Seven
Cikin watan Afrilu (April) ake, wanda yayi saura satika da basu wuce uku ba a fara azumi. A lokacin aka yi musu hutun makaranta na karshen zangon karatu, wanda idan sun dawo zata shiga aji na uku. Kamar koyaushe, wannan karon ma ita ta jagoranci yan ajinsu kamar yadda ta saba a kowane lokaci. Ta kuma cinye jarabawar 'mock' da suka yi ta shiga aji uku. Daliba ce mai hazaka da hangen nesa kwarai, malamai da dalibai kowa yana yaba mata ta wannan fannin.
A kuma satin da zai kama ne za'a fara bikin Badi, wannan shekarar ta gama karantar 'chemistry' a jami'ar Umaru Musa Yar'adua anan cikin Katsina.
Zuwa Katsina ya kama ta a dolen-dole, ba don ta so ba. Zata iya cewa rabonta da zuwa Katsinar ta kwana zata iya daukar shekara guda cikakkiya. Duk kuwa da cewa babu yadda Hajja bata yi da ita ba, da duk wasu korafe-korafe da take yi mata akan cewa ta yar da ita, bata je mata ziyara, Nana ta janye mata ita, da dai sauransu. Duk tayi kunnen uwar shegu da ita. Wani zuwa da tayi Dutsin-ma na karshe -kimanin watanni biyu kenan- ta sanya Ameenatun tayi alkawari akan cewa zata je tayi mata azumi a can.
Bata san cewa zasu yi hutu kafin azumi ba, duk tunaninta, sai tsakiyar azumi sannan zasu gama jarabawa, ashe ba dai-dai tayi lissafinta ba. Gashi nan yanzu tana cikin ruwa tsamo-tsamo. Ta san cewa bata isa ta cewa Hajja ba zata je ba, idan ma tace ba zata je din ba, bata da wata hujja karbabbiya da zata gamsar dasu.
Shi yasa tun da ta dawo daga makaranta bayan an basu hutun, ta shige can kuryar dakin Nana ta kwanta akan gadonta na karfe, zuciyarta cike da sake-saken yadda zuwanta Katsina zai kasance. Koda ma ace taje can din, bai fi tayi kwana hudu zuwa biyar ba ta koma, mawuyaci ne tayi sati daya. A cikin wadannan lokutan, mawuyaci ne ta hadu da wani daga cikin danginsu. Tunda a cewar Hajja, duk sun dauke kafar zuwa, ko su Badi dinma ba kasafai suke zuwa ba. Ko sun ma je ba wani kwana suke yi ba.
Ameenatu bata san me ya kamata tayi ba da jin hakan, farin ciki ko kuwa akasin sa?!.
Tana nan a kwancen Nana ta shiga dakin, kasancewar akwai dan duhu a dakin, bata sani ko barci take yi ko idanunta biyu ba, ta dai ganta a kwance kawai.
Tace "Ameenatu ba zaki tashi ki fara shirin tafiya makaranta bane? Tun dazu kike nan a kwance fa, gashi ko abinci baki ci ba. Ko baki da lafiya ne dai?".
Ta mike zaune a hankali, tace "lafiyata lau Nana, bana jin yunwa ne. Halimatu ta kai mana gurasa makaranta muka ci gab da za'a tashi shi yasa. Ganin lokacin makaranta bai karasa bane shi yasa".
Nana tace "lokaci na nawa kuma? Karfe uku da rabi ce fa yanzu. Yanzun nan ma zaki ji an kira sallar la'asar".
Aikuwa kafin ma ta rufe baki, aka fara kiran Allah daga masallacin dake bayan gidansu.
Ameenatu ta zabura ta dira daga kan gadon tana zuba salati. Bata san cewa lokaci ya tafi har haka ba. Nana ta bi bayanta tana girgiza kai kawai.
A gurguje ta shirya, karfe hudu da kwata ake fara tarar yan makara a ajinsu. Gashi malaminsu baya ganin girmansu, zagewa yake tun karfinshi ya nada musu na jaki kamar wasu kananan yara.
Tana sallame sallah ta jiyo sallamar kawayenta biyu; Basariyya da Hauwa'u. Dukansu anan cikin unguwar suke, ajinsu kuma daya a duka islamiyya da boko. Yayin da Halimatu take a can saman layinsu, duk da cewa dai basu da nisa.
Dama ta riga ta sanya kayan makarantarta, jakarta mai dauke da littafai ta dauka kawai ta fita. Ta samesu a waje suna gaisawa da Nana. Kamar koyaushe, ta dauki naira ashirin ta bata su kuma ta damka musu goma-goma. Suna sadda kai da 'a'ah, mungode' da komi, suka karba suna godiya.
Suna fita ta daka musu duka a baya su duka, "munafukai, ana so ana kaiwa kasuwa!".
Hauwa'u tace "ke fa kin ji matsalarki, shikenan kullum sai mu zo mu amshewa yar tsohuwa yan canjinta don mu karya mata jari. Dama ana haka ne?".
Tace "to tunda ita ta dauka da kanta ta baku, ba sai ku amsa ba? Ni idan baku so, ku dinga karba kuna bani".
Hauwa'u ta kyalkyale da dariya, "uwar son banza kawai. Allah Ya shiryeki wallahi".
Basariyya da tunda suka fara zancen bata tanka musu ba, dama ba mai yawan surutu bace. Tace "ku dai zauna kuna ta mayar da zance har mu makara. Idan kuka ji zafin bulalar Malam Umar ai zaku shiga taitayinku".
Ameenatu ta dauki kafa da sauri kamar zata tashi sama tana fadin, "ke fa Basariyya wani lokacin mugun fata ne dake wallahi!".
Suka bita a baya su ma cikin saurin, suna dariya kasa-kasa.
Allah Ya taimakesu ba Malam Umar bane a cikin ajin a lokacin, Malam Hadi ne. Duk da makarar da suka yi, ya barsu sun shiga ajin bayan kashedi da yayi musu akan kada hakan ta sake faruwa.
Tunda suka zauna Hauwa'u take raba idanu a tsakanin Ameenatun da Malam Hadi. Da alamu tana ta so tayi mata magana akan wani abu, Allah bai bata dama ba. Sai da aka tashi, suka dauki hanyar komawa gida sannan ta samu ta fadi abinda yake cikin cikinta.
"Ni fa ko? Sai in ga kamar Malam Hadi fa son ki yake yi Meenah!".
Ameenatu ta kalleta baki a dage, kafin ta kwashe da dariya. Har da ba Basariyya hannu suka tafa.
Ta kama haba tace, "ke fa watarana kamar kan ki yana motsi ko kuma tunaninki ya toshe! Yanzu don Allah, don Annabi, ina Malam Hadi ina ni? Mutumin da ina tunanin tun kafin ma a san da zaman cikina a duniya yayi aurenshi na farko?!".
Hauwa'u tace, "wannan kuma kema kin san sharri ne kawai kike mishi, amma ba tsoho bane, idan abinda kike son fada kenan. Kuma Allah sai dai in ke ce wadda tunaninta ya toshe. Amma idan alamu ne kike nema, duk ba gasu nan a bayyane ba? Tun daga kallon da zaki ga yana yawan yi miki a aji, ga yawan kira. Motsi kadan zaki ji ya fara make murya yana, _Malama Ameenatu dan ji mana..!_...".
Ameenatu tayi saurin katseta da cewa, "amma kin san saboda karatun da muke yi ne ko? Kuma kin san ba ni kadai ba yake koyawa ba ko?".
Tace, "amma me yasa duk yawan yan ajinmu ke kadai ya zaba, ya saka cikin ajin da ake horar da malamai?".
Ta dan yatsina fuska, "to ni ina zan sani? Illa iyaka na ga damar da zan kara samun ilimi, kuma na shiga".
Hauwa'u da Basariyya suka hada baki a lokaci daya wajen daya, "saboda yana son ki mana!".
Ta girgiza kai tana murmushi, a ranta tana raya, matsalar mutanenmu kenan, babu hali d'a namiji ya d'an nuna burgewarshi ko kulawarshi ga wata ya mace, sai a kekashe kasa ace ai sonta yake yi. Shin babu kulawa ta yan uwantaka ko kuma ta Allah da Annabi ne sai wannan kawai?
Tace "sai ku yi tayi ai, kan ku kadai ake ji. Ni na yi gaba".
Suna ta maida zancen har suka isa kofar gidansu. Anan suka yi sallama dasu, su suka wuce nasu gidajen, ita kuma ta shige gida.
A soron gidan suka ci karo da Malam Habu shi kuma zai fita, ta rabe ta gefe ta bashi hanya don ya wuce tana jefa mishi sannu da gaisuwa. Ya amsa mata tare da tambayarta, "har kun taso daga makaranta?".
Tace "ehh!".
Ya gyada kai a nutse cike da gamsarwa, ya wuce. Ta bi bayanshi da addu'ar 'a dawo lafiya', tasan cewa masallaci ya nufa daga nan.
A cikin gida Nana tana gaban murhu tana kwashe tuwo da ta gama tukawa. Ta daga kai tana mai amsa sallamar da Ameenatun tayi, ta kara da, "ya aka yi yau kuka so makara ne?".
Ta cire hijabin jikinta tana mayar da linki da karin gugar dake jikin hijabin, su ma sauran kayan nata haka take musu, sai ta mayar dasu kasan shimfida ta ajiye Washegari sai dai ta ciro su da karin gugarsu a jikinsu kamar ta goge su, ta sanya.
Tace "kin san ai yau ranar laraba, ranar karshen makon karatunmu. Malam Balarabe yake wa'azi idan an tashi, shi yasa".
Nana tace "kwarai kuwa na manta. Ki cire kaya, kiyi sallah don na ji har an fara kira a wasu masallatan. Ki zo ki mika tuwo gidan Tasalla".
Ameenatu tayi murmushi a hankali, Nana mace ce mai kyauta kwarai, abin hannunta sam bai rufe mata idanu ba. A kullum ta Allah idan ta dora tukunyar abinci a cikin gidanta, to ba su kadai za su ci shi ba. Ta kan zuba a mikawa makota, watarana ta kira almajirai ta zuba musu. Watarana haka zata yi abincin wanda zai iya ciyar da mutane da dama, ta bada akai masallaci ko asibiti inda ake ciyar da gajiyayyu.
Shi yasa kullum ga ta nan dakau da ita, idan ka ganta ba zaka taba cewa shekarunta sun kai wadanda take kai yanzu ba. Ga ta mata ce ta mutane kwarai da gaske.
*
Bayan tayi sallah, ta kai abincin inda Tasalla din ta hadota da tarkacen su tsami gaye da tuwon madara wanda take yi na siyarwa -saboda ta ki karbar kudin da ta bata- zama ta yi ta ci tuwon da Nanar tayi. Babu nama balle kifi, amma dadin da tayi kai kace an sanya abubuwan ne. Ko ba laifi, Nana ta iya sarrafa abubuwa, kuma ta san hanyarta in dai a cikin kicin ne.
Ameenatun ma ta biyo bayanta. A yadda take dinnan yanzu, babu kalar abincin da bata iya girkawa ba, musamman na gargajiya. Tunda na zamanin kam ba duka suka cika yi ba a nan.
Kan tabarma da suka shimfida anan tsakar gida ta zauna, ta dauko littafan karatunta tana bitar karatun da za'a mata washegari ranar alhamis a makaranta.
Babbar tocilan ta kunna, suke amfani da ita ita da Nana wadda take yan daure-dauren kayan sana'arta kasancewar babu wuta. Har Malam Habu ya shigo gidan wajen karfe takwas.
Sannan ta hade kan kayanta ta koma daki. Tana ji Nana na tambayarta ba zata je gidan su Hauwa'u tayi kallo bane? Tunda su gidansu ana kunna inji da dare, tace mata a'ah, don ta gaji.
Kafin karfe goma ma ta karasa tuni tayi barci abinta.
*
Kafin karfe bakwai na ranar Alhamis tayi, tuni ta kammala share tsakar gidan tas. Ta hada itace a murhu ta dora ruwan koko. Yana tafasa ta hada kokon.
Sannan ta leka dakin Malam Habu ta gaida shi, ya bata kudin sukari, ta fita can wajen tiredar dake cikin unguwarsu ta siyo. Ta tsaya wajen Ma'u mai kosai ta sayi kosai da biredi, kafin ta koma gida.
Zuwa can hantsi yayi, tayi wanke-wanke da gyaran daki. Ta je ta siyo madarar ruwa mai kauri da mai wadda take yin iloka da ita.
Tana komawa gidan ta samu Nana tsaye tana gyara zaman gyale a kanta.
Tace mata, "fita za ki yi ne?".
Nana tace "asibiti zamu je ni da Fatsuma mu dubo diyar Alhaji Bala da aka yiwa tiyata".
Ta kada kai, "auho, mu da yake kin san can hanyar makarantar mu ne, tun a jiya ma muka je muka dubata. Ku kara dubata da jiki, na san ma zuwa gobe mu sake komawa. Sai kun dawo, Allah ya kiyaye".
Nana tace "ameen".
Ta sa kai ta fita bayan ta bar mata sakon abinda za ta dafa da rana, koda basu dawo da wuri ba. Ta amsa da to.
Tana sauke ilokar, ta dora tukunyar abincin rana kawai.
Bayan ta gama liliyata da kirgawa, ta dauko farin madaidaicin bokiti mai garai-garai wanda ta saba zubawa a ciki, ta juye.
Tana cikin aikin ne sai ga Hauwa'u da Basariyya sun shigo. Suka saka bokitin ilokar nan a gaba suna sha kamar sun samu abinci. Ta sauke abincin ta zuba a kula, su kuma ta zuba musu anan suka ci suna hira. Suna cin abincin su Nana suka dawo.
Ta tashi ta mata sannu da zuwa, ta karbi ledojin hannunta wanda tasan kayan sana'arta ne a ciki, ta ajiye su a gefe.
Kafin Nana din ta gama sallah, ta zuba mata abinci. Malam Habu sai can wajen la'asar yake dawowa.
Hauwa'u tace "dauko kibiya ki zo ki lallabe min kai don Allah".
Tace "ni dama nasan cewa wannan ziyarar ba ta Allah da Annabi bace, da walakin... Ashe abinda ya kawo ku kenan?".
Basariyya tace "wai ka ji abinda matar nan take fada, ke ba ma kece mai ziyarar ta kama ba? Wadda bata ziyara sai ta kama ko kuma an aiketa?".
Ta daga baki cikin mamaki, tace "la'ila! Sharrin da zaki min kenan? Saboda Allah duka-duka yaushe rabona da gidanku ne? Ko a shekaranjiya fa sai da naje".
Ta jefa mata harara, "da Nana ta aikeki ki kaiwa Mama yakuwa ko?".
Kafin Ameenatu tayi magana, Nana ta cab'e tace, "kin san dai wannan magana idan kuka yi ja-in-ja, su zasu cinye. Don haka kawai ki amsa laifinki!".
Su Hauwa'un suka dauki shewa, ita kuma ta turo baki gaba ta fada daki. Ko daga can dakin tana jiyo hayaniyarsu. Tayi murmushi a hankali ta fara duba kibiya.
Ta san su da Nana duk gaskiya suke fada. Bata cika son yawace-yawace barkatai ba, musamman na gidajen kawaye.
Ta gwammace ta yini a gida abinta tana ayyukan da ba'a rasawa a cikin gidan, akan dai tayi ta yawo a cikin unguwa. Don ma wai kawayen nata sun san halinta sarai, shi yasa suke daga mata kafa. Amma sauran kawayen nata da basu samu damar fahimtarta yadda yakamata ba, basu mata wannan uzurin. Kullum cikin korafin bata ziyartarsu suke suma sun daina ziyararta tunda haka ne, da dai sauransu.
Itama sai tayi watsi dasu ta ajiye. Wadannan biyun su kadai, sun isheta. Kamar yadda tasan cewa itama ta ishesu.
Tana ganin kibiyar, ta hada da matajin kai ta fita. Kitson bai daukesu wani lokaci mai tsayi ba, Hauwa'u bata da yawan gashi, kuma ba wani tsayi ne dashi ba, sai shegen tauri. Kullum idan zata mata kitso sai ta mata korafin zai yanka mata hannu. Wani lokaci tauri da santsin shi kan sa yayi kaifi kamar reza.