MAI KWAÆŠAYI

7

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 7```


________Babu zato babu tsammani convoy É—in Motocin suka danno cikin layin garin guduwa kar su bugeta ta yi tuntuÉ“e ta faÉ—i kan cikinta dogayen Æ™waurinta motoci biyun suka bi da tayoyin biyun gefe É—aya kafin na ukun ya ci burki da Æ™arfi.


Burkin da driver ya taka da ƙarfi da kuma Ihunta ne ya sashi ƙara lumshe idanuwanshi sai dai bai motsa ba.


Bala ne drivern motar farko, cikin rawar jiki da fargaba dukkan su suka fito.

Sai mutum biyu da sukayi zamansu kamar ba su san maiyake faruwaba jin har tsahon minti biyar suna maimata abu É—aya ya sashi fitowa a hassale,farine sosai kallo É—aya zakayiwa fuskarshi kasan masifaffene yanda yake hura siririn hancin shi.

"Menene haka kuke ɓata mana lokaci"ya faɗa dai-dai lokacin dayake ƙarasowa wajen.

Allah Sarki botikin awarar Halime na gefe awarar ciki ya tarwatse gata asheme bata numfashi alamun ƙasusuwan ƙafafuwanta duk sun karairaye.

"Yarinya mitsila irin wannan tana fita talla,ku jata gefe dalla, kunemo iyayenta,wama ya bata izinin zuwa nan yin stupid talla haka, Samuel!" Ya ƙwalawa ɗaya daga cikin sojojin kira cikin hargagi.

Babu wanda baiga rashin Imanin FAISAL ba sai dai babu wanda ya isa ya tanka indai ba Oga kwata-kwata ne da kanshi ba.


Babu abinda kunnuwanshi ba su jiyo ba daga hargagin da Faisal É—in yake yi cikin buÉ—ewar murya kamar mai faÉ—a da wani.

A hankali ya buÉ—e idanuwanshi sai dai bai buÉ—e su dakyau ba.

Cikin zarra da fuskarshi dake tsamke ya fara ƙoƙarin saukowa,dasauri drivern da dama can bai fita ba saboda gudun yin laifi ya zagayo ya buɗemai.

Dogo ne sosai duk da ƙarancin shekarun shi da basu haura ashirin ba sai dai a ido kamar ya haura hakan, kalar fatarshi ba mai haske bane sosai amma tsananin hutun daya huda fatar sai ya tashi kamar light Brown colour.sanye cikin Saint Laurent navy blue sai Tod's ɗin daya haska ƙafafuwanshi ƙamshin Creed Eventus ɗin shi ne ya sanya Faisal juyawa ranshi na ƙara ɓaci,saboda gudun fushin shi.

Kowa matsawa yafarayi su na ba shi hanya, cikin takunshin dake cike da mazantaka ya ƙarasa inda suka janyeta bisa Umarnin Faisal.

A kan gwiwoyinshi ya ɗurkusa yana kallon fuskarta da ɗaya idonta dake manne yanajin tausayinta na kamashi duk da abune mai wahala gareshi jin tausayin mutane, idanuwanshi suka sauka kan ƙafafuwanta da suka suntuma kamar accident ɗin ya daɗe da faruwa.

Cikin muryarshi mai amo dake ƙarawa mutane tsoronshi duk da ƙarancin shekarun shi yake tambayar daga ina take.

Cikin rawar jiki da É—an tsoronshi domin bai taÉ“a ganin shi ba sai ranar, Bala ya amsa ya san gidan su.

Bai ƙara cewa komai ba sai idanuwanshi da suka sauya Lokacin daya tabbatar Halime talla takeyi saboda botikin awarar daya gani yashe a gefe.


Mota ya koma, cikin hanzari drivernshi da dama bai biyo bayanshi ba gudun laifi yaja motar da mugun gudu suka bar wajen zuwa ainihin cikin gidan.


Cikin tsananin jin haushi Faisal ya É—auke Bala da mari saboda bai so yanuna ya santa ba.

"Ku kullum makwaÉ—aita ne burinka ya cika zai baku kuÉ—i kaji daÉ—i" yana faÉ—a ya shigewa Mota kamar zai tashi sama, drivernshi gudun kar ya yi laifi ya shiga Motar da gudu yajashi suka bar wajen.


Yana ƙoƙarin ɗaukar Halime sai ga masu aikin gidan mata.

Da farko bai gane mai hakan yake nufi ba sai da yaji umarnin Oga ne.

Kai tsaye Asibiti suka wuce da ita.


Lokacin da Baba Shehu ya ke sanar da Innar Halime saƙon Bala shima cikin tashin hankali, bata motsaba sai take jin kamar ji ne batayi dai-dai ba.dagaske Halime ta rasa ƙafafuwata wacce irin ƙaddara ce wannan,

"Saude kinyi shiru ki tashi mutafi Asibitin ga Bala can najiran mu" Baba ya ƙara faɗa cikin jimami....


Lokacin da tayi tozali da ƙafafuwan Halime a nannaɗe alamun duk an yanke kuka tasa mai ƙarfi ta na zubewa awajen...


Muna tare?