Eight
Suna yin sallama dasu Hauwa'un a kofar gida inda tayi musu rakiya, ta juya cikin gida. Ruwa ta dauka a cikin bokiti ta fada bandaki ta yi wanka, daga can bandakin ta dauro alwala, kafin ta fito ta shirya zuwa makaranta.
Ta dauki iyaka littafan da take yi na ranar kawai, ta dauki ilokarta ta fito ta yiwa Nana sallama. Kamar kullum, sai da ta zaro naira ashirin ta bata kamar yadda ta saba, ba karamin dabi suka sha da ita ba kafin ta fara karbar kudinnan.
Ita kadai ta dauki hanyar makaranta ranar. A ranakun alhamis da juma'a, akwai wasu littafai na musamman da ake yi da kuma harda. A kowane aji na matan aure da yanmata, akan ciro mutane daya ko biyu, wadanda suke da bukatar koyarwa, domin a horar dasu.
Lokacin da Malam Hadi yayi mata zancen, kamar a mafarki haka taji maganar. Saboda ba'a taba daukar yan ajinsu ba, duk kuwa da cewa akwai wadanda suke yawan yiwa malaman naci. Hakan ya dan janyo mata bakin jini ba kadan ba a cikin ajin. Amma da ta kawar da kai, ta kuma rufe ido, gashi nan komi ya zama kamar tarihi.
Tana zuwa makarantar suka hau karatu. Tun kafin ta karasa aji ake tambayarta tayi iloka? Tace ehh. Nan aka fara saye, babu babba babu yaro. Da yake makarantar akwai yara yan tahfeez. Kafin su tashi daga karatu ta kare tas!.
Bayan anyi addu'ar tashi, Malam Hadi ya kirata gefe yana kara yi mata tambayoyi akan ko tana da wata matsala game da karatun da suka yi ranar.
Daga gefen idanunta ta hangi matarshi, Malama Rahane, itama Malama ce a makarantar wadda take koyawa a bangaren yara, jingine da bango nesa dasu kadan. Nisan da idan ta kasa kunnenta sosai, zata iya jiyo kalar hirar da suke tattaunawa akai.
Ba tun ranar ta kula da matar ba. Kodayake, bata ganin laifinta sam. Ita a karan kanta, bata ga dalilin da yasa Malam Hadi din yake da ra'ayin ya zameta ita daya kwal, yana mata k'arin karatu ko wayar mata da kai akan wata matsala ba. Amma kuma ta rasa ta hanyar daya kamata ta dauko mishi maganar. Tunda bai taba yunkurin yi mata wata magana wadda bata danganci karatu ba. Ko kuma ya aikata wani aiki a gareta wanda bai dace ba. Don haka bata da hujja.
Bata da matsala da matar shi, suna mutunci a tsakaninsu. Idan sun hadu za su gaisa, sannan idan wani abu na farin ciki ko na bakinciki ya samu daya daga cikinsu, zasu taya juna murna, su kuma jajantawa junansu. Shi yasa take takatsantsan, walking on eggshells around him, don bata son abinda zai bata dan zumuncin da yake tsakaninsu da ita.
Sai dai daga kallo da hararar da take yawan jefa mata, ta yau ta fi ta jiya, bata tunanin za'a dauki lokaci mai tsayi kafin su yi hannun riga da ita, kowa yayi nashi gu.
Malam Hadi ya kalleta cike da kulawa, yace "Malama Ameenatu lafiya kuwa? Yau kamar wani abu yana damunki. Wani abu ya faru ne?".
Bata san cewa ta dauke hankalinta daga kanshi kacokam ta mayar kan matarshi da ta coge a gefe tana harare-harare da kumbure-kumburen babu gaira babu dalili ba, sai data ji sautin muryarshi sannan ta ankara.
Tayi gaggawar maida kallon gareshi tana girgiza kai, "a'ah, Ko kadan. Wani abu?".
Yace "na kula ko a cikin aji yau kamar hankalinki baya jikinki don baki wani maida hankali. Idan wani abu ne yake damunki, ki fada mana. Kin san fa hausawa sun ce wai barin kashi a ciki baya maganin yunwa. Ko ban iya tabuka komi a kai ba, ai zan iya yi miki addu'ah ko?".
Tace "Malam babu komi. Kawai... Yayata ce zata yi aure a Katsina nan da sati biyu, ina tunanin yadda zan bar karatuna ne in tafi can, shine kawai".
Yayi murmushi yana girgiza kai a hankali, "banda abinki Ameenatu, menene a ciki? Bayan muma din gab muke da tafiya hutun azumi? Sai dai saboda wa'azuka da ake yi, su kuma ai naga a ko'ina ana yin su ko?".
Tana so tace mishi amma bai kai na makarantarsu ba, amma sai kawai ta basar ta buge da gyada kai. Tasan idan tace haka wata sabuwar hirar ce za'a tado, ita kuma ba wata doguwar hira take son yi ba duba da yadda matarshi ta coge musu a gefe ta ki gaba ta ki baya. Bayan haka ita fa ta gaji, gida kawai take so ta koma.
Ya kula da hakan shima da alama, yace "kada in tsayar dake Ameenatu. Ki wuce gida sai Allah ya kaimu gobe".
Bata ce komi ba sai, "Allah Ya kaimu", da "sai da safe", da ta kara.
Ta gaban Malama Rahane ta wuce, tace "malama sai Allah ya kaimu, a gaida gida".
Ta kakaro murmushi da ya tsaya a iyaka fatar bakinta tace, "to, Allah Ya kaimu lafiya!".
Ameenatu bata tsaya damuwa da hakan ba, ta karawa bujenta iska. A ranta tana mitar koma dai meye zai je yazo, ba ita ta nemi Malam Hadi da kanta ba. Bata taba nemanshi ba, bata kuma taba nuna bukatar ya koya mata karatu ita kadai ba. Don haka, Ko me zai je yazo, tsakaninsu. Ita kam, babu ruwanta!.
Da dare ta hade kan yan kudinta, ta cire ribar da ta samu ta mikawa Nana ta ajiye mata kamar yadda ta saba. Uwar kudin kuma ta killace su, washegari zata kara sayo madara tayi iloka. Nana ta karbi kudin ta yi musu wajen ajiya. Ta juya ta kalli Ameenatun a nutse, tasan cewa maganar da za ta fada mata ba lallai ta faranta ranta ba. Ta ambaci sunanta.
A nutse ta daga kai ta maida kallonta gareta tare da amsawa.
Nana tace "kinga biki yana ta matsowa, amma ban ga kina shirin tafiya ba, bayan kin san cewa Hajja tana can tana jiranki, kinsan cewa fa ita kadai ce a gidannan yanzu. Kuma kinga ga ayyuka a gabanta".
Take yar fara'ar fuskarta ta kau daga kan fuskarta, ta cuno baki gaba, "to ni dama nace ba zan je bane ba?".
Ta daga hannuwa biyu tana girgizawa, "ko kadan, ban ce haka ba. Naga lokaci yana ta tafiya ne, amma baki shirin tafiya. Dazu ma sai da Hajja ta kira tace zuwa ranar litinin fa take son fara aiki, amma ke shiru. Gashi Huwaila ta riga ta tafi Batsari sai an fara biki sannan ta dawo. Idan baki je kin tayata aiki ba, wa zai taya ta ne, iye mai babban suna?".
Gabadaya ta ji ranta ya dagule, duk wani abu da zai sabbaba mata zuwa Katsina ta yi yini daya ba son shi take yi ba, balle ya kaita ga kwana ko kwanaki. Ta turbune fuska, idan da ba don dare ba, da kuma rashin wadataccen haske, da zata iya ganin jan da kumatunta suka yi saboda yadda gudun zuciyarta ya canza, da yadda ranta ya baci a take.
Tace "to, naji. Ai zan je din, ni wallahi Allah babu wanda ya kai Hajja iya takura mutum a duk fadin duniyar nan. Tunda nace zan je, ba sai a barni haka nan ba, ko kuwa nace na fasa zuwa ne?".
Nana ta dafa kafadarta tana dan murzawa a hankali, tace "to ya zaki yi? Hajja dolenki ce, kuma kinsan baki da wadda ta fita. Daurewa zaki yi, ki tallafi yar tsohuwa, kije ko don ki debe mata kewa".
Tana so tace ita dai Hajja ba dolenta bace, Nana ce. Sai ta kame bakinta bata ce komi ba. Saboda tasan cewa sunyi irin wadannan maganganu sun fi sau shurin masaki, amma hakan bai taba haifar mata da da mai ido ba. Lakca ce zata fara mata wadda bata da ranar karewa. Sai kai kawai data gyada mata, tace "zan fara shirin tafiya gobe, shikenan?".
Nana ta saki murmushi a hankali, "haka nake son ji, Aminatuwa ta babbar budurwa. Allah Ya bar min ke, Ya baki miji nagari da 'Ya'ya masu albarka wadanda zasu jikanki, su kuma yi miki biyayya!".
Ta sadda kanta kasa, sai kunya ta rufeta. Ire-iren wadannan addu'o'i da take yi mata, kan sanya mata farinciki a cikin ranta, su kuma sanya ta jin kunyar Nanar matuka, kamar kasa ta tsage ta nutse a ciki.
Allah Ya taimaketa Malam Habu yayi sallama a dai-dai lokacin ya shigo cikin gidan. Da sauri ta tashi tana mishi sannu da zuwa. Tabarmar shi ta kaba ta dauko ta shimfida mishi ya zauna. Ta koma ta jido kayan abincinshi da aka shirya akan babban tire ta kai gabanshi ta ajiye.
Waje ta basu domin su dan tattauna, ta koma can kuryar daki. Shirin kwanciya barci tayi, ta zauna a gefen gado. Fitilar data kunna baturanta sun fara cinyewa, don haka hasken dakin dusasshe ne, ga sauro da yake bin sassan jikinta yana ciza tun karfinshi. Ga shi ta tsani kwanciya cikin gidan sauro.
Hijabi ta dauka ta dora akan kayan jikinta, ta daga jakar makarantarta ta dauki naira ashirin, ta fita.
Malam Habu da Nana suna zaune a tsakar gida har yanzu. Shi yana kishingide yana sauraron labaran duniya ta cikin radio dinshi, ita kuma Nana na nata yan abubuwan. Duk suka bita da kallo.
Malam Habu yace, "ina zuwa ke kuwa da wannan dare?".
Tace "maganin sauro na manta ban siya ba, shine zan je in sayo".
Malam Habu ya duba agogon dake daure a hannunshi, "karfe tara saura yanzu. Kinga, bari in leka nan tiredar Dantala in sayo yanzu".
Tace "Baba da kayi zamanka ka huta ai, nan ne fa babu nisa".
Yace "Haba dai, da wannan dare? A wannan zamani kuma da muke ciki, kina d'iya mace?". Ya tashi ya sanya takalminshi ya fita.
Tana nan zaune ita da Nana suna tattaunawa akan labarin wata mata da ta bata shekara da shekaru ana nemanta, aka tsintota a can kasar Sudan, tana safarar yara kanana can, ashe tserewa tayi ba sace ta aka yi ba, har Malam Habu din ya dawo da ledar maganin sauron, ya mika mata.
Suka cigaba da yin hirar tana bare maganin sauron har ta bare duka, ta kunna ta kai duka dakunan, sannan ta nemi makwanci.
Sai dai juyin duniya, barci ya ki ziyartar idanunta. Dole ta mike ta lalubo jakarta ta dauki littafin 'Khulasa' tana dubawa. Bata san lokacin da barci yayi awon gaba da ita ba.
••●•●••
Washegari ta fara shirin tafiya kamar yadda tace. Tun da safe ta fito da duk wasu kayanta na sawa da suka yi datti ta wanke su tas. Da yamma bayan ta dawo daga makaranta ta amso dutsen guga gidan su Hauwa'u, da yake an kai wutar lantarki, ta goge su gabadaya. Har bayan isha'i tana aikin guga kuwa.
Sai data gama ne sannan ta fara hada kayan tafiya, wadanda ba zata tafi dasu ba kuma ta maida su cikin kayanta wadanda suke ta tashin kamshi. Mace ce ita mai son tsafta da kamshi. Kullum zaka sameta jiki a kyalkyale, yana kuma tashin kamshi mai dadi.
Wata mutuniyar Maiduguri, Yana, da ta taba zama anan makotansu, ita ta koya mata yadda ake hada humrori da turarukan kaya da na jiki masu kamshi mai armashi. Da kanta take hada yan kudadenta ta sayo kayan ta hada, babu ruwanta da na kanti sai idan ta kama dole.
Da har na kudi take yi ta saida, sai dai da yake yanzu mutanenmu sun fi gane harkar bashi a sana'a, bata je ko'ina da sana'ar ba ta watsar saboda masu karbar bashi su kuma hanata kudin.
Idan ta samu dai tayi, ta kan daukarwa su Hauwa'u har ma da Nana. Kwanakine ma ta fara karbar na amare tana yi, akwai kuma wata mata yar uwar su Hauwa'u, a Kano take, tana saida kayan kamshi, itama idan taje Dutsinma takan kai mata ta mata wadanda zata kai can Kano ta saida.
A takaice ranar sai wajen karfe goma da rabi na dare sannan ta kwanta barci.
Washegari tayi duk abubuwan da ta saba yi da safe. Zuwa lokacin da su Hauwa'u suka biyo mata makaranta, ta shirya tsaf, jaka kawai ta dauka suka tafi.
Tun a ranar ta fadawa malamansu cewa zata yi tafiya.
Bayan an tashe su har sun fita daga gate din makaranta, ta ji ana ambatar sunanta daga bayansu. Duk suka juya. Nan suka ci karo da Malam Hadi.
Ta juya ta kallesu kamar mai neman izini. Basariyya tayi kamar bata san abinda take nufi ba, Hauwa'u kuwa har kara turata zuwa wajen Malam din take yi.
Ta taka a hankali, cike da natsuwa ta nufe shi. Sallama ta fara yi mishi, ya amsa. Yace "ai nayi tunanin tafiyar taki sai nan da zuwa alhamis haka ko juma'ah".
Tace "an samu wasu canje-canje ne shi yasa".
Ya gyada kai a nutse, yace "haka ne. Shi dama abinda Allah Ya tsara, babu makawa sai ya faru. Gashi idan kika tafi ba zan samu hanyar tuntubarki ko ji daga gareki ba har sai an dawo hutun sallah idan Allah Ya mana tsawon rai. Da ace ni wani dan gata ne, ai da kin taimako min da lambar wayarki, koda gaisawa ce kinga ai sai mu dinga yi lokaci zuwa lokaci ko?".
Bata san lokacin data murmusa ba saboda dariyar da maganganunshi suka bata. Tace "Malam ai bani da waya".
Yace "baki da waya ko kuma dai wayarki ta samu matsala?".
Ta girgiza kai tana dan murmushi, "sam bani da waya. Ban taba rike waya ba ni ai".
Yadda ya kama baki cike da tu'ajjibi ne yasa ta dan saki dariya ba don ta shirya ba. Ire-iren reactions da take fuskanta kenan idan ta fadawa mutane bata taba rike waya ba. Ita kuwa a ganinta, hakan ba wani abun tayar da jijiyoyin wuya bane. Menene a ciki? Ita fa wayar ba wani burgeta take yi ba. Bugu da kari kuma, bata da mutanen da zata dinga kira. Hajja da mahaifiyarta duk lokacin da suka so kira, zasu kira ta wayar Malam Habu a gaisa. Haka itama idan taso kiransu zata karbi wayarshi ta kira su gaisa din. To ba shikenan ba?.
Malam Hadi ya langabe kai gefe guda, yace "to ki bani lambar wani a can mana sai in dinga kira? Ki taimakawa dan bawan Allahn nan kinji?".
Ta daga kai da niyar bashi amsa, sai idanuwanta biyu karaf cikin na Malama Rahane da yau ma ta coge a can gefe tana jefa musu harara. Da sauri ta kawar da kanta kamar bata ganta ba.
Tace "gaskiya ko akwai ma, ni ban rike lambar kowa a kaina ba". Bata tunanin yadda ta rike lambar wayar Hajja ta rike registration number dinta.
Yace "to bari in baki tawa mana? In yaso ko da flashing ne sai kiyi min ni kuma in kira, ko ya kika ce?".
Ta juya ta kallo su Hauwa'u dake can gefensu, kafin ta juya ta kalleshi, Bayan ta saci kallon inda matarshi take. Tace "me zai hana gobe idan Allah Ya kaimu da safe in karba? Kaga yanzu ana jirana".
Ya shafa gefen wuyanshi yana dan murmushi, "haka ne Malama Ameenatu, to shikenan. Allah ya kaimu goben. Ki gaida gida". Suka yi bankwana.
A hanya su Hauwa'u suka yi ta mata shakiyanci da jan baki, tayi banza ta kyale su.
Washegari data je makaranta bata bari sun hadu da Malam Hadi ba har aka tashi. Da yamma Malam Habu ya dauketa a bayan mashin dinshi ya kaita tashar mota da kanshi. Sai da yaga tashin motarsu sannan ya juya zuwa gida.