Chapter 10.
*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*
*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
*Page 10*
*MAFARI.*
_20 DECEMBER 2008_
Anguwar GRA, Gombe.
Hankalinsa na kan ƙaramar wayar dake hannunsa yana yin game ɗin nan mai maciji, tun bayan da suka gaisa da Baba megadi ya koma gefe ya tsaya jefi jefi kuma ya na duba agogon fata irin na matasa a wancan lokacin dake ɗaure a tsitsiyan hannunsa na hagu, gani yake yi kamar yau Inna ta jima ba ta fito ba. Hon ɗin da ya ji an zuba ne har sau uku ya sa ya juyo ta wajen get din sai yaga wata mota mai ruwan toka za ta shiga gidan ba motar ba ne ta bashi mamaki illah daga baya ya hango wata matashiyar yarinya ta jikin window ɗin motar na gidan baya ta lafe sai kalle kalle take yii, da yake lokacin saka ma gilashin mota rufuwa bai zo ba ana iya ganin na ciki, sannan na ciki na iya ganin na waje shi ya sa ya iya hango yarinyar dake cikin motar itama ta samu nasaran ganinsa.
Abun da ya bashi mamaki ganin ta yi masa mirmishi sannan abun burgewa a tare da ita shine loɓawar kumatun ta ma'ana dimple sannan ta ƙara masa da ɗaga hannu, bai maida mata da martanin ɗaga hannun ta ba. Sai dai ya maida mata da martanin mirmishinta a gaban idanuwansa a ka buɗe get motar ta sulala cikin gidan, har kuma suka shige tana kallon shi yana kallonta shima. Sai da motar ta shige cikin gidan sannan ya sauke Ajiyar zuciya shi kaɗai acikin ransa yayi ma kansa tambayar.
"Wacece wannan yarinyar?
A iya sanin shi bai san akwai yara a gidan Hajiya ba, kafaɗa ya ɗaga alamun sanin wacece ita bai dame shi ba, maida hankalinsa ya yi kan wayarsa bai san fitowar Inna Mero ba sai da yaji tana kiransa.
"Baban Inna.."
Da sauri ya ɗaago sai ya ci karo da ita a gabansa ɗauke da wani kwano a hannunta, da hanzari ya saka wayarsa a gaban aljihun rigan dake jikinsa fara mai ratsi ratsin baƙi, sai baƙin wandon dake jikinsa. da sauri kuma ya saka hannu ya karɓi kwanon hannunta yana faɗin" Inna wannan kwanon fa?. Tana mirmishi ta ce"Hajiya ce ta sakani sai da na ɗauko abinci"
Sun fara tafiya a jere da juna ya ke faɗin" Inna ni fa ba na son kina ɗauko abinci daga gidan nan, sai mutane su rika tunanin ko kin raina ƙokarin Baba ne"
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" To ai mutane Allah ne kaɗai da ya hallicesu ke iya musu dai dai, ba ka biye ta mutane ba Baban Inna, kasan ai ba na son ɗaukowa Hajiya ce ke matsamin kuma in ban ɗauko ba sai ta ga kamar ban ji maganarta ba ne."
Gyaɗa kai ya yi batare da ya yi magana ba sai da suka yi nisa daga fitan layin gidan na masu hannu da shunu suka kama hanyar anguwarsu ta marasa karfi wato Arawa.
"Inna ki sha kurumin ki, in na samu aikin soja za ku huta ke da Baba In sha Allahu, ba za ki ƙara fita wani gida aiki ba."
Ta na mirmishinta da ba ya ɓacewa a saman fuskarta ta ce"Allahu ya sha Baban Inna Allah ya ida nufi na alheri."
Kai tsaye kuma ya amsa da Amin kafin ya ce"Inna ni fa ina son na yi aure da wuri, saboda na bar miki matata a nan in na tafi aikin soja ta rika taimaka miki da wasu ayyukan."
Inna Meri ta yi dariya mai tsawo tana mai bin yaron nata da kallo. Mansoor kenan manyan ƙasa shi kansa tsaye yake faɗin ra'ayinsa. Duka duka shekarunsa ashirin ne a duniya amman ya na da burikan ya zama wani abu saboda iyayensa su ji daɗi.
Tana jin sa ya cigaba da faɗin"Allah Inna da gaske nake yi, ina son na yi auren wuri ina son ganin na haifi ƴayan da zamu zama, muna kamar Yaya da ƙannensa."
Inna ta kaɗa kai tana dariya kafin ta ce"To Allah ya nuna mana Baban Inna."
Ya amsa da Amin Innata.
Suna tafe suna hira tunda akwai yar tafiya kafin su isa gida, ya saba kullun zai je kofar gidan da take aiki ya jirata har ta fito su dawo gida tare, Mansoor matashi ne mai ƙulafucin uwa mai kuma son mahaifiyarsa ba shi da mafita ne, da bazai taɓa bari Inna Meri ta yi aikatau a gidan masu kuɗi ba.
"Inna kamar yau kin wuce lokacin tashin ki ko?
Kai tsaye ta ce"Eh Hajiya ce ta tsaida ni na gyara ma jikarta da za ta zo mata hutu ɗaki shi ya sa na ɓata lokaci."
Kallonta ya yi kafin ya ce"Ko ita ce na gani an kawo ta a mota kafin fitowar ki?
Inna ta ce"Eh ita ce Fatima Hajiya na kiranta Binta mai sunanta ne shiyasa take sonta, yar wajen babban ɗanta ne wani Soja a Abuja." Yana jin Inna na mgana amman bai tanka mata ba itama sanin halinsa ya sa sai ta saki mganar ta kalleshi tana fadin"An taso islamiyar ne? Na ga kuma ai shidda ba ta yi ba? Kai tsaye ya ce"Ba'a ta shi ba Inna."
Ba tare da ya gayamata wani abu ya faru ba ta kalleshi lokaci ɗaya tana faɗin"Kai Jama'a yauma faɗan ka je ka yi da wani a makarantan Baban Inna,?
Mirmishi ya yi kafin ya ce" Inna ba faɗa ba ne, kawai dai yar cacan baki ne"
Inna ta ce"Cacan baki ai ƙanin faɗa ne Baban Inna, kullum ina yi maka faɗan shi fa rayuwa da kake gani sai ka yi hakuri in kana so ka ci riban duniya wannan baƙar zuciyar na ka tun yanzu ya kamata ka koyi yaƙi da ita in ba haka ba nan gaba ba za ka iya sarrafa kanka ba." Da sauri ya ce"Ba faɗa na yi ba fa Inna mgana ya gayamin ni kuma ma maida masa sai mallam Haruna ya koremu daga ajin gabaɗaya, ni kuma ganin an kusa tashi sai na biyo ta nan kawai."
Inna ta kaɗa kai kafin ta ce"Ai shike nan Allah ya kyauta, nasan dai bai wuce Agola ya kira ka ba, kuma na gaya maka ka daina damuwa da masu kiran ka da sunan nan, ai ba maƙale maka zai yi a jikin ka ba, ina ruwan ka da su ka kyalesu su yi ta kiran ka Agola hakan ba zai rage ka da komai ba kuma ba zai ƙare ka da komai ba"
Mansoor ya yi shuru kafin yace"Ba ma wannan ba ne, Shamsu gidan su man bala ne fa ya ce wai Mu'azzam ba ƙanina ba ne ni kuma nace Innar su ce ta auri Baba ta haife shi? Inna Meri ta fara salati tana tafa Hannu kafin ta ce"Na shige su ni Maryamu, haka ka gaya masa Baban Inna,?
Ko ajikinsa ya ce"To inna maganarsa ce ta ɓatamin rai shi ya sa na tambayesa ko Innar su ce ta haifi Mu'azzam ɗin?
Inna Meri ta kaɗa kai kafin ta ce"Ka bari ba kyau zagin iyayen wasu kaji ko? nima in wani ya zage ni ba za ka ji daɗi ba, duk duniya ba wanda ya isa ya ce Mu'azzamu ba ƙanin ka ba ne ya faɗa ne domin ya tunzara ka." Suna tafe ta na mgana kuma duk Nasiha take yi masa akan hakuri da kuma daina bakar zuciyan nan nasa nuna masa ta ke yi mai hakuri shi ke da ribar duniya kuma ya ke da ribar lahira.
Suna shawo kwanar layin su suka ci karo da dandalin yara da matasa sun taso daga makarantar islamiyan Mallam Ɗahiru, Mansoor ya hango Mu'azzam tare da su Nasir suna baya suna tafiya suna magana yana jin muryansu a sama gaddama ta sarke su kuma Mansoor na da tabbacin gardaman ƙwallo ce. Su binta kuma suna gaba tare da su Zuwaira amman Bintu na kamkame da hannun Walida da ita ce karama a kaf gidan Wanzamai ita da Mariya.
Bintu ta fara hango inna Meri sai ta saki hannun Walida ta nufi innar da gudu ta faɗa jikinta har garin gudu tana watsa ma Mansoor kasa a kafarsa dake cikin bakin takalminsa. Ransa ya ɓaci tsawa ya da ka mata yana faɗin"Ke zan ba ki wahala, ba ki da natsuwa ko? Sai a lokacin ta ganshi da Sauri ta makale bayan Inna ta na tura baki, dukawa ya yi ya na kakkabe kafarsa itama Walida ta zo da gudu ita a lokacin ko shekara goma ba ta kai ba, Bintu ce ta haura sha amman kuma ba Hankali.
Inna Mari ta tasa ƴaƴanta gaba Mariya da ke tare da su Jummai tana so ta je wajen Inna Meri Zuwaira ta riketa tana mata jan ido, Inna Meri ba ta damu ba ta kallesu tana faɗin"Ƴan makaranta an dawo?
Cikin su ba wanda ya kalleta har da sauran tawagan ƴaƴan su gaje kallonta suka yi suka watsar suka wuce gaba yan matan masu girma irin su Zuwaira suka tasa kannen su gaba sai gidan Wanzamai.
Wanda kaf garin Gombe gidan wanzamai ɗaya aka sani da ya yi shuru gidan da Inna Meri take aure a karo na biyu kenan.
Ba ta damu kanta ba tunda ai ba yau aka fara sai ta rike hannun Bintu da Walida ta bi bayansu, Mansoor kuma ya wuce wajen su Mu'azzam da suka tsaya gaddaman ƙwallon kafa sunan kuma sun dawo islamiya
Mansoor na zuwa wajen ya tankwafi keyar Mu'azzam yana faɗin"Wuce muje gida ka tsaya gaddaman tsiyanku na fama"
Mu'azzam ya dafe kanshi yana yar dariya Nasir ya ce"To mai ƙani ai mu kuma sai mu kwana a hanya."
Mansoor ya harare shi kafin ya ce"Nasir ka rika yin abubuwan ka cikin Aji don Allah."
Makama ya ce"Gaya masa ya cika zubar da class." Ahmad dake gefe ya kwashe da dariya Nasir ya sha mur bai yi mgana ba suna ta hararan juna da Mansoor.
Shi kuma bai damu ba ya tasa ƙaninsa Mu'azzam a gaba yana rike da kwanon da ya karɓa hannun Inna Meri suka wuce gaba su ka bar su Nasir a baya suna kallonsu.
Duka yan nan tsukun anguwan ne, kuma tare suka taso tun suna ƴan yara makaranta boko tare suka yi haka allo da islamiya.
Cikinsu Mansoor da Nasir ne sa'anin juna sai Ahmad sai makama ƙaramin sai Mu'azzam, kuma shima abin da ya sa ya zama tamkar abokinsu duk inda Mansoor ya saka kafa to a bayansa Mu'azzam ne ya na bala'in ji da ƙaninsa, yana kuma kafa kafa da shi to saboda yana shiga cikin su ne ya sa suka haɗe gabaɗaya su biyar ma su mabambamtan hallaya. Kuma duka ana ruƙunun anguwa iyayensu suke sun san juna shiyasa abotan su ta yi tsawon da kowani lokaci suna tare.
Gidansu Mansoor ne a gaba su kuma nasu Nasir sai an yi gaba shi ya sa su suka fara shigewa suka bar su Nasir ya yi tsaki kafin ya ce"Aji ɗan renin wayau ne, ya cika zafi da masifa" sunan Aji da Mansoor ya samu acikin sunan shi su Nasir suka fara saka masa sunan saboda shi mgana ɗaya biyu sai ya ce a riƙa yin abu cikin Aji ko ya ce wane ba ka da Aji tun yana ƙaraminsa Mutun ne shi mai kamewa da son harkan girma ba ya son reni da kuma yin abu na marasa aji. Shiyasa da suka sanya masa sunan suna kiransa har a makaranta wasa wasa yau da gobe har sunan ya bishi acikin anguwa sai an ce Mansoor Aji a ke gane shi.
Tun suna makaranta kuma sunan ya bishi Aji Aji, sannan a filin ball din su ma sunan shi kenan Aji mai Buga lamba goma tunda suna cikin group ɗin matasa anguwan da suke buga kwallo har Team ma garesu mai Suna NASARA TEAM.!
A lokacin da Inna Meri ta shiga cikin gida duka matan gidan suna tsakar gida, tunda gidan na a zamaninsa na baya kafin ya samu gyare gyare Gaje da Harira na tsakar gidan tunda a lokacin suna amfani da tsakar gida ɗaya ne. Dakin Magajiya ne a farko na Inna Meri na daga ɗan wani lungu kaɗan. Ta yi sallama ba wacce ta amsa mata kuma sun ji ta sai ta kada baki ta ƙara kwala sallama wannan karon Harira ce ta amsa sai Inna Meri ta ce"Ina ta sallama ba ku amsa ni ba."
Sai ma suka yi kamar ba su ji ba kowacce ta na ji da ƴaƴanta suna ta kawo labaran abin da ya faru a makaranta.
Bintu tuni ta warce hannunta ta wuce ɗakin Inna Meri ta na tura baki yunwa take ji ta fara binciken neman abinci, Inna Meri aka bari tsaye da Walida kamar an da sa su.
Magajiya na zaune saman kujera yar tauggono ta na tukin tuwo sai magana take yi da su Jummai kamar ba ta san da wanzuwar Inna Meri a wajen ba.
Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce"Sannu da gida magajiya, ba ki ji ni ba ina ta sallama ba ne" Kawai sai Magajiya ta fara masifa tana faɗin "To ina ruwana da sallaman ki da za ki zo kaina kina damuna, ni na tura ki gantalinki da sunan aiki da za ki dawo ki shaidamin kin dawo? nifa ba na son munafunci Meri ki yi ta kanki nima na yi ta kaina, ki yi harkarki na yi tawa tunda ba zaman juna muke yi acikin gidan nan ba"
Ta faɗa ta na wani kumfar baki dai dai lokacin da Mu'azzam da Mansor suka shigo gidan. Kuma tun a kofar gida suka fara jiyo jarabarta illai daman su san da uwar su ce tunda ta raina ta daman.
Mansoor da ba shi da hakuri ya ƙariso yana faɗin"Inna me ke faruwa ne?
Tana ganinsu gudun wata fitinar sai ta ja hannun Walida tana faɗin" kun ga ba wani abu ba ne. Mu je ku yi alwala ku tafi masallaci." Mu'azzam ya yi gaba shi da Walida Mansoor kuma ya tsaya yana kallon Magajiya kallon ki ki yayi kanki
Itama ta kalleshi ta watsar Inna Meri ta turashi gaba ta na faɗin muje Baban Inna an fara kiran salla. Da haka ta ja shi shashenta ta karɓi kwanoon hannunsa ta ce Mu'azzam ya saka masa ruwa a buta su yi alwala. Bintu kuma na tsakar ɗaki tana cin abinci Mansoor ya kalleta kafin ya ce"Ke kafira ce da baki sallah?
Abincin ya kasa shiga cikinta ta damkesa a bakinta ta na girgiza kai, wani kallo yayi mata kafin ya ce"Ki bari na kara kifta idona na ganki a nan wajen sai na wahalar dake."
Yana gama faɗin haka ya shige ƙaramin makewayin dake bangaren Inna Meri, Bintu kuma na tura baki ta mike Inna ta karɓe kwanon abincin tana faɗin"In ki ka yi sallar sai ki cigaba da ci tunda kin zama acici."
Mu'azzam na alwala ya na mata dariya sai ta dauko murfin kwano zata je fe shi da shi ya sha mur ya na kallon kofar makewayin kafin Ya ce"Yayanmu ga Bintu..'
Ai kafin ya rufe baki sai ga ta fito da gudu dai dai lokacin da yake fitowa daga makewayin.
Tun kafin ma ya kalleta ta ce"Ba buta ne ina jiran Yaya Mu'azzam ya gama ya bani ne" Dariya ta kusa kama Inna dake duke ta na gyara ma Walida sikat ɗin jikinta Mu'azzam dai sai da ya yi yar dariya yana yi ma Bintu gwalo. Sai da ya jira sa ya gama alwalan sannan suka fita masallacin tare suka bar Inna da su Bintu a gida suna yin nasu.
A can masallaci suka sake haɗuwa da su Nasir , Nasir har ya na ce ma Mansoor " Su Aji masu ƙani ka wani tasa shi gida, to mu ka ga ba mu je gidan ba."
Yana jinsa ya yi masa banza daman ai basa zaman lafiya ba su da aiki sai faɗa shi Aji taurin kai da saurin gusata shi kuma Nasir naci da neman mgana.
A kofar masallacin su ka haɗu da shamsu shima matashi ne kamar su ya kalli Masoor kafin ya ce"Ba dai ni ka zaga ba? Wlh sai naci uwarka."
Mu'azzam na jin haka da sauri ya ce"Kai me yayi maka kake zaginsa?
Nasir da Ahmad suka zagaye shamsu Aji na gefe ya harɗe hannaye a kirji yana jin wani irin zafin zuciya na taso masa wai shi shamsu zai ce zai ci uwarsa.
Su a kokarin su Nasir shamsu ya gaya musu abin da ya faru duk ajinsu ɗaya a islamiyan amman ba su san abin da ya faru ba tunda ba waje ɗaya suke zama ba malaman suna raba musu wajen zama saboda in sun zauna waje ɗaya ba sa karatu.
Mu'azzam kuma ba ajinsu ɗaya ba shi ya na Aji biyar ne su kuma shidda.
Kuma dukkansu wannan shekaran za su gama babban sakandiri illah Mu'azzam da ke aji ɗayan babban sakandiri tunda shekarunsa iyakarsa sha bakwai cikin na takwas ne. Ko kafin shamsu ya gama maida ba'asi Aji ya dunkule hannu ya kai masa naushi saboda yana maida mganar yana ƙara faɗin daga an ce Mu'azzam ba kaninsa ba ne shi ne zai zagar min uwa? Karya a ka yi kanin nashi ne? Ai agola ne zuwa da shi gidan wanzamai Innar sa ta yi."
Shamsu yaji zafin naushi ganin har jini ya fito shima ya dunkule hannu ya rama ko kafin su Nasir su shiga tsakani sun kaure da dambe dole mutanen dake cikin masallaci da waje suka zo rabon faɗa ciki har da su Baba Ɗanjuma da su Baba Ɗanlami har kuma da mahaifan su Nasir. Shi kan shi Shamsun har da uban sa. Sai da aka samu aka raba fadan amman fa Shamsu ya ci naushi duk bakinsa ya haye ga shi yana fitar da jini.
Mansoor fitinanne ne yana da baƙar zuciya in dai iya fara faɗa ba ya iya bari ana raba su fa domin aji ba'a si yana ƙara kaima Shamsu naushi. Baba sani ya yarfa ma Mansoor mari a gefen fuska yana faɗin"Kai kaci gidanku kai kaɗai ne mai zuciya anan wajen? Ana mgana ka bari kana kara wani hakilo to sai ka daki wanda za ka daka kaji ko? Ya faɗa Saboda ganin yadda Mansoor ɗin ya ke wani huci ya na kallonsa kirjinsa na sama da kasa zufa na keto masa
gashi ya dumkule hannayensa guda biyu ya na jiran ya kai naushi.
Baba Danjuma ya ce"Sani a bi a sannu don Allah." Baba Ɗanlami ya ce"Yaya Ɗanjuma ka daina saka baki in yaron nan na iskanci, ji abin da yake yi kamar shi kaɗai ne mai zuciya anan wajen" Shi dai Baban Danjuma ƙokarinsa a samu sasanci.
Shamsu aka fara tambaya abinda ya faru ya maimaita karya da gaskiya.
Baba Ɗanlami ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce"To mi ye abun faɗa anan ai ba karya ya yi ba me kuka haɗa da Mu'azzam ɗin? Kowa fa yasan zuwa da kai uwarka ta yi garin nan" Baba sani ya ce"Kuma ban da rashin tarbiya har da ce masa wai uwarsa ce ta auri Yaya Ɗanjuma ta haifi Mu'azzam kaji wani rashin ɗa'a yanzu ya dace aji wannan mganar a bakin yaro kamar Mansoor?
Nasir ya yi karaf ya ce"To amman shi ina ruwansa da cewa Mu'azzam ba kaninsa ba ne, kuma ai yanzu shi ya fara ganinsa ya zage shi." Su Ahmad ma suka ba da shaidar haka har da Mu'azzam.
Shi ko Mansoor an an yi ya yi mgana bakar zuciya ta hana shi, mahaifin Shamsu Mallam bala ya ba da hakuri ga Baba Danjuma shima ya bashi hakuri suna gayama juna ƴaƴa kowa fa ya haifa sai hakuri.
Su Baba Sani ke ta manganganu suna faɗin"Yaya Ɗanjuma duk kai kake sangarta yaron nan, yana iskancin da ya'yan mu ba sa yin irin shi." Da an yi mgana sai ka ce maraya ne ai kowa ma marayan ne muma ai marayun ne." Haka suke cewa sanda suke hanyar komawa gida, su Nasir kowa ya wuce gidan Mansoor kuma Baba Danjuma na rike da shi suna tafiya daga baya faɗi yake yi"Ka rika saka ma zuciyarka salama kaji ko Baban Inna rayuwar nan duka duka nawa take? Cikin jin haushin ya ce"Me ya sa ya ce Mu'azzam ba ƙanina ba ne? Ai ka auri Innata kuma ita ta rike Mu'azzam saboda haka kanina ne"
Baba Ɗanjuma ya ce"Kwarai ma da gaske ba wanda ya isa ya ce kai ba Yayan Mu'azzamu ba ne, suna tafe ya na ta bashi hakuri shi kuma ya na faman saukar da zuciyarsa Mu'azzam shi ya yi saurin yin gaba ya je ya gayama Inna abin da ke faruwa ko kafin su Mansoor su shigo labari ya kawo cikin gida tunda su Baba Sani tun a tsakar gida suka fara mangaganun Yaya Danjuma na ɗaure ma Mansoor kugu yana ma mutane rashin mutumci a gari da ko su ya'yansu ba sa aikata irin shi.
Gaje ta taɓe baki kafin ta ce"Da an yi mgana sai ace ya na da bakar zuciya ga shi ba ka isa ya ganka ya gaisheka ba a wulakance sai dai yace wai barka."
Suna cikin mganan Baba Ɗanjuma ya shigo rike da Mansoor su Gaje suka gaishe shi ya amsa kai tsaye ɗakin Inna Meri ya wuce da shi ya na kiran ta kamar yadda ya saba.
"Meri meri, ina Merin take ne?
Su Baba Sani da matansu suka bi shi da kallo Baba Ɗanlami ya nuna Yayan nashi lokaci ɗaya yana fadin "Ji be shi, yadda ya ke rawan jiki da yaron nan na tabbata ko Auwalu baya yi ma haka'
Magajiya daman na cikin ɗakinta tana sallah tana sallamewa ta fito tana faɗin" ko Auwalu da ya haifa baya masa son da yake ma agolan nan da Meri ta zo da shi gidan nan Ɗanlami, yanzu haka su yana nan nan da su amman Auwalu bai san ma in da yake ba sai can in ya ga bai ganshi ba ya fara ma mutane faɗan wai Auwalu ya koyi yawon dare, to ai gwara ya koya tunda bai iya jan sa a jiki ba sai Agolan da ba jininsa ba."
Baba Danlami ya ce"Magajiya lamarin Yaya Danjuma fa akan agolan nan na Meri sai Allah kawai, in muka yi mgana sai ya ga kamar muna nuna ma yaron bambamci ne, kuma mu tsakani ga Allah gaskiya muke gaya masa sai ya rika nuna mu ba mu san girman Amana ba, kuma sai ya rika nuna wai yaron maraya ne." Magajiya ta taɓe baki kafin ta ce"Ai ga shi nan ya za me ma Agola uba ya kuma maida ƴayan sa marayu"
Duk kuma manganganun da suke yi a kunnen Inna Meri da Baba Ɗanjuma, dake kofar ɗakinta saman tabarma.
Hatta Mansoor ɗin da Mu'azzam suna zaune, Bintu da walida dai suna cikin ɗaki tare da su Amina da ba su jima da dawowa daga gidan ba.
Kan Mansoor na kasa ya na huci Inna Meri ta cire tagumin da ta yi kafin ta ce"Ni na rasa yadda zan yi da yaro nan mallam, nasihan nan ko ɗazu muna tafe a hanya sai da na yi masa, kai dai Baban inna kana son kowa ya rika kama sunanka, to ka sani ba ka san bakin wani ba in wani ya yi maka baki ka lalace ba ruwana."
Baba Ɗanjuma ya sausaauta murya yana faɗin" ki daina faɗin haka Meri yarinya ta ne in ya ƙara girma zai daina in sha Allahu, ki zuba musu abinci su ci ko sai mun dawo salla ne?. Ya faɗa ya na kallon samarin nasa guda biyu, Mu'azzam ya gyaɗa kai shi ko Mansoor bai yi mgana ba.
Inna Meri tace"Sai kun dawo domin ban jima da yin talge ba."
Tunda daman tana da sauran miyan kukan jiya sai ta ce bari ta tuka tuwo.
Su Amina sai bayan mangriba suka dawo gidan daga can bolara gidan kakaninsu Mu'azzam bai je ba sai su kaɗai suka je su ka kwana biyu suka dawo. Da suna nan Amina ce babba ita za ta yi mata komai kafin ta dawo, tunda daman ita take bari a gidan in ba ta nan saboda ita Amina ta gama sakandiri ba kudin da za ta cigaba da makarantar.
Duk faɗan da aka yi ma Mansoor bai amsa ko ɗaya ba kansa na kasa yana sakin huci har aka kira sallar isha'i baba Ɗanjuma ya kara saka su suka yi alwala suka koma masallaci. A na idarwa ya taso zuwa gida suna zuwa kofar ɗakin Magajiya suka ga Auwalu na zaune na cin tuwo ya yi butu butu da kayan jikinsa tunda akwai hasken aci bal bal din da Magajiya ta kunna.
Baba Ɗanjuma ya kalle sa kafin ya ce"kai Auwalu yau ina ka je ban gan ka ba.?
Auwalu na sosa kai ya ce"Mun je aiki ne Baba." Kafin Baba Ɗanjuma ya yi mgana Magajiya ta tare shi da cewa"Ina ruwan ka da in da ya je tunda baka damu da shi ba, ai kana da makwafinsa Meri ta kawo maka Agola sannan Habiba ta mutu ta bar maka ɗan so duk duniya ba ka ganin kowa a gabanka sai yara nan guda biyu, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta."
Mansoor na ganin haka shi baya juran ganin magajiya ma yi ma Baba tijara ya sa ya tasa Mu'azzam gaba suka shige bangarensu.
Suka bar Baba Ɗanjuma na faɗin "Ki ji tsoron Allah magajiya kin ɗaure ma yaron nan kugu ya ki karatu na bokon tun tuni ya daina zuwa haka na arabin ma, shi zai yi takaici nan gaba ni dai Allah na gani na fita hakkinsa kuma maganar Baban Inna da kike yi ni fa na karɓo shi amana wajen danginsa ba wai domin sun gaza wajen rike shi ba, sai domin ina so na samu ladan rikon maraya. Kuma ni ba na tuna bambamci tsakanin ya'yana duka ɗaya suke a wajena ruwan ki ne, ki saka tunanin haka a ranki ko ki saka ina nuna bambamci Ubangiji na sama na kallon komai."
Da haka ya juya ya wuce ya barta tana faɗin"In da ka biya mishi kuɗin makarantar me zai hana shi zuwa? Ai ƴaƴan so dai su je su yi karatun mu ga sun zama shuwagabannin ƙasar nan.'
Inna Meri na kofar ɗakinta tana kwashe tuwo sai da ta yi dariya.
Duka ƴaƴan ta makarantar Gwammati suke yi. Su Amina kuma dangin mahaifiyarsu su ke tallafe sda manyan bukatunsu, ita dai ta na ɗauke mu su kananun da ba'a rasa ba da aikin da take yi a gidan Hajiya Fatima Dabo da shi take taimakon kanta da mijinta da ya'yanta amman sai Magajiya da sauran matan gidan su ke ganin kamar a kan ta da Ƴaƴan ta Mallan Ɗanjuma ya tare ita da ɗanta Mansoor da mutuwa ta yi sanadiyar auranta da Danjuma da ko a mafarki ba ta taba tunanin haka ba.
Babu amfanin zama ka yi ma wanda ba zai Fahimce ka bayani ba, tunda aka auro ta tazo garin nan tasan magajiya fitinanniya ce, kuma ba ta da kirki in da tana da kirki ai ba sai an aurota ba za ta iya riƙe ƴaƴan mijinta gam a hannunta ba tare da sai ita an aurota saboda ta zo ta riƙe ƴaƴan matarsa Habiba da Allah ya yi mata rasuwa ba.
Ta rasu ta bar ƙaramin yaro ɗan shekaru uku da wani abu duniya.
"Mu'azzam.."
*Janafty*