakin cikin ganin saurin ƙarewar awarartata yasa Inna Huwaila yin shewa haɗe da faɗin"Halime kanne manne,mekike sosawa"ba iya Halime ba hatta Innarta taji matuƙar zafin furucin Inna Huwaila.
Cikin ƙwalla da murmushin daya tsaya iya laɓɓanta tace"Inna ki daina cemin kanne manne banaso"
"Ai sai an tsiyayar ma da ragowar idanuwan garin banza burinki zaki dawo Halime manne gabaki É—aya"ta faÉ—a ranta fari fes saboda ganin yanda fuskar Innar Halime ya sauya duk da bata tanka mu su kota nuna taji mai suke faÉ—a ba.
Comments É—in ku ne zai sa nafara long page.
Alamar littafin yana muku dadi