DUNIYA BIYU

Four

by @jeddahlawals

Tsakanin unguwar su Anty Uwani, G.R.A, da asibitin Fama-G, tafiya ce mai dankaren nisa. Haka Aminatun ta shanyeta a ƙafafunta.

Akan hanyar ne Allah ya tunatar da ita wata sarka da Anty Hadiza ta taɓa aiko mata wani lokaci can daya wuce, a cewar Hajja duk da cewar basu tabbatar ba, ta daham ce. Akwai filinsu da suka yi gado a wajen mahaifinsu ita da Murjanatu da yake a hannun Baba Rakiya. Ta tabbata idan aka sayar dasu, zasu biya kudin gado dasu, su biya na 1awo, magunguna, da komi ma har a sallamesu. Sai taji zuciyarta tayi mata wani irin fari na sosai. Ta hau tuhumar kanta akan dalilin da yasa ta kasa tunowa dasu sai a wannan lokacin. Da kuzarinta ta ƙarasa asibitin.


Sai dai da yake kaddara ta riga fata, kuma kowane rai zai dandana dacin mutuwa, sannan shi Allah baya barin wani don wani yaji dadi, tana shiga dakin da aka kwantar da Murjanatun tare da wasu majinyata guda hudu, ta tarar da duk danginta dake wajen zagaye da gadon Murjanatun. Nana, Hajja, Malam Habu, Isiya direban gidansu Hajja, har da Asabe makociyar su Nana.

Likita yaja zani ya rufo Murjanatu tun daga kafafunta har saman kanta bayan ya sanya hannu ya rufe mata idanu. Daga can tsakiyar kanta take jiyo ihun kukan da Hajja ta sanya, da salati da sallallami da Malam Habu da Nana suke yi.


Kafafunta suka mata wani irin nauyi, ba shiri ta zame a tsakiyar dakin. Kwalwarta ta kasa cigaba da gudanar da duk wani aiki da take yi, wasu irin zafafan hawaye da bata tunanin ko barkono aka bada mata a ido zata ji irin wannan zafin suka dinga mata zarya a fuska. Ameenatu bata san ina ta faro ba, bata san ina kanta ya tafi ba.


Babu abinda take tunawa sai murmushi mai cike da dauriya da Yayar tata ta mata a lokacin da ta mata sallama akan cewa zata sake zuwa tambayar musu wani taimako, da kalaman godiya da addu'o'i data dinga mata. Tasan cewa tana cikin azabar ciwo. Murmushin ma tasan na dauriya ne kawai, maganar ma tasan cewa daurewa kawai take yi, karfin hali take yi. A hankali taji idanunta na lumshewa, baki yana mamaye su, taji tana tafiya zata kifa a durkushen da take, jinta take yi kamar wadda take a cikin ruwa, bata ganin komi bata jin komi sai dishi-dishi. Cikin wannan hali ta jiyo ihun kiran sunanta da sautin kafafu suna gudu. Duk da haka sai da ta kai kasa cikin halin suma!.


⋆☆⋆☆⋆


_Bayan Sati Huɗu..._


Ta zuge zif din jakar Ghana must-go da take sanya kayanta a ciki, ta ciccibeta zuwa waje inda Hajja take zaune ita kadai tana tsintar wake.


Cikin mamaki ta daga kai tana kallonta, "ke kuma fa ina zuwa haka kika ciccibo kaya kamar wata yar ci rani?".

Ta saki murmushi a hankali, cike da sanyin jiki, Dutsinma zan wuce wajen Nana!".


Hajja ta kara daga baki cike da tu'ajjibi, "ba sai rana irin ta yau zaki koma wajen nata ba?". Ta girgiza kai kawai.


Hajja tace "to ni wannan abu kuma naki Aminatu na kasa gane shi, wani abu aka miki ne? Wani ya miki wani abu ne? Idan wani ne yake takura miki ba sai ki fito ki fada ba?".

Ameenatu bata san abinda zata fada mata ba bayan sake girgiza wani kan, kamar ba a gabanta su Fauzah suke mata cin fuskar da suke mata ba, kamar bata sane lokacin da suka mayar da ita baiwar su ta musamman, kamar ba a gaban idanunta suka maida mata rayuwa mai zafi da tsanani ba, amma duk ta kauda kai. Bata da niyar fitowa ta gaya mata duk wadannan, tunda ko tayi hakan ma babu wani amfani da zai yi mata. Bata yawun bakinta kawai zata yi.


Hajja ta sake cewa, "to yanzu ni ban san ya kike so inyi ba kuma, ita Huwaila din da zata zo sai ranar da aka yi zaki tafi sannan, yanzu wa zai dinga taya ni aikace-aikace da sauransu? Kin ma sanar da su Nana din?". (Huwaila jikar kanwar Hajja ce, Baba Rakiya, da zata taya ta zama bayan Ameenar tayi kaura zuwa wajen Nana).


Sai lokacin ta daga kanta, "ehh, na kira Baba Habu na fada mishi".

Hajja ta jefa mata harara, "duk yaushe kika yi hakan ban sani ba?".

Ta dan daga kafada, "dazu na karbi wayar Isiya na kira su".


Hajja ta kada kai, "to ai shikenan, idan kinje kice ina gaishe su, Allah ya kiyaye Ya kuma tsare. Kina da kudin motarki a hannu?".

Bata ce mata komi ba ta gyada kai kawai.

Ta ajiye farantin dake dauke da wake a kasa, ta mike tsaye tana yafa gyalenta, tace, "to ai sai muje in taka miki zuwa kofar gida. Jamilu baya nan ne? Da ya taya ki daukar kayan zuwan bakin titi".


Tace "ai kayan ba wasu masu nauyi ba ne, zan iya dauka".

Ta kara ciccibar kayan suka fita. A bakin gate suka dakata, ta sake yin sallama da Hajja, kafin Hajjar ta maida kofar ta rufe, ita kuma ta dauki hanya.


Ameenatu ta daga kai tana kallon kakkauran marufin gidan daya kasance ruwan ja mai cizawa da kwalliyar silver a jiki. Ranar da aka kawota gidan da niyar zama na din-din-din, har aurenta. Lokacin tana yar shekara biyar ne, rasuwar mahaifinta da shekara daya. Tana tunana irin kukan data sharba a ranar da aka kawota, da yadda tana kallo mahaifiyarta ta mata sallama akan washegari zata wuce kasar Sudan inda ta sake yin aure. Bata sake ganinta ba daga ranar sai dai ta waya idan ta kira.


Bata taba manta wannan rana, bayan tafiyar mahaifiyarta da yammaci, ta koma falo can bayan kujeru ta rakube tana shesshekar kuka yayin da mutanen gidan ke ta shige da ficensu. Hajja tayi lallashin duniya akan tayi shiru ta ki, daga baya taji haushi tayi watsi da lamarinta. Lokacin Alhaji da lafiyarsa kyam, shi yaje ya sameta da tarin kayan wasan Fauzah da kayan makulashe, ya zauna da ita anan. Tun tana kin kula hira da wasan da yake mata, har ta daina kukan. Daga karshe a hankali ya samu ya hillaceta ta ware ta fara wasanta, wanda ba'a jima ba Affan da Fauzah da aka yi arashi a ranar suma sun je gidan, suka je suka dauke kayan wasansu. Ranar a dakin Alhajin ta kwana gabadaya. Washegari su Affan da suka je gaida shi sai ganinta suka yi kwance luf akan gadonshi cikin bargo tana barci.


Tana tunanin daga wannan lokacin ne tsanar su a gareta ta fara. Hayaniyar korafinsu ce ta tasheta daga barcin da take yi. Suna tuhumar Alhajin akan dalilin da yasa ya barta ta hau kan gadonshi har ta kwana, bayan su ko da wasa baya bari su hau mishi gado. Maimakon ma ya amsa musu, sai fada daya hau musu akan cewa sun tashe ta daga barci, ya kuma kore su daga dakin. Suka fita wasu na guna-guni, wasu na jefa mata zazzafar harara.


Ta girgiza kai a hankali, dan siririn murmushi na bayyana akan lebbanta. Kodayake, idan tayi duba zuwa baya, tasan cewa wannan lamari kawai kara ruruta wutar kiyayyarta yayi a cikin ransu, amma dama can basu sonta, dama can basu kaunarta, dama can basu dauki rayuwarta a wata tsiya a wajensu ba.

A hankali ta juyawa gidan baya, gidan da tayi rayuwar yarintarta a cikinsa, gidan da ya nuna mata duk wata soyayya ta duniya da za'a nunawa wani mahaluki, a lokaci daya kuma ya nuna mata kiyayyar da take ganin ba'a taba nunawa wani mahaluki ba. Sai dai duk abinda ya faru a cikin gidan, mai kyau da marar kyau, tayi alwashin maida shi bayanta, ta manta dasu. Sabuwar rayuwa take so ta gina. Tasan cewa kuma idan bata manta da rayuwarta ta nan ba, hakan ba zai taba faruwa ba.


Ta daga kafafunta da suka yi mata nauyi, ta fara tafiya. Wani bangare na zuciyarta cike yake da jimami, jimami na bankwana ga rayuwar da ta saba da ita, mutanen da ta saba dasu, abubuwan da ta saba dayi, tasan cewa duk ta bar su. Waya sani ko bari ne na har abada?.

Ta dauki titi zuciyarta na fada tana maimaita abu daya, bankwana!.


Tana fita bakin titi ta samu acaba ta tare, suka yi ciniki ya kai ta tasha ta hau motar da zata kaita Dutsinma. Babu kowa ma a cikin motar sai da ta jira fasinja, hakan bai dameta ba, ta zauna har sai da motar ta cika sannan suka dauki hanya.


Saukarta Dutsinma a bakin titi, ta gangara zuwa gidan Nana da yake anan baki-bakin titi suke zaune. Tarba ta samu sosai daga Nana, cima kala-kala har ta rasa kalar wadda za ta ci. Da dare ma da Baba Habu ya dawo daga wajen sana'arshi, haka ya riko mata balangu da tsire ta ci abinta.


Ranar litinin aka kaita makarantar yanmata ta sakandire ta gwamnati dake nan Dutsinma din, kafin zuwanta dama tuni aka gama mata duk abinda ya kamata. Daddyn Abuja da kanshi ya mata duk abinda ya kamata. Aka sai mata littafai, jakar makaranta, ya dinka mata kayan makaranta har kala uku, ga takalman makarantarta kala biyu, na fata da na roba, duk wasu textbooks da zata bukata sai daya siya mata, babu abinda za tace da wannan bawan Allah sai Allah Ya saka da alkhairi kawai. Ta fara zuwa makaranta abinta cikin kwanciyar hankali. Ranar Assabar kuma aka kaita ta Islamiya, itama dai duk Daddyn Abujar ne yayi duk abinda ya dace.


Nan da nan ta warware, dama can tana da saurin sabo, babu ruwanta da wani pickiness, duk hali da kuma wajen da ta samu kanta a ciki, ta kan yi adopting ba tare da wata matsala ba.


Cikin sati daya kacal da tayi a Dutsinma, ta san cewa sai lokacin taje gida. Bata da wata damuwa ko matsala. Nana da Mijinta Malam Habu ba wasu masu kudi bane, rufin asiri ne kawai na Allah. Nana tana sana'ar kulle-kullen kayan masarufi, su sukari, barkono, su daddawa da sauransu. Shi kuwa Malam Habu tsohon ma'aikacin gwamnati ne da yayi ritaya. Yanzu dai baya aikin komi sai yan abubuwan da ba'a rasa ba, da yake yana samun kudin shi na fansho, to rayuwar Alhamdulillahi. Idan ba yanayin rayuwa bane ya zagayo ba, ba'a rasa ci da shan safe, rana da dare a gidan. To ko a babun ma dai, haka ake gangarawa cikin godiyar Allah da tawakkali. Ita rayuwar dama haka take ai, ga wanda kuma ya fahimceta sai yaga bata taba mishi wahala.


Ameenatu dai ta samu kwanciyar hankalin data jima bata samu kamarshi ba, hakan kadai ya isheta godewa Allahn daYa halicceta.

Da yake yarinya ce mai godiyar Allah, kawar da kai da tsananin biyayya. Zama da Nana bai mata wahala ba. Nanar ma da mijinta haka suke. Sai suka kasance kamar 'perfect family' data rasa a lokacin yarintarta.

Lokaci zuwa lokaci ta kan tuno Hajja, har su Badi da su Isiya, ta kan yi kewarsu. Tunda ta tafi dai Hajja bata je ta ganta ba, amma sukan yi waya su gaisa idan Malam Habu ya kira, ko kuma ita ta kira.