BA ITA BA CE

Page 13

by @nanameera08

*BA ITA BA CE!..💖💖*



*Nanameera ce ✍️*



*MIKIYA WRITERS ASSO...*



```Page 13```


# *DESTINY*


"Keeeee!" a ɗan firgice Muhaira ta kalleshi sai kuma ta turo baki tana cigaba da kallonta kwafa ya yi sannan ya ce"ubanwa ya ce kije ki cinyen abinci ko ke kika siyamin? nabaki permission ne?" kallonsa tayi da manyan idanunta sai kuma ta zumɓura baki tana wasada fingers ɗinta a tsawace ya ce"ba dake nake magana ba!" sosai ta razana sai kuma ta fashe da kuka tana murza idanunta sakar baki ya yi yana kallon ikon Allah tsakanin shi da ita kowane ya dace ya yi kuka??, ƙarasowa ya yi cikin takunsa na isa ya zauna kujerar da take fuskarsa babu alamun rahama ya ce"tell me meyasa kika cinyemin abinci?" cikin shashshekar kuka ta ce"koba yunwa nake jiba shiyasa naci amma kana yimin faɗa to zan biyaka" wani kallo ya yi mata sai kuma ya ce"da gaske?" gyaɗa masa kai ta yi tana murza idanunta. Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce"shikenan biyani abincina tunda bake kika siyamin ba" kallonsa ta yi da idanunta wanda ruwa ya kwanta akai ta ce"to zan dafa maka wani" gyaɗa kansa ya yi ya ce"hurry up" sannan ya tashi ya fita, tura bakinta tayi wanda sukai jajur dasu sannan ta miƙe kamar wacce aka yiwa dole tayi waje kai tsaye kitchen ta nufa tsayawa tayi tana tunanin abinda zata dama masa sai kuma ta yanke shawarar tayi masa shinkafa tunda ita ta cinye masa dakyar ta iya kunna gas ɗin dan gaba ɗaya ta tsorata dashi, cikin sanyin take yin aikin dan lokaci ɗaya jikinta ya fara yi mata ciwo amma kuma tsoron faɗan da zai yi mata yasa ta daure ta cigaba above 2hrs kafin ta kammala dafa shinkafar da bata shige 1cup ba ko kaɗan batada saurin aiki kuma hakan ya samo asali ne dalilin ciwonta zuwa lokacin idanunta sun kumbura sosai gabaɗaya jikinta rawa yake da sauri ta kwashe a plate sannan ta fito parlon.



Zaune ta sameshi yana danna system ɗinsa yanda ya bada attention ɗinsa zaka gane abu yake gabatarwa mai muhimmanci a gaban table ɗinsa ta ajiye masa plate cikin sanyin murya ta ce"gashinan na biyaka" kusan 5mins sannan ya kalleta ya kuma kalli plate ɗin ya ce"ni abokin wasanki ne?" sunkuyar da kanta tayi ya ce"za ki ɗauke daga gabana ko saina ɓata miki rai shashasha kawai" da mamaki Muhaira ta kalleshi cikin rawar murya ta ce"amm.. amma kaine kace na biyaka kuma dakyar nadafa wlh" rufe system ɗin ya yi yana yi mata wani kallo ya ce"wai ke bakida tunani ne what are u thinking ni ne zanci abinda kika dafa kina ƙazama are you mad?" tuni hawaye suka fara ambaliya akan fuskar Muhaira cikin kuka ta ce"wl..wlh banyi ƙazanta ba kaci kaji"



"Tassssssssssss"


A matuƙar razane ta kalli plate ɗin abincin wanda ya fashe duk abincin ya tarwatse a parlon cikin tsananin ɓacin rai fuskarsa har wani jaa ta yi ya ce"get out of my side!!" da gudu Muhaira ta shige bedroom ɗinta tana kuka, faɗawa kan gadon tayi ta fashe da wani raunataccen kuka an daɗe ba'a ɓata mata rai irin na yau ba wani irin kuka ta dinga yi tana jan numfashi a hankali kuwa jikinta ya fara rawa sai kakkarwa sanyi take wani irin amai taji ya taso mata da gudu ta tashi ta shiga toilet tana zuwa ta fara yunƙurin amai madadin tayi aman wani abun sai wani guda gudan jini ya fara fitowa daga bakinta dafe kanta tayi sai kuma ta tafi luuuuu ta faɗi a ƙasa sumammiya.




Murmushi Taj ya yi ya ce"karka damu Sir nayi maka alƙawarin kawo maka yarinyar nan har gida kawai kabani 24hrs" numfasawa Dmash ya yi ya ce"nayarda dakai Taj sbd haka go on" sunkuyar da kansa ya yi alamar girmamawa sannan ya juya ya fita, furzar da numfashi Dmash ya yi ya ce"Zaki taka ta ƙare". Ƙarfe 8:20am ya fito daga bedroom ɗinsa sanye yake cikin wasu suit coffee colour ya tufke kansa da ribbon fari kunnensa ɗaya ɗauke da yarin diamond kallon parlon ya yi wanda yake tsaf dashi kamar ba wanda ya ɓata ba jiya sai wani irin ƙamshi mai daɗi ne ke tashi a parlon taɓe baki ya yi yana ƙarewa parlon kallo da mamaki ya kalli agogon hannunsa ganin lokaci yaja har haka gyara zaman Bluetooth ɗin kunnensa ya yi cikin wata murya ya ce"yarinyar nan ta fita school ne?" "No sir she didn't come out at all" gyaɗa kansa ya yi sannan ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga ƙarewa parlon ya yi ganin komai tsaf dashi kamar ba yarinyace a ciki ba taɓe baki ya yi sannan ya ƙarasa bedroom ɗin da mamaki yake kallon kan bed ɗin ganin babu kowa da alama ma ba'a kwanta akansa ba, kallon kofar toilet ɗin ya yi sai kuma ya ƙarasa ya yi knocking yana faɗin"keee! keee come out" shirun da yaji ne yasa ya murɗa handle ɗin without second thought kuma ya tura kansa cikin toilet ɗin. Cikin hanzari ya ƙarasa inda ya ganta kwance yana zuwa ya ɗagota da mamaki ya kalli wajen ganin gudan jini wanda ya daskare a wajen sosai hankalinsa ya tashi amma ko kaɗan babu hakan a kan fuskarsa da sauri ya ɗauketa yana miƙewa tsaye idanunsa ya sauka kan sink ɗin ganin duk daskararren jini yasa ya yi waje da sauri ya yi waje tun kafin ya ƙarasa driver ya buɗe masa motar yana shiga shima ya shiga kai tsaye kuma asibiti suka nufa, rungumeta ya yi sosai a jikinsa jin yanda jikinta ya yi sanyi klao da alama ta daɗe da sumewa dan duk jikin nata ya saki sosai kiran Taj ne ya shigo wayarsa gyara Bluetooth ɗin ya yi daga ɗaya ɓangaren Taj ya ce"Zaki kana gida?" girgiza kai ya yi ya ce"no" Taj ya ce"daman..." "Please Taj I'll call you back" da mamaki Taj ya kalli screen ɗin wayar sai kuma ya taɓe baki ya shige toilet, har suka ƙarasa asibitin bai ɗauke idanunsa daga kanta ba.




*Asokoro Villa*.


Murmushi Dad ya yi yana kallon Khalil ya ce"General ya amince da aurenka da Ma'eesha sbd haka yanada kyau ka fara shiri dan ba wani lokaci za'a ɗauka ba" murmushi ya yi ya ce"wowww Dad thank you I really appreciate naji daɗi sosai" girgiza kansa ya yi dan ba tun yau ba yasan irin son da Khalil yakewa Ma'eesha ko sanda zai bar ƙasar saida ya zubar da hawaye sbd zai rabu da ita gashi cikin ikon Allah kuma zai aureta bayan wasu shekaru, da sauri Mommy tabar wajen ta shige bedroom ɗinta zaune ta samu Ramlah tana kallo a TV tsaki ta yi sannan ta ce"keee maza-maza tashi zamuje wani waje" da mamaki Ramlah ta ce"Mommy ina zamu je da yammacin nan?" tsaki Mommy tayi tana yafa veil ɗinta ta ce"idan bazaki tawo ba ki zauna kina tambayata shashasha kawai" tana faɗin hakan tayi waje, buga ƙafarta tayi aƙasa sannan ta miƙe tabi bayan Mommy tana sauke veil ɗin dake kanta kasancewar Abaya ce ajikinta. Convey ɗin da sukaji yasa Dad ya ce"ina kuma ta sake fita da yammacin nan?" taɓe baki Khalil ya yi ya ce"Maybe ko wani abunne ya taso mata urgent, nima zuwa anjima nakeson mu tafi gida" girgiza kai Dad ya yi ya ce"but kafara tsayawa ta ƙara samun sauƙi sbd kaga can idan ka koma babu mai kulawa da ita" gyaɗa masa kai ya yi sannan ya miƙe tsaye ya ce"zan je asibiti" ohk Dad ya ce sannan ya juya ya fita.




Shiru General ya yi yana saurarenta har ta kammala maganar sannan ya ce"then me kikeso nayi akai?" murmushi Mommy tayi ta ce"A'a kawai daman naga ya kamata ace na sanar maka ne shiyasa" bai ce mata komai ba ya cigaba da sipping coffee ɗinsa, sakkowa tayi daga saman tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya murmushi Mommy tayi ta ce"Shalele an tashi" shiru Ma'eesha tayi mata tana zuwa ta zauna gefen General ta ɗora kanta a cinyarsa shafa kanta ya yi sannan ya ce"Shalelena meya faru?" shiru tayi masa hakan yasa ya leƙa fuskarta ƙuri tayi masa da idanu ya sake cewa"ƴar gidan Father tell me kedawa?" ganin tayi banza yasa Mami ta kalleta cikin ɓacin rai ta ce"ke bakijin ana yi miki magana ne kikayi shiru Ma'eesha ki kiyayeni fa!" ko kallonta Ma'eesha bata yi ba hakan yasa General ya sake kallonta idanunta a buɗe suke balle ace bacci take ɗago kanta ya yi ya ce"ƴar Baba meyasa kika yi shiru" a hankali ta ɗora hannayenta bisa fuskarsa ta shiga shafawa sai kuma tayi murmushi da tsananin mamaki duk suke kallonta General ya ce"faɗa min mene ke yi miki ciwo?" bakinsa tabi da kallo sai kuma ta girgiza masa kai miƙewa tsaye ya yi yana riƙe da hannunta ya ce"Ma'eesha bazaki magana ba?, ni abokin wasanki ne? Ma'eesha I'm ur mate da nake miki magana nd u remain silence?" da kallo kawai Ma'eesha ta bishi sai kuma ta faɗa jikinsa tana sakin wani kuka mai sauti" da sauri General ya kalleta sai kuma ya durƙusa yana kallon kyakkyawar fuskanta ya ce"Ma'eesha baki jin abinda nake faɗa miki ne ko kunnenki na yi miki ciwo ne?" bakinsa ta ƙalla sai kuma ta girgiza masa kanta da hannu ta nuna masa bakinta sai kuma ta nuna masa kunnenta da sauri Mami tace"Ma'eesha baki jin abinda muke faɗa, tell us Ma'eesha" ta faɗa tana jijjigata fashe tayi da kuka tana rungume Mami, cikin tashin hankali Mami ta ɗago fuskarta ta ce"Ma'eesha kinji abinda na faɗa?" kallon bakinta tayi sai kuma ta girgiza mata kai tana goge mata hawayen dake zuba a fuskarta. Cikin kuka Mami ta ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun Ma'eesha wane yayi miki haka?, Wa ya kurumtaki?, me kika yiwa wani? Inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun mun shiga uku" da sauri Mommy ta rufe mata baki tana kuka itama ta girgiza mata kai ta ce"ki daina cewa an shiga uku zaki ƙara wata masifar kawai muyi mata addu'a koma wane ya yi mata wannan abun Allah ya saka mata kuma ya bi mata haƙƙinta" fashewa Mami ta yi da kuka tana dafe kanta ta ce" me tayiwa wani?, yarinyar da bata shiga harkar kowa babu ruwanta da mutane wane mara imanin ne ya cuci rayuwarmu" ta ƙarashe maganar tana sakin wani kuka mai gunji. Miƙewa General ya yi wanda idanunta suka kaɗa sukayi wani irin jaaa waje ya yi ko gabansa baya gani sake tashi Mami tayi ta koma inda Ma'eesha take zaune tana kuka ta kama hannunta ta ce"Ma'eesha kinyi faɗa da wani ne ko akwai wanda ya ce zai yi miki wani abu?" girgiza mata kai Ma'eesha ta yi takama hannun Mami tana ɗorawa akan bakinta ta girgiza mata kai rungumeta Mami tayi tana sake fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya ita kaɗai ce ƴar data mallaka kuma take burin taga tayi aure kodan su samu ƙarin zuri'a tunda su basuda yawa sai gashi an samu wani mara imanin ya kurmantata dan babu shakka wannan abun ture akai mata ko jifa. Shigowa Farooq ya yi da mamaki yake kallonsu duka dan shi tunda sassafe ya fita ƙarasawa ya yi ganin yanda suke kuka kamar waɗanda aka yi mutuwa ya kalli Mommy ya ce"Mommy what happened?" kasa bashi amsa Mommy tayi saboda kuka da yaci ƙarfinta hakan ya sa ya ce"Mami dan Allah ku sanar dani abinda yake faruwa" kallonsa Mami tayi da idanunta wanda suka yi wani irin jaa ta ce cikin kuka"Farooq sun kurmantata sun cucemu Ma'eesha bata jin abinda muke cewa kuma bata magana" cikin tsananin tashin hankali ya ce"what!!!?" ƙarasowa gaban Ma'eesha ya yi ya kama hannunta ya riƙe cikin nasa cikin wata iriyar murya mai nuna zallar tashin hankali ya ce"Shalelen Father ki cemin ba haka bane abinda Mami tafaɗa ki yimin magana dan Allah Ma'eesha kice wani abu ko naji sanyi a raina nasan halinki da wasa dan Allah Ma'eesha stop joking tell me the truth kar zuciyata ta buga kiyimin magana naji muryarki kinji shalelen ƙanwata" da idanu kawai Ma'eesha ke binsa da kallo dan yawan maganar da ya yi mata yasa ta gaza fahimtar koda magana ɗaya abu ɗaya kawai tasani shine yana magana ne akan abinda ya sameta hakan yasa ta nuna masa bakinta da kunnenta sannan ta girgiza masa kai. Durƙushewa Farooq ya yi kamar ƙaramin yaro ya shiga rera kuka wanda ya daɗe bai yi irinsa cikin rayuwarsa ba kuka ne wanda yake fitowa tundaga zuciyarsa yana matuƙar son Ma'eesha bashida burin daya shige ganin farin cikinta koda yakeson ya rabata da iyayenta yana yine sbd hakan ya kasance ƙudirinsa amma bazai taɓa mance Alkhairin Ma'eesha a gareshi ba bazai manta irin so da ƙaunar da take nuna masa ba tabbas duk wanda ya yi mata wannan aika-aikar to ɓa ƙaramin maƙiyinta bane. General ne ya shigo cikin sauri gabaɗaya ya fice hayyacinsa wasu doctors ne guda biyar suka shigo sai Farooq da His Excellency Muhammad Tanka da sauri Khalil ya ƙarasawa wajenta ya kama hannayenta cikin sanyin murya mai nuna rauni ya ce"


_Ƙaddara a bace wacce bawa baya iya tsallaketa kowa da kalar tasa ƙaddarar kuma kowa da akwai silar tasa ƙaddarar ba'a iya guje mata domin ita ta kasance rubutacciyar aba ce tamkar zanen dutse haka take duk yanda zakayi bazaka iya gogeta ba no matter who are you or what you have nobody can change his/her destiny either good or bad ya rabbi ka bamu ikon cinye duk wata jarrabawar da zaka yi mana😭🤲🤲_.



# *Love*

# *Destiny*

# *Manifestation*

# *SQUAD 2024*

# *Nanameera ce ✍️*.