Chapter 3
*BAYAN SHEKARU BIYU!*.
"Anty Mommy, don Allah, don Annabi, ki taimaka mana!. Yau tun da safe aka ce za'a kore mu daga asibiti idan bamu biya kuɗin magani da na gado ba, bamu da yadda zamu yi. Ki rufa mana asiri don Girman Allah!!".
Ameenatu a rikice take, yadda ta baro jikin Yayarta Murjanatu, a gadon asibiti a kwance, kamar ba zata rayu ba, ya matuƙar gigitata. Wataƙila dalilin daya sanya kenan ta tsinci kanta duƙe, a gaban wadda taci alwashin ko zata mutu, ba zata taɓa roƙar wani abu a wajenta ba. Ko kuwa tsabar ƙagauta ne da neman mataimaki da rashin sanin abin yi?.
Hajiya Uwani da take hakimce akan wata kujera ta alfarma, a cikin haɗaɗɗen falonta wanda yafi kama da na wata hamshaƙiyar matar gwamna, ko ma ta shugaban ƙasa. Kodayake, a halin da ake ciki mijinta neman kujerar sanata yake yi, don haka babu mamaki idan aka haɗa gidan dana hamshaƙan mutane.
Duk da halin da take ciki, hakan bai hanata jinjina kai cikin tu'ajjibi ba. Gidan ya canza matuƙa daga yanda ta sani, a ƙarshen zuwan da tayi, haɗuwa da faɗin gidan bata kai haka ba, duk kuwa da cewa ko a wancan lokacin samun haɗuwa da tsaruwar gida irin wannan abu ne mai wahala. Balle a yanzu. Shekaru uku kenan rabon data taka ƙafarta cikin gidan, sai kuwa wannan satin daya kama. Shekaru uku kwanaki ne masu yawa. Abubuwa canzawa suke yi. Mutane canzawa suke yi. Haka zalika gidaje da garuruwa ke canzawa.
Murya cike da ƙasaita tace, "me kuma ake buƙata ne yanzu? Ba jiya muka je aka biya kuɗin maganin ba?".
Ta girgiza kai a hankali, murya a can ƙasa, cike da saddakarwa, tace "waɗannan ai kuɗin waɗancan magungunan aka biya dasu. Kuma za'a mata awon ciki, sannan...".
Bata kai ga ƙarasawa ba ta katseta, "to naji. Anjima zan zo asibitin in gani".
Tace "amma Anty Mommy...!".
Zuwa yanzu ƴar fara'ar da take ƙaƙalowa ta yaƙe ta kau daga kan fuskarta. Cikin alamun faɗa-faɗa da nuna gajiyawa tace, "wai ba na faɗa miki kije zan zo bane? Haba don Allah don Annabi! Wai da wanne ake so mutum yaji ne a wannan duniyar? Da hidimar iyalinshi ko ta wasu? Nace zan zo, tunda na faɗi haka da bakina ba sai a kyaleni ba kuma? Haba!".
Jikinta ya riga ya gama bata babu alamun cin nasara a nan, hankalinta ya kasu kashi-kashi, tunanin yadda zata yi. Cikin ɗaukewar hankali ta gyaɗa kai, babu amfanin ci gaba da magiya da roƙo a kunnen da basu shiga.
Tace "to Anty Mommy, mun gode, Allah ya ƙara girma".
Bata kara cewa komi ba, ta kakkaɓe zaninta ta tashi.
Wani irin dumm! take ji a cikin kanta, wata irin amsa kuwwa mai ɗimauta mutum. Damuwa ce, tunani ne, fargaba ce, tsoro ne, babu kalar abinda bata ji a lokacin.
A cikin wannan halin ta fita daga babban falon nasu inda ta wuce ta garejin motoci wajen da suke ajiye motocinsu. A ƙalla motoci sun kai guda biyar, manya na alfarma, ajiye a wajen, wasu ma a cikin tamfal alamun an jima ba'a taɓa su ba. Sai dai hankalinta ko kaɗan baya kan su, gabaɗaya hankalinta yana kan Yayarta dake kwance akan gadon asibiti. Tunanin yadda zata yi ta ceto ta daga agar mutuwa take yi.
Sati biyu kenan da aka kwantar da ita a gadon asibiti. Matsananciyar cutar gyambon ciki (chronic ulcer) ne ya kwantar da ita. Daga farko asibitin gwamnati aka kaita. Bayan sunyi iyakar bakin ƙoƙarinsu, suka faɗa musu abin yafi ƙarfinsu, suka haɗa su da wani likita a asibitin kuɗi, suka koma can. Abin ya ɗan lafa, sai dai tsananin tsadar magunguna da gado, abin yafi ƙarfinsu. Tun suna kame-kame da sayar da ɗan abinda ya rage musu, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci komi ya tafi. Ƴar sana'ar da take yi, ta haɗe kan jarin gabaɗaya ana sayen magunguna, suma suka tafi.
Waɗanda suke tunanin zasu taimaka musu kuma, sun ƙi kawo musu agajin daya kamata.
Anty Uwani itace mafi kusa dasu, sai da Ameenatu tayi zarya gidanta ya kai sau huɗu, sannan taga dama ta leƙa su. A tsaitsaye ta duba mai jiki, wadda tun da garin Allah ya waye bata sha magungunanta ba saboda sun ƙare, kuma babu kuɗin saye. A ranar Baba Habu, har sai daya sayar da wayar hannunshi, to ba wani kuɗin azo a gani tayi ba, sai abubuwan buƙata da suka ƙare kawai aka saya. Kuma maganar magungunan kusan dubu shida da ɗari takwas ake yi. Shine fa ta bada dubu bakwai. Aka sayi magungunan da su.
To kuma sai gasu suna maganar suna buƙatar a sake yi mata awon ciki, saboda suna so su tabbatar da kalar cutar, daga nan kuma a mata tiyata. Ga kuɗin gado don sunce tana buƙatar ta zauna a asibiti saboda zata iya buƙatar kulawar likita a kowane lokaci.
Da waɗannan abubuwa da ma wasu, Ameenatu bata san yadda zata yi ba. Abu ɗaya ta sani, shine cewa she can't afford to lose her sister, she just can't!.
Duk da cewa ba tare suka taso da ita ba, amma akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu. Wadda ko cikin ƴan'uwan da suka tashi tare, a waje ɗaya, ba lallai a sameta ba.
Bata san lokacin da ƙofar gidan ta buɗe ba, duk da cewa idanunta suna kan ƙofar gidan, ta riga tayi nisa a cikin tunaninta. Tafiya kawai take yi. Bata san lokacin da wata farar Benz GLC63 S ta shigo, tayi fakin a ɗan nesa da ita ba. Bata kula da lokacin da ƙofofin motar suka buɗe, mutanen ciki suka fito ba.
Matashi Affan ya bita da kallo ta cikin baƙin gilashin idanunshi na Armani. Kallo ɗaya mutum zai yi mata, babu tambaya zai san cewa tana cikin halin ɗimuwa da rashin sani abin yi. She was lost!.
Ya kalli babbar Yayarsu Badi'ah, data fito daga mazaunin direba tana gyara zaman gyalen data yafa a kafaɗarta.
Cike da mamaki yace "ita fa wannan meke damunta haka?".
Ta kalli Ameenatu dake tafe, ta taɓe baki. "Me yake damunta kuwa daya wuce yawon maula da roƙo? Tafi sati tana mana zarya a gidan nan tana roƙon Mommy. Ta ƙi ta bar mutane haka nan su huta sai kace wata dangin mayu, mtsww!!". Ta ƙarasa faɗa tana jan tsaki.
Bai yi wata-wata ba ya sanya hannu a cikin aljihu, ya zaro damin kuɗi, naira ɗari biyar-biyar da suka tsaya suka canza a filin jirgi. Saukarshi kenan daga ƙasar Amurka inda yake karatunshi na likitanci.
Dai-dai lokacin data ƙaraso kusa dasu, dai-dai lokacin daya miƙa mata kuɗin. Dai-dai lokacin da Fauzah ta fito daga cikin motar, wayar samsung manne a kunnenta. Murfin motar ya ɗan bugi Affan, kuɗin hannunshi suka sulluɓe suka faɗi ƙasa. Akan ƙafafun Ameenatu.
A lokaci ɗaya suka kai kallonsu wajen.
Wani irin tsananin fushi da ɓacin rai suka ziyarci ran ta. Ashe mutum bai isa ya nemi wani taimako a wajen ɗan uwanshi ba tare da an mishi kallon mabaraci ba? Ashe yanzu babu wani taimako daga wajen mutanen da baku fito ta tsatso ɗaya dasu ba? Shin, neman taimakon data yi shi zai sa a mayar da ita maroƙiya, kuma mabaraciya? Har a dinga tafiyar da ita a matsayin ɗaya (mabaraciyar?).
A wannan lokacin, taji duk wani abu da zai fita daga garesu, ko meye shi, ta tsane shi. Dag wannan lokaci tasan cewa, ko duniyar sama zata dawo ƙasa, ko zata rasa duk wani abu nata, sai dai ta rasa. Amma ba zata taɓa neman taimako a wajen mutanen nan ba.
Zuciyarta ta kawo wuya, hawaye suka ciko mata idanu. Ba na baƙin ciki bane, ba kuma na takaicin ta kasa samun abinda take so bane. A'a! Na ɓacin rai ne. Na tsananin ɓacin ran mutanen dake gabanta ne. Mutanen da take ikirarin ƴan'uwanta ne, suka fito fili ƙarara suka nuna mata ba haka bane. Wani ɗan'uwa ne zai ɗauki kuɗi ya jefa maka a ƙafa, kamar a zamanin sayar da bayi??.
Yana shirin ɗaga baki yayi magana, ta ɗaga rinannun idanunta ta kalleshi. Bai san lokacin daya ɗan ja da baya ba. Bai taɓa ganinta a haka ba. A iyaka shekaru da dama da suka yi a tare. Duk iya rashin kirkin da suke shuka mata, bai taɓa ganinta a haka ba. Ganinta a wannan hali a karo na farko a cikin rayuwarshi, ya bashi mamaki. Tsananin tsanar daya hango a cikin idanunta a wannan lokaci, ta matukar faɗar mishi da gaba. Gani yake yi kamar wani maƙiyinta ne, wanda idan ta samu hali zata iya aikata abu mara kyau a gareshi.
Ya samu kanshi da in-ina, abinda bai taɓa yi ba a rayuwarshi, duk tsoron da yake ciki kuwa. Yace "g...ga kuɗi nan ki ɗauka... kuɗi kike bukata, right?".
Ta sauke kanta kan kuɗin a hankali, fuska cike da disgust da distaste, kafin ta maida kallonta kan shi. Murya cike da ban tsoro tace "damn you and your money Affan! Bana buƙatarsu!". Tabi ta kan kuɗin ta wuce su da sauri, kamar zata tashi sama.
Gabaɗayansu suka bita da kallo. Badi ce ta katse shirun da suka yi, ta taɓe baki.
"Sai ka kwaso kuɗinka mu tafi ko? Allah ma ya ƙara wallahi, gobe ma sai ka ƙara ai. Wai shi nan taimako, ai ga abinda ya janyo maka nan!". Ta shura takalminta ta wuce su.
A falo ta samu mahaifiyarsu tana jiransu, ta zauna gefenta tana bata labarin abinda ya wakana a waje, bayan ta ƙara magi da gishiri. Ran Hajiya Uwani ya ɓaci sosai.
Cikin masifa take faɗin, "kaji ja'irar yarinya, har tijara zata yiwa ƴaƴana, a gidana? Lallai kuwa zata gani da idanunta. Wato su fa mutanen nan gani suke yi kamar su wasu hamshaƙai ne, wato gani take yi wuyanta ya riƙa ko? In banda ma ƙaddara Allah na tuba, me zai yi haɗin kifi da kaska? Amma zata gani ne! Ki sharesu kawai, shegen baƙin ciki ne danƙare a zuciyar mutanen nan da kike ganinsu, kuma ta Allah ba tasu ba. Kun riga kun musu nisa wallahi, don haka ku daina kula su. Ina autata da yayanta ne?".
Daidai lokacin da suka shiga falon, Affan na gaba Fauzah na binshi a baya. Ta miƙe tsaye da saurinta, bakinnan kamar zai taɓo kunne saboda fara'ah tana musu oyoyo.
Bayan sun gama gaisawa, ta ja su zuwa wajen teburin da aka shirya shi da kalolin abinci iri-iri, abinci kamar za'a ciyar da tulin mutane ba cikin mutane huɗu ba kawai.