6
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 6```
________Cikin ɗauriya ta danne Kukan daya taho ma ta har sai data dangana ga daki tayi ma'ishin ta.
Sun ƙara hannun awarar da ribar daya ɗan taru wanda hakan baƙaramin sosa ran Inna Huwaila ya yi ba.
Ranar da suka ƙara hannun bata samu siyarwa da wuri ba tun rana har yamma, Zaman jiran su ƙara samun sadakar yamma yasa taƙi tafiya gida ko zasu ƙara siya.
Motoci ne na alfarma duk bayan minti-minti suke ta giftawa wasu su tsaya su bawa mabaratan sadaka wa su kuma wucewar su sukeyi da gudu kamar zasu tashi sama,baki sake take bin duk motar data giftata da kallo.
Tsayawar motar da ko ita da ta ke cikin talauci tasan maitsadane ya jawo hankalin dukka mabaratan da ita kanta,cikin burgewa da burin son itama ta yi kuɗi ta siyawa Innarta da Babangida take kallon motar.
A hankali ya zuge gilashin cikin papa da ƙaryar da ya ɗorawa rayuwarshi.
Bala maƙocin su Halime shine driver mai yiwa mutanen gidan cefane, ya dade yanason Halime duk da nakasunta ,yafito ta ya yi da hannunshi. cikin rawar jiki ta nufeshi zurzutun kuɗi har Naira dubu biyar ya bata ya kuma Umarceta da tayiwa baratan sadakar ragowar awarar.
Bakin Halime da jikinta duk rawa suka fara yi hatta hannun da take zuba mu su awarar rawa yake yi tsabar ruɗewa da farin cikin daya mamaye ruhinta.
Albishir ɗin samun kyautar dubu biyar ɗin ta sam bai yiwa Innarta daɗi ba sai take ganin kamar wani ne yakeson lalata mata Halime"Banda kinyi siyayyar gobe da bazaki ƙara fita ba amma daga gobe shikenan sai ki haƙura tun da ansamu abinda akeso"Inna ta faɗa da iya gaskiyarta.
Bata da bakin yiwa Inna musu domin ita kanta kuɗin da Bala ya bata ya sanya shakkun manufarsa aranta duk da ƙarancin shekarunta.
★Inna na suyar awara suna hira batare da sun kula Inna Huwaila dake sakin habaicinta lokaci zuwa lokaci ba.
"Inna maiyasa ma su kuɗi basayin taimako,inaso na yi ilimi mai zurfi na zama kamar ƴaƴan gidan Alhaji can layin, na siya mana mota na dinga tuƙaƙi muna yawo"
"Waye kuma Alhajin can layin ina kika san shi?" Inna ta tambayeta tana dakatawa da suyar awarar da takeyi.
"Ta yaya zakisan gidan Alhajin da take nufi, tun da baki ɗorawa kanki maula da ƙwaɗayi ba,ita ai makwaɗaiciya ce dole tasan gidan ma su kuɗi marowata da kuma ma su kyauta" Inna Huwaila ta tsomo mu su baki cikin hassadar ɗan cinikin da suke yi da bai taka kara ya karya ba.
"A'a Inna ba ƙwaɗayi bane naga motoci dayawa sunata shiga gidan,shiyasa nake mamaki, gamu talakawa kewaye da su ko kuɗin karatu ba mu dashi amma sun kasa taimaka mana" ta faɗa da zallar ƙuruciya a muryarta.
Duk da Inna Huwaila tasan gaskiya ta faɗa sai tai mirsisi ta cigaba da kusheta.ita dai Inna bata tanka mu su ba.
ƘADDARA TA RIGA FATA
Cikin mamaki take kallon dogon layin da ke shifɗe da titi ashare tsaf amma yau babu ma su baran ko mutum ɗaya. sojoji ta gani sunata zarya a layin, cikin mamaki da ɗan tsoro ta fara ƙoƙarin fitowa daga layin ta na waiwayen su gudun kar su hango ta....✍🏻